Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   11 / 28

30K to 33K   out of 83.6K words

kai ki har zaure kafin in tafi"
A jere muka iso har ?ofar gida kana ya mi?o mun ledojin hannunshi.
"Wannan babbar ta Alhaji Baba ce. Ita wannan jakar taki ce. Sai da safe"
Juyawa yayi da sauri ya faWa mota ya tayar da'ita.
Murmushi nayi inajina tamkar sabuwar mutum ce ni, tabb soyayya duniyace. Da farin ciki na shiga gidan. Yanda na barsu a haka na taddasu maigogul na kan turmi yana basu labari anata dariya. Kallona yayi yamun murmushi ya yafitoni da hannu na nufeshi ina jin daWi sosai.
"Ya tafi Lolona Amman dai ba Kano ya kama hanya ya tafi ba ko? "
E yace sai gobe da safe in yazo yaci abinci sai ya kaiku kuga gidan kafin ya wuce. Wannan ledar yace in baka"
Dariya yayi ya cabke ledar ya buWa wasu irin shaddajine waganbari asalin manyan guda biyu da takalmi da agogon fata komai na cikin ledar mai bala'in tsada ne sosai.
"Hiye Lolo duk wannan kaSakin arzikin duk nawa ne. Lallai Lolo yanzu ne kika yi aure. Ke dake da Uzairu zuchiyata yanzu ne zaku nuna mini kun haifu yanzune asalin kuttun farin jini da Sa'a ya fashe a gidannan"
Da Rakiya da Hauwa tare sukai dogon tsaki.
"Aikin banza"
Cewar Rakiya dake dokin ?ofa tana cin gurasa da shayi. Ni da maigogul muka kwashe da Dariya a tare.
"Lolo ai kin gani tun daga gida kin soma fuskantar ?abulabe ko? "
Na gani Maigogul dama yace in sanar maka daga Umara zamu wuce Dubai mu siyo kayan akwatina"
Rakiya tace.
"Agen duk Maigogul Win? Lallai kin cika tabbatacciya Lolo yayi kyau Allah ya taimaka"
Rakiya bafa ni nace ba shi yace haka"
"Ba shakka sabida kin nuna fifikon Maigogul sama da nawa ba. Ba gashi ko tsaraba shi kaWai ya yoma ba ni ina zaune gaho"
Zan yi magana Adama tace.
"Haba Rakiya banda muhalli daya siya mana har wani abun muke nema kuma. Sannan mutuminnan fa ko maigogul yayi ma ai ke mai jin daWi ce"
"Batta Adama ta yi yadda take so. Lolo dai Wiyata ce, kuma kinsan da wuya ina tare da'ita bare da daWi. Kina zaune duk shekara zata kaini aikin hajji ba dai dani kike zancan ba? Ke lolo wuce ki shiga ciki abunki, ni Winkima zan kai a darennan dama bikine damu. Ku kulle gidan dan bazan kwana a gidan ba"
Da wannan ledar ya fice fuu. Rakiya tafi awa biyu cur tana zage_zage saida na dun?ula mata kuWi da takalmi wanda Alhaji Zaidu ya siyo mun sannan tayi shiru harda washe bakinta sai lokacin na yi ajjiyar zuchiya tare da girgiza kaina kawai.
Mrs Bukhari

Son so=??? [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI
9





Cikin dare ba sai bacci yace baima sanni ba. Ina ganin su Adama a kwance sunata baccinsu hankali kwance. Amman ni sai juyi kawai nake yi tunanuka biyu su suka ci ?arfin zuchiyaya. Tunani na farko shine tunanin Alhaji Zaidu da nake jinshi tamkar a duniyar mafarki, ko kuma duniyar tatsuniyoyi, ko hikayoyi. Ha?i?a na yaba, nayi ma Allah godiya daya dubeni ya jefo mun Alhaji Zaidu cikin rayuwata baban soyayya kenan. Allah shi ya tsara komai bamu da tsumi bare dabara shi yasa abubbuwan suke tafiya cike da almara. Cikin ?an?anin lokaci haWuwar da bata fi sau uku zuwa huWu ba. Mune muka mallaki gida, kuma wai yau ni Sabuwa Alhaji Zaidu ya biya ma Umara, lefena a Dubai zan haWo shi. In banda Allah mai iko da saukar ?udura wa zaimun wannan? Babu shi, a cikin jikina ina jin cewar da Auren Alhaji Zaidu zanyi amfani in gyara ma Maigogul Rayuwarshi, shine jigo nayi imanin idan ya shiryu abubbuwa da yawa na gidanmu zasu iya sauyawa. Muskutawa nayi na tashi zaune na jingina ina hararo al'amura ina fatan su kasance kamar yadda nake kallon hotunansu a idan zuchiyata.
?ayan sashen na zuchiyata kuma tunanin a irin ?urarren lokacin da Madubala yazo nake yi. Madubala ba irin namijin da za'ace an mance dashi bane sam wallahi domin masoyine mai sadaukarwa ga masoyiyarshi. Sai dai kash yaxo a ?urarren lokacin mai ikon saukar da ?udura baiyi shi zan aura ba. Amman nayi farin cikin ganinshi cike da kamala tabbas.
Rarrafawa nayi na fita na Wauro alwala. ?akin namu ma a mugun cike yake bazan samu wajen Sallah ba.
Gaza da Uzairu zuchiyata na kalla suna gefe a kwance a tabarma, su Ma'aru, dasu Sama duk sun kwakkwanta a tsakar gidan,murmushi nayi.
Allah sarki ?an uwa abun wuya. Duk lalacewar Wayanmu baya sawa mu gujeshi tafiyarmu tare take in sha Allah. "
?ankwalin materiyal Wina na shinfiWa na ta da kabbarar sallah.
Raka'a biyu nayi na zauna na dinga godiya ga Allah bisa turo mun Alhaji Zaidu cikin rayuwata da yayi Domin Allah ni dai na ro?i Allah yasa Wa ko ?arshi a jikina suke kunga laifina?
Bani da laifi babu macen da bata son kuWi, kuma babu macen da bata son mijin alfahari da nunawa, kuma babu macen da ba zata so ta auri Alhaji ta haihu dashi ba.
Ina shafa adda'ata ana kiran assalatu. Idanu Gaza ya buWe sakamakon Rahine data hau jikinshi tana shinshinar Uzairu zuchiyata.
"Ni Uzairu zuchiyata na shiga uku dan masifa da bala'i mutum yana kwance ana shinshinarshi kamar mushe Gaza wai wannan karyar taka lafiya kuwa, nine bata gane ba dan ubanta ko menene? "
Gaza ya harareshi kafin yayi magana yaran Rahine uku suma suka iso wajen suka kewaye Gaza.
"Kai mata maza malalaci mai zama cikin mata hattara maza bisa kanka wallahi. Wuya a hannun maza dan abu ta kazanka"
Wani ihu da Gaza ya danna da sauri Uzairu zuchiyata ya matsa. Ni da Gaza muka tuntsure da Dariya harda su Sama da Sama
"Lolo kinga wannan abokin naki akwai tsoro eh mijin baturiya ba eh bari in yi eh alwala in tafi masallaci eh wallahi"
Mi?ewa yayi sukai alwala suka wuce masallaci tare suna tafe suna zolayar juna tsakanin Gaza da Uzairu zuchiyata, su Sama kam wucewarsu suka yi. Ina jin Gaza na cewa zai sha?e Uzairu zuchiyata.
Kai na girgiza ina kallonsu nan da wani shekaru a matsayin waWanda bamu kaWai ba al'umma ma zatai alfahari dasu in sha Allah.
Da karfin guiwa da wani kwanciyar hankali da nutsuwa nayi sallah. Kana na tattashi ?an Wakinmu suka firfito dasu Rita da Madamcy, ?an Wakin Hauwa ma haka.
Gaza na shigowa ya dama madara ya kira Magenshi daya saka mai Uzairu.
"Zo Uzairu kasha madara maza"
Dariya nayi nace.
Wuu Gaza wannan muzuru zai yi mugun son mata, mata har gida zasu dinga biyoshi"
Kowa sai da yayi dariya Uzairu zuchiyata shi da Labbai harda birgima dama sune sarakan dariyar mugunta a gidanmu.
Shigowar Maigogul da Cicib faram_faram ita ta dakatar da hirar.
?aki Maigogul ya shige yana muzurai ko me ya faru oho dai.
Sai da muka shiga muka tarar dashi jikinshi yayi zafi kau ya lulluSa da bargo.
Duk muka rufu a kanshi anata mishi sannu.
Tutturesu nayi na zauna a kusa da kanshi ina shafa gashin kanshi ina mishi sannu.
A hankali har bacci yayi gaba dashi, duk sai suka watse ni kuma madadin in fita saina zauna dirshan na ?ura mishi idanu yana ta bacci. Murmushi nayi mishi ina sake godema Allah daya ?addara muka fito da tsatsan maigogul. Hmm zaku yi mamaki jin hakan?
Ai duk lalacewar iyaye Wa dole ya sosu ko da gidan karuwai maigogul yake rayuwa inason kayana balle yana dawowa gida. Kuma wallahi yana da shiga rai dole a soshi ne ba zaku gane ba.
"Ke dan ubanki wuce ki je ki samu su Labbai ki haWa ma mijinki kayan karin kumallo. Ya zaki tusashi gaba haka. Kika san dame sukai gamo? Basu da aiki sai zuwa hotel rayuwar ba?in ciki an girma ba'a san an girma ba. "
Jiki a mace na fice yadda Rakiya take a fusacennan nasan tsab saita mare ni ji take kamar du mu biyun ta dira a wuyanmu fa.
Biredi da soyayyan ?wai da shayi na tanadar ma Alhaji sai gurasa da su labbai sukai banWashenta. ?arfe tara nayi wanka fes na share tsakar gidan tas. Har zuwa lokacin maigogul baccinshi yake yi. Dole da Alhaji yazo sai ?akin Hauwa muka shiga dashi bayan ya gaisa dasu Rakiya.
Yana shan shayi yana ?arema tsakiyar idanuna kallo.
"Yaya darenki ya kasance Shalele? Naga bacci sosai a tattare dake me ya kawo bashin bacci uhm?"
Kafin in yi magana sai ga maigogul kamar an jefo shi ni dai banji ko yayi sallama ba ya shigo.
"Alhaji ashe ka shigo har ka soma karyawa. Ke Lolo abinda kika kawo mishi kenan meye wani shayi da ?oyi me yasa ba'a tasheni ba? "
"Ai babu komai Alhaji Baba. Ina kwana? "
Da sauri Maigogul ya bashi hannu shima a kunyace ya mi?o suka gaisa. Maigogul yaita sokiburutsu da Wakko labarai marasa kai da ma'ana. Shi kuwa yayi tsit sai ji yake yi. Yana so ya Wauko zancan kawalcinshi. Ganin nayi kamar zanyi kuka sai yayi wannan dariyar ya mi?e.
"Bari naje in jiraku a waje in ka kammala maje can gidan ko uhm Lolona ke kinci abincin ne? "
Kai kawai na Waga mishi halamun eh sabida ya fice.
Fita yayi yana ta dariya.
"Ina jinki bani labarin daren to?'
Yawun ba?in ciki na haWiye na ?ir?iro murmushin bogi na Waura kan fuskata.
To bazai wuce mamakin yadda aurena dakai ya kasance ba gaskiya."
"Me kika fi tunawa dangane dani? "
Murmushinka, domin shine abu na farko daya soma shiga tsakaninmu"
Kai ya jijjiga cikin gamsuwa yace dani.
"Ni abinda yafi tsaya mun a raina shine ?amshinki da taushi da Wumin hannunki, da ?yar nayi bacci. Shalelena na riga na kamu shin ba za'a sassauto da wannan tarewar ta kasance kuna dawowa ki tare ba? In fa ba haka ba zaki dinga sawo inta ziyartar Dutse ba tare dana shirya ba"
Kaina na sauke ?asa ina murmushi, shima murmushin yayimun, yasa yatsanshi Wan manuniya ya Wago haSata dashi muka zuba ma juna idanu.
Wallahi wani irin kallo mai taushi yake yi mun, ga wani mayunwacin sa?o da yake isarmun ta ?wayar idanunshi.
Lumshe idanu muka yi a tare, ya jawo numfashi daga huhunshi tare da fesar da iskar ta baki da hanci bai Waya.
Cikin muryar raWa yace.
"Ki shirya sosai duk ranar dana miki ri?on alawar yara mai rabamu sai Allah"
A hankali cikin irin salonshi nace.
Babu ma bai rabamu alawarka saika shanyeta tas in sha Allah"
Murmushi mai sauki yayi mun.
Ya jingina da bangon Wakin Hauwa yana ta kallona ?asa_?asa.
Ni kaina da ?yar nake numfashi Allah
Kunsan wallahi ji nake ban taSa soyayyaba ma, kalaman, da yanayin da nake ji, da shi kanshi mijin da tazarar fa kamar sama da ?asa ne tsakanin wannan Auren da auren Babangida, da samarin da nayi a baya.
Wallahi sai nake jin duk ba'a iya soyayya ba ga gindin maganin na'iso dai yanzu.
"Yaranki suna da labarin kinyi aure, ko basa zuwa inda kike ne?." Ya kawar mana da wannan yanayi da muke ciki dan gudun yin abun kunya.
Kallonshi nayi da kyau nace mishi.
Basu sani ba gaskiya ina jiran ?arshen wata in sun zo in sanar musu ne"
"To amman sun zo sun dubaki a asibiti ne? "
Cikin kallon tuhuma nace mishi.
Me ya kawo wannan tambayoyin? "
Dariya yayi wacce na kasa gane wacce iriyace. Saida ya kurSi shayi ya haWiye kafin yayi mun kallon ?asa_?asa yace.
"Bani amsar tukunna"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Sun zo, harma suke faWa mun ita babbar an amshi sadakinta zata auri yaron yan mahaifin nata"
?ur yayi mun da idanunshi.
"Babansu ne kenan ya kawosu ko dai su suka zo da kansu tunda ba yara bane? "
Shi ya kawosu. Sabida basa zuwa ko'ina sai dashi in ba makaranta ba."
GyaWa kanshi yayi tare da sauke ajjiyar zuchiya yace.
"To yaushe zaki gabatar musu dani a matsayin Babansu, izuwa yanzu ya kamata su san da zamana ko dai baki shirya hakan ba? "
Shiru nayi ina nazari dan ni har ga Allah na fi son sai lokacin tarewar tawa a fasa maganar kowa yaji.
"Baki ce komai ba Shalelena uhm"
Na jiyo muryarshi.
Da naso sai lokacin tarewar tawa in tazo saji labarin sabida ba'a sanarma kowa ba tukunna"
Murmushin dai ya kuma yi tare da cewa.
"To shikenan Allah ya nuna mana lokacin, ya kamata suma ace dasu za'ayi miki Rakiya ai ko? "
Kai kawai na Waga halamun E.
Da haka mukaita taSa hirar, a gaba ya tusani saida naci gurasarnan da kanshi ya haWa mun shayi ya mi?omun tattali iya tattali fa.
Haka Gaza ya le?o wai in zuba mishi madara a shayi da kanshi ya karSa ya zuba mishi.
Ya bani kuWi masu yawa yace in ajjiye a hannuna.
Yana gamawa muka fito kusan mu goma ashe Maigogul ma da mota a hannunshi. Sai na Wanji sanyi a raina.
Su Rakiya dasu Layuza da Raliya da cicib amotar su Maigogul suka shiga.
Ni kuma da Adama da Gaza da Uzairu zuchiyata muka shiga motar Alhaji Labbai dasu Sadiya suna gida da ragowar sauran dai.
Duka gidajen biyun saida ya kaisu duk aka zagaya aka shiga lungu da sa?o na gidan dai aka gaggani. Maigogul ina ganinshi yana sharar hawaye Alhaji Zaidu na bashi kalma. Kiya teka ne ya bada takadda maigogul ya saka hannu, Gaza ma ya saka, sauran saka hannun in an gama za'a dan?a mana takaddun gidan a hannunmu, nan da kwana huWu zamu ma iya tarewa kafinnan masu fenti sun gama fentin cikin gidan da wajen gidan duka ma.
Daga nan ya mayar damu gida kuma.
A mota mukai sallama bayan ya gama narkani da salon soyayyarshi, dani dashi da ?yar muka rabu wallahi, ina nima fa bazan iya wannan wata ukun ba wallahi tab Ya kama hanyar Kano, su maigogul ma kama hanyar mayarma da masu mota suka yi shi da ango naku na Labbai:.


BABANGIDA:.
A zaune ?ar shuwa take tana ta zuba mita da ?un?unni Babangida ya shigo ya nemi waje ya zauna, ga miyar sutu a gabanta da nama da wani biredi mai laushi.
"Aisha daga yau sai yau wallahi in na kuma jin labarin kin saka Ramatu aiki a gidannan ranki zaiyi mummunan Saci sosai ni dai na faWa miki sabida ba aurenta kike yi ba, kuma kamar yadda kike da juna biyu itama juna biyun gareta.
Sannan jiya naga nama cikin leda a ?ofar Wakinki shima a cikin kuWin ribarki ne koko yaya? "
A zuchiyarta sai kutuntumo ashar take yi. A zahiri kuma ta haWe ranta tamau tace.
"Nasan bazai wuce Sumayya mai shegen munafurcinnan bace ta faWa maka ba. Ni ba saka Ramatu aiki nake yi ba. Dafa kanta take zuwa karSa tace zata yi mun. Zan?i bata ne sabida Allah fa? "
"Zaki ?i bata mana itama ba sai ki barta taji da nata ba? "
"Hmmm"
Kawai tace shi kuma yayi shiru yana aiyana abubuwa da yawa a ranshi dangane da'ita.
"To kayi ha?uri Jannaty. Nama kuma ragon da Mama ke kiwatawa ne ya kasa shine ta yanka ta aiko mun da rabi tace koma nawa ne in kawo"
?ur yayi mata yace.
"Dama tana kiwone ban sani ba? "
"Tana yi sosai ma har kaji tana kiwonsu"
"Uhm amman ba'a cikin gidanku ba ko, dan naga gidan babu sararin da za'ayi kiwo a ciki. Kuma in a ciki ne zan gani ko? "
?an zare idanu tayi, tayi shiru tana nazari.
"A ma?ota take yin kiwon nata sabida gidanmu babu waje akwai ma?otanmu suna kiwo shine ta ro?esu ta zuba nata"
Haka dole ya yarda badan ya gamsu ba amman yaya zaiyi tunda baisan inda zaije yaji gaskiyar batun ba.
"Mardiyya an kowa sadakinta ba da jimawa ba za'ayi bikin nata dan ko shekara ba zai yi ba"
A razane ta dubeshi har tana ?warewa tace.
"Da Sauban Win kuma za'a Waura wai? "
Mi?ewa yayi saida yakai bakin ?ofa yace.
"E dashi za'ayi. Ai Baba Malam baya magana biyu kema shaidace. Ni na fita saina dawo"
Dama jiranshi take yi. Yana saka ?afa daya fice ?ar shuwa ta saSa mayafinta ita da Da Jami suka fice. Jami ta nufi hotel wajen ba?onta ?ar shuwa kuma ta nufi gidan Kulu suka rankaya wajen bokan data ce zata kaita.
Bayan boka ya gama jin bayaninsu tsab ya buga ?asa ya dubeta yayi dariya.
"Ai Hajiya ga Waukakanan tana biye dake tamkar inuwarki. Zaki yi arziki ki buga rayuwar da kike mafarkin samunta. Amman akwai tashin hankali, ruWu, da damuwa sosai, ga gargada a hanyar. Amman dai hanyar arzikice.
Cikin murna ?ar shuwa tace.
" To duk wani abu mara kyau a hanyar malam a kawar mum dashi. Akwai wani taro da zan halarta a Abuja ina ji a jikina daga nan Waukakata take da asali. Matsalata Waya mijina asiri baya kamashi har mata boka da siriki boka yayi amman haka suka buga suka barshi"
Ta kwashe dai tabarin yadda take son ayi mata kab ta labartama wannan boka.
"Uhmmm ita Sabuwan ai ga ubanta nan yanata muku turen aiki akan lallai sai Sabuwa ta dawo Wakinta ko kuma ke su rabaki da mijin naki kowa ya rasa.
Ita kuma mai aure Mardiyya ai babu haske a auren ?unci, kuka, tozarci na hango a cikin zaman. Sai dai yaron zai iya zame mata gata sosai dan yana sonta kuma da Wan abun hannunsh"
"Tabbas yana da gidanshi ya gina, kuma da ?ar motarshi. Ni Malam ba nitsattsen miji nake son ta aura bairin Sauban Wan malamai ba. So nake ta auri Wan iska, ita kanta fa uwar Wan bata so sabida yarinyar bata hanyar aure ma aka sameta ba. Malam za'a iya wargaza auren? "
?asa ya zazzana, ya share ya kuma zanawa yace.
"Kai akwai rabo a tsakaninsu. Matsawar aka hana auren kota halin ?a?ane sai wannan rabon sun samar dashi. Kinga tarihi zai maimaita kanshi kenan"
Murmushi ?ar shuwa tayi taji wani sanyi a ranta.
"A hana auren, ita yarinyar taje ta kwaso abun kunyar haka nafi so. ?an iska ya aureta shine daidai da gidan uwarta."
Dariya bokan yayi yace.
"Wannan zamu iya. Amman shi ubanne dole sai mun duba wasu kwanaki da zamu yi amfani dasu dan ganin an mallakeshi. Amman fa shi ba zaki iya mallakarshi kita juyashi ba. Sai kina yi kina sabunta aiki akanshi kusan duk sati. A lokacin

11 / 28