rayuwata".
Na ce "To ni da bin hanyar ya kama sai ka lamince mini, zan bita idan kwana ne ya k'are Allah ya gafarta mini albarkacin zumuncin da zan je yi. Ni ba jiya ka ke fad'a mini an tattauna da y'an bindiga zasu daina addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja ba?"
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Eh na fada miki tabbas, amma na ce miki an cimma matsaya ne da su?"
Na hurar da iskar b'acin rai. Na ce "To ko ba'a ci ba zan yi shahadar zuwa in sha Allah, Zan dawo lafiya".
A hassale sosai ya ce "Idan kuma tsautsayi ya sanya kuka yi arangama da su fa? Kinsan dai ko sun bar kowa suka kyalla ido suka ganki babu tantama jeji zasu wuce da ke tunda za ki dauki hankalinsu".
Na zuba masa ido takaici iri iri na cina na numfasa na ce "Ko mun yi arangama in sha Allah da masu raunin akan mace zamu yi kiliya ba jarumai akan al'amarin ba".
Nan da nan sai ya sha jinin jikinsa ya kasa furta kalma ko guda akan batun.
Ganin haka ya saka na ce "Gobe nake son tafiya Kano sai mu hadu da Yaya Hamida mu tafi".
Ya ce "Ki dawo lafiya amma ni dole kika mini, menene na zuwanki? "
Na zabura na ce "Ban gane menene na zuwana ba. Matar Yaya Asad fa na ce maka ta rasu ba wani kalen dangi ba".
Cikin ko in kula ya ce "Ansari ya ce mini zai je Bai isa ya wakilce ku ba. Ina ce nan da Mami ta rasu bai bar abin da yake yi ya zo muku gaisuwar mahaifuyarku ba, shine ke kike rawar jikin zuwa yi masa ta'aziyar matarsa?"
Bak'in ciki ya kawo mini wuya na tunzura ainun cikin fishi na ce "Baban Amra na roke ka fita a cikin sha'anina da dangina, ka daina saka bakinka a cikin duk abin da ya shafe cikin gidanmu tamkar yadda ban taba tsoma bakina ko yi maka katsalandan a tsakaninka da danginka ba. Ko bai zo mana ta'aziyar uwarmu ba to iyayensa da matarsa sun zo ya kuma yi mana a waya. Na tabbatar kuma baya k'asar ne, ko ma yana nan bai zo ba, to na yafe masa. Tunda rashin zuwansa ba zai saka Allah ya k'i yi mata Rahma ba".
Ya yi sakare yana kallona ya kasa furta kalma ko guda.
Na kwanta a gefen da nake kwanciya ba tare da tunanin yadda ya tunbatsa da fushi ba. Ni kuma na fara gajiya da yadda ba ya daukar damuwata da muhimmanci ko kad'an.
Washegari sassafe na shirya cikin tsaleliyar Egyptian abaya da na siya a wajen Umm asalan mazauniyar Eggypt(2349162662750, 201121544627).
Na shirya kayana da na yara a karamar jaka tunda a hutune. Ya kuwa tubure ba zan tafi da su ba.
Na cire kayan Amrah da na Yaya Farouk.
Na saka musu a wata k'aramar jaka tunda ya ce gidan Hajiyarsu zai kai su.
Ya ce "Ita Farha ba ni da iko akan ta ko Bilkisu?"
Yadda ya yi magana cikin rauni sai zuciyata ta nemi ta karaya. Amma na daure na ce "Ba haka nake nufi ba. Bana son na tafi ne ni kad'ai sannan nafi son duk inda kaddara zata wulla ni ta wullamu tare da ita. Idan aka yi rashin sa'a y'an tada k'ayar baya suka sace ni, tunaninta ne kad'ai zai fi saurin yin ajalina. Amma idan ina tare da ita zan samu sassaucin tashin hankali."
Ya ce "Saboda su ya'yan da kika haifa basu da haƙƙin akan ki ko?"
Na ce "A a saboda ita din itace zata fi zama abin tausayi idan babu ni. Don kuwa kasan ni din ce uwarta da kuma ubanta".
Cikin takaici ya ce"Abida da ranta haka nan Ansari da ransa idan ni ban ci arzikin rikonta a mini karar nima ubanta ba ne".
Na yi yak'en da babu nishadi na ce "Abida ai karimiya ce wajen magana d'aya tabbas ita ta haife ta. Amma har k'asa ta rufe mata ido ba zata jinginawa kanta Farha ba don kuwa tasan tawa ce."
Daga haka na ce "Zaka samu kaimu tasha ne ko mu je mu hau Napep?"
Ya ce"Mu je na ajiye ku"
Muka tafi tare da su Amrah suka kai ni tasha ya tafi da su zai kaisu wajen Hajiya na sani kuma ya hana tafiya da sune dan kada a sace su. Yaya Farouk sai kukan sharb'e yake yi. Haka Farha sai ta zama wata iri don gani take yi Yaya shine abokinta. Tafi sonsa akan yayarsu.
Sanin da na yi Yaya Hamida ba yarda zata yi mu je gaisuwar tare ba. Sai na tsaya a Kaduna gidan Saddiqa cikin sa'a ta gamsu zata bini mijinta kuwa bai hana ba, tunda ma a Abuja yake aiki. Don haka ya siya mana ticket din jirgin k'asa na k'arfe shida na yammaci. K'arfe takwas muka isa, muka tarar yana dakonmu.
Da kansa ya kaimu Wuse2 gidan da su Momi suke zaune anan kuma ake karban ta'aziyar.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cike da alhini suka karbe mu.
Washegari muka gaisa da Yaya Asad duk da yana cikin gigita ya ji dadin ganinmu. A sanyaye ya ce "Sannunku Bilkisu da Saddiqa na gode Allah ya bada lada."
Haka ma Baba Babba da Momi.
Abida mun gaisa ba yabo ba fallasa. A wannan karon dakinmu daban Momi ta bamu. Duk inda Farha ta yi junior na binta na dinga mamakin hakan tasirin jini ne ko kuwa kammaninsa da yake ga ni a tare da ita ne? Ya dinga janta ta zo su je d'akin Ammi ko su yi wasa ita kuma sai da k'yar take binsa a cewarta ita ba yarinya ba ce kamarsa.
Da azahar Ansari ya iso.
Haka dai aka dinga karɓar gaisuwa ana sharar hawaye. Ya'yanta abin tausayi.
Ban sake tsorata da mutuwar ba sai da na ji sanadin mutuwarta.
Ashe wai allurar da ake yi a spinal cord take yi da take saka girman mazaunai da cikar kirji tare da fidda cikakkiyar sura mai dauakar hankali. Ashe hadarin da yake cikin irin wadannan alluran da magungunan bature da mata suke dirkawa kansu da sunan k'arin girman halittunsu ko ragewa yafi hadarin jirgin sama muni. Lafiya k'alau ta kwanta amma tashi ya gagare ta. Haka aka kwashe ta zuwa asibitin koyarwa na jamiar Fatakot. Sai dai gabad'aya wajen kugunta ya dagargaje a dalilin yadda ake mata allura a wajen da yake da had'arin gaske wato spinal cord. Ciwo bai bayyana ba sai da ya gama raraketa. Ko da aka je asibitin suka ce ba abin da zasu iya don hatta fatar ta da nake ganin tana glowing na mussaman ashe akwai sindarin hydroquinone a mayuka masu tsada da take tu'amalli da su.
Sinadarin da yake kwaile fata amma a wajen matan yau glowing ne. Tabbas da na ganta a haihuwar junior na ga halittarta ta sauya gabad'aya sannan fatarta ta zama ta alfarma jikinta ya zama rugu rugu tamkar tana cikin shekarun kuruciya, ta mini kyau ta burge ni, ni kaina mace, bare mijinta. Ashe da kuɗinta ta siyawa kanta lalurar da zata k'wamushe rayuwarta gabad'aya.
*
Hankalina ya rub'anya tashi tare da tunanin ta ina za'a bayyanawa mata illar kasassabar da suke yiwa kansu a dalilin maza?
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!
Sannan na sake tsorata da yadda mahaifiyarta take kuka tana fadin ita damuwarta yaran nan da ba wadda aka aurar duk da Aysha a lokacin ta kammala makarantar call to Bar a Enugu. Barrista ce ta gado Yaya Munira.
Sai fadi take yi a mayar da Laura kanwartta da take ruk'onta d'akin marigayiyar tunda ta saba da yaran, itama ta kammala jami'ar a wannan shekarar.
Na rasa me zan ce don na lura ita kubucewar Asad a matsayin surukinta yafi nukurƙusanta.
"Ke Duniya!
Na furta hakan cikin d'imuwa mai yawa.
A yammacin ranar Saddiqa mijinta ya zo ya tafi da ita inda yake akan gobe sai saka ta a jirgin k'asa na safe ta koma Kaduna. A dalilin Yaya Asad ya ce "Gobe mai d'akin gwamnan Katsina da wasu mukarraban gwamnati zasu yi masa ta'aziya a madadin gwamna da baya nan. Yana Saudiyya yana gabatar da umrah. Dan haka na bari sai na shiga jirginsu mu koma tare na huta da dogon zaman mota.
Ban yi masa musu ba na amince. Na zauna Sai dai basu zo washegarin ba. Sai da suka k'ara kwanaki biyu suka iso ranar sadakar bakwai da wuri.
Wanda mahaifiyarsu Anty Rukayya so ta yi daga taron sadakar bakwai a mayar da Laura d'akin yayarta. Na rasa gane wannan gaggawar da take yi. Ai ta bari a yi arba'in duk saurinta. Yayin da gogan ya yi biris bai tanka ba sai dai kallonsa kawai zaka yi ka gane bai gamsu da tayin da take ta yi masa ba.
Ranar da zamu tafi junior kuka tuburan Sai ya bi Farha. Na dinga mamakin yadda yake sonta kai tasirin jini yawansa ya kai k'urewa. Kuka sosai ya rik'e ta. Na kalli Abida na ce "Ko na tafi da shi idan hutunsu Farha ya k'are sai na dawo miki da shi?"
Ta girgiza kai tare da ce wa "Bar shi kawai Bilki Idan ya biki kafin gari ya waye zai dame Ki da kukan nemana ".
Na kalli Farha da take rike da hannuna na ce "Farha to Ki zauna nan da 7days sai a kai ki Kaduna gidan Anty Saddiqa daga nan sai Dady da yaya Amrah Su zo Su d'auke ki ku dawo gida ".
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta ce "Tare da ke zamu zauna?"
Na ce "A a ni yanzu zan tafi ke kuma zaki dawo nan da just 7days".
Ta make kafada tabbacin bata yarda ba.
Na ce "Ki ga fa junior na kukan bai so ki tafi".
Ta ce ",To shi ya zo mu tafi gidanmu mana ni dai ba zan zauna ki tafi Ki bar ni ba".
Ganin haka ya Asad ya sure shi ya kaiwa momy shi yana ta faman kuka sosai.
Kowa Sai da ya yi mamakin junior sosai.
Wannan karon har harabar gidan Abida ta rako ni. Ta k'asa hakuri ta ce "Bilki telan da yake yiwa y'ay'anki dinki ya iya sosia".
Na kalli leshin da na sanyawa Farha na tabbatar kyaun da ya yi Mata ne da yadda ya zauna cif ya saka Abida k'asa hakuri ta yaba a fili.
Na ce da junior mace ce da sai djnga yi mata. Mace amma Kano take. Indai dinkin yara mata ne da zannuwan gado to kawai kin je makura wajen samun waccyta kware."
Abida ta ce ", Gaskiya na gamsu. Amma zan karbi lambar na bawa ya'yan Yaya Asad tunda hasu Noor da Amal nan duk da sun fara girma".
Na ce "babu damuwa zata yi musu kuma ta aiko musu kayansu cikin aminci."
08080266674 ga lambarta ga masu son ganin y'ay'ansu cikin d'inkuna na garari da zannuwan gado na alfarma.
Haka na shiga cikin tawagar first lady muka juya Katsina.
Tun kafin mu tashi na fadawa Baban Amra a jirgi zamu dawo ya taremu a iyafot nan anjima.
Cikin sa'a kuwa a iyafot din na tarar da yara suna dakonmu.
Farouk ya ce "Mamah kinsan a jirgi zaku dawo kika tafiya da ni? Kinsan dai ina son shiga jirgi ko?"
Na murmusa na ce "Da ikon Allah yayana zaka hau jirgi zaka biyawa wasu ma Su hau in sha Allah ".
Dad'i ya kama shi ya ce "Ameen Mamah."
Amra ta ce "Amma ni fa Mamah ni Ki Abujan ma ban tab'a zuwa ba".
Na ce kema haka Amra duka ina yi muku addu'a. Abuja kuwa zaki je hae sai kin gaji".
Ta ce "To Mamah. Ammina mai ta baki ki kawo mini"
Na ce ",Sai mun je gida leda ne a daure ban bude ba, idan na baki sai ki bude da kan ki."
Ta murmusa tare da ce wa "Na gode ".
Ina gaba yara na baya. Ya kalle ni ya ce "Ya k'arin hak'uri?"
Na amsa da "Alhamdulillah!
Ya ce "Na ji dadin ganin ki sanye da hijab din nan ya rufe ki ruf sannan kuma ya miki kyau sosai."
Na murmusa ina jin dad'i har k'asan raina don zan iya cewa wannan ranar ta shiga cikin ranakun da ba zan mance ba don kuwa yana wahalar gaske ya yaba mini idan na yi kwalliya.
A raina na ce "Madallah da Gunis hijab. Hijabanta duniya ne don kuwa yankan hijabanta zama suke a jikin mutum daram a kuma sake sosai a cikinsu. Ga yadin masu dad'in sawa, ba masu saka jin zafi ba ne.
(08163761797 gunis hijab and more)
Muka isa gida Amra ta dauki jakar kayanmu yayin da Babanta yake rike da tawa. Shi kam Yana son rike mini jaka. Yana wahalar gaske yarana ko wasu mutane na waje Su gane yana musguna mini don yadda yake mini a gaban mutane ya saka danginsa suka washe ni. Kowa kallon sha'awar zamana da mijina yake yi amma a zahiri ni kad'ai nasan gashin kumar da yake yi mini.
*Bayan watanni hud'u*.
Sannu a hankali sauyawar Sahal ta cigaba da yawaita. Kamar yadda na fada ba wai fada ko sababi yake yi mini na kaitsaye ba, kawia shagulatun bangaro yake yi da ni. Matuk'ar waya na hannunsa ba shi da lokacin komai ko fahimtar komai. Sai dai kawai ka ga yana ta danne danne a waya yana murmushi. Sannan kaffa kaffa yake yi da wayar kamar me. A da baya dare a waje duk inda bakwai take ya dawo gida, ya ci abinci ya tafi sallar isha Idan ya shigo sai kuma gobe. A yanzu sai ya kai tara wani lokacin har goma bai dawo ba. Na fara damuwa sosai, ga rashin samun biyan bukata wanda na lura tamkar ya manta ina da haƙƙin akan haka. Sannu a hankali na shiga wani irin yanayi da likitoci suka tabbatar mini ciwon damuwa na (depression) ke son kama ni. Suka bani shawarwarin na k'arantawa kaina tunani da ragewa kaina damuwa. Aka d'ora ni kan magunguna.
Basma ta dinga fad'in "Idan ba ki shafawa kanki ruwa akan lamarin Baban Amra ba sai hawan jini ya kama ki Bilki. Ki tattara shi ki koma gefe ki rungumi ya'yanki ki bashi dama ya yi abin da yake so".
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ina son na bude baki na fada mata abubuwan da nake fuskanta sai na kasa, sai na ji Abida kawai nake son farkewa damuwata ko da kuwa zata balbale ni da sababi ne. Amma dai Maman Abdul ta riga ta fahimci rayuwar da nake yi a gidana.
Shiyasa ta tsani Sahal, shima kuma ya tsane ta ainun.
Wata rana da daddare sai juyi nake yi a gado gogan yana kwance lamo da alamu ma barci ke shirin d'auke shi. Na daure na cire kunya na mirgina kusa da shi na saka hannu a kansa ina shafawa zuwa kunnesa a kokarina na isar masa da sakon gayyatar da nake yi masa.
Tsawon lokaci ina yi masa hakan ya k'i yin motsi sai ma lumshe idonsa da ya yi.
A hankali cikin rada na ce "Dady wake mana".
Murya ba amo ya ce "Wlh kaina ciwo yake yi mini, Ga gajiya da ta yi mini dabaibayi gabad'aya".
Ina jin haka na gane ba zai amsa gayyatar da na cire kunya na yi masa ba.
Na cije na ce "Anya Dady kana lissafin adadin watannin da muke kallon juna tamkar hoto kuwa?".
A takaice ya ce "Ki yi hakuri in sha Allah jibi zamu yi, ki shirya tarbata sosai '
Jiki na k'warai na matsa daga jikinsa. Amma zuciyata ta yi nauyi sosai.
Haka na hak'ura ina fatan Allah ya kaimu jibin lafiya tunda dai ina so, ba ni kuma da mai yi mini sai shi.
Da hantsi na yi magana da (Bojuwa herbs 08032773332 what'sapp only) na saka order din ciccibin garari da Tsumin saiwowi a kokarina na sabunta kaina a wajensa. Na tura kuɗin na tabbatar gobe sassafe zata turo mini Katsina. Ban ji ko d'ar ba tunda dukkan costomers din Surayya Halin yau mun tabbatar bata magana biyu, na shaida a gobe da safe zan karba na ci kafin dare ya bi jikina in sha Allah.
Na je saloon na wanke kaina. Nadinga bare bare tamkar me. Amma me da jinin ta zo sai bawan Allan nan ya yi barcinsa da na tashe shi sai ya sake ce mini ya sake d'agawa sai wata jibin a dalilin jikinsa na yi masa ciwo. Daren jiya ke nan wanda hakan ya sababa mini bacin rai da tsananin tashin hankali. Daga baya kuma na zo na gano soyayyar da yake yi da dalibata Hawwah. Da irin sababin da ya dinga yi mini. Har ya zama ba'asin da na shiga d'imuwa da tashin hankali. Da yadda Basma ta zo gare ni ta kai ni asibiti har zuwa lokacin da ya tabbatar mini yana neman aure.
Na ja gauron numfashi tare da goge hawayen da ya k'i yanke mini don kuwa na famowa kaina abubuwan da suke nauyaya zuciyata.
A fili na furta "Allah ka yaye mini nauyin zuciyar da ya dame ni.
Allah ka taimake ni ka kawo mini ɗauki da kanka. Allah ka bayyana mana Yaya Sulaiman idan yana da rai, idan kuwa raine ya yi halinsa Allah ka masa rahama."
*Nan ne karshen hakaito labarin da Bilki ta bamu.*
*Sai a gyara zama don jin danbarwar da zamu sake kutsawa da kuma abin da zai biyo ba.*
*Ina baku tabbacin zaku nisahdantu a gaba.*
*MalaysianFabrics*
*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*
*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*
*7020695644.*
✍️✍️
Surayya Dee
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilkisu ta gama hakaito duka tarihin rayuwarta, gabaɗaya jikinta ya mutu ba ƙwari. Tana zaune tana sauke tawagen numfashi lokaci ɗaya tana mai tsiyayar ƙwalla.
Kirjinta ya yi nauyi. Tarwatsewar gidansu shine mafi tashin hankali a rayuwarta. Sai dai nade k'afar wandon da Sahal ya yi yake