Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   3 / 28

6K to 9K   out of 83.6K words

da rabi jirginmu ya Waga zuwa Kano ta dabo tumbin giwa gari in ba Kano ba dajin Allah.
A Aiport muka tarar da motar da Alhaji Bilya ya turo azo a Waukemu tana jiranmu.
Kai tsaye jigawa muka dosa muna tafe Maigogul nayi ma Alhaji Bilya hira bashi yayi shiru ba har saida bacci yayi awon gaba dai dashi kana ya samarwa da kanshi lafiya.
Wajajen sha biyu da rabi muka tsaya a ?ofar gida. Rakiya muka gani saSe da mayafinta zata fita ga zoSo tana sha a leda.
Ganinmu ne yasa ta tsaya tayi turus tana kallonmu da fara'a Wauke a fuskarta. Uzairu zuchiyata kuwa yana fitowa Rakiya ta soma tafi tana kiran sunanshi.
Da gudu Labbai ta fito ko mayafi babu a jikinta ta rungumeni muka saka dariya. Uzairu zuchiyata sai wani dariya da ?wanbo yake yi.
Maigogul kuma yana cikin mota bai fito ba har saida muka sauke kab kayanmu kana suka fito da Alhaji Bilya.
"Kayi nayi gafa surukinki ki matso ku gaisa"
Alhaji Bilya yace.
"A_a Maigogul wai ya kake magana haka kamar ba'a farsa maka bakinka bane. Ni ai ya kamata inje in gaisheta ka fiye katoSara"
Wannan kalmar daya faWama Maigogul da daki zuhina sosai. Amman nasan bashi da laifi babban mai laifin Msigogul ne.
Da haka na ja akwatina kiii zuwa cikin gida nan na tarar da Hauwa dasu Layuza da Aliya suna zaune suna cin taliyar murji da manja da yaji.
"Ahh kaga mutan turai ashe kuna tafe ai tun jiya muke saka rai daku"
Ayya Hauwa dake jiya an samu matsala jirgin bai samu damar tashi ba sai yau."
Shigowar su Adama dasu Uzairu Zuchiyata ne ya katsemu.
Adama kece kika ?one haka a hannunki ashe har abun ya kai haka Adama?"
A gigice na ?arasa gabanta ina kallon hannun. BuWar bakin Hauwa tace.
"Gaza ai yaje ya rama mata tunda Allah ya hore muku Gaza ai saiku taka uban kowa. Miji kuwa tunda ta dawo gida ko ?yeyarshi bamu... "
"Munafuka kai Hauwa halinki sai dai abar miki. Anya Hauwa zaki dena munafurci kuwa? Ba zaki ga Annabi ba"
Shewa Hauwa ta saka. Uzairu zuchiyata har dashi a shewar Wan yi.
"To ?arya nayi ne ko yazo? . ?ila ma auren ai mutuwa yayi ake rufe mana. "
"To a rufe miki kewa. Naga Aliya ce gata ta dawo daga yawo karuwanci da ciwo ya kamata aka dawo miki da'ita. Binta fa tana Waki an sakota, ga Layuza da kike ta?amar itace mai gasa da Lolo itama an sakota. To na me zan Soye miki dan an saki Adama aikin banza a kab Wakina babu wata mace data tafi yawon karuwanci har ba'a san inda take ba saida ciwo ya kawota"
Bakina na taSe na shige ciki Uzairu zuchiyata ya biyo bayana.
Su Rakiya saida Maigogul ya shigo kana ya tsawatar musu.
"Aikinku kenan Waga murya sai kace gidannane kaWai gida. Kundai ji kunya wallahi.
Ke Adama Labbai ku shige mu je ciki mu tarbi su lolo yaushe ma zaku daka ta Hauwa da ?a?anta"
Suka shigo suka bar Hauwa da kumfar baki.
"Lolo kije kuyi sallama da Billy zai tafi maza jeki Wiyar kirki"
Mayafina na zura na fito.
Hararata Layuza tayi da muka haWa idanu. Ni kuwa nayi mata dariyar mugunta na kaWa kai na fita.
A zaure naci karo da magazin.
"Ahh Hayya hayya babbar yarinya kaga Sabuwa mai sabon aiki. Baki kwantan aiki ai wallahi ina gwanin wani ga tawa. Ai na dawo Fada yake faWa mana ashe Uzairu zuchiyata ya samu wata baturiya zata aureshi shine kuka tafi tare.
Ya ina batun tsaraba Lolo? "
Dariya muka yi duka nace.
Magazin duniya tsaraba maza shiga kada a kasafta baka"
Ina faWin haka na fita, shi kuma ya shiga gidan da mugun gudu yana ihu.
?arasawa nayi jikin motar Alhaji Bilya na jingina kawai na zuba mishi fararen idanuna.
Hannayenshi harWe bisa ?irjinshi yanata kallona.
"Wato Sabuwa kina da kyau mai tasiri sosai hasken idanunki kaWai ya isa in shagaltu da kallonki"
Zai sake yanko magana na datseshi ta hanyar cewa.
Yanzu dai kaga na gaji hutu nake bu?ata sosai. Kuma ?an uwana ma suna bu?atar lokacina ka saka rana sai ka dawo ko? "
Murmushi yayi ya gyaWa kanshi.
"To to naji. Nan da yaushe kike ganin zan dawo mu tattauna ni dake mu tsayar da matsaya guda Waya sabida ni bana son auren ya wani Wauki lokaci gaskiya. "
To inaga nan da kwana huWu ko biyar kana iya zuwa kafinnan na huta sai kaji ra'ayina ko? Nagode ni zan shiga ciki"
Hannu ya saka a ajjihu ya Webo kuWi ya bani nasa hannu na amsa nayi godiya. Daidai yana bani kuWin Layuza ta fito turus tayi da ganin ?atuwar motar da muke jungine a jiki.
To Alhaji nagode ka gaida iyalan, sai munyi waya"
Na ?arashe ina fara'a ?a?as. Saida naga yaja motarshi ya gangara sannan na nufi gida Layuza na tsaye ta babbake a ?ofar gidan.
Malama zan wuce ko? "
"Aikin banza dan wannan tsohon yazo wajenki shine har kike fiffi?a? Sabida shi kenan kika kaso auren dan kizo kici gaba da iskanci a gaban Rakiya uwark... "
Buf Gaza ya buge mata bakinta ta baya ya hankaWota tazo ta rungumeni.
"Ke Rakiya rabin raina wai kike zagi dan abu ta kazanki yarinya sai ba?in ciki da hassada ashe baki dena hassada da Lolo ba?
Eh wallahi lolo tafi ?arfinki kina gidannan zaki ga irin mijin da eh zai aureta. Dena kallona dan abu ta kazan ehhh. "
Ba shiri tayi ?asa da kanta Gaza kuma yace.
"Ke lolo shige gida ni fita zanyi zanje wani aiki ne saina dawo ma haWe ko a mutu ko ayi rai. Ko a kasheni a kawo muku gawata, ko in kashe, in tsere, ko a killaceni a gidan yari eh wallahi Allah"
Ya gangara da Rahine a kafaWarshi jikinshi da kayan farauta.
Murmushi nayi ma Layuza da naga jini a bakinta ya wanke mata ha?ora.
Ina shiga Wakinmu na tarar Maigogul yayi zaman daSaro da akwatuna a gabanshi anata ganin kaya. Uzairu zuchiyata yana ta wawware ma kowa tsarabarshi.
Nan su Aisha ma suka shigo muka ba kowa tsarabarshi kayana kuma duk na tattare.
Maigogul ya cika cake a baki ga lemun kwali yana korawa yace.
"To batun auren kuma Uzairu zuchiyata ni shi yafi damuna yaushe kuka tsayar ne kaga in baiyi tsayi ba ai sai a haWa dana lolo tunda Alhaji Bilya shi yace baya son ya Wauki lokaci.
Uzairu zuchiyata yace.
" To ita tace tana son nashi ne a dai bi a hankali gaskiya. Ni aurena da Felisha nan da wata uku ne.
Ni abinda yafi damuna iyayenta sun nuna dole anan Najeriya suke son a Waura auren suna son ganin iyayena da dangina kafin mu Wunguma muje ayi bikin coci. To ni Dad maigogul a wannan gidan zan kawosu? "
Dariya duk muka kwashe dashi Maigogul harda dukan cinyar magazin. Saida ya kuskure baki da jus kafin yace.
"Wannan fa mai sau?ine wallahi a rashin hankali irinna turawa sai kaga in suka ga gidannan ya burgesu babu mamaki suita Waukar su Rakiya hoto dasu da gidan sabida sha'awa Ni inaga fenti kawai za'aima gidan ai. Wannan katangar a ?ara mata tsayi a saka ?ofa wai ba shikenan bane, sai filastar tsakar gida ai an gama"
Ai kuwa ina wuta Rakiya ta saka maigogul da ?yar rikici ya lafa.
Adama tace.
"Gaskiya ne ba sai kayi wata ?aryar ba sufa turawa babu ruwansu rayuwa mai sau?i suke yi."
Hararar Adama yayi yace.
"Tabb nifa gaskiya sai dai mu koma wani gidan koma gidan hayane na wani lokacin sai dai mu kama"
"To Allah ya kaimu ai sai a kama ?aton gida ayi bikin ba shikenan ba. Ni zanma iya samo mana ?aton gida ayi komai a gama mu da muke da Alhazai ko wani ges house Win zan iya samo maka. Ince dai dani za'a tafi bikin cocin ko? "
Maigogul ya tambaya yana zare idanunshi.
"Yauwa yanzu naji sanyi wayyo DaWi.
Dakai da Rakiya da lolo, sai Adama ko Labbai, ko kuma Gaza ko Magazin dai a cikinsu za'a Wauki Waya sukenan iyakar ?an rakiyar dai da muka tsara da'ita Felishar su su Salaha ko suna in ta haihu sa zo tunda bazai yiwu mu tafi dukka ba"
Mun sha hira sosai ranar hirar yaushe gamo.
Bayan la'asar muka fito muka Waura abinci taliya da kifi sutu sutu Hauwa sai kallonmu take yi. Tsarabar biskit da lemun kwali na bata tai ta murna tana godiya dai.
Bamu muka samu kanmu ba sai bayan isha sannan muka runtuma zuwa Wakinmu kuma fitowata wanka kenan wayata naji tana ruri ina Wagawa naga Alhaji Zaidu ne. Idanuna na lumshe na Wan murmusa kafin na Wauki wayar muka gaisa a tsanake, muka tambayi juna gajiyar hanya.
Baka gida a irin wannan lokacin, ko kaima mai zaman majalisar maza ne? "
Dariya na bashi sosai sai da yayi ta isheshi kafin yace.
"Me zaman majalisar kike nema, ko kuwa shi kike gudu? "
Kunji tambayar hankali da hikima a wajen manya ko? Murmushi nayi nace.
To sai naji a wanne bigire kike kafin inyi aman abunda ke raina"
"To naji wayon. Ai Antinki ba zata taSa barina inyi zaman majalisa ba sam. Ni da ko aiki zan fita sai munyi tababa da'ita kafin ma ta amince wata rana ma sai dai muje tare mu dawo tare. Kin ganni dai yanzu nake shirin komawa cikin gida ma?ocinmu ne yayi sallama dani."
Allah sarki ai ta kyauta kuma haka akeson mace. To nagode da kulawa yana da kyau ka shiga gida"
"Kafin dai muyi sallama zan sanar miki gobe inaso zan shigo dutse da fatan zan samu tarba? "
Idanu na zare nace.
Me zaka zo yi a Dutse? "
Sai da yayi murmushi tare da ambaton Shalele kafin yace. "
"Ni kaina bana ce ba. Ni ba yaro ba, kuma ba sabon shigan soyayya ba. Sai dai taki ta kasance ta musamman. Zuchiyatace take fusgata lallai tana son jin cikakkiyar amsar wanne muhalli muka samu. Wata zuchiyar kuma tace dani garin kallon ruwa Zaidu kada kwaWo yayi maka ?afa"
Idanu na lumshe a hankali na furta.
Allah ya kawoka lafiya, ya tsare hanya"
Da wannan mukai sallama.
Na labartama su Labbai waye Alhaji Zaidu. Amman na lulluSe sirrinshi na rashin haihuwa. Sai dai sun san bashi da yara dai
Sun haWu sun taya ni murna sun kuma bani shawarar gara in Waukeshi in yi fatali da Alhaji Bily indi maigogul.
"Amman ki killace kayanki gaskiya ki bashi daman zuwa sau Waya rak. Ragowar komai a gama a waya kinsan Allah yazo ya kuma kema kinsan sauran. Tunda ku ba yara bane dama za'a haWa dana Uzairu zuchiyata ai da yafi. Ohh ranar za'a ga abu. Allah yasa kafin lokacin hannuna ya warke"
Labbai tace.
"Uhm wallahi gaskiya aka faWa miki kiyi auren sirri kawai.
Ohh ke dai lolo sa'a tafiya kuke yi kunnen doki, daga gama idda sai samun mazajen aure harma saida kika zaSa. To ni zanma Maigogul magana ya haWani da shi Bily Win nima in ci albarkacinki gaskiya"
Adama tace.
"A jarraba gaskiya Labbai. Inma yace a_a gasu Salaha, su Aisha ya zaSa ya dirje. Ke lolo ke zaki yi mana wannan. Ko ni yace yana so wallahi da gudu zanje in amso takaddata tunda dama auren tangal tangal yake yi"
Dariya nayi nace.
Gaskiya wannan kishiya ba za'a zaman lafiya da'ita ba.
Amman ?ila tunda Gaza ya taSata ta sama miki lafiya. Ke dai ki lallaSa ki koma zaifi miki"
Baki ta taSe tace.
"Gashi anata bashi shawarar ya tsaya takara ba. Kai amman fa bambamcinshi da Alhaji tili na kofur zubaina Ghana wallahi kaWanne ke lolo kinga yinwa. Amman inna tuno ko gidanmu ma kai kake nema ka ciyar da kanka sai inji dama dama can Win dai. Allah cuta Allah magani dai abun wallahi."
Mun kai kusan biyun dare muna hira mune harda shewa. Labbai kuwa dariya harda tsugunnawa dan mugunta. Allah sarki ?an uwa akwai daWi musamman mata, in kuma akaci sa'a kawunanku basu rabeba babu ba?in ciki a zuchiyar kowa.
Da tunane _tunane na kwana a raina.
Washegari na tashi da shirin tarban ba?o. ?arfe tara ya baro kano dake a ranar yake son komawa.
Ba shirin na shiga shirin tarbarshi zuchiyata na bugawa da ?arfi da ?arfi.
Labbai na Wauka muka je ?ar kasuwa cefane muka dawo nandanan muka fito da risho ?ofar Waki na soma aikin abinci.
"To wai Lolo amman shigowa zaiyi yaci abincin anan gidan dai ba'a waje zai tsaya ba ko? Nifa ina jiye miki ?an unguwarnan su ganshi ne.
Kinsan Allah ko uwar ?ar Shuwa taganshi sai tayi duk yadda tayi taje ta tareshi har titi ta tona miki asiri. Ni dai shawara kawai kai tsaye ma da kin le?a kice mishi ku shigo. "
Ina kwashe kazar dana soya na tsoma cikin jajjagen attaruhu nace.
"Kinsan gidannan gidan matan aurene gasu da munafurci na masifa taya zan Wakko namiji in shigo dashi dama kallon karuwaima suke mun. Kuma na faWa miki sunyi hira ta awa guda da Maigogul me kike tsammanin ya saura a cikin sirrinmu ma? "
Adama da fitowarta daga ciki kenan zata tafi wanka tayi ?asa da murya tace.
"Uhm abinda labbai ta faWa miki shi za'ayi"
Dole na amince da haka Labbai ce ta ?arashe mun girkin ni kuma nayo wanka na shirya cikin wata jar atampa mai agon ba?i da fari abinka da farar fata sai atampar ta haskani sosai. Kirana yayi ya sanar mun gashi a cikin layin dana kwatanta mishi in fito.
Turare na fesa.
Ci gaban zai zo fejinne ya yanke........
' [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: ?ARASHEN PAGE 2 NE KADA KU RU?E
Turare na Wauka na feffesa na zari mayafina na nufi zaure.
Adama da labbai suna gefen Wakin a tabarma suna hirarsu.
Ina fita na hangoshi daidai ?ofar gidansu maigogul. Saida naji faWuwar gaba cike da taraddadi na soma haurawa. Yana da wata iriyar nutsuwane da kamala kamar Baba Malam yanayinshi yake yi mun.
Wata farar mota ce ta wuce ni ta paka a bayan motar Alhaji Zaidu.
Wata farar kyakkyawar macece ta fito cikin shigar kamala.
Wuceta nazo zanyi ina kallon Alhaji Zaidu dake jingine a jikin motarshi yana kallona fuskarshi cike da annuri kuma da gani a shagale yake wajen kallon nawa. A cikin ?wayar idanunshi nake iya karanta sa?on da zuchiyarshi ke Wauke da'ita
"Amm baiwar Allah dan Allah ina tambayane gidansu Maigogul Kawali"
Dum naji ?irjina ya buga da sauri na kalleta mukai kallon kallo da'ita. Gashi batai kama da mutuniyar banza ba a ido balle inyi tunanin ko irin jama'arshi ce. Sannan nasan ya dena harkar tsubbu balle ince ko magani tazo ya bata tunda daga irin motarta kasan mai arzikice zaiyi wuya tayi hulWa dasu Maigogul.
"Ai kece ma wacce nake nema bake bace Sabuwa tsohuwar budurwar mijina Khalid ba. Kwartuwa mai bin mazan mutane ayi zina da'ita akan gadon sunnah. Ko da yake ubanki ai kawaline dole ma ku zama haka dan abu ta kazan ubanki"
Illahirin kunya ne ya kamani wallahi zuchiyata har tsalle take yi mun tsabar tashin hankalin dana shiga.
Kaina naga tayo a hassale daidai fitowar Gaza su Rahine da yaranta na biye dashi harda wani muzuru ba?i mai Waure da ?atuwar ba?ar laya a wuya
Mrs Bukhari.


Na ?o?arta nayi muku Typing da yawa.
Amman maganar gaskiya sai zuwa Monday dai zaku jini in sha Allah
A fito ayita sharhi kawai
Son so
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA HU?U
SHAFI NA UKU



GIDAN B HOUSE:.

?ar Shuwa ce yau da girki gobe kuma zata wuce Bamaina wajen Sameerah ta gama shirinta tsab ta zuba kayanta a akwati, ?annenta da suka zo ta basu su Fati sun tafi dasu gida.
Tuwon shinkafa miyar kuSewa Wanya tayi harda nama gundun_ gundun. Yanzu ai ?ar Shuwa daWi take ci sosai musamman ranar da Babangida baya Wakinta tunda in yaga abun yayi yawa yana yawan tuhumarta ta fahimci yana zarginta sosai. Sai tayi mishi ?aryar kasuwanci take yi ?annenta ke saida mata acan layinsu. Ya dai jine amman bai yadda ba.
Tana kan kwashe tuwo Babangida ya shigo jikinshi saye da biri da wando na aikin Baban bola da yake yi ya shige ciki.
"Sannu da shigowa Jannaty"
"Yauwa sannunki da aiki anata aiki kenan"
Ya shige kai tsaye banWaki ya shiga zai watsa ruwa yaga ?ar Shuwa ta siyo wasu sabulan wanka manya na ruwa masu tsada ko a ido, ga wasu kayan ?amshi da sabulan ?amshi duk a banWakin. Har buta da randar banWakin ta sauya da sababbi.
Cike da damuwa da fargaba ya gama wankan a gurguje ya fito ya wuce masallaci tare da su AWWa'u
Sai da akayi isha ya soma yima magidanta karatu a masallacin tunaninshi yana kan to ina ?ar Shuwa take samo kuWi take wannan siyayyar. Haka dai ya lallaSa takwas da minti hamsin ya tashesu ya shiga gida.
Saida ya tambayi mardiyya babu abinda suke bu?ata suka tabbatar mishi babu kafin yayi musu sallama tare da umartarsu suyi adda'ar bacci kafin su kwanta. Sauran matan nashi saida ya bisu ya duba lafiyarsu data yara ya tambayesu ko akwai abinda suke bu?ata kafin ya yada zangonshi a Wakin da yake.
Sababbin kuloli Webi da kanka yaga an zuba mishi abinci harda zoSo mai sanyi.
Zama yayi yana ?arema ?ar shuwa kallo tayi ?unshi da lalle na tafiya yana lure da'ita har gyaran jiki yaga tana yi kallonta kawai yake yi.
"Jannati ga ruwa ka wanke hannunka kaci tuwo. Ko a baki za'a baka ne? "
Murmushi yayi yace.
"A_a zanci da kaina nagode"
Wanke hannunshi yayi a robar ruwan wanke hannun ta zuba mishi tuwon ta turo gabanshi.
Cinyar kaza da Sangaren ?irji ta saka mishi ga bushssshen kifi yana gani ido da ido harma da Wanyen kifi dukka.
"Duk a kuWin dana baki kiyi cefanene kika sai kaza da kifi? Nifa na kasa gane irin kuWin da kike kashewa da irin canja abubbuwa da kike yi ke ki faWamun a inda kike samun kuWi abun ya wuce kuWin kasuwanci har nawa kike juyawa cinikin nawa kike yi haka a rana nifa ba mahaukaci bane, ba kuma Babangidan da kika sani da bane mai adankiya da iyalanshi"
Yayi kicin _kicin da ranshi har da ture abincin

3 / 28