Idan Kaya Ya Gaji Gammo Ma Ya Gaji 4 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Fareesa Category :  Romance

Chapter   17 / 28

48K to 51K   out of 83.6K words

gashi ana fita daga ihram, kuma Umara ta cika. Duk abubuwan da aka haramta a ihram sun halatta
Bayan kammala umara
Ana iya yin Sallah a masallacin harami
Ayi addu'a da shukar Allah domin cikar ibada.
Idan mutum yana son yin umara fiye da Waya sai ya fita zuwa masjid Aisha domin shiga sabuwar ihram.
Zuwanmu da kwana biyu Alhaji Zaid shima ya iso.
Ni da Maigogul gabaki Waya wani irin farin ciki ne shimfiWe a fuskokinmu. Duk wata adda'a nayi ta alkhairan duniya dana lahira na ro?ama kaina, ?an uwana ?a?ana aurena mijina, iyayena musamman Maigogul.
Alhamdulillahi irin kukan da naga Maigogul yayi ta yi nayi imanin na nadamane da dana sanin rayuwa inaji yana faWama Allah da muryar kuka.
"Allah ni da kawalci har abada"
Gashi wannan Hajiyan sai haba haba take yi damu.
Ita ta rakani na saka ha?ori na gwal Alhaji Zaidu ya dubeni bayan mun fito suna tsaye da Maigogul nayi dariya ha?orin ya bayyana
Sai naga Maigogul yana share hawaye shima ya ?ara ha?orin makka a bakinshi. Kunsan mutumin naku babu dama ne.
Idanu Alhaji Zaid ya kashe mun kawai Hajiya Balaraba kuwa hankalinta na kan Maigogul.
To daga haka kuma muka dai siya tsarabar gida, Maigogul ya sai kaya da turaruka masu yawa.
Nima na yima kaina ?aramin akwati, zannuwan gadona a can na siya Alhaji Zaidu yace za'a saka kayan a jirgin kaya, nice harda siyan labule da irin kafet na larabawa mai kwalliya mai kyau. Zannuwan gado masu bargo manya nasai biyar harda maigida sakko mu gaisa, saina ?ara da ?ananu guda biyar
Haka aka auna kayanmu zuwa Najeriya mu kuma muka nufi Dubai
A bakin hotel Winmu muna tsaye da Hajiya Balaraba tace.
"To Lolo ga katina dan Allah in kun dawo Najeriya ki kirani inaso muyi magana.
Sannan inason zanyi magana da Alhaji Baba in babu damuwa"
Murmushi nayi mata na juya muka kalli bayan Maigogul a tare nace.
Babu damuwa Hajiya Balaraba nagode sosai Allah ya bar zumunci"
Harna juya tace.
"Af lolo ji mana"
Juyowa nayi na dubeta.
"Amm nace ba Maigogul matarshi Wayane? Kiyi ha?uri kada kiji zafina Sabuwa wallahi ba laifina bane Allah ne ya jarabceni na sani, ina son abu mai kyau"
Da murmushi da farin ciki a fuskata nace da'ita.
Matanshi biyu kuma muna da yawa yaranshi. Amman Hajiya Balaraba ai namiji mijin mace huWu ne. Ni kaina na muku sha'awar juna sosai. Kuma Maigogul mutum ne mai sau?in kai sosai kuma shima zai soki na tabbatar. Ina ganin tunda kinji kina ra'ayinshi ku sasanta kanku kawai. In kika bani dama ma sai in shige miki gaba ki samu abinda zuchiyarki take so"
Murmushi tayi ta Wanji kunya har a fuskarta.
"Bakya tsoron Hajiyarku taji labarin ke kika haWa tayi fishi dake. Kinsan mata da ?iyayyar kishiya?"
Kunji wai Rakiya ce Hajiyarmu tayi tunanin Maigogul ai wani ?usane, bare tana ta faWin Alhaji Baba yasan abubbuwa masu tsada.
Babu komai ai bama zasu ji ba. Muna da kyakkyawar ala?a da Maigogul zamu kashe mu burne tare in dai kina ciki"
Da haka mukai sallama akan saita jini in sha Allah.
Gaga_gaga haka muka shiga Dubai cikin hukuncin Ubangiji bisa jagorancin Alhaji Zaidu mukai duk siyayyar data dace na akwati nice harda setin sar?a da Wankunne na zinare.
Na sai kayan cin biki, na sai abubbuwa da dama.
Maigogul ma yasai turaruka, da gogul, da takalma da agogoguna. ?akin hotel uku Alhaji Zaidu ya kama mana sai lelena yake yi. Da daddare yana shigowa Wakina muyi hirarmu ta masoya, muji Wumin junanmu.
Maigogul kuma yana fita harabar hotel Win ya zauna a rumfa yana shan jus yana kallon kyau da tsarin hotel Win.
Bayan mun kammala siyayyarmu muka tarkato muka dawo gida Najeriya muka kwana a kano washegari Alhaji Zaidu ya Wauki mota ya mayar damu gida da tarin tulin kayanmu rigi_rigi
Ganinmu ya hautsina gida da murna Gaza da Uzairu zuchiyata harda Murna, su Labbai sai tattaSani suke yi suna farin ciki.
Muma farin ciki fal ranmu wallahi.
Da ?yar na yakice na samu Alhaji Zaidu a falo na zuba mishi abinci yana ci yace.
"Shakelena nan da sati biyu kuma sai mu shiga maganar tarewa kawai. Kinga banyi maganar kayan gado ba a Dubai ko?
Sabida bazan iya jure har kayan su iso bane muna da kayayyakin waje a Kano zaki iya samun duk abinda kike so Uhm Shalelena?"
Murmushi nayi mishi ya mayar mun har yana kashe ido Waya.
"To kuWin kayan gadon in tura a asusun bankin Alhaji Baba ko in tura a naki uhm? "
Sai da naji faWuwar gaba. Amman haka na daure nace.
Sai yadda kace kaina bisa wuya ranka shi daWe da girman kujerarka"
"To shikenan zan tura miki a asusun bankin ki tunda sai kun shigo kano zaku siya.
Sai kuWin Winki da ragowar hidima ko? KuWin hidimar abincin biki da abincin tarban dangina masu zuwa Waukar Amarya zan tura a asusun Alhaji Baba. Shalelena ai musu tarbar da ba zasu mance ba. Wannan jan leshin da sar?arki ita zaki saka in sun zo Waukarki ki fito kamar sarauniyar data lashe gasar kyau ta duniya nasan Hajiya da'ita za'azo. Tunda haka take maramun baya a duk aurena na baya.
To bani labarin tanadin da kikai ma darenmu na farko uhm Shalelena sabida nima insan irin shirin da zanyi ma Shalelena uhm kinga inata tattalashi ai nayi ?o?ari bana wasa ba. Inasone ya kasance na musamman mai tsayuwa a zuchiya da rai"
Kallonshi nayi irin kallon da nasan lallai zan burkitashi a shagwaSe nace.
Harshe da ha?ori ba zasu iya fasalta maka tanadin da nayi maka ba. Kai dai ka shirya ka zauna da shirinka kawai"
Murmushi kawai yayi mun irinna cikar Dattijantaka
Bai jima ba ya kama hanyar Kano
Washegari ya sako mun manyan kuWaWe sosai na kayan Wakina da na Winki da ragowar hidindimun biki dai.
Nan muka shiga buWe tsaraba ana rabawa su Adama kuma suna kan akwatunan lefe da su zannuwan gado dana siyo gida dai ya kaure da kacaniyar biki. Mun tura da Winki kano wajen wani tela da Sadiya ta haWamu dashi.
Na ba Labbai zanin gado babba mai bargo da ?arami. Su Adama dama na siyo musu kayan fitar biki duk tare aka kai mana Winkin na biya.
Alhaji Maigogul ma an cika mishi banki da kuWi sai washe baki yake yi sunata hidimar zuwa Kasuwa da shi da Cicib
A ranar da muka dawo na kira Hajiya Balaraba na feWe mata biri har wutsiya a game da halin Maigogul da sana'arshi da halin da gidanmu ke ciki.
Duk da kanta ya buga amma ta amince da aurenshi sabida ta riga da ta kamu har wuya na gani.
Gefe na jashi na labarta mishi halin da ake ciki sabida murna rungumeni yayi tsam yana ta saka mun albarka na Wauki lambar Hajiya Balaraba na dan?a mishi sauran aikin nasan nashi ne.
"Lolo yanzu wannan matar dai ni take so? Allahu Akbar ashe kallon da take ta yi mun kenan?
Lolo gaskiya kina sona, wallahi nima ina sonki fiye da kowa cikin ?a?ana"
Ai kuwa kwananmu huWu da dawowa da safe sai ga Maigogul ya le?o Wakinmu ya kirawoni na fito muka shiga Wakin su Uzairu zuchiyata shima yana ciki
"Lolo Hajiya Balaraba ta nemi son ganina domun mu tattauna batun aurenmu tunda mu ba yara bane mun riga da mun daidaita kanmu shine nace ko zaku rakani ke da Uzairu zuchiyata tunda ke kika haWa abun ta inda aka hau tanan ake sauka. Ku shirya muje yau mu samu mu dawo danma Cicib baya nanne dama da shi zai rakani"
Fita a Wakin yayi zuwa shiryawa, Uzairu zuchiyata ya dubeni baki har kunne niko na labarta mishi ai sai ya mi?e da daka tsalle harda ihunshi.
"Lolo shima Dad wuf za'ayi dashi kenan hiye
Kece ma kika haWa ki kuka da kanki in Rakiya taji wannan labarin ke da ita ya?are wallahi yadda take kishin Dad abun azimun. Gashi tunda kuka dawo an samu canji sosai agun Maigogul kiga jiya tujarar da Rakiya ta sakar mishi amman bai kula ba
Mrs BUKHARI

Son so=??? [10/4, 10:29 PM] +234 810 593 2041: MRS BUKHARI
14



Kiga jiya tijarar da Rakiya ta sakar mishi amman babu abunda yace mata har saida ta ?ureshi ne ya cire rigarshi ya doka da ?asa to da dai taga ranshi yayi mummunan Saci shine tayi shiru. Da dane ai wallahi da sai sun daku ya wuni yana tijara. Lolo gaskiya dai mu zuwa Canada ya zame mana dalilin alkhairi tunda dai a ta dalilin canadan kuka haWu da Alhaji Zaid harya aureki, ta dalilin dai kuka je Umara har Maigogul akayi gamo dashi. Kinsan Allah dama shi ba nanan bane sam yaushe su Rakiya suka yi macin dashi ?addarace da talauci kawai ta haWe su waje guda ai ya fisu kilas"
Uzairu zuchiyata kai dai wallahi ka iya bakin ka narantse maka da Allah. Bari inje in shirya mu tafi."
Nan da nan muka shirya gashi yau su Mardiyya suka ce mun zasu zo karSar tsarabarsu sai kiransu nayi nace su bari tukunna gobe inna dawo zanje wajen Baba malam zan tafi musu da tsarabar sai mu haWu acan tunda ta labarta mun halin da Babansu yake ciki sanadin jin labarin Aurena. Amman yarinyarnan sabida tarbiyyya da tsananin kunya bata faWa mun ta samu sanin asalinta ba, ta dai cemun sun koma ?ar?ashin kulawar Baba Malam.
Allah sarki wallahi shi yasa ban mance dashi ba nayo mishi tsaraba mai kyau sosai gobe na ?uWurce a raina zanje dama.
Cikin minti talatin muka fito
Wallahi Maigogul zaku Wauka gwamnane tsabar kyau da caSa kayan ado. Turarukanshi kuwa ?amshinsu saida suka danne namu tas babu yadda muka iya.
"Wai nace Maigogul inata magana tun a Waki kayi banza dani. Nifa naga kwana biyunnan ka sauya koma ince tunda ka dawo umara gabaki Waya ka zama wani iri ko fita ka dena yi Allah yasa lafiya ya zakaita zama a gida haka? "
Murmushi yayi yana gyara agogon hannunshi yace.
"Rakiya kayi nayi kenan. Kamar kinfi sha'awar ganin ina biye miki muna buyagi ko? To ni Allah ya shiryeni ya tarfama garina nono. Lolo yarinyarnan ta zaunar dani munyi magana sosai wallahi Rakiya na fahimci kusakuraina Allah yasa ki fahimci naki shashashar mace wacce bata san komai ba sai jaraba, in baki yi wasa ba sai kinci yari nake faWa miki. Ku muje abinku mu mun tafi Kano sai Allah ya dawo damu."
Sauka muka yi muka bar Rakiya a tsaye illahirin mamaki ya kamata sama da ?asa ta rasa me zata ce sai ido kawai da aka batta dashi.
A wata ?atuwar jeep muka nufi hanyar Kano muna tafe Maigogul na ba Uzairu zuchiyata labarin umara da irin taimakon da Hajiya Balaraba tayi mana.
"Wallahi ashe ita kuma ni take so nifa banyi mamaki ba. Sabida mata da yawa suna tallatamun kansu in auresu basa dai gabanane na gidanma yaya na'iya dasu. Akwai wacce ma tace zata sha guba in fa ban aureta ba wallahi. Nace ai kuwa sai dai tasha fitinar Rakiya da ace ni Win ba jan wuya bane ai da yanzu ta kaini ?asa nake faWa muku. Gaskiya kusan ko da yaushe muka je biki ko dai wani taron manya ina samun mata kusan uku da zasu nuna ra'ayina. Ina da jama'a sosai kuma ina da farin jini sosai da sosai. Kai da Lolo ai farin jinina kuka Webo, duk da ita kanta Kayi nayi tayi Sharafi sosai"
Dariya muka yi duka Uzairu Zuchiyata yace.
"To ai Dad wallahi kayi ne dole mata suce suna sonka kamar Hauwa ma ita tace tana sonka ko? "
Wannan dariyar yayi yace.
"Har da gyatumar taka ma ita ta ?yalla ta ganni tace tana so da dai naga itama ba baya ba wajen kyau saina yadda na aureta gata da gashi"
Haka Uzairu zuchiyata yaita takalo Maigogul shi kuma bil ha??i yaita bashi labarai da wanda ya dace da wanda ma bai dacen ba duk shi kaWai
Ni dai dariya kawai aka barni dayi.




Babangida:.

Kwananshi biyu a asibiti baima san inda kanshi yake ba, sau Waya ya farka ya sake komawa bacci.
Ta Sangaren su kawu Manga sunje gombe kuma Allah cikin ikonshi sun tadda Hameeda tananan batai aure ba, ko da mahaifinta ya kirata ya sanar mata da abinda ke tafe dasu Kawu Manga sai taji ta amince dama tana son mijinta kuma a hakanma tana yawan tura mishi sa?on gaisuwa da tambayar yara, tun yana ce mata yara suna lafiya sai taga to bari ta shigar da kanta a karo na biyu ko zata dace tunda har zuwa lokacin babu wani tsayayye ga takurawar iyaye da sosaitin da muke ciki daya addabeta. Dama ire iren tsangwamarnan ke sawa bazawara ta koma gidanta ko babu daWi, ko kuma duk wanda yazo ta amince mishi ko ya cancanta ko bai cancanta ba. Hameeda ta amince Kawu Manga da kanshi ya bata sadakinta dubu hamsin a ranar aka mayar da auren.
Su su kawu Manga suka tawo da Hameeda da ?anwar mahaifiyarta.
Washegari motar kaya ta biyosu sukai jerensu tas a Wakin Sabuwa, sannan kuma suka shiga sunturin asibiti su ukun. ?ar Shuwa dai tana gidansu shiru shiru babu wanda yazo itama bata je ba tana tsoron Baba Malam dan tasan bashi da daWi.
A hankali Babangida ya buWe idanunshi a rana ta uku kenan.
Hameeda tana zaune tayi tagumi tana ta sa?e _sa?e a ranta, Ramatu kuma shigowar tata kenan suka ga ya farka, Ramatu ce ta juya ta kira likita yazo.
"Ku Wan bamu waje dan Allah"
Ya faWa a Waure tare da juyowa kan Babangida.
Babangida kuwa ?irjinshi da kanshi ne suka mai wani irin nauyi sosai ya kaWu hankalinshi ya tashi matu?a da jin labarin aure Sabuwa, to amman yaya zaiyi bashi da tsumi bashi da dabara. Soyayya kuma gaskiyace zaici gaba da ro?on Allah ya yakice mishi soyayyarta a zuchiyarshi da jininshi ko zai huta.
Nan likita ya gama yi mishi aune aune da gwaje gwajen da zaiyi mai da tambayoyi biyu dai.
Babangida kuwa Allah kawai yake ambato yana neman ya cire mishi tunanin matar wani a zuchiyarshi.
"Astagafurullah Astagafurullah Astagafurul"
Abinda yaita nanatawa kenan har su Hameeda suka shigo. Shayi Hameeda ta haWa mishi mai kauri ta bashi daidai sha. Yana son tambayarta amman bata tata yake yi ba ta kanshi yake yi tukunna.
Yasa hannu ya karSa yana sha a hankali sakamakon Waci da bakinshi yake yi mishi.
Malama Babba da Mustapha da Adeeza ne suka shigo Ramatu tayi maza ta mi?e taba Malama waje.
"Babana ka tashi? "
"Natashi Malama Baba Malam yazo kuwa? "
A sanyaye yake magana kamar baida laka. Mustapha ne yace.
"Kwananka uku a kwance, kwanaki biyu duk yazo yaune kawai baizo ba. Babangida ni abinda nake so dakai tunda komai ya ?are a tsakaninka da Sabuwa ya kamata shiga damuwa a kanta ya isa haka kuma. Kaga dole dama ba zata dauwama a zaune babu aure ba in ba dai jarabawa ta samu ba wanda kuma bama mata fatan hakan. Ba daidai bane ka zube dan kawai kaji Sabuwa tayi aure ba. Ya kake tunanin iyali zasu ji? "
Idanu ya lumshe kawai baice komai ba malama tace.
"Sannu Babana yaya kake jin jikin naka yanzu? "
"Ina jin jiri sosai amman gida nake son in koma a sallameni babu komai. Kuma abinda ya farunma ba da gangan bane ?addarallah. "
"Hakane Babana babu komai Mustapha a tambayi likita ko za'a iya bashi sallama ai sai mu tafi gidana yaje can ya ?arashe jinyar"
Fita Mustapha yayi yana fita su Mardiyya da Baba Malam suna shigowa.
Da sauri Malama Babba ta mi?e cike da girmamawa take tayi mishi sannu.
Babangida ya kallesu yana jin wani irin zafi a zuchiyarshi daya kasance silar raba auren lalle.
"Kai ya jikin naka? "
"Da sau?i Baba Malam "
"To madallah. Sannunku ku kuma da ?o?arin jinya Allah ya ba da lada ko? "
Su Hameeda suka amsa da Ameen.
Su mardiyyane suka ?arasa suka duba Baban nasu da jiki mardiyya sai kallonshi take yi, shima idanshi a kanta.
Cikin dai ?an?anin lokaci aka sallami Babangida tare da kafa mishi dokiki da bashi magungunanshi. Dake likitan ma na gidane yace zaici gaba da kulawa da Babangida a gida har zuwa ya warke
Malam ne ya hana Babangida bin Malama yace yaje iyalanshi suyi mishi jinya.
"Yaro an?i a barshi ya girma yanzu wannan gona_gonan shine sai an tafi dashi jinya? Kai Babba son Babangida zai halakaki"
Ganin su Mardiyya sun bisu Baba malam ne yake tambayar Mustapha dake tu?asu zuwa gida su suna gaba su Malama su huWu a baya.
"Ai sun koma gidanku. Hameeda kuma ta yi jere a Wakin Sabuwa zaka ji bayanin koma menene ka bari jikinka ya warware ukunna"
"Allah sarki."
Kwanan Babangida biyu a Wakin Hameeda ita ya tambaya ta bashi labarin iyakar abinda ta sani na game da komen aurensu.
Ragowar zancan Malama ce tayi mishi.
Idanu ya runtse kawai ya shiga hawaye mai zafin gaske.
"Shikenan hankalin Aisha ya kwanta ta fallasa asirin gidana. Allah sarki Mardiyya baiwar Allah yarinya mai ha?uri. Malama ba dan ina tsoron fishin Baba Malam ba dana sallami Aisha wallahi. Na tsaneta fiye da tunani, kuma abadan bazan sake ganin girmanta ba, wanne irin zama zanyi da'ita? Har zata ce Mardiyya ba jinina bace to jinin uban waye ita"
"A_a Baba kada ka sallameta ka dakata kaji me malam zaice kawai. Amman Baba ai ka bani mamaki kasa na washi yarinyar mutane kai ashe daduro ka ajjiye harda rabon Wa wannan sheWanci naka da yawa yake Babangida. Idan kasan akwai wani abu da kake Soyewa gara ka bayyanashi tun wuri zuchiyata ta samu ta buga lokaci guda kawai ka huta.
Batun mardiyya ba ?arka bace baima taso ba yarinya kamarka Waya da'ita har shi Amir Win Babu kokonto Wankane na jini.
Baba kayi iyakar yinka kaje ka ro?i gafarar mahaifinka ya yafe maka. Ha?i?a ka sake saka Malam a cikin wani hali ina tsoro kada kayi sanadin mutuwar malam Babangida "
Hawayenta ta share shima ya share nashi yace.
"Zan ro?i gafararshi kuma dan Allah ki rakani muje tare har kema ki ro?i gafararshi ko Allah zaisa ya mayar dake"
"To Allah yasa Baba ai zanso sosai sai dai in bai samu bane shine zan ha?ura"
Sun daWe suna

17 / 28