Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   8 / 37

21K to 24K   out of 110.8K words

ina sauraron littafin *Ta fita zakka* daga tashar Tsakar gida ta mai sanyi bayan na kammala jin *Abdul Qadir na Lubna*

Kiran Abida ya fado wayar. Na dauka ko gaisawa bamu yi ba, ta Fara korafi da ce wa ",Yanzu Maigado ace har yanzu baki turo mini maijego package din ba?"

Na ce "A a Abida ya ya muka yi ne? Ba ce wa kika yi sanyi flusher big galon za'a fara turo miki, idan kin kammala sai a turo sauran kayan gyara din?"

"Hakane! To Ki yi maza a turo mini nan da gobe?"

Na ce "Tom ina little?"

Ta ce "Ga ta can a hannunsa a falo".

Bata jira komai ba ta yanke wayar tunda ta riga ta isar da sakonta.

Ban ajiye wayar ba sai da na tuntubi Surayya Bojuwa@08032773332 na saka order ta bani tabbacin jibi dan sassafe za'a tura mini kaya Katsina. Na bada lambar Yaya Sulaiman don nasan shi zai je ya karbo kayan.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Muka yi sallama bayan na yaba mata kan nishadin da ta sanya ni cikin labarinta na Sabo da kaza. Abida sai ce mini take yi na samu lokaci na karanta HALIN YAU da Bakar Ta'ada lallai zan ji dadinsu. Amma na kasa karatun sai dai tunda na k'ulla abota da jin audio zan saurare su d'aya bayan d'aya da zarar na samu lokaci da nutsuwa.

*

Watan Abida shida da haihuwa nima na haihu bayan na sha kafirar wahalar gaske. Lafiyayyar yarinya mai kama da Amrah. Sai dai kwanaki biyu tak ta koma. Alhini sosai muka yi mussaman da ba wani ciwo ta yi ba, haka na hakura na cigaba da kula da kaina cikin dangana. Kowa ya zo ya gaishe ni.

Wata biyu da haihuwar Sahal ya tubure Katsina zai koma ya gaji da zaman Kano, tunda dama Mahaifinsa ya rasu watanni uku da suka shud'e.

To wai Hajiyarsu ta ce ya koma gida tunda ba aiki yake yi ko wata harka mai k'arfi ba. Tunda akwai wajen zama a cikin gidansu.

Na yi kasake ina kallonsa lokacin da yake yi mini wannan jawabin, tare da tunanin bai fada mata ni harkokina masu k'arfi ba ne a Kano?

Amma na hadiye ban yi inkari ba, kawai na ce "Allah yasa arzikinka a can ne"

Na dinga zullimin yadda zan yi da aikina da sana'ar da na kafu akan ta.

Sai dai cikin sa'a W.H.O din da ta ce babu damuwa sai na cigaba da yi mata aikin a ma'aikatrsu ta jihar Katsina.

Haka muka tattara muka koma. A wannan zaman na sake ninka hakurin da nake yi, domin a lokacin na fahimci dangin Sahal kallon mai farar k'afa suke mini. Zasu zo gidan sai ta kure da su shigo inda nake mussaman ace sun hadu da shi a cikin gida ko a waje sun gaisa.

Ranar wata Talata na dawo daga wajen aiki na shiga sashen Hajiya na tarar da kusan duka ya'yan gidan da yake akwai wanda babarsu ta rasu duk sun girma ga kuma 'yanmata wadda babarsuce amarya.

Ba laifi Hajiyarsu Sahal din ta rungumi dukkan ya'yan gidan nata da ba nata ba cikin hakuri da kyautatawa

Sai dai kamar kowanne gida baka rasa tsuguri tsoma irin na y'an ubanci. A zahiri kansu a hade yake amma a badini kowa da yan dakinsu yafi mu'amala.

Yar kanwar babansu ce ta haihu yau ake suna. Shine duk suka hadu a gidan daga nan sai su d'unguma su tafi gidan maijegon.

Na saba matuk'ar zan fita zan je na gaishe ta, haka idan na dawo sai na je mun gaisa ta ga

dawowata.

Ba ni da matsalar komai da Hajiya don mace ce mai addini da tsoron Allah.

Ina dosar bangaren na jiyo muryar Yaya Turai wacce itace babbar gidan, kuma dakinsu daya da Sahal diyar Hajiya ce.

Fadi take yi "Yo dama ai tsaurin ido ya yi, wannan yarinyar ai tafi karfinsa yadda yake salau salau ta ya ya zai iya da ita?

Dirarriyar mace mai zati, komin k'yashi ai ba matar yara ba ce. Amma da ya kwasowa kansa ai ga shi nan a tsugunne. Iyayenta matansu daya, kaf sisters dinta babu mai kishiya. To shi kuma ya gaji k'arin aure dukkan iyayenmu babu mai mace d'aya sai baba na Zaria shima ai ya yi mutuwa ta yi amaryar wajen haihuwa har yanzu kuma bai k'ara ba .

Gabadaya ban yarda da ita ba shiru shirunta ba na alheri ba ne. Tana da saka hannu wajen zamansa haka, ku duba ku ga irin tashen kudin da ya yi. Amma daga rasa aiki ace komai ya k'are ta kankane ta rik'e komai tana juyawa ta hana komai wai ita mai sana'a kuma ma'aikaciya. Na riga na gano makircinta, a hakan kuma idan rabo ya tsaga sai ya yi auren ko tana so ko bata so, ko kuma rabo ya kawar da ita da k'arfin tuwo dukiyarsa ta dawo hannunsa ya samu y'ar yarinya ya aure".

Ummu wacce take bin Sahal ta ce ", Wallahi kuwa Yaya ni fa ga ni nake yi ma ta girme masa".

Ragowan suka ce "Haba dai sai dai su yi sa'ani ko ya fita kad'an".

Hajiya ta ce "kai kuna da shiga sha'anin da bai shafe ku ba, tunda yana zaune lafiya da iyalinsa menene damuwarku ne? Sannan ai mace bata fin k'arfin namiji. Ni dai ban ga laifinta ba yarinyar akwai hakuri da mutunta babba"

Yaya Ture ta ce "Ga ungo ko Hajiya?"

Gabadaya suka kwashe da dariyar iyashege.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Zuciyata ta buga ashe haka suke mini kallo?

Ina fama da wahalar d'anuwansu su suna mini kallon nice sanadin tsiyacewarsa, sannan na danne komai nasa? Menene da shi da na danne? A wanccan lokacin ba yadda ban yi ya sayi gida ko na raianwa ne amma ya k'i. Wanne irin son kai ne haka? Da ransa ba mutuwa ya yi ba har na hana shi abin da yake nasa ne, kuma yana kallona? Allah na tuba, ba dan shi ba, da tuni bansan adadin dukiyar da zan tara zuwa yanzu ba.

Wato duk kokarin kyautatawar da nake yi musu, shima ya yi musu da nawa kudin ashe basa mini kyakkwan zato?

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!

Na furta a hankali. Da k'yar na ja kafufuwana da suka yi mini sanyi na isa kofar falon. Na yi sallama na shiga. Kusa da Hajiya na durkusa ina gaishe ta, ita kuma ta amsa cikin sakakkiyar fuska tare da yi mini barka da dawowa. Na juya muka gaisa da su cikin walwala sun shanye haushina suna ta fadin sannu da dawowa.

Yaya Turai har da tambayar yara wai idan an yi hutu na bari suje Su mata kwanaki.

Maimakon na ji dadin hakan sai raina ya sake bak'i domin Hausa ta yi mini. Wato idan ban amince ba, ubansu bai isa ya kai mata ba.

Na sake hadiye komai na yi yake na ce "Ko yanzu ma kike so sai ki tafi da su, sai su dinga zuwa makarantar daga gidanki, indai kin fada masa ba zai tankwabar da buk'atar ki akan ya'yansa ba".

Na juya ina fadin "Bari na je na yi salla.".

Har na isa bangarenmu zancen zuci nake yi tare da tunanin yadda mu'amala da fuska biyu ta zama ruwan dare a wannan duniyar.

Haka nan son kan da dangin miji mata suke yi akan matar d'anuwansu kullum k'ara hau hawa yake yi tamkar Wutar* jeji( littafin Salaha Abubakar Zaria).Mai bukatar littafin da tsofin littafanta na baya za'a same su in soft copy in sha Allah. 08033773332.*

Haka na sake daure wa ban fada masa abin da na ji suna tattaunawa ba. Amma dai nasan inda na ajiye su, don yadda yake sanyi kalau ko na fada ma ba komai zaice ko ya yi ba, to hakurin shi yafi don nasan a karshe zai iya ce wa zama da sune bana so.

Komai na tafiya mini daidai ta fuskar aikina domin albashina da ake ba ni mai tsoka bai samu tasgado ba, sana'a ce ta samu tawaya domin na fi karfafa a Kano. Amma nan din ma ina dan yi kullum kuma abin gaba yake yi ba baya ba.

Dawowata Katsina ya kara kusanta ni da Abida da kuma Basma Maska Maman Abdul. Duk weekend Abida take turo mini d'iyata da nany dinta su yini a wajena. Tana girma kammaninmu na sake yawa, banbancina da ita na fita haske duk da ba bak'ace irin Abida ba tana da d'an haske irin na Yaya Sulaiman.

Sam bata mini k'iwa lafiyayyar yarinya mai cike da kuzari rarrafe take yi, komai ta kama sai ta mik'e.

Bamu cika wata biyar da komawa Katsina ba aka musu rabon gado. Inda muke zaune ya fito a na kaninsa da suke ciki daya autan Hajiya.

Shi Baban Amrah inda Hajiyarsu take zaune ya gada.

Wata daya a tsakani aka mai waje ya sanar masa watanni biyu masu zuwa aurensa kuma a nan yake son zama.

Duk da nasan sharrin Yaya Turai ne amma dadi ne ya lullube ni domin tamkar akan k'aya nake zaune haka nake jina a cikin gidan.

Na tabbatar ba yadda zai yi ya tashi uwarsu kamar yadda kaninsa ya tashe shi. Gara na yi nesa da su tun basu k'ure hakurina mun fara tashin hankali ba.

Su ko tunanin inda zai samu muhalli cikin k'ankanin lokaci basu yi ba, na yi murmushi don tozarcin dai ba ni suka yiwa ba d'anuwansu suka jefa cikin cankacakare.

Sai dai cikin ikon Allah auren ya fasu dan haka tashinmu ma ya fasaya.

Duk da ni so na yi na kama mana haya mu tashi din din na gaji da gutsuri tsomarsu.

Ni dai na dinga mamakin yadda zartar da hukunci na gaskiya irin na Hajiya baya tasiri akan ya'yan cikinta domin haka take kamar agwagwa duk abin da y'ay'anta suka ce ko suke so bata tursasa musu. Wannan duniya cike take da kalubale kala kala ko ina ka buga babu dad'i.

Don ba dan auren ya watse ba da tabbas zuba ido zata yi a tashi Sahal.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: da Abida, Allah ka hana ni kunyata, Allah ka taya ni rikonta Ubangiji ka sanya soyayya da tausayi a tsakanina da wannan yarinyar, Allah ina neman tsari da son da zada zai

hana na yi mata cikakkiyar tarbiya, Allah ka so Abida ka so Yaya Sulaiman, na gode sosai Allah ya saka muku da alheri ."

Duk taurin ran Abida sai da ta yi hawaye yayin da Yaya Sulaiman ya yi shiru idanuwansa sun fito sosai.

Tunda na saka hannu na karbi Farha ta kwanta a kirjina barci ya sure ta. Basu wani jima ba suka tafi jikinsu a sanyaye.

Sai me ba sai Baban Amrah ya tada sababin dan me zan karbi rik'o babu yawunsa?

Na sassauta na ce "Ni dai nasan ba zan iya tuna adadin sau nawa nake fada maka Abida ta bani abin da ta haifa tun shekaru masu yawa da suka shud'e watakila ma tun kan mu yi aure."

Da kumfar baki ya ce "Saurara baiwar Allah ai ni duk dauka na yi labari ne irin na k'anzon kurege."

Na yi yak'e tare da ce wa "Yanzu sai ka gane gaskiyar lamarin da girman sha'aninsa."

Ya tunzura ya ce "Ki mayar mata da 'yarta da ranta da lafiyarta ba zan rike mata y'a ba alhalin ba mutuncina take ga ni ba, ita idonta da kwalli ta kawo mini d'iyarta gidana? Ko yanzu na girmane a idonta?"

Haka kawai na kufula na ji zuciyata ta yi nauyi tare da wani irin fishin da nake neman tsarin Allah a kansa.

Na dago muka hada ido. Na ce "Farha d'ya ta ce da Abida da Sulaiman suka haifa mini. Za ta zauna da ni a duk inda zan rayu ko da kuwa cikin ramine. Idan har kana da matsala akan zamanta cikinmu to kawai ka dauki mataki amma ba zan mayar da ita ba, domin ni zan rike ta ba kai ba, ka sa ni!

Ganin na tunbatsa da fushi sai ya yi maza ya sassauta ya ce "Yi hakuri Billy gabadaya an shafe mini ce war d'iyar Sulaiman ce. Nima ai d'iyata ce zan sakata cikin ya'yana zan taya ki sonta, huce uwar Amrah! Amma idan ta uwar iya zan daka ko kallon inda yarinyar nan take ba zan yi ba.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Watanni uku*

Gabadaya hankalin musulmai ya koma kan shirye shiryen wata mai alfarma na azumi. Ni da Abida muka had'a kud'i kamar yadda muke yi muka yiwa su Baba hidimar neman albarka.

Muka yiwa iyayenmu mata d'inkuna.

Farha ta warware kamar ba ita ba, bata yi mini kuka sai da dalili, sai kuma idan har ta ganni bata yarda da kowa sai ni.

Mai aikina ita take kula mini da ita idan zan je wajen aiki. Ranar da ba zan jima ba na saka ta a gaba mu tafi.

Tun kafin azumi ya kama na kammala yi mana d'inkuna ni da yara har da shi ogan na yi mana ankon shadda.

Karon farko da na fara jin haushin suturar da nake siya masa. Don kuwa rabon da ya shigo mini da wani abu a leda da zummar ya siyo ya kawo gidansa ko da kuwa karas ne ko yalo na manta don kuwa shekarun da yawa. Bare maganar sutura. Shi ya ji a jikinsa ko y'an gwanjo ya siyo ya kawowa yaransa zan ji dadi suma su ji dadi amma sam baya yi, ban da Maman Zaria da take aikowa takwararta Amrah kayan sallah ba wanda yake yiwa ya'yansa kyauta da sallah duk danginsa. Dukkan kayansu daga ni sai dangina. Kuma ko d'ar baya ji, ya riga ya sanagarce ta bakin Abida. Don sai nake ganin tamkar yana ganin hak'kin kula da iyalinsa ya sauka daga kansa ne. A kullum na zauna mamakinsa ke kama ni, ta yadda baya damuwa ya tashi ya nema, ba kuma ya jin kunyar taba kudina duk da hidimar rik'e masa gida da nake yi tsawon lokaci. Abida kadai ta fahimci halin da nake ciki , a cikin dangina sai ko Yaya Sulaiman ban taba jin kuma sun fadawa kowa ba.

Na zama abin misali a wajen su Baba. Duk wacce ta je da gidan da sunan bacin rai sai an buga mata misali da ni.

Fadi suke yi "Bilki ce tunda muka aurar bata taba zuwa ta kawo mana matsalar miji ko ta danginsa ba, shekara da shekaru tana zaune lafiya da dadi ba dadi dai tana zaune abinta, ku dinga koyi da ita mana."

Sannu a hankali ido ya dawo kaina ana mini kallon na n taki sa'a mijina ba sawa ba fitarwa yasan alheri, ni kam na dace ba ni da matsalar miji da ta danginsa.

A duk sadda suke irin wannan washin yake nake yi domin ni kadai nasan me nake fuskanta a aurena. Kawai hakuri nake yi kan hakuri. Allah ya sani ina son Sahal da dukkan nak'asun da yake da shi. Dan Allah nake sonsa shiyasa ban gajiya da zamana da shi ba.

Watan azumi ya kama dukkan alummar musulmai aka tsunduma ibada tare da kankan da kai wajen mahaliccinmu.

Ana jibi sallah Yaya Asad ya dira a Funtua tare da iyalinsa akan zasu yi sallah a gida.

Haka Yaya Usman.

Dan haka Abida da Yaya Sulaiman ma suka tafi ana gobe sallah.

Ni kaina so nake ace na tafi sai dai ba zai yiwu ba.

Amma washegarin salla na tafi ni da yara.

Gida ya cika aka yi ta dabdala cikin jin dad'i.

Uku ga salla kusan kowa na gidan an hadu idan aka cire Yaya Munira da bata K'asar.

Yaya Salaha da Yaya Hamida sun iso don yau ake taron da muke yi duk sallah tunda a gobe su Yaya Asad da Yaya Usman zasu juya garuruwan da suka fito.

Wannan yinin da muka yi na cikin ranaku masu dadi da ba zamu manta ba. Don kuwa itace ranar karshe da muka hadu cikin walwala da begen junanmu, kafin ibtila'in da ya fado cikin zari'ar ya tarwatsamu gabadaya.

Tare da dukkan iyayenmu hudu aka yi walimar cikinmu suka zauna suka ci abinci tare da mu.

Baba Babba ya dinga nasiha Yana fadin "Ku kadai kun ishi junanku, ku yi hakuri da sha'anin rayuwar nan, duk halin da kake ciki ubangiji ya sani, ku yi juriya ku zama masu afuwa! Ku yi kokarinku ku zama masu yin hakuri dan Allah. Idan masifa ta same ku to ku yi hakuri na gaskiya ku barwa Allah. Idan kun k'i yi kuwa to ku sani zaku yi hakurin dole wanda babu lada a cikinsa tunda mutum bai isa ya canjawa kansa k'addararsa ba.

Tamu ta zo k'arshe ku ninka hak'uri da junanku, ku kula da y'anuwanmu ku sada zumunta da su. Kunsan dai goggoninku kune masu gaishe su, ba sune zasu dinga gaishe ku ba. Allah ya muku albarka gabadaya ".

Jikin kowa ya yi sanyi Baba k'arami kuwa ce wa ya yi ", Yadda muka hadu a nan ubangiji ya hadamu a aljannarsa kamar haka! Muka had'a baki wajen fadin "Ameen Baba".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya numfasa ya ce "Sulaiman kamo mana Munira ita kad'ai ce bata wajen nan."

Nan da nan kuwa Yaya Sulaiman ya ce "To Baba!

Ya fito da wayarsa ya kira ta, bugun farko ta dauka hotonta ya bayyana

Tana zaune tare da ya'yanta da mijinta, cikin nutsuwa ta gaisa dasu Baba. Sannan aka bamu wayar muka cure guri kowa na yi mata magana. A sanyaye ta ce "Yanzu saboda Allah idan ba so kuke na yi kuka ba, menene na wannan hayaniyar bana fahimtar kowa. Ina Bilki da Abida?"

Muka ce "Ga mu Yaya Munira!

Ta ce "Bilki Abida ta kawo miki d'iyarki?"

Na hasko mata Farha da take gefena na ce "Tuntuni, ki ga yadda ta girma kammanina na sake bayyana a tare da ita".

Ta yi dariya ta ce "Kunsa na matsu na zo gida, baku ji dad'in da na ji da na ganku dukkan ku a tare

8 / 37