Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   21 / 37

60K to 63K   out of 110.8K words

kuwa tunda ta sauko ta ganta gaban Malamarta ta ji tana neman rasa confidence din da ta shigo gidan da shi. Duk yadda suke ganin kyaunta ashe daga nesa ba komai suke ga ni ba. Wata irin mace mai kirar kalangu sannan mai dongon hanci da manyan idanuwa ga ta fara tas, sannan doguwar mace sambal. Bayan wadannan kallo d'aya za'a yi mata a gane ilimin rayuwa da addini sun yi mata k'awanya don ba alamun girman kai ko izgili a tare da ita. Sannan kuma kudi sun zauna mata sosai tunda ga yanayin k'amshinta, fatarta da suturarta da kuma yadda ta kawata wajenta da kayan kawa na alfarma.

Duk yadda ta gamsu Sahal na sonta sosai amma yadda ya kira matarsa da Bili sai da ta ji wani iri don kuwa ta zaci ai ta wuce ya dinga yi mata irin wannan soyayyar, ta dauka tunda ta tsufa babu wata soyayya sai zaman hakuri da juna.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan sai taga daga ita maik'uruciyar har shi mijin nasu sun zama kamar masu barance a gaban Bilki. Kamewar Bilki da yanayinta na rashin hayaniya ya sake mayar da ita mace mai aji sosai.

Da sanyin murya ta ji Bilkin ta ce "A a bai yi ba, amarya ba zata zauna jiran sai an bata abinci ba. Ta dinga yin abincinta muna yin namu. Duk mai girki a cikinmu ta dinga baka. Bakinta ita kad'ai na za a dora mata hidimar bawa mutanen gida abinci sannan ga hidimar karatu ".

Sahal ya diririce don ya gano Bilki ba zata ba shi tallafin rike masa amarya ba ko kad'an.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Gabaɗaya zuciyarta ta ƙuntata ta rasa me Sahal yake nufi da ita tana ta rufe masa k'ofifin fitina a gida amma ba ya ga ni.

Ciwon kai da jiri sun sako ta a gaba tafi son ta riƙa zama ita kaɗai. Ta yi ta tunani mai zurfi, ba ta iya cin abinci nan da nan ta fara rama tana zaune sai ta ji kawai tana hawaye, miji ba ya ta kanta bai damu da halin da ta ke ciki ba. Daga yaranta sai Alti da Alawiyya sune kawai suka damu da ita, ita kanta tasan ba ta da lafiya. Dole ta shirya ta je asibiti likita ya sake ba ta tabbacin tana bukatar natsuwar jiki da na zuciya domin depression ya kamata ya yi ta mata faɗa akan ta kula da lafiyanta idan ba haka ba za a samu matsala ya bata shawarwari sosai sannan ya rubuta magunguna ta biya phamarcy ta siya sannan ta dawo gida tana zuwa ta ga Basma ta zo tana jiran ta, ko ba ta faɗa mata ba ganin ta kawai da ta yi ya sa ta san ba ta da lafiya.

"Bilki me ke damun ki ne? Kin ga yadda kika lalace?

Bilki ta kasa ba ta amsa sai ido kawai kamar wata doluwa.

"Bilki ki yi mini mgaana ki fidda abin da ke ranki in ba so kike yi ki kashe kan ki ba."

Basma ta faɗa cikin tausayin Bilki, ledar magungunan ta ɗauka ta dudduba nan ta ga halin da Bilki ta ke ciki.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.'

"Bilki kin kusa mutuwa ban sani ba?

Ta fada cikin tausayawa kamar ta fashe da kuka.

"Ki yi kuka, ki yi kuka ko za ki samu natsuwa Bilki"

Basma ta fad'a cikin d'imuwa.

Tsawon lokaci bata samu ko kalma d'aya Bilkin ta furta mata ba. Amma ita tuni ta gano damuwarta. Bai wuce juya baya da miji ya yi mata ba har hakan ya yi mata sanadin depression.

Ta dauki wayar Bilkin ta fita zuwa falo ta lalubo Yaya Hamida.

Kamar ba za'a dauka ba sai kuma ta dauka.

Ta gaishe ta da girmamawa tare da ce wa "Yaya Hamida zan fad'a miki Bilki bata da lafiya tana bukatarku a kusa gudun sai ta yanki jiki ta fadi da ku ji".

Duk tsiyar Yaya Hamida sai ta rikice da tambayar me ya samu Bilkin?"

Basma ta ce "A zahiri tana zaune lafiya amma a badini tana fama da jinya mai had'arin gaske don magungunan da aka d'ora ta na ciwon damuwa ne.

Dan haka ku yi kokari ku dinga yi mata abubuwan da zasu dinga Debe mata kewa da takaici."

A tsorace Yaya Hamida ta yiwa Basma godiya tare da cewa tana tafe cikin satin nan.

Da haka suka yi sallama sannan da ta koma cikin daki wajen Bilki.

Ta cigaba da bata hakuri, har ta samu cikin kuka sosai Bilki ta fad'a Mata wulakancin da Sahal yake yi mata, sannan duk abin da matarsa ta ce Amrah ta yi sai ya hau ya zauna ya hau sakin kalamai masu ciwo.

Bayan haka abu kadan abu zai had'asu ya yi mata gorin bata da wajen zuwa gidansu ya tarwatse saboda son zuciya.

Hankalin Basma ya tashi ta ce Shi Sahal din ne yake miki gorin ahalinku sun watse kuma iyayenki masu son zuciya ne?"

Da gunjin kuka ta gyada mata kai.

Ta numfasa ta ce kinsan dai mahaifiyata yar Mashi ce Ko?"

Bilki bata ce komai ba illah kuka.

Basma ta ce "Fadar wannan maganar ba abin dad'i ba ce sannan idan ya ji a bakinki har abada ba zai sake miki gorin abin da ya faru a gidanku ba.

Sannan zai iya zama sanadin da zai sake ki. Shin na fad'a miki ko na kame bakina kada ki fad'a masa ya zama sanadin da zaku rabu ki d'ora alhakin mutuwar aurenki a kaina!

Da kuka sosai ta ce "Fad'a mini Maman Abdul na riga na gaji da zama da shi kullum ina addu'ar Allah ya yi mini zabin alheri a rayuwata amma na gaji da Sahal gabad'aya ba shi da kirki bai san adalci da yakamata ba".

Basma ta tashi ta rufe d'akin sannan ta zauna daf da Bilki. Ta sassauta murya ta ce "Kin san Iro Mashi?"

Murya ba amo Bilki ta ce"k'anin babansu Sahal ne, Baban Abuja suke ce masa."

"Madallah! Basma ta fad'a a hanzarce.

"Ko kin taɓa jin labarin ya lalata Yaya Turai? Turmi da tab'arya mahaifinsu Sahal din ya gansu sanadin haka ya fadi shike nan har ya mutu bai sake tafiya ba!

A lokacin Yaya Turai bata zama budurwa sosai ba, kamar dai su Amra haka ya dinga haike mata kamar bunsuru, kuma ya dinga tsorata ta akan idan ta fad'a sai ya yanka ta. Sai da dubu ta cika aka gane. An ce har yanzu yana nan a Abuja yana cigaba da fasadinsa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tashin hankalin da aka yi ba kad'an ba ne kuma wannan bak'incikine ya kashe uwarsu, kakarsu Sahal din kenan.

Kan dole aka hak'ura aka danne maganar a tsakaninsu. Amma wadanda suka sa ni sun riga sun sa ni.

Dan haka kada ki sake damuwa dan ya goranta miki kun yi shari'a da Baba Babba ko kuma Baba Babba ya yi shari'a da ku nasu abin kunyar na tir ne da neman tsarin Allah da shi".

Bilki ta saki ajiyar zuciya ko kadan wannan labarin bata ji dadinsa ba tunda ta had'a zuria da su. Sai dai tabbas idan ya cigaba da taɓa mata darajar gidansu zata fad'a masa. Idan ya so komai ma ya faru .

A gidan Basma ta yini tana ta bata shawara da ban bakin ta yi hakuri ta cire damuwar komai ta kula da lafiyarta. Sai da ta tabbatar da cewa ta samu natsuwa sannan ta ta fi gidanta.

Kwanaki biyu sai ga Yaya Hamida ta iso. Ta ajiye komai ta shiga kwantarwa da Bilki hankali wanda saukowar Yaya Hamida ya sanyaya zuciyarta sosai ta fara warwarewa tana cin abinci.

Sai da ya yi kwanaki hud'u a maimakon biyu da ta zo da niyyar yi sannan ta koma Kano tare da alk'awarin wani watan zata sake dawowa ta ganta.

Tun da likita ya faɗawa Bllkisu cewa idan ta dage nan da lokaci kaɗan za ta warke daga cutar da ta ke damunta. Jin haka ya sanya ta dage ta cirewa kanta dukkan wasu damuwowi da tunanika masu birkita ta, ta dage da adduar samun nutsuwar zuciya. Ta mayar da hankalinta gun shan magungunanta sosai take kula da kanta da lafiyarta. Saboda idan ta biyewa Sahal da amaryarsa ta tabbatar lokaci kaɗan ya rage mata a duniya za ta mutu saboda baƙin cikinsu da takaici, ta kuma ba shi da asarar komai tunda ga shi da ranta ma ya samu madadinta ya'yanta da danginta ne zasu yi asarar rashinta kawai. K'iri k'iri yake danne mata haƙƙin aure amma ko a jikinsa bai damu ba ganin ta zura masa ido sai hakan ya ba shi lasisin yin duk abin da ya ga dama babu fargaba.

Ya daɗe yana yi mata abubuwa a baya sai dai ta zauna ta yi kuka kuma yana zuwa mata da daɗin baki sai ta ji ta yafe masa, amma zuwa yanzu ta daina cewa ta yafe masa domin ta fahimci an kawo gab'ar da komai da saninsa yake yi sannan da son ransa yake aikatawa. Daga lokacin da ya yi auran nan zuwa yanzu ta ga baƙin d'abiu da yawa daga Sahal waɗanda ba ta taɓa saninsa da su ba, daga nan ne ta fahimci cewa ita ce kawai ya daina ra'ayi kamar ma yana zaune da ita na dole ne. Wataƙila kuma tana yi masa zaman ƴaƴansa ne, ko kuma zaman mai yi masa wahala da gidansa, tunda ta fahimci haka ta shafawa kanta lafiya game da lamarinsa da matarsa iyakarta da shi gaisuwa.

Ba ya shigowa bangarenta sai tana da girki, shima barcinsa kawai da huta gajiya yake yi. Amaryarsa kuwa sai su yi sati ba su ga juna ba wani lokacin ma sun fi haɗuwa a haraba gida ko ta makaranta su kan gaisa sama sama, duk addu'ar Bilki na kar a bata ajin su yarinyar nan sai da aka jona ta da su a wannan semister ɗin.

Ba ƙaramin jarumta Bilki ta yi ba, da karfafa guiwar da Basma ta fara ɗaukansu, duk da tana ganin ƙawayen Hawwa suna nuna ta ana dariya bata taɓa nunawa ta gane abin da suke yi mata ba, abin da ya kai ta kawai take yi da ta gama za ta yi fitowarta, ba ta damu da maganar kowa ba, don ta riga ta gamsu sai ta cire tunanin kowa da k'arantawa kanta damuwa shine zaman lafiyar zuciyarta. Sannan kwakwalwarta ta samu hutun da ake bukata. Dan haka harkar gabanta da ya'yanta da koyarwarta ta saka a gaba. Kullum tana shan maganinta da taimakon yaranta don ko Farha kullum sai ta ce "Mahmah kin sha magani ko na dauko miki ruwa ki sha?"

Bare Amrah da kusan kullum ita take bata. Da ta sake komawa asibiti likita ya yi ta yabon kokarinta ya ce nan da lokaci kadan zai sauke ta akan magani.

Don haka sai ta rumgumi aikinta da yaranta masu sanya ta nishaɗi da farinciki sannan Alti ma tana iya bakin kokarinta. Ga ƙawar amana irin Basma duk bayan kwana biyu sai ta zo ta zauna da ita ya debe mata kewa.

Sosai aka samu cigaba a lafiyar Bilki don tana cin abinci ta warware ta fara mayar da jikinta.

Wani zuwa da Basma ta yi ta dinga yi mata tsiya.

"Hajiya Balki, ko dai Sahal ya lallaɓa ya yi wata ajiyar ne?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bilki ta fara dariya a zuciyanta ta ce yaushe rabon duniya da ayyaraye?

A fili kuma sai ta ce' Ai ni na gama, yanzu lokacin amarya ne ta yi ta zazzaga masa yara.".

Domin ta fahimci ya fi ɗokin haihuwar daga bangaren amarya tun da yadda yake b'arin jiki kan cikin nan ko a lokacin da ta yi cikin Amrah ba ta ga ya yi wannan ba'rin jikin ba. A yanayin da ta ke ciki bata ma fatan ta sake haihuwa to ta ina ma ta ga mijin ballanta har ta sake samun ciki? Mutumin da yanzu sun fi wata biyu bai neme ta ba tun samuwar cikin matarsa, ranar kwanan ta ma yanzu ba ta ganewa domin a sati bai wuce sau biyu yake kwana a dakinta ba shima a tafe yake kwana haurawa sama yana duba yar gwal, asuba na yi idan ya fita ba ya sake dawowa. Gabadaya ta rasa ma ina tsarin gidan yake kawia tana cigaba da binsa da ido ne Amma akwai ranar kin dillanci. Yana ta karakaina a kanta, haka ƴan'uwansa ma kullun cikin zuwa gidan suke da sunan duba amarya. Haka nan itama Hawwan k'annenta biyu sun zo daga Kaduna sun fi sati sannan suka tafi, ita dai sai dai ta ga ana shiga ana fita. Wanda ya shigo wajenta su gaisa wanda bai neme ta ba, ta yi kamar bata san ma ya zo gidan ba cikin irin rayuwar da take ciki ke nan.

Shi kan shi maigidan tamkar wanda aka yi musu farraku abin kullum hauhawa yake yi, ta kuma tabbatar ba wani farraku kawai sabbin bita yake mata cikin littafin kitabur ra'asi. Dan haka bata jin zafi domin ƴan'uwansa sun nuna rashin kulawa a kanta. Ba ta ɗorawa kanta damuwarsu a zuciyarta ba. Ta tabbatar wulak'ancin Baban Amra yafi jan kaso mai yawa na ciwon damuwar da ya kamata fiye da kason damuwar abin da ya faru cikin ahalinta.

Tunda tun kafin ya yi aure yake nausa mata bak'in ciki, yanzu da ya yi aure tozarta ta yake yi ta hanyar fifita yarinyar da bata wuce ta zo a mai yi mata hidimar gida tana biyanta ba.



Ana cikin haka semister ta yi nisa har an yi gwaji, sai ga Sahal ya zo yana yi mata magana, akan darasin da ta ke daukar su Amarya. Wai ta yi musu gwajin(test )kuma ya ga ta bata karamin maki 6 a cikin 20 me take nufi da hakan?"

Ya fada yana wurga mata takardan gwajin a jikinta. Lokacin tana cikin ɗakinta tana duba wasu takardu ne na makaranta ya shigo yana yi mata wannan jawabin.

Ko ɗagowa ma ba ta yi ba, ta cigaba da duba takardun hannunta. Idan shi ba adali ba ne to kar ya yi tunanin kowa ma irin sa ne, wato tunda tana matarsa ta bata maki 20/20 saboda shi, lalle Sahal ba shi da kunya to ai bai tsinana mata komai na abin arziki ba tun bayan auransa ballatana yarinyar ta ci darajarsa.



"Magana fa na ke yi miki kin yi mini banza?"

Ya fada a fusace Bilki ba ta son hayaniya shi ya sa ta dakata da abin da take yi ta dago tana kallon sa.

"Akan me ka ke magana?

Ta tambaya cikin nuna kamar ba ta gane in da ya dosa, duk bai sa ya fahimci ba ta da lokacinsa ba sai ma ya sunkuya k'asa ya dauko takardar yana nuna mata.

"Kin kyauta ke nan abin da kika yi Bilkisu?"

"Me na yi Baban Amrah?

Itama ta tare shi da sauri.

"Au ba ma kin san laifin da kika yi ba ko?"

Ya fada cikin harzuƙa.

"Ban sani ba, idan na sani ai ba zan tsaya ina tambaya ba."

Ya mika mata takardan yana fadin" Duba ki ga ni."

Ta karba ta duba sannan ta kalle shi tana fadin" Wannan kamar darasina a ina ka samu?"

Ta fada har tana bayyana mamakinta.

Baki ya saki yana kallon Bilki tana nufin ba ta san ko takardar wace ce ba?

"Duba sunan?

"Hawwa Hamza!

Bilki ta karanta a bayyane sannan ta mayar da fuskarta gare shi ta ce

"Wace ce ita? "

Ta tambaya cikin mamakin. Sahal ya yi wani sororo, wuyansa ya lamgwabe kafin ya ce" Kina nufin ba ki ma san ta ba?

"Ban gano wace ce ba, kasan daliban nawa suna da yawa ba zan iya rik'e sunan kowa ba."

Ta fada tana mik'a masa takardar hannunta amma ya kasa karɓa saboda mamakinta.

Ajiye masa ta yi a gefen gado ta d'au takardunta ta cigaba da dubawa.

"Kina nufin ba ki san sunan matata ba Bilki? Amma dai ai kinsan kin fara daukarsu darasi?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Don Allah fa?"

To ban ma taɓa lura ba, kuma ita ta fada maka ina daukarsu? Idan na shiga ajin bana tsayawa tantancesu abin da nake yi basu darasi da tabbatar da sun fahimcin darasin da kyau. Bayan haka bana sanin komai akansu illah zakwakuran cikinsu, Wanda hazakarsu ta wuce gigiggiwarsu. Bana ji itama ta dauke ni malamarta mai daraja don ban tab'a ganinta a aji ko a makaranta ta yi mini gaisuwar da zan shaida ina koyar da ita ba"

Ta fada tana kallon sa.

Kafin ta sake ce wa" Ka fada mata ta mai da hankali gaskiya, ta rage rawar kai a tsakanin kawaye if not , ba zata kai labari ba."

Sahal ya kai k'ololuwar fusata wato da gangan Bilki ta yi wannan muguntar?

"Ke nan da gangan kika kayar da ita a gwajin ko?

"Allah ya tsare ni, abin da ta rubuta shi ta samu."

Bilki ta amsa masa, a ɗan zafafe domin ita kam ta gaji da wannan ihun da ya ke yi mata a saman kanta.

"Ko da ba ta ci ba ai darajata sai ki bata maki mai d'an dama Bili"

Ya fada yana wani rage murya har da fadin sunan da rabon da ya ambace ta da shi ta manta.

Ta kalle shi shekeke kafin ta ce" Ai ba na haka, duk inda na ke adalci na ke yi ba zalunci ba, bana k'arawa mutum hak'kin da ba na shi ba."

Sai jikinsa ya yi sanyi domin sai ya ji kamar shagube Bilki ta yi masa.

"To ki d'an k'ara mata ko zuwa goma ne ga ta can tana kuka."

Haushi ya kama Bilki ta mike ko magana ba ta yi masa ba ta shige tiolet ta bar shi nan da ya gaji ne da tsayuwa ya fice sai

21 / 37