Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   30 / 37

87K to 90K   out of 110.8K words

yi masa jirwayen cewa za a tura su seminar Lagos kuma daga can yana tunanin za a tura shi America domin samun horo kan matsslolin tsaron da muke fama da su a Nigeria.

Baba Babba ya kalle shi yana faɗin" Kai Asad a kullum ba ka da wata magana sai ta aiki. Aiki aiki dai ba ka tunanin ma sake ajiye iyali ko ba domin kanka ba domin mutumcinmu iyayenka da yayan ka, kana da yara yanmata da suka isa munzalin aure. Da bakinka ka ce mini iyayen manemin Aysha suna so zo tambaya, a haka zasu zo su same ka, ba ka da mata sai yawon an tura ka can aiki, an tura ka can, kana ganin zaman ka a hakan alheri ne?

Anya ka yiwa kanka adalci Abubakar?"

Ya faɗa yana kallon Asad ɗin da ya sadda kan shi ƙasa.

Sai da Baba ya dire faɗan sa, sannan ya ɗago ya gyara zema yana faɗin.

"Baba sai ka ta yi mini faɗa akan zancen aure. Alhalin bani kaɗai ba ne bani da auran nan, ga yara nan a gaban ka. Gwara Abida da aure a kanta Maigado fa? Ai ba ta da aure amma ba a takura mata ba sai ni?"

Ya faɗa cikin ɗan ɓata rai shi a dole ba shi kaɗai ba ne.

Baba Babba ya karɓe da ce wa" Kai ba ka duba Bilki lallaɓata ake yi? Ta shiga gararin rayuwa kala kala ga rashin miji, ga mutuwar iyaye ga shi an raba ta da garin da yaranta suke yaka ke so ta yi? Ai Bilki abar tausayi ce, idan ba a rarrashe ta an gayyato mata farinciki ba me kake so a yi?"

Ya Asad ya ji daɗi an zo gabar da take so.

"To ni Baba ka bani ita na aura. Sai na taya ka rarrasan maka ita."

Ya faɗa yana sosa kansa alamun kunya.

Cikin mamaki Baba Babba ya kalle shi kafin ya ce" Asad da gaske kana son Bilkisu?"

Kansa na ƙasa ya ce" Wallahi Baba ina son ta, tsakanina da Allah!

Farinciki ya bayyana a fuskar Baba Babba.

"Idan kana son Balki to ka nemi yardarta idan ta amince, nima na amimce kasan yanzu ba yarinya ba ce tana da wannan damar sannan kar ka manta ko da suke yara ban yi musu auren dole ba bare yanzu tana da y'ancin ta yiwa kanta zaɓin da take so. Idan ta amince da kai to zan fi kowa farinciki zan kuma taya ka da addu'a Allah ya tabbatar. Idan har hakan ya faru komai zai daidaita, wakiar da ta nisantamu da juna zata bushe a zukatanmu. Ƴan'uwanta za su samu damar zuwa gidanka su yi zumunci, kai ma naka za su je gidanta, daga nan komai da ya faru na rashin jituwa a baya zai wuce ba na fatan na mutu na barku a cikin wannan halin. Sulaiman ya tafi ba mu san inda yake ba, idan yana raye Allah ya bayyana shi. Idan kuma ta san inda yake ta boye mana, idan ta zo hannunka kana hillatar ta duk za mu ji komai."

Yaya Asad ya ji ƙarfin guiwar tunkarar Bilki a wannan gabar tunda ya samu amincewar Baba Babba da Abida. Dama Abidan yafi ji da Usman amma tunda Abida bata botsare ba yasan Usman ba zai samu tallafi ba. Mamakin yadda Abida ta huce ta yi sanyi akan ahalinsu Bilki yake yi.

Da Bilki ta dawo ba wanda ya yi mata zancen zuwan Asad shi yasa ba ta san ya zo gidan ba. Shi kuma tun tafiyar shi kullum da safe zai tura mata sakon gaisuwar safe da asubar fari. Da daddare ma akwai na mu kwana lafiya. Ga k'iran waya akai akai, yana kashe murya yana yi mata kalamai irin na jirwaye duk da ta fahimci manufarsa amma sai ta nuna masa bata gane komai ba. Kuɗade masu nauyi yake turo mata akai akai, idan ta ce sun yi yawa ko ya daina. Ce mata yake yi idan Sulaiman ne ya tura mata kuɗi ai karba za ta yi ta gode masa, ba ta ce bata so ba jin haka yasa jikinta ya yi sanyi, bata sake ce masa komai ba, idan ya tura mata kuɗi sai dai ta yi godiya amma a cikin zuciyarta ta kudire yayaa Asad ba zai iya siyan soyayyarta da kuɗi ba. Kuma tana jiran ranar da zai gaji da ƙumbiya kumbiyarsa ya fito fili ya faɗa mata, daga ranar za ta fada masa ya daina wahalar da kansa don kuwa bata ra'ayinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A ranar da take wannan tunanin ya yi mata sakon yana so ya shigo gobe tana gida? Ta amsa masa da cewa tana wajen aiki. Bai ce mata komai ba sai ta ɗauka tunda ta ce tana wajen aiki ya fasa zuwa ne.

Sai me? Washegari zuwan da yamma tana ma shirin tashi daga wajen aiki sai ga wayarsa har sau uku, ba ta ɗauka ba sai da ya sake kira ta ɗaga nan yake shaida mata yana harabar ma'aikatansu ta NAFDAC.

Mamaki ya kama ta, ta ɗauka wasa yake yi sai da ta leka ta taga ta gan shi tsaye shi kaɗai ba masu tsaron shi sannan kamar ba da mota yazo ba. Dariya ta kusa subuce mata ganin gogan ya ci k'ananun kaya har da uban zanzaro.

Dole ta tattara komai nata ta yi sallama da abokan aikinta ta fito haraba tana mai kallon Ya Asad tana danne dariyantan in har saboda ita ya yi wannan gayun, to ta gwasale domin ba ta jin zai sace zuciyarta da haka.

Ita ta ɗauke shi a motarta suka bar haraban ma'aikatar. Cikin nutsuwa ta ce "Gida zamu je ko gidanka zan ajiye ka?"

Cike da kulawa ya ce "Yunwa nake ji sosai Maigado. Mu je L&N mu ci abinci ".

Zuciyarta ta harba amma ta had'iye komai. A hankali ta ce "To sai ka dinga nuna mini inda zan bi kasan ba ko ina na sa ni a Abuja ba. Idan kuma zaka karbi tukin to?"

Murya ba amo tsabar yadda ya shagala da kallonta tare da ayyana al'amura masu yawa akanta. Ya ce "Mu je zan yi guiding din ki in sha Allah ".

Bata ce komai ba ta cigaba da tukinta.

Bayan sun je sun natsu ya yi musu oder abinci daga ita har shi suka ci abincin domin itama yunwa take ji, kuma bai dame ta da magana ba sai da suka gama cin abincin suka natsa..

Sannan ya kalle ta yana sake gyara zama.

Bilki itama kallon shi take yi tana raya saka kananun kaya ba zai zama tawaya gare shi ba, tunda kullum cikin zanzaron kakinsu na yan sanda yake.

"Maigado."



K'iran sunanta da ya yi shi ya katse mata tunaninta.

"Na'am Baban Bilkisu."

Ta amsa tana kallonsa.

"Yau ga ni a gabanki ba a matsayin yayanki ba sai a matsayin masoyinki. Mai barar neman yardarki."

Ya yi shiru yana kallonta domin fahimtar yanayinta.

Ta yi k'asa dakanta tana wasa da zoben zinaren da yake hannunta.

Ya numfasa ya ce "Ina sonki kamar me, wani irin so nake yi miki da ba shi da alak'a da sha'awa, k'yale kyalen rayuwa. Tun kina budurwa nake sonki har yau din nan da kika zama uwar ya'ya ban ji son nan ya gushe ko ya ragu ba. Dan Allah Maigado kada ki bari ki sake subuce mini a karo na biyu. Ki ji tausayina ki kalli dinbin soyayyar da nake yi miki. K'addara ce mai karfi ta sake had'a mu. Idan a da kin k'i karɓar soyayyata saboda ina da mata, to Ubangiji ya sake hadamu a yanzu alhalin ba ni da mata. Ki ba ni dama na nuna miki dinbin soyayyar da nake yi miki Balkees".

Ta yi shiru ta kasa ce wa kanzil.

Maigado ɗago ki kalle ni.'

Ya sake faɗa cikin wani irin amo. Amo irin na ma'abota soyayya da bege.

A hankali ta ɗago tana kallonsa saboda jikinta ya mutu da kalamansa.

"So nake na killace a d'akina, na yiwa sauran maza kwalelenki. Dama ɗaya nake so ki ba ni. Damar da zan mayar da ke sarauniya da ta yiwa mata dubu zarra. Don Allah Balkees kada ki tankwabar da soyayyata, na yi miki alkwarin za ki yi farinciki a tare da ni in sha Allahu."

Ya faɗa kamar ya yi mata kuka.

Bilki ta ga idan ta zauna tana jin kalaman bakinsa tausayinsa zai kamata ta iya ba shi dama, shi ya sa kawai ta haɗe rai tana kifta idanuwana kafin ta nisa ta ce

"Gaskiya Baban Bilki ka yi hakuri. Ba yanzu na shirya sake aure ba "

Ta fada kai tsaye tana kallonsa Gabansa ya faɗi murya na rawa ya ce'" Haba maigado, me yasa za ki ce haka? Ai ba za ki dauwama ba ki yi aure ba, tunda ya zama mahadin rayuwa kuma aurene mutuncin mutum mussaman mace."

"Ni dai gaskiya ka yi hakuri. Kai yayana ne shi ya sa ba zan so na ɓata maka lokaci ba."

Cikin mazarin jiki ya ce" Maigado ba za ki bukaci yin shawara ba?"

"Bana bukatar yin wata shawara na riga na faɗa maka matsayata."

Saboda kar ya sake yi mata wata magana ta ɗau jakarta ta bar shi a wajen.

Yana kiranta, amma ba ta dawo ba, ta bar sa a wajen ta shige motarta ta kama hanyar gida.

Shi kuma hankalin shi ya tashi nan take ya kira Abida ya fada mata abin da ya faru.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "To ka bar komai a hannuna Ya Asad ba dai ka fada mata ba ai ka gama mai wahalan."

Daga haka suka rabu saboda damuwa da tashin hankali ma. Tawagarsa ya k'ira suka dauke shi tamkar yadda suka kai shi Nafdac office.

Abida kuma ba ta yiwa Bilki maganarsa ba ko da ta dawo, saboda ba ta so ta fahimci kamar za ta yi mata dole ne, amma tana lura da ita domin ta samu wata damar da za ta kawo mata maganar.

Kwana uku tsakani, ranar jumma'a bayan Baba Babba ya dawo daga masallacin Bilki ta zo wajensa suna hira.

A cikin hiran ne ya kalle ta yana fadin"Bilki ina son na yi wata magana da ke."

Bai ba ta damar maganar ba ya cigaba da fadin" Aure nake so na yi miki Bilki. Saboda ina son na ganki kin samu natsuwar irin ta aure, ko Abida da kika ga ban yi mata maganar aure ba ina ji a jikina Sulaiman na nan a raye kuma ina ji a jikina zai dawo in sha Allahu "

Bilki ta yi shiru kawai gabanta na faɗuwa.

"Idan har zai yiwu ina son na ba da auranki a karo na biyu Bilkisu."

Baba Babba ya sake fada mata..

So take ta ji wa kuma Baban zai aura mata.

"To Baba."

Ta amsa mishi tana son jin wane ne?

"Idan kin amince Asad zan aurawa ke. Ya zo ya duka mini da rokon na ba shi auranki, nima kuma na so ku da juna amma duk yadda na so abin idan har ba kya so, to ba zan yi miki dole ba saboda sharia ba ta ce na yi miki dole ba"

Bilki ta kalli Baba Babba ta kasa fadin uffan sai kawai ta fashe da kuka har da gunji kamar wata k'aramar yarinya.

*Surayya Dee*

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Cikin ruɗewa Baba ya ce" Subhanallah me ya faru kuma Maigado?"

Amma ta kasa daina kukan, yi take yi har tana gunji yana fidda sauti har sai da Abida ta baro ɗakinta zuwa falo domin ta ji kuken Balki sai ta yi turus ganinta durƙushe gaban Baba tana kuka, duk da ba ta san dalilin kukan ba amma a zuciyarta ta zargi kan maganar Asad ba ne.

"Daina kuka yi shiru Maigado. Ki faɗa mini matsalarki, Ai ba dole zan yi miki ba.

Ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda Balki ta ruɗe da kuka kamar ranta zai fita.

"Baba."

Bilki ta kira shi da girmamawa

"Na'am Bilkisu."

Ya amsa mata cikin kulawa.

Kai tsaye ta ce" Baba don Allah ka bar wannan batun. Ni gaskiya kallon d'anuwana nake yi masa, bayan haka babu wata alak'a da zan k'ulla da shi".

Ta fad'a cikin kuka na sosai.

"Share hawayenki magana an barta. Amma abin da nake so da ke, dan Allah Maigado ki bawa masu sonki dama. Kada ki ce za ki juyawa aure baya. Aure sutura ne kuma mutunci ne. Allah ya yi miki zabin alheri "

Daga nan ya sallame ta ganin har lokacin ba ta daina kuka ba.

Abida ta ji haushin Bilki ainun ko kunya ba ta ji ba? A gaban Baba Babba za ta ce ba ta son ɗansa? Gaskiya Bilki bahaguwa ce ta k'arshe.

Ba ta nuna mata ba, amma dai ta rage mata walwala alamun ta hasala ita kam Bilki bata san tana yi ba, murna ma take yi tun da Baba ya ce an bar maganar tana son kuma zai dakatar da yaya Asad daga nacin da yake yi mata, shi ya sa ba ta ma kula da yanayin Abida ba, ballatana ta fahimci tana jin haushinta ne.

Ba zata yi auren da bata so ba.

Bilki ta sakankance Baba ya takawa Ya Asad Burki akanta tunda ta ce ba ta so, amma sai me? Sai ta ga ma kamar ya sake kunno kai ne zuwa gare ta da cewa ba gudu ba ja da baya kiran waya saƙonni haka zai baro wajen aikinsa ya zo mata yana takurata mata ita kuma ba za ta iya masa wulakanci ba da za ta iya wallahi da ta yi masa ko ya shafa mata lafiya.

Ranar juma'a ya tafi Auka ta jihar Anambra. Tun yamma yake k'iranta tana ga ni ta yi biris da shi.

Asabar tana idar da salla wayarta ta fara kuwwa. Tasan shine , ta k'yale. Sai dai Kiran ya cigaba da shigowa babu gajiya.

Ta gaji ta amsa amma a zafafe don kuwa ya yi matuk'ar shiga rayuwarta.

"Assalamu alaikum Maigado!

Ya fad'a cikin taushin murya sosai.

Ta amsa murya babu amo.

"Jiya na yi ta kiranki, baki dauka ba, sannan ba ki biyo baya ba".

"Ban samu lokaci ba ne".

Ta fad'a a gajarce tana tuna lokutan baya da take k'iransa da niyyar gaisuwar zumunci baya dauka sannan ba ya biyo sawunta.

Ya tausasa harshe ya ce "Yanzu Maigado ba za ki ji tausayina ki raba ni da zaman kad'aicin da nake ciki ba. Menene aibuna ne da kike ta yi mini yawon k'i tuntuni?"

Ya bata tausayi amma ta maze ta ce "Baka da aibu amma gaskiya Baban Bilkisu bana ra'ayin aure a yanzu, sannan ko zan yi to gaskiya ba da kai ba. Kallon yaya nake yi maka, ka yi hakuri kawai, mu bar shi a haka".

"Gaskiya ba zan iya hak'uri ba Maigado!

Ya fad'a da dukkan gaskiyarsa.

Ta hassala ainun tare da fadin

"Ni fa na ce bana yi, na faɗa maka, na faɗawa Baba kuma na san ya faɗa maka. To gaskiya ka shafa mini lafiya dan kuwa gaskiya ka takure ni ".

"E tabbas ya faɗa mini kin ce ba kya so na."

Ya faɗa cikin wani irin sauti marar amo.

"To kuma duk ka san da haka binbinin da kake yi mini na mene ne?"

Ta tambaya a fusace saboda ta gaji, yana takura mata da yawa.

Maimakon ta ji ya fusata ya ce ta yi masa rashin kunya. Sai ta ji yana fad'in "Saboda ina son ki. Ina son na killace ki a gidana shi ya sa na kasa haƙura na ƙyale ki."

Mamaki ma ya hana ta magana sai kawai ta yi masa shiru tana jin sa yana ta mata magiya cikin wata yar murya mai kama da nishi wai shi a dole sai ya ja ra'ayinta, shi bai san ma haushi yake ba ta ba.

Da ta rasa yadda zata yi da kasalar da yake haifarwa gangar jikinta sai kashe wayarta ta yi saboda gabad'aya nishinsa ya ruru mata jikinta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Duk wulakancin da take yi masa bai saka ya karaya ba. Ya dinga yi mata manyan kyautuka masu gigita tunani. Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in.

Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu.

Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce "Amma ina na Abida kasan tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce".

Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba."

Ya kammala fad'a yana shafa kansa .

"To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan."

Ta faɗa tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa.

"Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki taya ni shawo kanta."

Ya fada cikin jin kunya.

"Ba ruwanmu a ciki. Ka cigaba da ƙokari in sha Allahu za ta amince."

Ya amsa da Allah yasa tunda kowa na ba shi k'warin gwiwa ai sarewa bana shi ba ne yanzu.

Bai tafi ba, yana zaune yana dakon isowarta.

A falo ta tarar da shi, shi kad'ai, fuska babu sukuni ta zube sosai ta gaishe shi tare da yi masa sannu da dawowa. Daga haka ta doshi k'ofar da zata shige ciki ta nufi d'akinta. Takaici ya mak'ure shi.

Ya bude murya

30 / 37