Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   19 / 28

54K to 57K   out of 83.6K words

kamani ganin yadda yake ?arema Hajiya kallo yana buWe ido yana mayar dasu ciki.
Hum zan yi sallah Hajiya naji kamar kiran Sallah akeyi ko? "
"Eh lokaci yayi akwai masallaci a gidannan su Alhaji Maigogul sai suje ke kuma bari Saude tazo saita kai ki Wakina kiyi sallah. Saude, saude"
"Na'am Hajiya"
Saude ta amsa da sauri sai gata ta iso.
"Ki kai wannan ?ar tawa Wakin baccina tayi Sallah. Shi Alhaji in ya dawo ki wuce dashi babban falo, wannan yaron nawa kuma ki buWe mishi Wakin Gaddafi a kai mishi abincinshi can"
Ni dai Saude nabi zuwa Wakin Hajiya.
Masha Allah"
Na furta a fili bayan fitan Saude Wakinne ya bani sha'awa sosai komai a killace gashi babu wani tarkace komai na ajjiye a muhallinshi.
BanWaki na faWa shima sai ?amshin turare yake yi, kai gaskiya Hajiya na ta'amali da turarukan wuta masu ?amshi da ri?e waje, ko wacce kusurwa ta gidan nata ?amshi take yi. ( ga dai dama na muku adashen gata kuma zaku samu damar cin kyautar da zanyi ma duk masu adashen ko da kunfi mutum Wari. Hajiya in fa ba adashen zaki yi ba kada ki shiga dan Allah)
Alwala na Wauro na tada sallah dan Saude ta shimfiWa mun dadduma a gabas.
Ita kanta daddumar da nai sujjada ?amshin turaren wuta take yi wallahi mai wani irin ?amshin daWi.
Ina sallamewa wayata ta shiga ruri. Murmushi nayi dana ga Alhaji zaidu ke kirana.
Dama ko bai kira ba na ?udurce a raina ina idar da Sallah zan kirashi in sanar mishi gani a Kano nasan zaiyi farin ciki sosai.
Amincin Allah ya tabbata a gareka kykkyawa. Ga kano naga yau ana ?walla rana ga zafi ko? "
Murmusawa yayi yace.
"Tabbas kin canka Shalelena. Kiyi ha?uri kin jini shuru ko? Aiyukane suka taso mun zuwa jibi ma ?asar zan bari gobe zaki ganni"
Sha kuruminka gani a kanon ni nazo ganin abun ?aunata kana ina inzo in sameka har inda kake? "
Sai da yayi dariya kana yace.
"Yanzu haka dai ina kamfanina na motoci dake mun shigo da motoci ana ta lissafe_ lissafe. Da gaske kin shigo Kano kuma me kika zo yi Uhm?"
Na shigo kano Maigogul muka rako ni da Uzairu zuchiyata kazo ka Waukeni inason ganin kamfanin motocinka ka zazzagaya dani inga ko'ina"
"To shikenan Shalelena ki turo adireshin unguwar da lambar gidan yanzu zan bar duk abinda nake yi inzo in Wakko matata ta kaina."
Sallama muka yi na ajjiye wayar sai ga Hajiya da Saude sun shigo. Abinci Saude ta ajjiyemun ta fita ita kuma Hajiya bakin madubinta ta nufa ta gyara hodar fuskarta ta Wakko wata humra a kwalba mai kyau ta shafe jikinta dashi ?amshin wannan humara ta karaWe ko'ina a Wakin. Kwalbarma ta musamman ce wallahi a ido kawai kaga humrar kasan duka Wauka ne
Kai Hajiya Balaraba a saudiyya, ko sudan kike siyan kayan ?amshine naji ?amshin humrarnan da turarukan wutan na musamman ne"
Dariya tayi ta zauna akan gado tace.
"Ai kuwa anan gida Najeriya nake siye a hannun Mrs Bukhari ?ar mutan Kanuri wannan marubuciyar littattafan hausan wacce sanadin littafinta na Shanono na santa. Bari kiga akwatin turarukan wutan dana siya a hannunta, amman anan kano hannun Anty Zee Agent Winta na karSo dake Worayi da zama dake ita a Lagos take Aure amman har Saudiyya tana tura kayanta, nijar, kamaru, Ghana duk tana tura kaya kuma cikin aminci"
Ai kuwa kwalin da turarukan suke ciki kaWai abun kallone, bare kwalaben uwa uba ?amshin turaren nata. Gashi turarenta saita zuba a leda ta silin Winshi sannan zata zura a cikin kwalba kamar dai kayan kamfani. Ga wasu irin humrori da turarukan wuta. Hajiya Balaraba tai ta sammun ina shafe jikina dashi, har humrar gashi da kulaccham ta gashi saida ta bani na shafa. Naita santi wallahi.
"To abunda za'ayi tunda nan da sati biyu zaki tare nayi miki al?awarin show Glass guda zan saka ta haWa miki daga nan sai Wakin mijinki in sha Allah. Wannan Winma ki tafi dasu ki soma amfani dasu kafin ki tare duk suturunki ki turaresu da turaren turara kaya dana fesawa yayin turarawa, wannan kinga na tsugunnone, wannan turaren turara jikine kullum ki dinga yi.
Kinga wannan ?ar kwalbar ita kuma humrar mata aurece da kike ganinta. ?awata ta jima tana bani labarin humrarnan da tasirin da take ma maza. ( masu son siyan WaiWai su tumtuSeni akwai kayana a Kano hannun Anty Zee dake ?orayi. Sannan akwai a hannun maman Inteesar kaduna)
"Kinga na bar Alhaji Maigogul yana cin abinci kema bari in barki haka.
To shikenan Hajiya nagode sosai nima Alhaji nake jira zai zo mu Wan fita kafin ku gama"
"To shikenan muma in ya gama zamu je wajen yayana dashi su gana mu ba yara bane Hajiya Sabuwa in za'ayi ayi kawai nan da sati Waya ma sai a Waura auren ai"
Fita tayi tana cike da farin ciki marar musaltuwa.
BuWe kular abincin nayi naga jallof Win soyayyar shinkafa wacce ta wadata da kayan lambu ga hanta baja baja Wayar kular kuma kazace soyayya ta cikin jajjagen attaruhu da albasa ga wani lafiyayyen kunun aya.
Zubawa nayi naci nayi ?at na kora da kunun Ayannan. Sai ga Alhaji ya kirani yana ?ofar gidan
Mi?ewa nayi na fita na tadda Saude a falo tana turaren wuta.
Saude dan Allah wajen Wan uwana zaki kaini zamu fita"
"To Hajiya muje in kaiki"
Kaini tayi Sarayin yaron Hajiya Uzairu zuchiyata harda cire riga yana ta Wura abinci babu wasa. Yayi WaiWai a kafet.
Taso muje ka rakamu zaga Kano ni da Alhaji Zaidu ko in barka kana kallo? "
"Wallahi Lolo prison break nake kallo an tsaya a daidai inda na tsaya na kalli season 1 a gidan abokina. Amman muje dai zamu dawo ai in sha Allah sai an auremu a gidannan zadai a yita da Rakiya dan bata da daWi sai dai fa mu duka muna bayan Maigogul wallahi nan gidan yafi dacewa dashi ita kanta tafi dacewa dashi su Rakiya yadda kika san su suka haifeshi fa.
Dariya muka yi ya wanko hannunshi ya shirya muka fita.
Alhaji Zaidu saina ganshi a wata ?aramar mota mai kyau ja sai she?i take yi.
Gaban motar na buWe na shiga, Uzairu zuchiyata ya shiga baya.
"Ashe gidan Hajiya Balaraba kuka zo ai dama kince itace ba sai kin sha wahalar turo adireshi ba tunda sananniyar ?ar siyasace sun sha gwagwarmayar siyasa ita da marigayin mijinta shi ai ya ri?e kujerar Wan majalisa ma. Suna da kirki da son talakawa sosai gata da yawan sadaka da yawan ziyartar asibiti da gidajen marayu da gidan gyaran hali"
Murmushi nayi tare da farin cikin jin Hajiya Balaraba mutuniyar kirki ce wala Allah Allah ya turo mana itane ta zama sababin shiriyar Maigogul, in Maigogul ya shiru magana ta ?are ni zanji da sauran.
Gaisawa muka yi baki Waya Alhaji Zaidu sai juyowa yake yi yana kallona ni dai ganin shirun yayi yawa sai nace.
Wannan ?aramar motar tayi kyau sosai "
"Kema mai sha'awar ?ananun motocinne? Motar Hajiya ce yau da tawa ta fita shine nima na Wakko tata na fito."
Kai kawai na jinjina Alhaji muna tafe yana nuna mana wajaje yana faWa mana sunayen wajajen har muka iso kamfanin motocinshi.
Ashe katafaren wajene mai Wauke da motoci masu yawa, ga sababbi tiya leda ga kuma kwatano tokumbo kenan, harda bus_bus dasu j5. Haka yaita zagayawa damu yana nunnuna mana wajaje.
"Kinga inda nake son in Wakko Gaza in bashi kulawa da wani Sangaren. Dan kinga kamar can Sangaren ?anin Hajiya ke ri?e dashi, to shi Gaza in so samu ne ma sai a dinga fita dashi kwatano suna shigo da motocin da sahalewar hukumar fasa ?wauri tunda naga jarumine kuma kinga tafiyar ta jajirtattuce"
Murnace ta lulluSeni har akan fuskata na kasa Soyewa. Haka ya shiga damu ofishinshi ?ato na alfarma muka zauna a kujera.
Shayi yasa sakatarenshi ya haWo mana ya kawo.
"Kunga yanayin wajen ko tare zamu dinga zaman ofishinne kina taimaka mun da lissafe_lissafe ko kema kinfi sha'awar buWe shago kina fita ?asashe saro kaya kamar dai Hajiya? Nayi nayi da'ita mu dinga aiki tare in bata wani Sangaren ta ri?e ta?i tafi son tabi tawagar ?awayenta zuwa ?asashe sare_saren kaya. Ko harkar fuloti nace mata mu dinga yi tare duk da sana'ace da maza suka fi yawa a cikinta in da matanma basu da yawa. Hajiya sai tai ta mun dariya sabida bata so. Alhaji Gali abokina tare suke ko wanne irin kasuwanci da matarshi kullum suna tare. To ni sai abun yake burgeni naita kwaWaitama Hajiya wallahi ta?i"
Murmushi nayi sai nake jin kamar ya haska mun wata hanya ne. Aiki tare dashi bazai hanani buWe shago ba ai sai nake ganin ai gara in zauna muyi aiki tare domin in samu gogewa tunda ni ba karatu nayi ba, kuma ba sabawa nayi da shiga cikin mutane inyi gwagwarmaya ba, bani da wayewar juya kuWi, da wayewar mu'amala, aiki dashi zai fi mun sau?i sosai zai buWe mun ?wa?walwata kafin in samu ilimin"
Ai ni kuwa tare da kai zanyi aiki duk inda ka kutsa nima zan kutsa"
Dariya yayi ya juya a kujera yace.
"Allah yasa zaki iya tafiye_tafiyen da yawa Shalele uhm. Yanzu kinga wannan tafiyar China zamu je babu shiri ko zaki zo muje tare ne?"
A_a gara kaje kai kaWai ni kuma inci gaba da shirye_shiryen tarewa. Amman daga wannan tafiyar babu inda zaka dinga zuwa sai tare dani"
Dariya yayi yace.
"Uzairu zuchiyata ka zama shaida tunda tace zata yi aiki dani to dole ta bini ko ina sai ki zama mai bada shawarana ko uhm? "
Ya ?arashe yana kallona ta gogul Win dake ma?ale a idanunshi. Uzairu zuchiyata yace.
"Ai zata ma yi ba sai kace dole ba. Wannan kasuwanci aina gata ne. Fita ?asashe ai wayewace da buWewar kai Alhaji"
Kunji fa mutuminku
Mun jima sosai a ofishinnan har suka je sallar la'asar suka dawo nima a nan nayi sallata zuchiyata fes da farin ciki. Sai wajajen ?arfe biyar Maigogul ya doshi kiranmu.
Kwatance Alhaji Zaidu yayi mishi na kamfanin sai gasu shi da Hajiya itama a tata motar da dukkan halamu daga nan sai Dutse.
An zazzagaya da Maigogul ko ina dako ina a kamfanin ya gani.
"Alhaji nima na faWa maka da nayi saida motoci har kwatano nake zuwa, yanzunma wani sa'in nakan taSa harkar dake kasan harkar kawalci baya barin mutum da lokacinshi amman yanzu dana dena anya ba nan zan dawo da aiki ba kuwa"
Kunya kamar ?asa ta buWe in shige tsabar kunya. Hajiya Balaraba tana daga gefe tana ta waye_ waye.
"Ai yanzu girma ya kamaka Alhaji Baba sai dai wani aikin ba wannan ba. Zamu tattauna da Shalele muga me ya kamata a maka amman banda harkar tafiye tafiye ai bazan so kasha wahala ba.
Ai sai yayi dariya yace.
" Har kwatano da ina kawalci ni da babu.... "
"Haba Dad dan Allah tunda ka dena wannan kawalcin bai kamata ka dinga maganar ba. Alhaji Zaidu sirikinka ne fa"
Cewar Uzairu zuchiyata wanda ranshi ya riga daya gama Saci niko idanuna sun kaWa sunyi jawur dasu.
"To to hakane kuyi ha?uri ba zan sake ba. Alhaji aita ha?uri dani zan gyara"
Sai tausayinshi ya Warsu a zuchiyata sosai Alhaji Zaidu kuwa ya iya tafiyar da Maigogul sosai da sosai.
Anan Hajiya Balaraba ta saka mun akwatin turaren Mrs bukhari a mota tayi mana sallama ta tafi sabida ana jiranta
Uzairu zuchiyata da Maigogul suna cikin mota ni kuma na tafi Wakko jakata a office.
Ina shiga na saki kuka mai tsuma zuchiyar mai saurare. Juyowa nayi sai kawai na jini ?am a ?irjin Alhaji Zaidu yana ta shafar bayana da sigar rartashi.
" Sai ?amshi kike fitarwa mai daWi Shalelena har kanki ?amshi yake yi uhm.
Shalele bana son kuka. Sannan kada a sake tsinka Alhaji Baba in yana magana baki ji tausayin daya bani ba. Ni Wanshi ne ba laifi bane dan yayi magana ko wacce irine dani. Haba shalele uhm menene to na kukan share hawayen kada ki sake kuka kina dani, Alhaji Baba nawa ne fa."
?agoni yayi ya shiga share mun hawayen da yatsunshi yana ta murmushi.
Nima murmushin nayi na dubeshi da kyau nace..
Dama kasan sana'ar Maigogul ne? "
Kai ya gyaWa mun yace..
"Na sani ya faWa mun da bakinshi tun kafin muyi aure dake, kuma nima na bincika Shalelena"
Amman a hakan kaji kana so in zama matarka shin baka ji.... "
Bakinmu ya manne waje guda dole nayi shiru na lumshe idanuna wasu hawaye masu Wumi suka gangaro mun. Mun jima a wani yanayi kafin ya zare bakinshi ya tallafo fuskata da hannunshi biyu yana kallon tsakiyar idanuna yace.
"Ki dena dawo da hannun agogo baya Shalelena
Shi abu inya wuce ba'ason dawo dashi baya musamman abinda ba kyau bane dashi, abunda bashi da kyau rurrufewa akeyi fa. Abu mai kyauma ba ko wanne ake buWewa ba.
Ni dai ina sonki a duk yadda gidanku yake uhm.
Yau ?amshinki yayi mun daWi fiye dana ko yaushe tun a mota ?amshi yake ta sauke mun kasala, shi yasa kika ga duk na susuce uhm"
Bakinshi ya kuma mayarwa cikin nawa.
Mun jima a tsaye a haka da ?yar muka rabu amman saida ya sakani na mance duk wani Sacin rai ya sake jaddadamun yana fa ?aunata fiye da tunani.
Fitowa yayi suka yi sallama da Maigogul muka Wauki hanya sai wajen goman dare muka shiga gida.
Haka abubbuwa sukaita shurawa kamar da wasa ranar Juma'a aka Waura Auren Maigogul da Hajiya Balaraba sadaki dubu Wari amman ba wannan gidan da muka je zasu zauna ba tace tana da sabon gida data gina wannan gidan da muka je gidane da suka rayu da mijinta da ?a?anta maza uku.
Sai da daddare Maigogul da Cicib suka shigo ashe a ranar aka Waura Aurenshi da Labbai shima kawai aka wuce wajen.
Muna tsakar gida suka shiga rabon goro Maigogul wai ku kunga gaye kuwa fararen kaya ?al ya saka komai fari har zabban azurfan hannunshi masu fararen duwatsu ya saka yadda kuka san gwamna, takalmin ?afarshi kuwa mai kwale_kwale irin na ?an gidan sarauta mai karen muski ne a ?afarshi gaskiya yayi kyau sosai wallahi. Uzairu zuchiyata sai ?unshe dariyarshi yake yi a bayan Labbai, ku kuwa gabana sai dokawa yake yi. Nasan Rakiya babu kyau babu daWi wallahi.
"Wai wannan rabon goron na menene Maigogul kuma na ganku kamar daga biki kuke ko?"
Cewar Rakiya kenan da take Sallar goro.
"Goron Waurin Auren Labbaine da kuma goron Waurin Aurena. Allah ya nufa yau an Waura Aurena da Hajiya Balaraba in Allah ya kaimu sati mai zuwa zata tare, ko nine zan tare ma gashinan dai"
"Me kace wai? Abu ta kazannan..... =??
Kuna ganin za'a wanye lafiya da Rakiya kuma?
Mu haWu ranar monday muji yadda zata kaya
Mrs Bukhari

Masu adashe ina jiranku
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041:  Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/FyrOjhxZpaIDkhKKwuhZOO?mode=ems_wa_t


MRS BUKHARI
16






" Abu ta kazan uba, kace me? Aure naji kana faWe Maigogul kake ko uban wa?
A ina zata tare wai? Narantse da Allah baka isaba ni Rakiya zakaima haka ko sabida kawai ka samu bakin ajjihun mijin ?ata shine da kishiya zaka saka mana. Hauwa fito kinji alo tsiya alo danja. Au Lolo kitimurmurar da kuke ?ullawa ke da ubanki kenan? Mitsiyaciya dama babu ?auna a tsakaninmu inda ?auna ya za'a haWa baki da Wiyar cikinka ai maka kishiya"
Cicib yace.
"Ayi ha?uri Rakiya bakin al?alami ya bude"...
" Rufa mun baki ba?i ba?in munafuki mai kutungullar tsiya Wan daudun banza, ka auri Wiyata kazo kana wani cewa ayi ha?uri. Kema ki rasa wanda zaki Aura a duniya sai wannan wanda dake dashi banga ta inda kuke da bambamci ba"
Maigogul ya kalli Cicib yace.
"Kaje daga sama Labbai zata zo bari in gama dasu kasan Rakiya kishinta ya ?azanta. Zamanin Hauwa ma haka ta cukumeni muka faWi ?asa mukaita burgima muna dukan juna wallahi har kusa da lambatu."
Wucewa Labbai tayi gaba Cicib ya bi bayanta suka haura sama.
Rakiya ta cukume Maigogul gam tai ta jagalanci tana jjigashi tana zage_zage mu kuma mukai ca a kanta muna kiciniyar kwace Maigogul. Abun mamaki sai ha?uri yake bata lallai abubbuwa da yawa sun canja da dane a wannan gida da dambe har ma?ota.
"Lallai Maigogul ka cika makiri wallahi. Muna zaune cikin ba?in wahala babu ci babu sha babu sutura yanzu daga sake mana gida ka kwashi kuWin kayan Wakin lolon kenan shine kayo aure ko. To a ina kake so ta zauna a sama tare da Rakiya ko? "
"Allah suturu bu?wui sai dai ta zauna a ?asa tare dake wallahi ni da gidan ?ata. Ni ya sakeni ma in huta ko zan samu sabon miji mai ciyarwa gara mu rabu narantse da Allah insan bani da miji makiri"
Maigogul tun yana lallaSa Rakiya da Hauwa har sai da suka tunzurashi suka shiga kokawa da Rakiya ya samu ya kwaci kanshi ya haWata da Hauwa ya gwarasu da juna. Ya cire malum_malum Winshi zai doka da ?asa Uzairu zuchiyata dake tsugunne ri?e da ciki yayi saurin karSe rigar. Rakiya ta dira a wuyan Maigogul da kokawa harda cizo fa wallahi, ga kuka tana yi kashirSan. Hauwa kuwa Raliya ce tazo ta ri?eta gam. Sai da Maigogul ya kusan raWa Rakiya da ?asa Rahama tayi saurin fisge Rakiya gefe. Sama da ?asa Allah bai bani ikon cewa uffan ba.
"Lafiyanku ?alau kuwa sabida raini daga cewa na sake aure shikenan sai wannan cin mutuncin a gaban yarana da girmana akwai uban daya isa ya hanani aurene ke da ke duk wacce take jin ba zata iya zama dani ba ?ofar gidana a buWe yake.
Wannan wanne irin masifa da bala'ine yake damun Rakiya nene? Rakiya matar dana Aura a Kano ma take tana da gidanta ba Waya ba ba biyu ba, kuma tana da motocinta ba wai irinku bace wagairahun wannan Hajiyace mai ji da kanta ?ar gidan mutunci. Ku bini a hankali wallahi in ba haka ba tsab zan fatattakeku danni ba ajinku bane yanzu"
Fuu ya shige Wakin Hauwa yana huci. Rakiya bafa ta ha?ura ba binshi tayi suka ci da gabzawa dambe tsakanin Maigogul da Rakiya wallahi har waje Rakiya ta dinga janshi suka fita.

19 / 28