Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   13 / 28

36K to 39K   out of 83.6K words

a kasalance.
"Wai meye sunan da kika saka mun na soyayya ya kamata in sani ko? "
Murmushin dole nayi nace.
Yana sebe a cikin wayata sai dai kuwa in kazo ka duba da kanka"
Mun daWe muna waya da dai naga dare yayi nace.
Wai kai kaWai kake kwana a Wakinka ne? "
Dariya yayi sosai kafin ya bani amsata.
"Lokaci zuwa lokaci Hajiya takance tana bu?atar ta kwana a Wakinta. Musamman in ta gaji sosai dake tana da shagonta da wani sa'in take zama a ciki duk da bata fiye zaman ba. Amman in tana bu?atar za'a jera kayayyaki a shago a gabanta ake komai. To yau Winma hakance ta faru a shago ta wuni cur ta gaji. Kema jira nake ki shigo sai mu tattauna batun kasuwanci dake sai ki zauna kiyi tunanin wacce sana'ar kike so, in kuma babu sai in tattauna da da Hajiya muga me zai yiwu sai ayi ko? "
Jinjina kaina nayi na ri?e haSata, sai nayi mishi murmushi ba tare da nace uffan ba.
Haka dai mukaita hirarmu cike da soyayya da tattalin juna, nima tuni na kwale nake nuna mishi iyawata har su Adama suka daddawo Labbai ma ta shigo da shofin cikin leda fara. Jin hayaniyarsu ne yasa mukai sallama ba dan zukatanmu sun so ba.
Ina sauke wayata sai ga Uzairu zuchiyata da Magazin sun shigo sunyi tsaye.
"Labbai wai duk wannan kajin Cicib Winne ya kawo har da jus ni Uzairu zuchiyata tsohon Wan daudu da soyayya"
Labbai tace.
"Ni kaina abun wani iri yake yi mun wai kunga soyayyar da yake nuna mun kuwa?
Ga tesa_tesan soyayya iri da kala"
Ranar gaskiya munyi dariya sosai Uzairu zuchiyata haka yaita ri?e ciki yana burgima yana wayyo Allahna tsabar mugunta.
Haka dai aka rarraba kaji da jus Winnan a tire kowa ya kwashi rabonshi, Rakiya ma aka mi?a mata nata.
Yau munyi wani irin kwanan farin ciki wanda baki bazai iya faWeba balle al?alami ya rubuta muku ku fahimta.

Babangida:.
Bashi ya farka a bacci ba sai takwas na safe lokacin ?ar shuwa tana Kitchen tana tuyar ?wai suna waya da Sameerah taji yana kwaWa mata kira. Da sauri ta kashe wayar ta shiga ciki.
Yana tsaye dafe da kanshi baccinma ba sakinshi yayi ba.
"Garin yaya kika barni naita bacci baki tasheni ba kina kallon lokaci kuwa takwas fa? "
"Baban Fati kenan ai nayi maka tashin duniya tashinne bakai ba kuma naji jikinka da zafi. "
"Amman ko ruwa ba kya shafamun ba zaki barni inta bacci"
Tsaki yayi ya wuce banWaki ya Wauro alwala yazo ya gabatar da sallah bai tashi akan daddumar ba da duk baccin da yake ji yana zaune yana azkar ta shigo mishi da tiren abincin karyawarshi ta dure gabanshi kana ta zauna.
"Ni na gama shiryawa kai nake jira dama in tafi banso na kai takwas a gida ba"
?agowa yayi ya zuba mata idanunshi bai tanka ba sabida tsabaragen bacci bakinshi har rawa yake yi.
"Kina da kuWin mota ne dama sannan kwana nawa zaki yi? "
Ajjiyar zuchiya ta sauke har wani dariyace ta suSuce mata kafin tace.
"Ina da na mota sai dai na shan ruwa a hanya ko? Sannan kwana biyu zanyi babu yawa ko in ?ara ne sabida kaine dama nace biyun Maiduguri da nisa"
"Yaran fa dasu zaki tafi ne? "
"A_a yara kam zan barsu a hannun Jami tunda bazan daWe ba. "
Kai kawai ya jijjiga ya tashi da ?yar ya haye gado.
Ita kuma ta turo akwatinta suka fito ita da yaran
Taci wani lashi mai matu?ar tsada, takalmi da jakanta ma masu tsadane suna daga cikin kayan da Sameerah ta bata Winkakku.
A bakin titi taga motar Samira, shigewa tayi nan suka ni?i hanya zuwa yamma sai gasu a garin Abuja.
Zangon ba?i (Hotel) Sameerah ta kama musu, a dogon falon da ake zuwa a biya kuWi Sameerah ta haWu da wata Hajiya tana tare da yarinya ?arama da bata wuce shekaru ashirin ba. Ashe ita wannan Hajiya sune manyan memba na wannan ?ungiya ta mata masu maWigo. Sameera da girmamawa sosai ta gaisheta. Ganin hakanne yasa ?ar shuwa itama tayi saurin rusunawa ta gaisheta. Ai kuwa da fara'a ta amsa har tana taSa mata kafaWarta tana mata wani irin kallo.
"Hajiya Sameerah yarinya kika sake ne da wurwuri haka? "
Samerah tace.
"Wallahi kuwa Hajiya kamawa tayi. Ita waccan yarinyar ?asar suka bari da iyayenta kinji dalili. Amman har yanzu muna magana da'ita ta waya"
Hajiyannan tace.
"Nima kinga sabuwar Babyna rijista za'ayi mata bata daWe da shigowa hannuna ba. Ni kinsan ina da yara da yawa sai dai wallahi ba ?aramin caza mun kaina suke yi ba gasu da cin kuWi. Mujenku to kowa ya sha hanya an gaji. "
Shigewa suka yi ko wacce ta shige Wakin data kama.
A daren wannan ranar ?ar shuwa ta bambance tsakanin zare da abawa. Da bakinta tayi ma Sameerah al?awarin a wata sau Waya zata iya mallakama Babangida jikinta. Sabida taga yadda Sameerah duk ta gigice mata sai sambatu take yi mata jiki yasha gyara sosai gashi ko ina a jikinta ?amshi yake fesarwa har kuka Sameerah ta dinga mata da wasu irin tambotsan sambatu na tashin kai irin nasu ?an madigo ( wa'iyazubilla).
Washegari da misalin ?arfe tara su Yar Shuwa suka gama shiryawa tsab cikin ankonsu na lace mai matu?ar tsada, gwal Sameerah ta ciro ta saka ma Yar Shuwa a wuyanta da kunnenta.
"Kinga wannan sar?ar zinare ce na mallaka miki itace tukuicin daren jiya. Amman abinda nake so dake kiyi biyayya ga ?ungiya banda kuma fitar da sirrin ?ungiya waje yin hakan babban kuskurene. Kuma ?ungiyarmu in aka shiga ba'a fita duk tsanani. Akwai waWanda sukai yin?urin fita kinsan meya faru da biyar daga cikinsu? "
Tana maganar tana shafa wuyan ?ar Shuwa data Wauki wanka kwalliya tabi fatarta ta kwanta kyawunta ya sake bayyana. Kai ta girgiza domin san jin abinda ya same su. Duk da taji faWuwar gaba taji nadama na neman sakko mata. Tana bala'in son kuWi tana son zama babbar mace, amman tana tsoron abinda kaje kazo wanda bazaiyi mata kyau ba. Tana mutuwar son aurenta bugu da ?ari
"Uku daga cikinsu haukacewa suka yi. Biyu kuma har lahira suka mutu? "
Idanu ?ar shuwa ta zare tace.
"Hauka da mutuwa duka sabida sunce zasu tafi?"
"Ai ba wai tafiyar bace. Tsoron tunuwar asirinmu muke ji a ?asa najeriya muke, kuma da kika ganmu ko wacce mijinta sanannene, da damansu ?an siyasane wasu daka cikinsu kujera ce a hannunsu, matanma da yawansu siyasar suke yi. To kinga tonon asirinmu nasu ne.
Sannan saida suka mallaki gidaje, motoci, da zunzurutun kuWaWe sannan zasu ce zasu fita a cikinmu?
Kinga taso muje sauran bayanin zaki jisu a wajen taro"
?ar Shuwa bata gama tsurewa ba saida ta ganta a cikin manyan hamsha?an mata waWanda suka Wauki duniya da dukiya ba'a bakin komai ba, wasu da yawa tasansu a jaridu, da kafafen yaWa labarai, wasu kuma tasan sunan bata taSa tunanin zata iya matsowa inda ma suke ba
Hmmm a wannan rana ta zama memba ta wannan ?ungiya harda shaida aka bata, tare da saka hannu a wasu wuraren yarjejeniya.
Kuma su sababbin zuwa suka ji manufofin ?ungiya da aiyukan ?Ungiyar.
Ba tare da tunanin komai ba Yar Shuwa ta raftaSa hannunta akan yarjejeniya. A tunaninta kuWi sune komai a rayuwa..
Anci an sha anyi duk abinda ya kamata matane masu tarin yawa. Ita shugabar kungiyar ba zata wuce shekaru arba'in ba, ta samu duniya gata kyakkyawa tamkar ita tayi kanta.
Duk da matan ?ungiyar wasu irin zaSaSSun matane waWanda Allah ya hore musu kyau zati ga kuma kuWi dake maida mummuna ya zama kyakkyawa, ina kuma ga kyawawan ga kuma kuWi.
Atampopi supa_supa da takalma aka raba a wajen taron, taro fa sai dare ya ?are babu sallah babu salati.
Abubuwa da dama na ?azanta sun faffaru ba abu bane na daWin rubutu ba. Kuma ba abu bane da zanta bayyanawa wa'iyazubillah Allah ya kiyashemu taSewa kawai.

Babangida:.
Bashi ya farka ba sai azahar shima kiraye_karayen sallah ne ya tasheshi. Wanka yayi a gurguje ya wuce masallaci.
Daga nan bai dawo gidan ba sai dare.
A Wakinsu Mardiyya ya yada zango ya tarar sun tusa AWWa'u a gaba suna mishi faWa yana ta kuka.
Shigowarshi ce yasa sukai shiru, amman shi bai daina kukan fitar rai ba.
"Mardiyya menene ya faru? "
"Baba sata yayo a ma?ota kuWi masu yawan gaske fin dubu saba'in. Yama ci da yawa daga cikin kuWin sai yaune Malama take faWa mana"
Idanu Babangida ya lumshe maganganun Baba na shago ya shiga kaWa mishi ?ararrawa a kunnuwanshi akan su guji ranar da nasu ?a?an zasu dinga sasu magana, ko su hanasu bacci ma kamar yadda sukai musu.
A hankali ya zauna kusa da Aminu yana ?arema yaran nashi kallo sune yara mafi soyuwa a rayuwarshi, sai dai kashi ga Adda'u ya Webo halin sata. Yana ro?on Allah ya yaye mishi, kuma kada Allah yasa yaranshi su Webo halinshi ko na mahaifiyarsu.
"Bazan sake ba Baba"
Ya faWa yana kuka. Mardiyya ta shiga Waki ta fito da kuWi dubu casa'in da shida ta dan?ama Babangida ya saka hannu ya amsa.
"Ina ka Wakkosu a mayar musu dashi. Sannan Adda'u me kake so wanda bana muku, me zakayi da kuWin daka sato, shin a ajinku ba'a faWa muku sata bata da kyau bane? "
"Bazan sake ba nayi al?awari. Dama inaso in siya ma Ummi kayan abincine naga gobe zamu je wajenta"
Babangida baisan sanda hawayenshi suka sulalo ba, da sauri ya goge hawayen da dabara ba tare da yaran sun sani ba.
"Duk abinda kake son siya ma umminka ka tambayeni sai in baka ka siya mata. Allah yayi maka albarka tare da ?an uwanka baki Waya. Ina ka sato kuWinnan to? "
"A Wakin maman Hamusu mai kifi"
Baki Babangida ya buWe tare da cewa.
"To nawa ne duka kuWin daka Wakko Win? "
"Dubu Wari ne"
"To shikenan AWWa'u dan Allah ka kiyaye. Ke mardiyya zaki iya mayar mata da kuWinta ba tare data san an sata ba? "
Kafin mardiyya tayi magana yace zai iya shi a bashi suje da Mardiyyan.
Ai kuwa kuWi Babangida ya zaro ya cikace kuWin ya basu dubu biyu yace su siyo kifi.
Da haka wannan asirin ya rufu.
Yai musu sallama akan goben su shirya sai ya kaisu wajen Ummin nasu.
"Baba sun sake gida muma bamu san gidan ba. Dama ummi tace sai Baba Gaza yazo zai mana kwatancen layin"
Cewar malama take gaban Babangida ya tattake ya faWi haka kurum yaji hankalinshi ya tashi da ?yar ya iya magana.
"To shikenan in ya kwatanta sai in kaiku zanje in kwanta. "
?akin Ramatu ya shiga ya tarar da'ita a gaban kulolin abinci tana ta tubkewa da warwarewa bata sanma Babangida yazo inda take ba. Yayi sallamar yayi ya maya yaji babu amsa a tunaninshi ko tana can Wakin ma?ota tunda haka ta saba sai yaga ashe tana Wakin. Sai da yayi magana a kanta ta Wago da sauri suka haWa idanu.
"Lafiya kuwa Ramatu wannan wanne tunanine haka? "
Ajjiyar zuchiya ta sauke.
"Sannu da zuwa. Hmmmm"
Zama yayi suka gaisa ta zuba mishi shinkafa da miya da soyayyan sukunbiya, da jus Win kankana.
"Menene yake damunki Ramatu? '
Ya tambayeta cike da tuhuma.
" Wallahi bashikan da suke kaina suna da yawa. Ga Safiya zata yi aure dubu hamsin hamsin aka yanke mana mu mata nasan dana tambayeka zaka ce baka dashi. Bashikan da ake bina kuwa wallahi sunyi dubu Wari biyar koma fi"
Idanu ya zare, sai da ya kurSi ruwan kankana ya dawo daidai.
"Dubu Wari biyar ni kuwa ina na ganta, ai ko dubu hamsin Win bani da'ita gaskiya. Abinda zaki kula shine bafa ke kaWai bace ku uku ne. Shin inna baki dubu hamsin suma ina da hamsin hamsin da zan basu ne? Bani dashi ki ba Mama ha?uri kawai. ?an bashi kuma ke kika san yanda zaki yi dasu Ramatu ke da na baki jari masu yawa tun kafin ki tare. Yanzu haka ai na raba muku jari ke mai kike saidawa? "
"Bana siyar da komai tanadin haihuwa nayi da kuWin kanaso in haihu ?awayena suzo suna mun dariya ne? "
Mamakine ya ?ume shi magana wannan ya kasa sai ya mayar da hankalinshi kan abincinshi kawai.
Amman fa da tunanin sake gidan da akace su Sabuwa sunyi ya kwana. Ya kira wayar ?ar Shuwa kusan sau takwas duk a kashe ake ce mishi.
Kai kawai ya girgiza.
Da wannan aka wayi gari.
Sassafe sai ga matar da take bin Ramatu kuWaWe tazo tana neman yi mata tereren bankaWa a cikin gidan haya mai sha?e dam da mata, ga kishiyoyi.
Mrs Bukhari
Ubangiji Allah ya tashe mu lafiya ameen>?2? [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI
11





Ita akan dole sai an biyata kuWinta take ko kuma ta Webi kayan kuWinta.
A lokacin Babangida ya fito wanka kenan. Sauri sauri ya shirya ya fito ya tadda wannan mata tana rantsuwa. Ganinshi baisa ta risina ba sam.
"Baiwar Allah kiyi ha?uri ko biya biyar ne in sha Allah sai in miki. In kuma zaki bani wata shida akwai adashe da zan Wauka sai in baki baki Waya nawa ne kuWin naki?"
"Wai kuWina zasu yi Wari bakwai. Kuma wallahi ko biya biyu zaka yi mun bana so kuWina sunyi shekara narantse da Allah ko kuWina ko in yashe Wakinnan tas wallahi kasan Allah ?ar hau ce ni ta gaske"
Ai saita tuSe Wankwali ta ja Wamara mamanta suna sama suna ?asa tsabaragen jijjigar da take yi" Shima Babangida a ranshi ya aiyana
"Kura tayi lafiya lallai harmu za'a faWa ma hau, mu da hau Win inta gammu gudu take yi"
A zahiri kuma yace.
"To Allah ya kyauta. Tunda abun haka ya zama ke Ramatu sai ki barta ta kwashe kayan ayi mata ciko in kuma sun kai kuWinta shikenan."
"Haka zaka ce Abban mardiyya ta kwashe kayana in zauna dame ko gida kake son inje, ya ina da kishiyoyi zaka bari ayi mun haka? "
"To bani da yadda zanyi ban baki damar zuwa ko'inaba kuma na baki umarnin ta kwashe kayan in dai hakan take ganin zaiyi mata ba zata zubar mun da mutunci ba. Ga kuWin cefanenki ni na fita"
Saka kai yayi ya fice zuchiyarshi na tafasa.
Matan gidan ashe duk sun fito suna tsaye cirko cirko. ?akin su Mardiyya ya shiga ya kirawosu suka kama hanyar titi dan taran abun hawa.


SABUWA:.
Haka muka wayi gari a sabon gida cikin amince da jin daWi.
Mutuniyarku Labbai tana kichin tana ta tuyar ?wai.
Su Adama sabo da zaman tsakar gida yasa sun sakko ?asa sun shinfiWa tabarma a ?ofar Wakin Gaza. Su Uzairu zuchiyata anata brush a wajen famfo, magazine kuma yana zaune yana shafa kan Uzairu dake shan madara ( magen Gaza fa)
Mu?arraban Wakin Hauwa ma suna waje wasu da wanki suka tashi, Hauwa kuma sai gyare_gyare take yi.
Masa kuma yana zaune yana taya Aliya tsifa.
Raliya kuma gawayi take kunnawa a kurfoti, su Qamriyya kuma anata shafa hoda.
A hankali na sakko.
"Lolo barka da sakkowa fa. Kai gaskiya mun gode miki wannan gida munyi kwanan farin ciki sosai"
Cewar Raliya kenan. Layuza taja tsaki ta kawar da kanta.
Murmushi nayi na dubi Raliya wacce duk ta fice daga hayyacinta ta zama ?ar ?auye futuk ?afarta duk kaushi kaushin ya Webi annakiyar dauWa yayi ba?i abinka da farar fata sai ya fito sosai.
Raliya ya gida ya sabon waje? "
"Ga sabon waje nan wallahi ni dai jiya da ?yar nayi bacci balle na saba da Wakin jinka"
Dariya gabaki Waya aka kwashe dashi Uzairu zuchiyata harda tuntsurawa tsabaragen dariya.
Wannan dariyar yasa Gaza ya fito hannunshi da kofin shayi cike ga mummu?i a Wayan hannun.
"A lafiya dai Matar manya. Eh wallahi Sabuwa mai sabon aiki Babbar yarinya da tauraruwarta ke haskawa. Da gama takaba da aure, miji duka Wauka eh wallahi babu wani shege"
Zama yayi su Rahine suka baibayeshi ya shiga basu shayinnan da mummu?i.
Ana cikin haka Labbai ta le?o ta sama tayi kiran su Aisha suka sakko mana da abun karyawa.
Duk muka yi da'ira.
Wai Sama da Rita basa gidanne? "
Adama tace"
"Ita dai tayi mana sallama zata aiki. Shi kuma yana ciki yana baccin asara na rashin zuchiya"
?urum sai gashi ya fito.
"Ke Adama waya faWa miki baccin asara nake yi?
Wallahi ?waya nasha taimun karo ga gajiyar tu?in wurbaro. Ni kudu ma zan tafi kirsimeti ya kusa muje muci kasuwar balam_balo ko na samu na ragon suna"
Amman Sama ai gara ka zauna ta haihu kananan cikin ai yazo watan haihuwarshi tace ma ya wuce watanshi na goma sha Waya kenan fa kamata yayi ka kaita asibiti. Wanne kuma kudu zaka nausa yanxu ga cikinta da girman gaske tun yana wata biyar da ?yar take turawa fa."
Yana zare idanu yana cusa ?wai a baka yace.
"Bafa ki sani bane tajajje asibiti wallahi cewa akayi nan da sati in bata haihu ba aiki za'ayi mata. Shi yasa nake son lallaSawa in gudu in yaso in ?urar ta lafa nadawo"
Gaza yace.
"Gaskiya baka da hankali an samu matsala eh matar taka zaka kuikuyama wannan akuyancin eh? Wallahi babu inda zaka je dole ta haihu a gabanka in kuma so kake Wanka ya zama arne ai shikenan. Ke madamcy! Madamcy!! Fito muci ?wai matar manya ta Wauki nauyinmu"
Madamcy ta fito itama aka dama da'ita Sama yayi shiru yanata tunani ko tunanin me yake yi Allah masani.
Bayan mun karya duk muka watse muka shiga gyaran gida da kaye kaye. Ina shanya masa yazo yace.
"Sabuwa dan Allah Wakin mai gadincan dake bakin ?ofa in da hali a bani zanyo aure muyi zamanmu dan Allah Sabuwa.
Wallahi rayuwarce sai a hankali da kuka rabu da ganina kinsan Allah gadi nake yi a wani kamfani haka siddan akayi sata a kamfanin aka ?ala mun banji ba ban gani ba. Ke kinsan bana sata sai dai barni da iskancina kin gane? To Sabuwa naji labarin mijinki yana da kuWi dan Allah ki nema mana aiki a wajenshi ko rayuwar zatai mana sau?i"
Shiru nayi ina saurarenshi sai warin sigari yake yi bakinshi duk yayi duhu har dasashinshi ga tomtom yana ta tsotsa a mugun cake yake ya tsaya

13 / 28