Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   20 / 37

57K to 60K   out of 110.8K words

shirin nuna mata ainihin shi namiji ne yana matuk'ar sakata zullimi da fargaba

Ba ta san iya lokacin da ta ɗauka zaune tana kuka ba sai da Alti ta leko don ta yi mata sannu sai ta iske ta cikin kuka.



"Yanzu Hajiya ba ki bar wannan kukan ba?

Ashe ba zaki dangana ba?"

Jin haka yasa ta sake rushewa kuka ta ya ya za a ce na bar kuka ahalin abin kuka ne ya dabaibaye rayuwarta

"Na sha faɗa miki Hajiya, kuka ba shi ne magani ba addu'a zamu cigaba da yi. In sha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe. Dazu har murna ta kama ni, ganin kin karbi rarrashin da na yi miki kin ware sai kuma ki sake rikice wa?"

Alti ta sake fad'a lokaci daya tana dafa kafaɗarta bayan ta ƙarisa shigowa cikin ɗakin ke nan.

"Alti kullum fa haka kika ce mini. Ga shi shekaru sai sake turawa suke yi amma babu wani abu da ya sauya."

Ta ƙarishe faɗa cikin kuka da har muryata ta dishe bata fitowa sosai.

"Kar ki cire rai ga rahamar Allah. Ubangiji yana sane da ke, ina da yaƙinin ya amsa addu'arki Nikawai mu jira lokaci Hajiya."



Ta tsinci kanta da share hawaye tare da gyaɗa mata kai.

"Na gode Alte kin kasance da ni a lokacin da ba kowa a kusa da duniyata. Ba zan taɓa mantawa da kasancewarki tare da ni ba."

Bilkisu ta fad'a cikin dauriya.

"Ba komai Hajiya mun zama ɗaya."

Da daddare da Baban Amrah ya dawo bai neme ta ba. Itama bata neme shi ba, saboda ta riga ta shiga damuwar da ta zarce fishinsa takura, tana cikin wani yanayin da take bukatar kadaici. Ranar ita da shi kowa a dakinsa ya kwana sai da safe ne ya shigo ɗakinta da shirin fita aiki.

Kallon kallon suka yiwa juna.

Kamar ba zata gaishe shi ba, saboda haushin faɗa in faɗan da suka yi da shi Har da ce fad'in ko yanzu kasuwa ta watse d'an koli ya ci riba. Maganar ta yi mata nauyi da yawa. Amma ganin ya biyo ta thar ɗakinta sai ta daure ta gaishe shi a takaice.

Ya amsa da fad'in "lafiya lau, ya jikin na ki?

A ginshire ta amsa masa da cewa ta ji sauƙi daga haka shima bai ƙara tofawa ba, ya saka kai ya bar mata ɗakin. Ta bishi da kallon mamaki tana ayyana, shi yanzu jira yake yi ta ba shi haƙuri ahalin shi ne ya yi mata laifi! Murmushin gefen baki ta yi lalle ko sai dai su dauwama a haka abin da Abban Amrah bai sani ba, yanzu ba ɗaya ba ne da baya. Abubuwan da ta ɗauka a wancan lokacin yanzu ba zata iya kauda idanuwa a kansu ba.

Anya kuwa Bilkisu?

Amma dai mu cigaba da bin ta a hankali.

Sun shafe sama da sati duna zaman doya da manja. Yadda baya shiga harkarta itama bata shiga harkarsa.

Daran da suka yi sati basa kula juna ya biyo ta har ɗaki ya ce "lokaci ya yi da zai ta shi daga gidanta ya yi saboda ya ga abin ya zo da cin mutumci tun da har 3na fara yi masa gori."

"Ni na yi maka gori Baban Amrah?"

Ta tambaye shi a gajarce.

Cikin gadara ya ce" E kin yi mini gori kin faɗa mini maganganu masu zafi saboda kin ga ina zaune a gidanki, to kar ki manta nima ina da nawa gidan saboda haka can za mu koma."

Har ya fice na kasa iya tanka masa. Dariya ma ya ba ni domin sai na ga ƙarfin halinsa ma, ya manta da ce wa ginin gidan kaso mafi girma da dukiyata aka yi shi? Amma yana faɗa mini cike da gadara wai na yi masa gori zai tashi daga gidana ya koma gidan shi. Lallai ma!

Sahal.

Zaune a cikin mota suna hira da budurwan shi a bakin hostel ɗinsu don ba yar Katsina ba ce karatu ne ya kawo ta amma asalin ta y'ar kaduna ce.

Tun bayan isha'i ya zo suna ta hira. Tuni kuma ya gana da mahaifinta tun farkon zuwansa gidansu a lokacin da suka je Zaria da Amrah Bilki ta wuce Abuja a wannan tafiyar ya je Kaduna gidansu tunda suna hutu ta je gida.

A wannan ranar sai ta gan shi duk wani iri a hargitse.To

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "My Dear me yske faruwa ne?"

Ta faɗa tana kallon shi, lokaci ɗaya tana kashe shi da kallo da ita kaɗai ta san yadda kallon yake tasiri a wajen Sahal.

Kamar yadda ta sani ɗin ya yi tasirin domin nan da nan ya susuce ya fara mata sambatu.

"Zullimi nake shiga kada samarin zamani su mini shigar sauri, so nake ki ba ni dama gemu da gemu su zauna akan batunmu. Kin ga dai ni ba yaro bane dan zan yi ta jan doguwar hira a tsakaninmu ".

Cikin tattausan lazafi ta ce" To ai kai nake jira My Dear! Mun gama fahimtar juna, kuma ka nemi izini magana da ni wajen Baba. Na aminta da kai. Yanzu sai ka turo magabatanka gidanmu don magana ta nuna".

Da sauri ya ce" Na gode sosai in sha Allah ba za ki yi nadamr aurena ba "

Nan da nan fara'an fuskarta ya ƙaru ta shiga kashe Shi da kalaman da ta san suna kunna shi, shima yana mayar mata da martanin cikin soyayya da kulawa kamar ba shi ne ya ajiye kamar su Amrah a gida ba.

Sai wajen goma da rabi ya bar makaranta zuciyarsa kamar farin takarda ranar kwanan farinciki ya yi, gwara ya yi auran nan ko Bilki za ta shiga taitayinta shi yasa aiki na yi masa sauƙi ya je Zaria wajen Baban zaria ya kai masa maganar auren da ya ke son ƙarawa. Akan ya yiwa Baban Mashi magana su nema masa auran.

Cikin mamaki Baban Zaria ya ce" Aure kuma Sahal? Daga samun aikin ka sai k'arin aure ya biyo baya? Anya kuwa?"

Cikin ƙankan da kai Sahal ya ce" Baba Allah ne ya ba mu umarnin mu ƙara in za mu yi adalci sannan da halin ƙarawar. "

"Jin haka ya sanya Baban Zaria fadin "Tabbas haka ne. Na gamsu da mganarka."

Jin haka ya sa ya gyara zama yana sake faɗin" Kuma ni da matata muna da fahimtar juna ina da tabbacin babu wata matsala Baba."

"To Alhamdulillah. Haka na da kyau. Za mu je zan yi magana da Baban Mashin in sha Allahu"

Sahal ya ji daɗi haka ya baro Zaria cike da farinciki, bayan ya cika Baban Zaria da iyalasa da alheri suna ta godiya.

Tunda ya dawo akai akai yake kira Baban Zaria ya ji yadda ake ciki shi. Baban ya sanar masa sun yi magana da Baban Mashi ya faɗawa yarinyar ta shaidawa iyayenta suna nan zuwa ranar lahadi. Murna wajen Sahal ba'a magana daga shi har ita Hawwan suna cikin farinciki, tuni ta sanarwa mahaifiyarta ta faɗawa Babansu ta kuma turawa Sahal lambar kanin babanta shi kuma ya turawa su Baban Zaria.

Baban Zaria da Baban Mashi sun isa Kaduna nemawa Sahalu aure kuma an yi musu karban mutumci sosai, bayan dogon jawabi da dalilin zuwansu aka yi fatan alheri. Tare da cewa sun bawa yaro yarinya. So da sun zo da sadaki na sai a daura auren kawai.

Su Baban Zaria suka bada uzzirin Basu zo da shiri ba Aman Su sauarare su nan ba da jimawa nan da sati biyu za su dawo da sadaki da kudin gaisuwa. Ma'auratan kuma su yi gwajin lafiyarsu.

Da wannan daddan labarin suka dawowa da Sahal. Wanda shi tayar masa da hankali labarin ya yi tunda Bai shirya babl. Sai Dai Bai yi turjiya ba tunda yana so Yana Kuma son ya tsura da mutuncinsa a idon yarinyar da iyayenta. Haikan ya tashi ya fara fafutukan kamallah ayyukan da suka rage a sabon gida. Allah ya taimake shi akwai kayan band'aki da suka yi ta siya yanzu kawai ma'aikata ya kira aka fara aikin wasu na fenti wasu na hidimar hattama band'aki da sauransu. Yanzu hankalinsa da burinsa na wajen gama wannan gida da auransa. Bilki ta fahimci baya cikin natsuwarsa amma ba ta kawo komai a ranta ba ta ɗauka maganar da ya yi mata yasa yake ƙoƙarin ganin gidan ya kammallah ashe shi nasa shirin dabam.

Cikin sati biyu aka gama komai hatta fenti an gama. A kuma lokacin su Baban Zaria suka koma suka kai kudin aure tunda sun kira su daga can sun ce su zo sun gama bincike. An saka ranar aure wata daya kamar Yadda Sahal ya bukata a masa alfarma haka tunda bai yi lefe ba.

Ganin Sahal ya kammala da hidimar gini ya kuma bawa Yaya Toure kudi akan ta je Kano ta hado masa lefe. Ta ce kudin ba zai isa ba. Amma zata cika masa daga baya sai su warware.

Ya samu Bilki ya ce an gama gida zasu tare amma yana so ta zaɓi bangaren da ta ke so ko kasa ko tsakiya saboda can sama nasa ne.

"Ban ga ne na zaba ba, dama ba duka bangaren ne namu ni da yara ba?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilki ta tambaya cikin mamakin sa matuk'a da gaske.

Cikin halin ko in kula ya ce" A a bangare ɗaya zan iya ba ki daga ciki."

Mamaki ya sake kamata to me ya sa zai ce haka kafin ta ce komai , ta ji ya cigaba da magana

Cikin dakiya ya ce "Dan mu gama maganar gabad'aya. Ki nutsu ki ji ni da kunnen basira, batun auren da na ce miki zan yi ne ya matso, za'a yi shi a karshen wata mai kamawa idan Allah ya yarda".

Kan Bilki ya sara, zuciyarta ta harba da tsananin gaske. Gidan da ita ta gina da kuɗinta shine zai saka wata macen a ciki?"

Wanne irin zalunci ne haka?"

Take ta tuno Abida ta sake tuna Basma da ta ce mata ta yi wautar zuba makudan kudade wajen ginawa miji filayensa. "Tabbas na yi wauta Basma! Komai ya na neman kubuce mini Abida ga shi kin yi mini nisa.!

Bilki ta furzar da wadannan kalaman cikin fitar hayyaci.

Ya make kafaɗarsa tare da fad'in dama "Ai nasan wadannan halittun guda biyu basa sona na kuma tabbatar a yanzu Basma ce take d'ora ki a keken bera tunda uwar iya kun yi tawarwatse da su".

Kuka sosai Bilki take yi wanda Duk mai imani sai ya buge shi amma haka ya saka kai ya barta.

Kukanta ya k'aru a dalilin ta ji ciwon yadda ya goranta mata tarwatsewarsu da su Abida ".

Ta dinga yinsa har ta gajiya dan kanta tunda a d'akinsa suka yi da a d'akinta ne tasan da tuni Alti ko Alawiyya sun leko dan ganin lafiyarta.

Da k'yar ta fito zuwa d'akinta ta yi wanka ta yi salla tana adduar neman sassauci daga azabben kishin da yake neman fasa mata zuciyarta.

Washegari ya sake tuntubarta akan ina take so sama ko k'asa don iyayen yarinyar zasu zo ganin d'aki.

Cikin yanayin da yake fahimtar iya gaskiyarta ta ce " Ni ba zan kaura ba ka bata duka bangare biyun. Ni kuma ina nan da yara idan ka samu sararin zuwa ka leko mu".

Ya zuba mata ido amma kuma ya tabbatar da she means her words.

Ya kasa ce mata komai ya share maganar.

Amma gabad'aya jikinsa ya yi sanyi ya tabbatar idan ya amince da hukuncinta sai duniya ta yi masa tofin Allah tsine bayan haka kuma haƙƙinta ba zai bari ya rayu a gidan cikin nutsuwa ba.

Kansa ya kulle ya rasa dabara. Kawai sai ya ya ɗauko mata Hajiya har gida ya ce ta yi mata faɗa, nauyin Hajiya da yadda ta dinga bata baki da fadin kishiya ai y'aruwace me zai saka ta bar mijinta saboda da wata alhalin shi bai barta ba. Haba Bilki ya da haka kuma? Ke da na ke yabon kirkinki, tunda ya samu ya gama gina gidan nan ki yi hakuri ki karbi bangare ɗayan ki koma, ai yanzu sai mutane su yi ta yamididin ya samu wadata zai yi miki butulci idan na isa da ke ki bi umarnin mijinki, bai kyautu a ce wata ce za ta zo ta fara shiga gidan da aka yi gwagwarmaya da ke ba."

Bilki ta kasa magana tana kallon Hajiya, saboda darajarta yasa ta amince za ta koma gidan babu dogon turanci.

"Ba komai Hajiya in sha Allahu zan koma."

Ta fad'a a takaice.

Hajiya ta yi ta saka mata albarka.

Har haraba ta rakata inda Sahal din ya mayar da ita kamar yadda ya dauko ta.

Tunda kuma ta yi wa Hajiya alkwari ta shiga fakin din kaya Alti da aluawoya na taya ta.

Yara suna ta tsallen murna tun da Dady ya faɗa musu zasu koma sabon gida.

Bata siyi komai ba tunda kayanta sabbi ne basu ji jiki ba. Cikin sati ɗaya da zuwen Hajiya suka tare a sabon gida, k'asa ta dauka ita da ya'yanta, ta bar musu tsakiya da saman shi da amaryarsa.

Dama kuma zanen gidan kasa da tsakiya duk iri d'aya ne. K'afar benen akwai inda za a shiga ta falo da kuma ta kofar baya.

Dan haka amarya zata dinga amafani da ƙafar benen baya ne ba wacce take cikin falon Bilki ba.

Tunda kuma suka koma sabon gida Bilki ta sake zama shuru shuru, duk da ba ta ji zancen saka ranar auran Baban Amrah ba amma a kalaman Hajiya ta fahimci auran ya zo sai shi da kanshi lokacin bikin saura sati biyu ya ke fada mata, ko a fuska ba ta nuna masa damuwa ba ta yi masa fatan alheri. Shi kansa ya fara damuwa da yadda shirunta ya k'aru har yara sun fahimci rashin son yin maganarta ya ninku sosai sannan kuzarinta ya ragu ainun. Gabadaya ga ni take yi tamkar yarinyar na nunata ko Sahal ya gama fad'a mata yadda suke zaune.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bayan haka abin da Sahal ya yi mata na tarewa da sabuwar amarya cikin wannan gidan ya yi matuk'ar tsorata ta tare da jefa mata firgici da faduwar gaba mai yawa.

An yi biki sosai a can gidan Hajiya duka y'anuwan Sahal sun taru, Bilki ko daga ita sai ya'yanta sai ko Basma. Bata gayyaci kowa ba don kwata kwata bata kwarafniya tafi son yanayin shiru.

Kayan fadar kishiya ma bai yi mata ba haƙuri kawai ya bata tare da gabatar da uzzirin cewa abin ya zo a kurewar lokaci ne. Amma zai mata ita da yara. Bata nuna masa komai ba, don kuwa bata saka rai zata samu wani abu daga bangarensa ba.

Ko ranar ɗaurin auran haka ya yi ta rawan kafa da safe kafin su tafi daurin aure. Sannan gayyar abokai ya yi sosai tunda gidan suka biyo suka dauke shi. Daga dauren aure ba su dawo ba sai da tawagar a amarya Tuni Bilki ta sanya Alawiyya da Alti sun yi snacks sosai, sai dai ba'a soya ba, ta adanasu a firij sannan an zuba ruwa da lemu a fridge, ta yi hakan ne idan iyayen amarya sun girmamata sun zo dakinta zata basu idan kuwa basu neme ta ba, sai ta bar abinta a firiza. A gidan Hajiya aka fara sauke amaryar sai daga baya aka kawo ta nan gidan. Kaitsaye falon Bilki dangin amarya suka yada zango.

Sosai Basma da Alti suka karbesu yayin da Bilki take zaune fuskarta a sake. Nan da nan aka kewayesu da ruwa da lemu.

Aka yi addu'a da fatan alheri.

Sannan yan'uwanta suka bawa Bilki amana ta kuma ce ta karba Allah ya basu zaman lafiya.

Sannan suka wuce saman amarya.

Bilki ta saka Alti ta yi musu abinci a daran da safe ma ta ba da umarnin a yi musu abin kari duk da gogon ya kawo musu daga gidan Hajiya Alti take faɗa faɗa mata. Wataƙila yana tunanin Bilkin baza ta yi ba ne.

Washegari da zasu tafi ta saka aka soye musu samosa da springrols aka zuba musu babbar container aka basu. Godiya kan godiya suka yi mata. Ita da kanta Bilkin ta tabbatar mutanan Zaria karimai ne ta gane hakan tun sadda ta yi zaman garin. Yanzu ma sun nuna mata halin girma tunda wasu dangin amarya idan sun kawo ta tun daren suke dasa fitinar da ba wadda yasan inda zata tsaya su tafi su bar y'arsu cikin garari. A zuciyarta ta dinga fatan yarinyar ta yi halin y'anuwanta tare da jin nasihar da suka yi mata. Idan har ta bata girmanta ita kuwa zata yi mata adalci don ba ta yi mata laifi ba, don ta zo gidanta a matsayin second wife. Ba kuma ita ta kawo kanta ba, maigidan ne ya kawota bayan ya durkusa a gaban iyayenta ya nemi alfarmar a ba shi a ita. Shima kuma Allah ne ya halasta masa k'ara aure. Idan kuwa haka ne zata yi iya kokarinta ta danne duk beken Sahal da take ga ni zata yiwa yiwa yarinyar adalci matuk'ar ba ta nuna mata d'ab'iar albasa ba.

Bayan an watse ranar da zai shiga ɗakin Amarya ya tarasu a bangaren Bilki ya yi musu nasihan zaman lafiya. Ita dai Bolki ta bashi tabbacin bata da matsala. Amaryan ma ta ce haka.

Ya ce " Maganar girki sai nake ganin a dinga yi tare tunda ke da ita kuna makaranta kullum. So idan Alti ta yi sai a dinga zuba mata Alawiyya na kai mata kafin ta kammala makaranta sai ta fara yin nata.

Me kika ce akan wannan batun Bili?"

Ya fad'a cikin sigar soyayya lallashi.

Take Hawwah ta ji wani iri a zuciyarta, ta sake karaya don

20 / 37