Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   6 / 28

15K to 18K   out of 83.6K words

yi da ?yar sukai sallama ta ajjiye wayar ta zaro kayan ciye_ciyenta taci ta sha shayi tabi lafiyar gado.
Washegari da misalin goman Safe ?annenta suka kawo mata su Faty a lokacin tana kan haWama Ramatu kayan wanke wanke.
"Ga kwanukannan in kin gama ki Wan kife mun a kwando, wannan wajen ki Wan share mun shima, da dai abinda kika ga ya dace. Ku kuma mujenku"
Tsaki tayi ta shige ciki, Ramatu ta Wauki bawon wanke_wanken tana mamakin dalilin da yasa bata iya musu da ?ar Shuwa duk da tana jin zafin abinda take yi mata a ?asan zuchiyarta amman bata iya faWa mata.
"Anty Mama ce dama tace in akwai kuWi a hannunki ki bata ko dubu biyar ce bata jin daWine take son zuwa asibiti"
?ar Shuwa ta taSe baki tace.
"Ku kenan tambayar kuWi dai. Ita Mama madadin ta ji?a ararraSi tasha. To na dai ji in zaku tafi zan baku. Yauwa Binta cefanen miya zaku yi mun tunda gaku kunzo saima ku taya ni muyi miyar tare."
KuWi ta zaro ta basu suka nufi cefane ita kuma ta nufi tsakar gida tana son shiga Wakin Jami ?awarta ta ?ut da ?ut.
Fitowa tayi tana tafe WaiWaya ji take yi tafi uban kowa. Ashe tsautsayin za'ayine ya fitar da'ita tana fitowa ta tarar a tsakar gidan anata caccakarta akan aikinta da Ramatu take yi mata a ko da yaushe ga ?aramin ciki du su biyun suke laulayin a tare.
Sumy da bata san ?ar shuwa ta fito ba tace
"Uhm asiri tayi mata fa. Wallahi ina ganinta har a ?ofar Wakina ta barbaWamun. Yarinya bata sanni bane wallahi shi yasa take wasa da wuta. "
"Ai dole kice asiri nayi mata sabida yarenku basu yadda da Allah Waya ba. Munafuka nan kin fito ne kuka dasa gulmata ko? "
Sumy ta dubeta tana wanke tukunya ta mi?e da tukunyarta a hannu ?ar shuwa batai aune ba Sumy ta gabWa mata tukunyarnan take goshin ya fashe.
Dambe ne na Allah tsine uwar mai ?arya ya kaure tsakankaninsu Sumy ta fita ?arfi da girma da ?yar aka raba wannan faWan Jami ta tura ?ar shuwa Wakinta dake sun fi kusa.
Babangida da yayi mantuwar fefofin gwaji ( test) na Walibai ya dawo Wauka ya tarar gidan a cike ana dambarwar tsiya ga ?ar shuwa jini ya wanke mata fuska amman dan masifa a guje ta fito ta sake dirarma Sumy.
Sum_ sum_ sum ya wuce ciki yana jin tamkar ya haWiye zuchiyarshi ya mutu duk a huta.
Ihu ne yaji ya kaure a tsakar gidan ana ambaton.
"Jini ya Webeta ta suma"
Ledar naman daya Wauka yana kallo ya saki ya fita.
Ranga_ ranga Babangida ya Wauki ?ar shuwa zuwa asibiti yana jin kamar zai yi hauka. Kiran makaranta yayi yake sanar musu halin da yake ciki ba lallai ya dawo makaranta ba ?ila sai zuwa gobe dai. Dan hatta shima da za'a aunashi gado tsab za'a bashi ?ila harda ?arin ruwa koma jini gabaki Waya baya jin daWin duniyar baki Waya.
Dr daya fito daga Wakin da ?ar shuwa take ne ya katse mishi zaren tunanin shi ta hanyar cewa.
"Ka Sameni a office ya Sheik. "
A baya ya bishi tin_ tin_ tin har zuwa office ya nemi waje ya zauna.
"Babu wata matsala mai girma gaskiya zama ku iya tafiya gida yau da zaran ta tashi a baccin da take yi. Abinda ke cikinta kuma yana lafiya babu wata matsala.
Godiya kawai yaima Dr
Ya je ya biya kuWin magunguna da komai da komai ya tusata gaba kawai yana kallonta da goshi kumbure yana ta ?issima abubuwa da dama a ranshi.
Daya tuno da chus sai yayi murmushi ya zaro wayarshi ya shiga ma'ajiyar hotunanta dan ya kalla yaji sanyi hotunan Sabuwa sune abincin zuchiyarshi dama idanunshi.


ALHAJI ZAIDU:.
Yana kwance a Wakin hotel fitowarshi wanka kenan shine ya samu ya kwanta dan bala'in zazzaSi yake ji tun lokacin da matar Khalid ta cakumi Sabuwa ta soma feso maganganu marasa daraja da duk ma dai abinda ya faffaru masu tarin muni a gabanshi.
Idanunshi ya lumshe yana hango fuskar Sabuwa da kuma irin sanyin halinta da irin muguwar kunyar da aka sakata a ciki, da irin yadda yaga ta muzanta.
Amman babban abinda shine yafi komai jan hankalinshi cutar damuwar dake damunta
Matarshi tayi cutar damuwa wanda sun sha wahala bata wasa ba. Da farko ma an Wauka jinnu ne la'akari da irin abubbuwan da take yi. Irin su ihu, fisgewa a guje, keSewa a Waki, rashin son ganin haske, da kuka, da rashin bacci.
(To a daidai wannan gaSar ga tsokacina ?an uwa. Akwai mata da yawa da suke fama da cutar damuwa ake ta Wirka musu magungunan hausa, wata ma aita mata ru?iya ana labtarta a tunanin makusantanta cutar jinnu ke damunta. An Wauketa an aita wajen masu bada magani na bogi daya kalleta sai yace aljanu sunfi Wari bisanta alhalin ?aryane cutar damuwa ke damunta.
Shawarata anan dan Allah duk macen data shiga Waya daga cikin waWannan halamomin dana lissafo asibiti shine inda ya dace a soma kaita aba masana dama su gabatar da aikinsu. Ubangiji Allah kasa mu dace ameen? )
Sai daga baya da cutar tayi tsananin da ta soma raunata kanta ne aka kwasheta zuwa Asibiti. Da farko Alhaji Zaidu asibiti yaso a kaita danginta da danginshi suka haWu suka danneshi cewar cutar bata asibiti bace saida ruwa ya ?arema Wan kada kana aka dangana wajen likitoci suka tabbatar musu cutar damuwace. Ta Wauki damuwar duniya akan rashin haihuwa ta Waurama kanta, duk inda taji mai magani saita je ta karSo musu sunzo sunyi ta Wibga da dai taga abun yaci turane girma nata tunkarota har ta kusa isa ?adamin mainofos aimun afuwa ban iya turanci ba ( khadija maidoki=?? zo ki gyara musu) shine wannan cutar ta damuwa taci gabala a kanta. Amman yanzu ta warke sai dai fa abun yana zuwa mata tamkar zuwan iska
Ajjiyar zuchiya ya sauke yana tunanin irin gidan da ?addara ta zana mishi ya auri ?ar gidan. A zahiri tausayinsu shine abu na biyu daya jashi wajen auren Sabuwa.
Na farkon shine ya jarabtu da matsananciyar ?aunarta wanda abun har mamaki yake bashi irin yadda lokaci guda zuchiyarshi ta jarabtu. Fatanshi Allah yasa ya zamema wannan zuriyar wani matattakalar da zasu gyara Wabi'unsu yayi imani a Wan zamanshi da Sabuwa da Uzairu zuchiyata yasan sun bambamta da ragowar ?an gidansu ?addararsuce a haka basu da tsimi bare dabarar sauya ma kansu ?addara. Kuma ya lura harda laifi al'ummar da suke rayuwa a cikinta.
Ajjiyar zuchuya ya kuma saukewa tare da fesar da iska..
Tunaninshi ya sauka izuwa kan uwargidanshi kuma baisan yadda zata Wauki lamarin ba, da sau?i ko akasinshi oho. A baya dai bata fiye Waga hankalinta ba, amman a yanzu da yake ganin kamar ?ara ninka mata sonshi akeyi sai yake ganin kamar ba zata ji daWi ba.
Kiran wayarta ce ta katse wannan tarawa da Webewar.
Yana kara wayar a kunne sai yaji ta sauke ajjiyar zuchiya. Tausayinta ya tsirga mishi sosai.
"Alhaji dare yana ta yi, ni banji kace mun ka taso ba bare kace mun ko gaka a kano da dai makamancin hakan? "
Ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya saki murya ya ware..
"Ai dawowar dai bari muga mai gobe zata haifar. Ni kin ganni a Wakin hotel ina kwance. Kiyi ha?uri ban kiraki ba har kece kika rigani kira. Kainane ya Wauki zafi sosai abubbuwane sukaimun yawa man kaina duk ya kwaranye"
Dariya tayi tace..
"To ko dai zance kaje ne Alhaji kafa faWamun gaskiya Alhaji. Naji kace dubiya zaka je ta wuni guda sai kuma ka Sige da bari aga abinda gobe zata haifar bafa tabbas a goben kenan? "
Dariya yayi sosai.
"Hajiya kenan ke baki da dama. Zanyi ?o?arin ganin ko jibi ne na dawo, inma na gama abinda nake yi gobe zaki ganni kwatsam"
"A_a banda kwatsam ka mance gobe Amaryar Yaya isiyaku zata tare zamu je ma Hajiya Baturiya dannar ?irji? "
Murmushi yayi yace.
"Zaku je dai gutsiri tsoma irin naku na mata da in bakui ba bakwa jin daWi. Dan Amaryar Isiyaku zata tare har sai kunje ma Baturiya dannan ?irji Baturiyan da yara biyu ta kai gidan miji."
Dariya suka yi yana dafe da kanshi da yake mishi ciwo.
"To ni kam Hajiya saina dawo asha dannar ?irji lafiya. Ko akwai wani abun da kike da bu?atane? "
"Eh to babu zance akwai kuWi a hannuna, masu hayar shaguna ma sun soma biyan kuWaWensu"
Murmushi yayi yace.
"Kice a Hajiyarki kike, to a siya mun wani abun a cikin kuWin. "
Dariya tayi tace.
"Da dai zaka ?aro aurene da akwati zan haWa ma amarya in fansheka."
Dariya yayi kawai sukai sallama ya kashe wayarshi ya fahimci zarginshi take yi da zuwa zance, shi yasa take ta soko zancan cikin raha.
Dole sai da dabara zai sanar mata batun auren ta sigar da hankalinta bazai tashi ba.
Tunane_tunanene cikin kanshi wanda da ?yar suka barshi ya runtsa. Mamaki yake yi wai daga ziyara sai Waurin aure matar ma na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
"Allah ya baki lafiya Shalelena Allah shine shaida wallahi ina sonki. Tarihinki bazai hana in soki ba"
Tuno fuskar maigogul da Cicib yasa saida ya saki murmushi ba tare da ya shiryama hakan ba. "


ASIBITI:.

Washegari bayan maigogul ya dawo daga masallaci yana zaune a kan kujera yana haWama Rakiya shayi nashi yana gefe ya gama haWawa.
"Wai ni maigogul kace wai Cicib Labbai yake so matarshi ta rage wannan kishin nata ne?
Afa duba jibi Adama a gida a ?one kada fa a kuma matar da ta rabkama kishiya muciya. Yanzu da ba dan kun shiga kun fita ba Allah kaWai yasan shekaru nawa zata yi a gidan yari"
Shayi mai kauri ya mi?a mata ya yaga mata biredi mai kwakwa mai musulmin daWi.
Saida ya ci biredi ya kurSi shayi kafin yace.
"Rakiya hoo to ita labbai kanwar lasace, ko kuwa tayar baya ce irin wacce aka rabka mata muciyar?
In sun daidaita da Labbai ba shikenan ba dafa su zamu yi mu sha romon?
In ta yi mata itama ta yi mata, su kashe junansu ba shikenan bane?
Ai gara taje ta zauna koma yayane.
Ke dai ki godema Allah yara uku a tsukuku guda ace suyi aure ai ba'a taSa haka a wannan gidan ba.
Kina ganin yaran Hauwa babu ma mai shinshinarsu. Layuza ce ma naga yaron wajen malam Habu tsohon mijin Labbai yana Wan le?owa wajenta.
To malam Habu in sama da ?asa zata haWe kinsan bazai yadda ba. Gaba yake yi mun tunda dai abinda Gaza yayi ya yanke mai tumakai.
Ni ina mamakin inga ana ri?o, ko fishi sai inta mamaki. Rakiya ashe wai damuwa ciwo ce? Allah sarkin girma inji kishiyar mai mazaunai.
Harararshi Rakiya tayi tace.
"Haka fa"
Dariya yayi yace.
"Kada ki kawo rikici cikin hirarmu wannan Alhaji da Allah ya kashe ya mallakama lolo Rakiya ai damu da talauci kakarmu ta yanke sa?a. Yana daga cikin sanannun mutane a Kano, gaskiya yana da kuWi mazajen kuWi fa ba irin na wancan mitsiyacin Babangida ba mai gorin tsiya akan abinci. Familinsu sanannune kuma ?osassu da ilimin addini."
Rakiya ta washe bakinta tace.
"Wa ka gane mun gidan da lolo zata tare.
Kai nayi farin ciki ma?iyanta sun faWi tim ?asa babu nauyi.
Wannan abu yayi mun. "
Hauwa ce ta shigo ita da Layuza da Aliya
Sai ?arema Wakin da ledojin gaban maigogul kallo suke yi.
Rakiya kuwa kanta ta juya ko kallo basu isheta ba.
Hauwa tace.
"Naji wani yashasshen labari a bakin su Labbai wai an Waura auren Lolo a gidan cicib dama Lolon tana da wanda suka daidaitane mu bamu da labari? "
Rakiya tayi dariya tace.
"Yafi ?arfin yashasshen zance. Kin ganta nan matar hamsha?in mai kuWi ce. ?arewarta ma a jirgi suka haWu"
Dariya da Rakiya da Maigogul suka fashe dashi wallahi harda tafawa
Wanda yayi daidai da buWe idon lolo"


SABUWA:.
A hankali na buWe idanuna ina ta jiyo maganganu a kaina da irin muryoyin dana kasa tantancewa.
Dishi _dishi na soma ganinsu.
Idanuna suka washe tanwar a kan fuskar maigogul sai murmushi yake yi mun.
Idanuna na runtse maganganun da matar Khalid ta yaSa mun suka shiga dawo mun
Da sauri na sake buWe idanuna domin in tantance a inda nake, ga kaina sai sarawa yake yi.
"Sannu Lolo maigogul kaje ka kirawo ma'aikatan jinya. Sannu lolo"
Cewar Rakiya kenan.
Kai kawai na Waga yanzune na gane akan gadon asibiti nake Rakiya na ri?e da hannayena har maigogul ya shigo shi da ma'aikacin jinya.
Ya fi minti uku yana mun tambayoyin yadda nake ji a jikina kafin ya dubi Maigogul yace.
"Tana bu?atar hutu sosai.
Sannan mutane sunyi yawa a Wakin ku bata sarari dan Allah kada a cika yawan magana a kanta kuma.
Yanzu abinda ya dace ta samu taci abinci zuwa anjima za'ayi mata allura Allah ya ?ara afuwa"
Ya saka kanshi ya fice.
" Matar manya sannu. Rakiya tasheta a hankali kinji? "
Maigogul yayi sauri ya tsugunna ya haWo mun shayi mai kauri ya saka mun cokali.
"Lolo zaki iya ri?e kofin ko in baki a baki dan Allah? ".
Hauwa da suka tashi zasu fita ta rabka salati maigogul ya juya a fusace.
" Wallahi kaji kunya kai kam maigogul tur da wannan mummunan ta'adar taka. Kuzo muje kada ba?in ciki ya kashe mu"
Fuu Hauwa ta fita su Layuza suka mara mata baya.
Kofin na karSa a hannunshi. Ina ta kallonsu Rakiya yadda suke ta tarairayata.
A hankali na soma shan shayin ina lumshe idanuna, bayan Maigogul ya tagazamun na tashi zaune na jingina da ?arfen gadon. A zuchiyata nace.
Bariki ba riba jibi abinda matar Khalid tayi mun a gaban Alhaji Zaidu. Hmm nasan har gaba da abada bazai sake waiwaye na ba. Yo ni ko ya waiwayeni bani da idanun kallonshi.
Ina cikin zancan zuchi naji Maigogul ya saka mun biredi a baki.
Kafin in tauna sai ga Gaza da Madamcy da kayan abinci.
"Ah lolo eh ashe kin farka? A lafiya dai Sabuwa mai sabon aiki. Eh ya jikin naki to? Su labbai duk tare muka tawo dasu eh suna waje wajensu eh Hauwa"
Jikin da sau?i Gaza nagode. Madamcy nagode" Na faWa a sanyaye dan kaina mugun sarawa yake yi
Ina ?arashe sh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an shayin na kwanta dan kaina saramun yake yi har ina ji kamar zai Salle. Ma'aikaciyar jinya Gaza ya kirawo tazo ta yi mun allura.
Tun ina iya ganin shigowar ?an Wakinmu da fitarsu har idanuna suka rufe
Bani na sake farkawa ba sai washegari da safe uwar lokacin da akaimun allurar jiya.
Alhaji Zaidu na gani a zaune shi kaWai a Wakin ya nannaWe hannayenshi a ?irjinshi yana ta aikin kallona. Idanuna na sake rufewa na buWe a karo na biyun ma dai na ganshi dan nayi tunanin ko kawalwainiyane.
"Sannu Shalele kin farka?"
Ya tambayeni cike da kulawa. Idanuna na lumshe hawaye suka soma zubo mun. Illahirin kunya tasa na kasa buWe idanuna nice harda kuka mai gunji"
"Ko menene ya sanya ki kuka ki tureshi gefe dan Allah. Ko dan Alhaji Baba da ya damu da lamarinki ki yi ha?uri. Sannan fa ki sani bake kika zana ?addararki ba Shalelena. Kuma Allah na iya kawo miki agaji ta ko wanne irin yanayin da zato bai zata ba. In nine bakya son gani zan fita yanzu"
Sama da ?asa Allah bai bani ikon na buWe idanuna ba har saida na soma juyo takun takalminshi ?was_ ?was kafin na buWe idanuna na dubi bayanshi wasu hawaye masu Wumi suka sake zubo mun.
Wallahi banji zan iya haWa idanu dashi bane ku fahimceni ku tuno irin cin mutuncin da cin zarafin da akayi mun a gabanshi.
"Ahh Alhaji Zaidu zaka tafi ne? "
Cewar Maigogul da suka ci karo.
"E Alhaji Baba zan koma Kano maiWakina itama munyi waya da'ita bata ji daWi ba shine zan koma.
Amman kafinnan inaso muyi magana"
Baki maigogul ya washe yace.
"To to Bismillah muje. Lolo ina zuwa Labbai zata shigo ta zauna dake"
Fita suka yi Labbai ta shigo ta zauna tayi tagumi.
Labbai wani abunne ya kuma faruwa ko. Naga Alhaji Zaidu bai tafi ba har yanzu"
Hannun da tayi tagumin ta sauke tace.
"Bari a kira ma'aikatan jinya su duba ki. Amman kafinnan ko akwai abinda kike da bu?ata? "
E inaso inyi fitsari, kuma bakina ma babu daWi"
"Taso in rakaki ai tun jiya naga Maigogul ya tawo miki da kaya harda man goge baki da asuwaki. "
Labbai ce ta taimaka mun nayi wanka da ruwa mai madaidaicin zafi sabida masu hawan jini ba'aso suna ta'amali da ruwan zafi sosai musamman a lokacin da ciwon nasu ya tashi.
Da nayo wanka na Wauro alwala, na sauya kaya sai naji har wata iska mai daWi nake sha?a.
Ina zaune a kan gado ina cin fatan dankalin turawa Dr ya shigo.
"Sabuwa yaya ?arfin jikin naki? "
Kallon labbai yayi yace.
"Ina fatan babu gishiri da yawaitan WanWano a cikin abincin ko? Kamar dai yadda akayi muku bayanin yanayin abincin da zata dinga ci"
Labbai tace.
"Babu gishiri, WanWanonma baya baya aka saka mata Dr"
"To shikenan in babu matsala inaso ki bani waje zamu yi magana da Sabuwa"
Mi?ewa Labbai tayi ta fice.
Kujera Dr ya jawo ya zauna yana fuskantata.
"Sabuwa"
Ya kirayi sunana murya da sau?i. Sama da ?asa Allah bai bani ikon amsawa ba kaina na ?asa kawai. Shima dai bai kira da tunanin in amsa ba.
"Shawara zan baki kyauta Sabuwa sabida yanayin jikinki da kuma yadda aka kawo mana ke ranga ranga.
Ita rayuwa Sabuwa Wan adam a duk yadda ya Wauketa yawanci haka take zuwa mishi. Na sani akwai waWanda al'amura suke zuwa musu akasin abinda suke tunani.
Mutum ya zama jarumi ma wani abune.
Ita damuwa abokiyar gaba ce. Daga lokacin da kaga abokin gabanka ai ?o?arinka ka sauke fara'a koda ta bogi ce a fuskarka dan gudun kada yaga ka gaza. Haka in ka samu ni'ima so kake ma?iyinka ya gani domin ya ji duniyarshi tayi mishi zafi.
Wannan ?aramin misali kenan akan damuwa da jarumta.
A lokacin da wani tashin hankali ya tunkaroka Allah zaka ambata shine garkuwa madogara. Wannan Allahn shi zai baki kariya kiji ki kan ?afafunki wata jarumta na bayyana tattare dake.
Damuwa dama kin

6 / 28