Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   7 / 28

18K to 21K   out of 83.6K words

gama da'ita.
Shikenan zaki tsinci kanki cikin irin mutanen da babu abunda yake girgizasu a duniya.
Ai in dai muna rayuwa mu ayyana komai ka iya faruwa in muka yadda da haka kamar yadda muka yadda mutuwa da hisabi gaskiya ne sai kiga mun zauna lafiya."
Shiru yayi yana nazartata.
A hankali nake jin wata nutsuwa na sakkomun abun har mamaki ma ya bani.
Numfasawa yayi yace.
"A yanayin da jikinki yake ciki akwai haWari a faWuwarki. Ita ?afa da kike gani ana tattakawa kaje inda kake so a lokacin da kake so. Baka gane asalin amfaninta da gudummawar da take badawa sai ranar da ka tsinci kanka a kwance baka da ?afafun dogarawa. Bazance ?afa itace komai ba tunda akwai idanu da ?wa?walwa mahimmancinsu suna da yawa.
Sabuwa ki daure duk wani tashin hankali ke da kanki zaki guje shi. In a cikinshi kike rayuwa kiyi yin?urin ?aurace mishi. In hakan bazai samu ba kuma kiyi ?o?arin zama dashi a haka ba tare da ya cutar dake ba.
Sunana Dr Rabo nine terafi Winki ina fatan zaki kasance cikin farin ciki"
Mi?ewa yayi ya fice ajjiyar zuchiya nannauya na sauke na tada kabbarar sallah ina daga zaunen na shiga rama salloli.

ALHAJI ZAID

Fita suka yi har harabar asibitin suka samu ?eSaSSen waje suka tsaya.
"Alhaji Baba dama dangane da tarewar Shalele ne nake son ince kada a takura mata a barta da kanta ta fitar da lokacin da take ganin ya dace.
To magana ta biyu dama inaso. A nemi wani ?aramin gidan haya a kamashi baki Waya inaso gidan zan mishi gyara ne kafin lokacin biki in sha Allah ko kuma ince zan rusheshi, kuWin hayar zan biya in sha Allah"
"Alhaji kace zaka mana gini? Alhaji mungode mungode sosai. "
Tsugunnawa maigogul yake shirin yi bakinshi tamkar ya yage tsabar farin ciki. Da sauri Alhaji Zaidu ya taroshi.
"Kai haba Alhaji Baba ai ku iyayene duk abinda akayi muku ladane ka cancanta ne. Sannan kana da paspo ne Alhaji Baba? "
Idanu Maigogul ya zare cikin zakwaWi yace.
"Ina da paspo na Alhaji"
"To shikenan Abinda za'ayi zaku tafi umara da kai da ita Shalelen ka rakata taje tayi addu'o'iinta ko zuchiyarta zata yi mata sanyi, in kuka dawo ta nutsa.... "
Rungumeshi Maigogul yayi ?am tamkar zai Sallashi dan jin daWi da murna ta ?in ?arawa ya dinga sumbatar hannayenshi
Godiya Maigogul ya dinga zubawa harda shesshe?ar kukan farin ciki da murna.
"Wai Alhaji me zance maka ne, ha?i?a ka Waureni da jijiyoyin jikina abinda zance maka kamar yadda ka faranta mun kaima Allah yayi maka haka. Ubangiji Allah ya raya maka Haula"
Maigogul har bakin mota ya rakashi kuWin hayar ya dun?ulo ya bashi, da wasu kuWaWen daban na hidimar asibiti. Har saida maigogul yaga Sacewar motar Alhaji Zaidu kana ya sauke hannunshi daga adabon da yake yi mishi.
Wayarshi ya ciro yana zumuWi ya kira cicib a waya.
"?awata ya akayi ne? Ka ganni gida zamu sake notis na rashin daraja aka bamu. Gidana da nake ginawa kasan na rufe Wakuna huWu falle falle babu dai daSe a Wakunan, nagaji da turajar masu gidan haya da irin tozarcin da suke yi mini can gidan zamu koma yanzu haka mota Webe mana kayanmu take yi"
"Cicib kaya ya tsinke a gaSa. Bani ragowar Wakunan mu shiga kaji akwai labari in muka haWu gidan nawa ma rushemun za'ayi kaga in Allah ya taimakeka kaima a jikin mijin lolon zaka samu kuWin ?arashe wannan ?addararren ginin naka da ya?i ci bare ya cinye. Har umara yace zamu tafi ni da Lolo"
Ihu cicib yayi harda buga cinya yace.
??awata a ina zamu haWu to. Kun kwashe kayan naku ne? "
Dariya suka saka Maigogul yace..
"Yanzu zanje gidan mu tattare komai zamu haWu kawai a can gidan naka ?awata nima in Wana abun naku na ?an Daudu.
Tabb haihuwa ashe dai zataimun rana tabbb.
Mrs Bukhari ce


Sai mun haWu gobe
[10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: Shafi na shida

Babangida:.

Yana tubkewa da warwarewa sai jiyo muryar ?ar Shuwa yayi tana faWin.
"Ko sama da ?asa zata haWe bazan taSa yadda Sumayya taga logona ba wallahi"
Idanu Babangida ya zuba mata ya kasa cewa uffan.
Duk wata da?i?a yana mai nadamar aurenta da yayi ta shigo cikin rayuwarshi.
Ko da yake hausawa na cewa mugu baya cika mugu in bai ma kanshi da kanshi mugunta ba.
Wallahi a wannan lokacin baya jin ko Wigon sha'awarta ko sonta yana dai kawai dannewane yana mu'amulantarta ba tare daya nuna mata ba.
Wallahi yasan da ba dan aurota da yayi ba da Sabuwa zata yafe mishi ?ila da yanzu tana Wakinta a zaune"
"Jannaty inata magana tuntuni fa"
Ya jiyo muryar ?ar Shuwa. Jannaty inta ambaci wannan sunan sai yaji tamkar ta watsa mishi ruwan narkakkiyar dalma. A ?o?arinshi na son kawar da damuwar ya juyo yace.
"Maikika ce Sabuwata? "
A zabure ta mi?e zaune kanta ya sara mata sosai amman tsabar masifa na cinta ko zafin ciwom kan bata ji ba sai zafin kiranta da suna Sabuwa da yayi.
Ganin yanayinta yasa ya tuno da suSutar bakin da yayi na kiranta da suna Sabuwa"
"Ka kira sunanta a mafarki, ka kira sunanta in muna mu'amalar aure, kana ka kira sunanta a matsayina. In na bacci kace mun baka da ikon mallakar kanka, shima yayin mu'amala kace baka sanin kana faWa to wannan fa? "
Ta ?arashe maganar cikin shesshe?ar kuka.
A Wakin Sumy a daren da washegari zai baro Wakinta saida haka ta faru a tsakaninsu. Ranar kwanciyar auren da ba'a gama ba kenan ta hankaWeshi saida ya faWo. Yau gashi ya maimaita inama Sabuwa ta yadda su gina Sabuwar rayuwa mai ingancin da sai duniya ta buga ma ma'aurata misali dasu, sai sun zamema dangi da jama'ar gari ababen koyi sai dai kash ko da ta amince shari'a ta riga ta raba wannan aure har sai Sabuwa tayi wani auren ta fito. Inya tuno Sabuwa watarana dole ta zama matar wani saiyaji kamar ya lumama cikinshi wu?a yanaji a jikinshi zai iya rasa ranshi in Sabuwa ta auri wani.
"Ki taso mu tafi gida"
Yana gama faWin haka ya saka kanshi ya fita ba tare da ya juyo ba. Allah ya sani yana jin zafin ?ar Shuwa kuma yasan zaici gaba da jin zafinta abadan muddin zai buWe idanunshi ya rufe ya ganta. Ga haihuwa matanshi biyu duk ciki garesu ai dole ya Wauki matakin tsare iyali sabida halin rayuwar.
Har suka isa gida basu yi magana da juna ba sam ko wanne da abinda yake sa?awa.
Suna shiga gidan aka shiga jajanta musu, shi dai yana kaita Waki ya fice a gidan ya nufi unguwarsu kawai.
?ar shuwa tana zaune suna waya da Sameerah tana sanar mata halin da ta shiga, ga taron Abuja sai ?aratowa yake yi tarone na manyan mata tunda wasu daga ciki mazauna ?asashen ?etare ne amman wannan taron basa wuce shi sam tunda shekara_ shekara akeyi, kuma su tasu harkar a ?ungiyance suke yinshi akwai abubbuwa da yawa da Sameerah ta rufe ma ?ar Shuwa sosai.
Shigowar Jamila da Kulu ne yasa ta datse wayar. Suna zama wayar Jamila ta soma ruri.
Matsawa tayi ta dinga no?e muryarta tana kashe idanu dai ?ar Shuwa tayi kasa?e tana kallonta har saida ta gama.
"Jamila sabuwar soyayya ce ta tsikareki Baban Musba Win ake kashe ma murya haka? "
Dariya Jamila tayi suka haWa idanu da kulu suka tuntsire da dariya.
"Ha'a lafiya kuwa? "
Jamila tace.
"Wanne Baban Musba ana zaune ?alau. Ni da Alhajina nake waya ya shigo gari shine nake lallaSashi sai gobe da sassafe zan iya zuwa mishi dama gobe Baban Musba zaiyi lodi zuwa Inugu. "
Baki ?ar Shuwa ta ri?e.
"Jamila wai dama ashe ?ar hannu ce kema matarnan shine duk wasu abubbuwa na ?awa sai ki fito dashi tsakar gida kice mijinki ne yayo miki tsarabarsu? "
"Uhm kinsan Allah ni nake yima kaina komai. Ba mazajen yanzu basa iya sauke nauyin iyalansu ba? Kuma ko sun ganki da kuWi suka tambaya Waya biyu da kince sana'a kike yi sai kiji baki gum ba?. Nifa mitsiyacin mijina inya tashi dawowa ko lemon totuwa baya ri?owa. Idan ya tafi sai yafi wata guda bai waiwayoni ba. Nera dubu ashirince yake bani ni da yara uku.
A ciki zanyi awo, a ciki zansai kalanzir, aciki zansa mai da maggi, kayan miya, kifi ko nama, a ciki zan sai ruwa, wani sa'in har kuWin wuta. Shin zama zanyi talauci ya kasheni, ko kuma in zama bazawara ana zinWena a unguwa?"
Kulu tace.
"Uhm dani da'ita duk fa hakan take. Kuma ke kanki da halama kin shiga sahu dan munga sai gyare_gyaren Wakinki kike yi kinyi ma abokan zamanki zarrah"
?ar Shuwa tace.
"Ai saina ma haihu zanyi sunan da sai kishiyoyina sun gane ruwa ba sa'an kwando bane wallahi. Kuma inanan kafin suna saina sake komai na Wakinnan nawa ya koma sabo fil. Ashe dai sirrin kenan Kulu ke da Jamila kullum shar daku?
Jamila tace.
" Wai kinsan wa ya Waurema Kulu ?un?uru kuwa? Baban Shafa ma?ocin Wakin Ramatu kishiyarki fa"
Idanu ?ar Shuwa ta zare tace.
"Baban Shafa na gidannan wai? Tabbb ashe da Maman Shafa zata sani da sama da ?asa ta haWe tabb. Ni bama wannan ba wanne malaminne yake baku Sa'a ne. Nifa wallahi mijinmu mugun taurin kai gareshi asiri baya kamashi sam. Gashi da mita da saka idanu. Sannan ga matsalar da nake fuskanta kan tsohuwar matarshi kunsan ko mu'amala muke dashi sai kuji yana ambaton sunanta. Ga matsalar Sumayya wannan abinda tayi mun wallahi bazai tafi a banza ba sai nayi maganin ?ar banza"
Kulu tace.
"Ke na taSaki da alkhairi. Muna da boka a hannu duka Wauka abu ma in bazai yiwu ba shi baya cin kuWinki zai tsage miki gaskiya. "
"Yaushe zaku kaini dan Allah? "
Jamila tace.
"To ni gobe ina da fita kin dai sani. Amman ga Kulu ko gobe ai sai kuje. Amman fa ki tanadi kuWaWe dan wallahi aikinshi kinsan muguwar tsada? To akwaita ?an siyasa sun lalatashi da manyan kuWi. "
"KuWin bazai zama matsala ba inaso a rufe ma Baban Fati baki ne. Sumayya kuma sai ta zama bola a gidannan in sha Allah"
Sun jima sosai suna tattaunawa sune har la'asar sakaliya kafin suka tafi dama haka suka saba zama su shantake ko wanne Waki suka shiga.
Daga wannan ranar aminci da yadda da juna ya samu gurbi a zukatan waWannan shaiWanun mata ukun.

Babangida:.
Gidan malama Babba yaje yayi kwanciyarshi zazzaSine kau a jikinshi a duk lokacin da tunanin sabuwa da son kasancewa da'ita ya motsa mishi ciwo sai ya kaishi ?asa. Wajen malama Babba yake gudowa yazo yayi kwanciyarshi. Yanzu ta Salla mishi fanado ya haWiya.
Yana kwance a doguwar kujera Sa'a ta shigo tana ta kururuwa da kwaroroto. Kudidi na biye da'ita.
"Wai Sa'a lafiyanki kuwa?"
FaWin malama babba"
"Ina lafiya Baba malam ne ya kira Baban yara suka tsaida lokacin auren waccen shegiyar yarinyar wai nan da shekara guda. Kuma kiji malam ya nema mata gurbin karatu a jamila Sangaren islamik sitadis. Abinda mu bai yadda munyi ba bai jawo yaranmu ya basu koyarwa ba duk sai mardiyya ita kaWai ya Waukaki yaran abun har yayi yawa. Gurbin karatu a jami'a fa"
Babangida ya mi?e zaune yace.
"Sa'a kada ki sake ki sake kira mun yarinya da shegiya dan nine ubanta shege kuma wanda baida ubane ita kuma mardiyya nine ubanta. Idan rayuwata da duk abinda na mallaka zai salwanta zan bata kariya ina bayanta yana da kyau ki ri?e mutuncinki sabida na lura baki san abinda ake kira kawaici ba sam."
Ba Sa'a ba har malama Babba sai da suka shiga Wimuwa Wakin yayi tsit anata kallon Babangida.
Da sauri Sa'a ta mi?e tana shirin marinshi yayi carab ya ri?e hannunta ya matse jikinshi har rawa yake yi ya ?ura mata idanunshi da suka rine.
"Ni kake ri?ema hannu Babangida shaye _shaye ka koma kome? "
Murmushi yayi daya tuno sanda yake jifan Sabuwa da irin kalmar sak.
"Ba shaye _shaye nake yi ba amman ki sani akan mardiyya zan iya rungumarki mu yi mutuwar kasko a kiyaye taSamun ita. Sannan tunda dai Baban yara ya amince da auren ai shikenan. Har cikin raina bazan so Wiyata tayi auren ?as?anci ba domin zumunci zai iyayin lalacewar da zato bai zata ba. Sa'a bana jin zan iya kawaici ki ci mun zarafin Wiya, kuma wallahi ba zata zama borar miji da dangin miji ba. Sannan wallahi in labarin asalinta ya fito ta bakin ki har abada ni dake"
Shirin fita yake yi. Malama tace.
"Dawo Baba me yayi zafi. Dawo ka zauna nace. Ke Sa'a menene haka muna zaman zamanmu kinzo kin hautsina mu akan abinda kika san tun yarannan suna ?anana aka haWa, yaronnan ba daWi yake ji ba yanzu na bashi magani ya haWiya fa. Baban yara zai?i bin umarnin Malam ne a matsayinshi na almajirinshi?
Kai kuma Baba kayi ha?uri duk a taru a rufa ma kai asiri tunda malam ya matsa kasanshi da kafiya."
Zama suka yi Sa'a tana faWin har gaba da abada ba zata so Sabuwa da zuriyarta ba.
Kuka ta fashe dashi tana faWin.. "
"Ni wallahi an cutar damu me yasa Sauban aka zaSa ma Mardiyya ba'a bata wani ba. Baga yara maza a Wakin kudidi da Wakunan su Wawo da su Bashir ba me yasa sai Sauban? "
Kudidi tace.
"Allah mai iko. Ni wallahi zanje in tari Baba malam da batun a haWata da Surajo na wajena dama ya kusan kammala jami'arshi ta madina in ya amince wallahi ko gobe a Waura. Sa'a mardiyya fa bata da laifi cikin wannan lamarin. Inma akwai fa to wannan shashashan shine mai laifin."
Babangida yace.
"Ba Surajon da zata aura. Wallahi Sauban Win muke so sai dai ita Sa'an ta mutu"
Kawu Manga ne ya shigo ya zauna tare da cewa.
"Zancan Surajo baima taso ba Kudidi Allah yayi miki albarka zamu ce kawai. Kai kuma ga Sadakin Wiyarka Malam ya biya nera dubu Wari da hamsin za'ayi bikin da wuri in sha Allah gudun matsala da ance nan da shekara to labarin ya canja. Ke kuma Sa'a zaki gane Malam kika taSo wallahi, yana can yana fishi dake sosai tashi ki fice a gidannan mutuniyar kawai"
Sa'a fita tayi tana kuka. Babangida ya karSi kuWin ba dan yana so ba sai dan rashin zaSi kawai
Malama Babba tace.
"Ai shikenan wato shi Malam tsaurinnan nashi yayi yawa ace bazai iyaye su zaSa ma Wansu matar aure ba wai dole ni sai Malam ya kasheni da ba?in ciki ne? "
Kallonta Babangida yayi tana shirin zubar da hawaye. Idanun da suka haWa taga idanunshi jawur yasa ta fasa kukan ta kuma ji kunyarshi ainun. Kanshi kawai ya sauke yana jin shima kamar ya zubar da hawayen.
Sun jima sosai suna tattaunawa Babangida dai sai da yayi sallar isha ya hau mashin Winshi ya tafi gida.
Kai tsaye Wakin su Mardiyya ya shiga ya taddasu suna ta karatun Qur'ani mai girma. Shiga yayi sukaita rare ?ira'a cikin suratul ali imran
Idanunshi suna rufe sun taru da hawaye suke wannan karatun sun daWe sosai suna yi kafin daga bisani suka gama.
Suna shirin yin adda'a wayar Mardiyya ta yi ruri Labbai ke kiranta. Da zumuWi ta Waga wayar ta saka a hannu huta ( hands free)
"Ke mardiyya gobe ki tambayi Baban naku kuzo ku duba umminku a asibiti bata da lafiya kinji ko?"
Babangida yayi shiru kanshi a ?asa.
"Umma Labbai meke damunta dan Allah, ya jikin nata? "
Yaran duk suka dawo wajen Mardiyya.
"Hawan jininta ne ya tashi Mardiyya"
Ai da sauri Babangida ya amshi wayar sai jin muryarshi Labbai tayi.
"Labbai me ya sameta har hawan jininta ya tashi. Ya jikin nata dan Allah, ko in kawo su yanzu? "
"Jikin da sau?i ba sai kunzo yanzu ba.
Gobe in Allah ya nuna mana kwa tawo Win nagode sai da safenku"
A hankali ya sauke wayar zuchiyarshi yaji ta sake karyewa sosai.
Inama Sabuwa zata iya sake ara mishi dama su sake zaman aure. Da taga gata ma'ishi gatan da sai ta zama abar kwatance abar sha'awa a dangi.
"Mardiiyya ku shirya gobe sai muje mu dubota irin wajajen sha Wayannan ina da Walibai masu jarabawa inna sallamesu sai in zo in kai ku.
Zan baki kuWi gobe kiyi cefane ni da kaina sai in girka mata abinda ta fi so."



Sabuwa:.
Ina yin Sallah Labbai ta shigo ta zauna naga ta sake gasa tagumi.
Ina idarwa nace.
Wai ni Labbai lafiya kuwa kina ta tagumi.
Sannan me ya faru naga Rakiya da Maigogul sai riritani suke yi ne? "
Ajjiyar zuchiya ta ja ta sauke kafin tace.
"Lolo wai kinsan waye yace yana sona harna kasa bacci na kwana cikin tubkewa da warwarewa kuwa? "
Kai kawai na girgiza mata ina saurarenta.
"Cicib ne wai yake so zai aureni kuma da gaske yake yi, yace ma in dai na amince sai a haWa bikin lokaci Waya dana Uzairu zuchiyata kinji abinda ya kaWa mun kai"
Dariyar dole ce ta suSuce mun na dubeta na maya.
Ke kuma to kina son nashi ne Wan daudun? "
"Lolo mu faWa ma kanmu gaskiya. In na?i Cicib wa zanso. In shi ?an Daudu ne ubanmu menene shi? Dashi da Maigogul babu wani bambamci Allah. Lolo wallahi nagaji da rashin aure na gaji.
Nifa a wannan karon zanso ma Maigogul ya kafe ni a gidan Cicib inna shiga mutu ka raba. Wallahi lolo na gaji. Ke dai kakarki ta yanke sa?a"
Kafin nace wani abun sai ga su Uzairu zuchiyata sun shigo dasu Gaza harda magazin. Uzairu zuchiyata sai rufe bakinshi yake yi tsabaragen dariya akan batun soyayyar Cicib da Labbai ne nasani.
"Amarya kin sha ?amshi matar manya kaga mai Sa'a"
Kaine sai ya kuma Waurewa na dubi Uzairu zuchiyata nace.
Ban fa gane me kuke nufi ba Uzairu zuchiyata ya bani da lafiya kuna kirana amarya. Wani abunne ya faru ne ku faWa mun? "
Maigogul ne ya shigo zuruf yace.
"Zanyi miki bayani Lolo da kaina. Ta inda ake hawa tanan ake sauka. Ku bani waje ni da'ita"
Ficewa suka yi suka barmu.
Bayan shiru ya wanzu na lokuta sai Maigogul ya fayyacemun duk abinda ya faru.
"To dan haka abinda nake nema dake Sabuwa ki rungumi mijinki sawu da ?afa ki zauna

7 / 28