Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   20 / 28

57K to 60K   out of 83.6K words

Gaza ne ya raba wannan dambarwar ya jawo Rakiya da Hauwa, ni kuma na ri?o Maigogul ni da Cicib Rakiya ta yaga mishi riga daga sama har ?asa.
"Haba Rakiya dan kawai Dattijo eh yayi aure shine wannan eh kuikuyamai Win da eh kike yi har waje eh shikenan a gidannan mu babu mu babu yin eh abu cikin sirri ne. Eh naji ana cewa namiji mijin mata huWu ne eh dan yayi aure eh Rakiya yanzu Maigogul kike kishi eh haka har kina kuka rabin raina, ni banga abunda yake tsinana muku ba da eh kuke wani sonshi Allah. Hauwa eh duka kuyi ha?uri dan Allah eh ku barshi haka ni kunga eh Kano zan koma kamfanin motocin Alhaji eh Zaidu zan dai dinga zuwa. Eh abinda kuke so ai zanyi eh muku in sha Allah. Shi kuma eh kuyi mishi Adda'a tunda yace Hajiyace ?ila shima yayi kuWi eh ko Allah zaisa ya kula daku kuskuren da aka aikata eh a gyara dan kurakuren maigogul da yawa, duk ba shi eh ya mayar damu ?an iska ba, jibi rayuwata fa yadda ta koma wai kuna tunanin daWi nake ji ne eh?
Haba uwargida an buga dake an barki, waye yace dake bake ba dan abu ta kazan ubanshi muma eh muce dashi bashi ba. Kece Uwargida a gidan Maigogul masoyiyarshi ta farko kuma uwar ?ayanshi manya eh kece fa rabin ran Gazanshi uban Rahine da Uzairu da Maigogul ?arami, da Rakiya ?arama eh Allah eh a huce a huce a huce eh a lafiya Rakiya kayi nayi, wuya a hannunki, wuya da zafi a zuchiyarki, eh Dattijo ya kuikuya miki a huje a huje uwargida ran gida Allah.
Uzairu zuchiyata yana tsugunne yana dariya Gazan shima kanshi Dariyar yake yi wallahi.
Ni dai lallaSa Maigogul nayi yace mun zai haura sama yayi kwanciyarshi, Cicib ma dole haka dai ya tafi babu arziki.
Har tsakar dare wallahi Rakiya basu dena artabu da Maigogul ba sai da yayi mata hauka hauka ya cire rigarshi ya maka da ?asa ya rungumeta sukaita gabzawa da taga wuta ne ta rabu dashi sannan muma muka sarara. Adama tace.
"Allah mai iko Allah yaso ki Rakiya bata san ke kika haWa wannan auren ba yau da sai buzunki wallahi zargi dai take yi, duk da in hankalinta ya dawo jikinta wallahi ki kuka da kanki, ke yau ni naga masifa ido da ido Lolo."
Labbai tana dariyarta ta mugunta tace.
"Rakiya kishi saita dinga nuna bata damu da Maigogul ba amman in abun kishi ya motsa nanne zaku gane kishinta"
Rahama tace.
"Dan Allah mu bar batun Rakiya da Maigogul ni wallahi murna na taya shi fatanmu Allah ya basu zaman lafiya shikenan fa. An tsufa gidannan jiya iyau. Yanzu Labbai menene abun yi yaushene tarewar musan wanne shirye _shiryen zamu yi ko ba gaskiya ba. ?arashen ginin gidan Cicib Win da Alhaji Zaidu ya Waura Gaza an gama ne? "
"Yau aka gama fenti ma, yace mun gobe iyalinshi zasu tare. Ni da so samu ne in tare nan da kwana uku sabida lolo ta samu damar Rakani nima in Allah ya soni sai kuga ya barni na rakata. Ai shima nasan yana can ana dambarwar tsiya dashi ya faWa ma matarshi wa zai aura kafin a Waura auren yace mun ya barota tana ta Wure_ Wuren ashariya ni dai ku taya ni da adda'a Allah ya bamu zaman lafiya kuma Allah ya dafa mun Cicib ya dena kawalci kamar yadda Maigogul yace ya dena. Nasan in ya dena zai dena wannan karairayar a hankali ma. "
Na yi dariya nace.
Amaryar Cicib zafa asha Amarci nan da kwana ukun ai sai a tare. Ya batun kayan wajen Rakiyan nawa tace ta bar miki dan kayan sunyi sabunta kuma sunyi kyau ko Adama? "
"Sunyi gaskiya dubu Wari biyu fa Rakiya tace ko sisi ba zata kankareba wallahi wai itama Wari da saba'in ta siyo nayi _nayi ta bar mata da saba'in Win kinsan kayi nayi da kuWi. To tukwane ma fa naga yau ta Wan ?a??aro harda su kulolin cin abinci da su plate ko Labbai? "
"E Cicib ne ya bani dubu sittin shine na harhaWa na siyo tunda babu a wajen Rakiya"
Ranar bamui bacci ba gaskiya haka mukaita hira muna musu harda shewa kamar ba dare ba. Sai da mukai sallar asuba kana muka kwanta bacci.
Cikin kwanaki biyunnan Maigogul da Rakiya sai rikici dan ma baya saurarenta haka zata tsaya a kanshi tai ta yaSo mishi maganganu wasu yayi murmushi wasu yayi dariya dai.
Mu kuma motar kaya muka kira aka lode kayan Labbai muka wuce harda Hauwa da Baba Laraba mahaifiyar Tsahare itama Tsaharen jiya tazo tare da su Rakiya ?arama duk muka Wunguma har da su Madamcy dasu Rita zuwa gidan Labbai.
To nanma har muka kammala jere wallahi Maman Shafa bata dena zage_zagen wai anyi auren cin Amana ga gidannan Labbai tazo taci uwar da zata ci. Sai da ma suka hau sama dasu Adama suka duro.
?aki Waya Labbai ta samu amman babbane gaskiya sosai. Gadonta ?aramine bai kai shida da shida ba (6by6) ?aramine gaskiya amman mai kyaune sosai, sai doguwar kujera da ?ananu biyu, sai sib Winta mai ?ofa takwas bango Waya ta cinye tas kuma duk da haka mutum huWu zasu iya jeruwa suyi sallah a filin tsakar Wakin.
Mu dai ko ruwa bamu sha ba nice ma na fita na siyo mana Awara muka ci muka kora da ruwa. Bamu muka bar gidan ba sai bayan magriba muka shiga gida duk a gajiye sosai.
Washegari da magriba muka kai Labbai Wakinta taci kwalliya da kayan dana siyo musu daga Dubai dan jiya Winkinnu ya iso daga kano.
Maman Shafa dai babu yabo babu fallasa haka muka kai mata Labbai Wakinta.
"Ba shakka aure ba Waya ba ba biyu ba ai dole ki shigo ido a buWe maciya amana"
Labbai tayi murmushi kawai.
Maman Shafa ta zagemu tatas.
"Maman Shafa bawai tsoronki muke ji ba da kika ga munyi miki shiru ba. Aure kike yi itama aure tazo yi. Kinsan dai in tijarane baki kai Labbai ba, in kin so ku zauna lafiya in baki so ba ku kashe kanku. Baba ku taso muje saida nace muku kada a wani kawota Wakin Maman Shafa amman baku ji ba"
Cewar Adama kenan da take ta ruwan zazzaga. Baba Laraba tace.
"Allah ya kyauta Ku taso muje dare nayi. "
Mi?ewa muka yi muka shiga da Amarya a ?ofar gida muka tadda Maigogul da Cicib Maigogul na mi?a mishi ledar kazar amarci.
Tare muka juya da Maigogul zuwa gida.
Haka dai al'amuran biki aka shiga nawa.
Ana jibi tarewata Alhaji Zaidu yake sanar dani zamu yi ba?i Hajiya tayi mun akwati tace zasu zo a kawo akwatin da taso azo da'ita amman dai ta wakilta su Hajara da wasu daga cikin ?awayenta zasu zo.
Dawowata daga wajen Baba malam kenan ma, na sake zuwa na sameshi a makaranta ya dafa kaina yaita mun adda'a wannan Dattijon arziki har kuWi masu kauri ya bani kuma yayi mun al?awarin zai saka Wawo ya kawo shi, kuma zai turo Malama ?arama da'ita za'a kaini har Wakina.
Tunda na kashe wayar sai naji jikina yayi sanyi, su Sadiya kuwa tuni aka aikesu kasuwa siyo kaji, muka tanadi kuWin tukuici dan Alhaji zaidu dubu Wari biyu ya turo yace a basu duka.
Kaji bakwai aka soya musu jar suya Maigogul ya gwafe yayi musu, anayi Rakiya na habaice habaicenta, sai cincin mudu biyu da Adama tayi, sai ?ar Jallop kaWan da Maigogul yayi musu, harda wata shinkafa mai ?wallo da Maigogul naga yayi ya kuma tsoma a ruwan ?wai ya soya kamar yam bolls amman na shinkafa yayi musu dan fita kunya.
Maigogul sai shige da fice yake yi yana tambayar ba?in suna ina yaci ado yayi kyau dashi.
Ai kuwa suna shigowa Dutse Hajara ?anwarshi wacce suke Waki Waya sai ta kirani. Maigogul ne ya rubuta mata adireshin unguwa da lambar gidan ya tura mata.
Ni kuwa naci kwalliya na saka wani babban lace, na Wauki ?aramin Wankunne da sar?ar gwal wannan nawan na saka Sadiya tayi mun kwalliya sukaimun Wauri. Ana kiraye kirayen Sallar la'asar suka shigo mota biyu suka ciko cike da mata ?osassu ji?a??u kuma ni dai daga taga dana hangosu da irin gwalagwalan dake wuyansu da kunnensu duk saina tsure.
A haka su Adama suka sakko aka hauro dasu sama da akwatunansu har uku sha?e wallahi da kaya ha???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?r akwati guda tayi mun na kayayyakin bacci masu kyau, ga akwatin dogayen riguna, sai akwatin zannuwa da lesuka, ?aramin akwatin kuwa sar?o?ine fashion harda na azurfa babba sosai.
An bubbuWe kaya anata san barka tare da godiya, Maigogul dai ya shigo sun gaisa ya gabatar da kanshi kana yayi shigewarshi ciki Allah ya soni.
"Babu komai ai Hajiya tafi haka kuma mutum ce guda har da Sari"
Wata zabiya ina jinta tace tana son ganin Amarya. Adama tayi carab tace.
"Gashi bata nan bata daWe da fita ba anata hidimar biki"
Ajjiyar zuchiya na sauke. Yanzu na gane dalilin Alhaji Zaidu da yake cewa in sai kaya mai tsada sosai, sannan ya zaSamun kayan da zan saka in akazo Waukana.
Wannan kajin da su ruwa a mota aka saka musu Adama ta basu tukincin dubu Wari biyu har saida motarsu ta bar cikin layin kana na sauke ajjiyar zuchiya tsorone ya kamani ni dai
Ina jiyo su Adama anata hayya_ hayya. Nima fitowa, Maigogul sai Waga zannuwa yake yi. Zama nayi ina daga zaune suna ta kallon kaya ana mamakin Hajiya wacce iriyar macece.
"Lallai lolo kinfa shiga babban famili mai girma. Ke kinga yadda wasu mata su uku suke ?arema gidannan kallo suna yamutsa fuska kuwa? Gashi sun sha gwala_gwalai, sun raina gidanne, to waWannan da gidanmu na dane anya zasu iya shigowa ma kuwa? "
Cewar Rahama. Ni dai jikina a mace mus yake sai naji duk na raina kaina sosai wallahi.
Wayata ce ta sake kuka. Da sauri na shige Waki a ciki na samu Uzairu zuchiyata yana ta ninke kayanshi da yayi wanki, shima sai shirye_ shirye yake yi bikinshi da Felisha yanata ?aratowa.
Bayan na Waga wayar da sallama ya amsa mun sai yace.
"Ashe su Hajara har sun kamo hanya? "
E wallahi sun tafi ai"
"Tace mun baku haWu ba kin fita ni kuma nasan kinanan menene matsalar Shalelena tsoro kike jine ko menene uhm? "
?an murmushi nayi kawai nace.
Ba tsoro nake ji ba. Nadai fi so sai ranar da na tare a cikin gidanka tukunna zasu ganni ai yafi ko? "
"Uhm hakane hakanma babu laifi Shalelena.
Yauwa ?awayen Hajiya su nawa ne akazo dasu? "
Sai da yayi murmushi yace.
"Su uku ne ragowar duk danginane kinsan fa nace miki muna da yawan gaske. Biki suna ba'a rabo dashi yanzu haka ?anwata Fatima ta haihu yau kinga ?ila dake za'aje suna ma"
A raina na aiyana ?awayen Hajiya sune mata ukun da Adama suka ga suna ?arema gidanmu kallo suna taSe baki.
Shima dake hidimace a gabanshi sosai gaskiya bamu yi wata hira mai yawa ba.
Washegari da Adama, da Labbai Amarya da ango ya kawota sassafe, sai Hauwa, da aminiyar Hauwan, da Uzairu zuchiyata da Magazin, da Rita da Baba Laraba suka nufi Kano kai tsaye gidan Hajiya Balaraba suka wuce sabida Maigogul yace ita yaba kuWin kayan Wakin nawa yace ayimun abinda ya dace. Sabida tana da kamfani da take da ?wararrun kafintoci da kayan aiki show room gareta ?ato wanda take siyar da duk wani abinda ya danganci gida ?atuwar plaza ce har kayan Kitchen duk tana saidawa, katifa, fulo, kafet, su tv da komai daya shafi ?yale_?yalen gida tana yi. Sanna tana yin intiriyo dakwareshon
Dan ta kirani take tambayata ko akwai kalan da nake sone nace na bata wu?a da dama..
Daga nan dake shatar bus su Adama suka yi sun tafi da ragowar komatsaina. Rahama kuma da su Madamcy su sai gobe zasu bi tawagar kai Amarya kuma. Ni dai sai naji komai da kowa sun fice mun akaina. Yadda kuka san in gudu wallahi.
Gashi gobe akwai Dina da za'ayi anan duk Soye Soyen da nake yi na rashin son a ganni ya kau dole kowa yaganni.


KANO:.
Su Adama sun isa Sabon gidan Hajiya Balaraba. Anan suka ga aikin girma da karamci sunci kaji sun goge wuya dashi.
Bayan sun huta da yamma kuma suka nufi gidan amarya motar kaya tuni tayi gaba su daga baya suka isa.
Motocinsu a harabar gidan suka ajjiyesu dake tsakar gidan akwai yalwa sosai dan motoci suma kusan biyar suka samu a tsakar gidan banda motar kaya da su Uzairu zuchiyata suke ta saukewa da Magazin.
Sun tarar da taron mata masu yawa a tsakar gidan anata musu sannunsu da zuwa Musamman da akaga Hajiya Balaraba a cikinsu harda aminiyarta itama kuma sananniyace a idanun al'ummar jihar Kano dan har yau har gobe ana damawa dasu ta fannin siyasa da wayar da kan mata musamman na karkara.
Hajiya Laure ce ta jagorancesu zuwa ciki dattijuwar arziki wacce Alhaji Zaidu yake bi ita a Ghana take aure bikinne ya kawota.
Falon Hajiya suka soma shiga dan?am yake da ?an uwan Hajiyan har babu masaka tsinke da gani itama daga babban famili ta fito.
Sai a falo na biyu su Adama suka taddasu ita da ?awayenta amintattunta.
"Ah Hajiya Balaraba kune a gidan maraba sannunku"
Cewar Uwargidan Alhaji Zaidu dan tare suka yi makarantar kwana da Hajiya shirine dai basa yi har suka gama makarantar ko ga miciji basa yi.
"Wallahi kuwa nice. Mune muka kawo kayan Amaryarki"
Sai da suka yi turus tukunna amman dake macece mai wayau sai ta saki fara'a tare da cewa.
"Allah sarki ashe kinsan bazawarar da Alhaji ya auro Hajiya Balaraba. To bari a baku kin Sarayin nata. "
"To shikenan. Yarinya kam ai ?ata ce mahaifinta nake Aure. Kinga wannan ma Kishiyarmu ce duk iyayenta ne mu waWannan fararen kuma yayyinta ne"
Ta nuna Hauwa wacce ta sha leshi da Wan sar?a da Wankunnenta na azurfa wanda Layuza ce ta ara mata. Leshin jikinta kuma Loloce tayi musu anko da Rakiya. Akan ankonnan ma Rakiya ansha artabu da'ita ta dai yi rantsuwar itafa ba zata saka ba.
Hajiya da kanta ta tashi cikin tafiyar ?asaita ansha kayan ado taje ta buWe musu Sarayin Amarya ta dam?a kin a hannun Hajiya Balaraba.
Nan suka shiga aikinsu ma'aikatan kamfani kusan su sukai aikin rabinshi da kwatanshi su suka san a inda zasu ajjiye komai cikin tsari
Su Adama a gyaran Kitchen da wanke banWaku aka barsu. Su Uzairu zuchiyata ma bafa a barsu a baya ba sam.
?arayin na lolo yadda yake da farko dogon hanya zaki shiga itace a farko Corridor kenan. Daga nan zaka murWa ?ofar da zata sadaka da babban falo a cikin falon akwai Kitchen da wajen cin abinci daining kenan, sai Wakin ba?i da banWaki a ciki sannan akwai ?afar bene da in aka hau akwai ?aramin corido a inda Wakunan suke ciki guda biyu Waya daga ciki shine akaima lolo jeren kayan gadonta, Wayan kuma kafet aka malala mata sai wata doguwar kujera guda Waya da aka saka mai suffar L da teburinta.
Gaskiya gidan lolo yayi kyau matu?a gaya.
Kafet da labule da ta siyo a Saudiyya a uwarWakinta aka saka mata.
Yadda aka tsara Sarayin da yadda Hajiya Balaraba ta zaSa mata kayan kece raini babu raini tattare da Sarayin duk kuma wanda ya shigo ha?i?a yasan iyayen Lolo sunyi mata bajinta. Ga gara mai yawan gaske da aka haWota dashi. Dukka fa wannan ?o?arin Alhaji Zaidu ne dan Maigogul sau uku yana kiranshi yana sanar mishi kuWin kayan Waki bazai isaba. Shima ya fita da fitarshi ya Winka kayayyaki na alfarma waWanda zaici Amarcinshi dashi ya kuma Winka kayan da zai sa ayi dinar Lolo. Ya dai yi ?o?ari ya sai kayan abinci basabamba ya raba ma Hauwa da Rakiya abinda bai taSa yi ba a rayuwarshi ya siyo ya jibge. Ko a da can kafin su tara iyali da yake ?o?arin ganin ya taimaka awo dai suke yi. Gwangwani uku huWu na shinkafa da wake daga baya ma ya zirarama idanunshi kwalli.
Hajiya Ta saka an kawo abincin masu jere shinkafa da miya da kaji manya manyan yanka aka kawo musu sai salak da lemukan kwali da ruwan gora, su cincin sinasir alkubus nakiya duk an kawo musu fanteka fanteka na nuna isa da son bajinta da burgewa.
Godiya su Adama suka yi nan Labbai ta shiga rabon abinci dama a gajiye suke tulus suka ci suka ?oshi da Waya da Waya dangin ango sukaita shigowa suna santin wajen da gaisuwar ba?i.
Basu suka baro gidan ba sai wajajen goman dare a hakanma sun tawo da kayan abinci rigi_rigi wanda aka kuma lodo musu na dare.
Har dai suka tafi basu haWu da Hajiya ba sakamakon gidan ya kuma Winkewa da Jama'a.
Suna komawa gida sai bacci an gaji washegari gari kuma itace ranar tarewa.
Hajiya Balaraba sunyi waya da Maigogul yake sanar mata Alhaji Zaidu yace Rano za'a wuce da Lolo kai tsaye. Akwai iyaye acan da za'a kaita ayi mata nasiha lafin a wuto kano.
Sunyi dashi akan su Manyan zasu wuce Ranon in yaso ko su Adama sai su wuce gidan Amarya su jira zuwansu.


Mrs Bukhari ce
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: https://chat.whatsapp.com/I7uDGV8V2DQDVS5RHRi0St

https://wa.me/message/QBXV2PDE2Y3CI1

Kina neman inda zaki samu ingantattun kayan gwanjo wato thrifts ma yaran ki kwantar da hankalin ki yar uwa oumokasha thrifts store ta kawo muku kala kala kaya na fita kunya akan farashi mai sauki tun daka kan overalls jumpsuits bodysuit bibs jeans tops blouses da sauran kaya na kece raini from 0 to 15 years
Muna garin abuja koh kaduna
Muna tura kaya ko wani gari da yarda Allah quality da sauki shine taken mu

MRS BUKHARI
17








Lolo
Ni dai da zazzaSin tsoro da fargaba na kwana ga gidanmu ya cika ya batse da ?an unguwarmu na da harda Maman ?ar Shuwa tazo tana Wakin Hauwa duk da ta tarar abokiyar gulmar tata batanan amman hakan baisanya ta tafi ba.
Sau?inta Waya mutane sunyi yawa kuma ranar ta farin cikice tabbas da yawan waWanda suka zo bikin duk gulmace kawai

20 / 28