Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   37 / 37

108K to 110.8K   out of 110.8K words

a tare da Altin.

Sakwanni biyar suka saki junansu dukkansu fuskokinsu d'auke da bayyananen farinciki.

Alti ta zauna a gefen kafet yayin da Bilki ta zauna a inda take zaune.

Suka gaisa cike da karrama juna. Jimawa kad'an Alti ta fice.

Jummai wacce yar kabilar Nufe ce ta shigo d'auke da tiren ruwa da lemo ta dire a gaban Bilki sannan ta durkusa cikin gurbatacciyar hausarta ta ce "Anty barka da yanzu, sannu da zuwa".

Bilki ta amsa da fad'in "Ba hausa mun same ku lafiya?"

Ta murmusa ta ce "Lafiya kalau Alhamdulillahi Anty.

Sannan ta fita. Jummai zata yi shekaru ashirin da biyar ta taba aure har da yaranta biyu suna can garinsu a Bidda a wajen Babansu, tunda suka rabu. Tun kafin a yi mata aure take hannun marigayiya Rukayya sosai ta iya gyara babu gajiya, haka nan ta iya girkin gargajiya daban daban dan idan tana yin sakwara sai ka zaci ba da hannu ake yi ba. Sannan ta iya rainon yara da juriyar fitinarsu. Amal da Noor sun yi matuk'ar shak'uwa da ita. Shiyasa har yanzu take nan tana kula da su.

A zuciyatar Bilki ta kudire Alti da jummai kawai sun ishe ta amma charity sai ta bar gidan ba zata zauna ahalil kitabu na yi mata girkin abinda zata ci ba.

A matuƙar sanyaye Abida ta ce "Yanzu Maigado ba za ki tausaya mini ki fad'a mini gaskiya akan Yaya Sulaiman ba. Ke ko tausayina ba kya ji. Dubu yadda vitamins din da ake zuba miki na watanni biyu kacal ya mayar da ke amma ni kullum k'ara baki nake yi ina yamushewa, sai na bude baki na fad'a miki ina da buk'atar a zuba mini ne?"

Dariya ta subucewa Bilki ta sosai. Ta numfasa ta ce "Allah Abida kalamanki na kashe ni da kunya. Amma fa watannin baya na yi miki rantsuwar ban san inda yake ba. Wallahi tunda ya tafi ban sake ji daga gare shi ba."

Hawayen nadama suka k'wacewa Abida babu zato. Cikin rishin kuka ta ce "Na gaji Bilki, Wallahi na gaji, ni kam na shiga ukuna".

Tausayinta ya kama Bilki sosai ta matsa kusa da ita ta rik'e ta. Murya a dakushe ta ce "Sannu Abida ki k'ara hak'uri mu cigaba da addu'a da ikon Ubangiji idan yana raye zai bayyana.".

Cigaba

Ta d'ago idanuwanta hawaye na tsere duk wata izza da jin kai sun k'wace mata ta ce "Wallahi yana nan da ransa, Wallahi bai mutu kawai tsabagen wulakanci da zalunci ne".

Bilkisu ta kasa ce wa komai. Can ta numfasa ta ce "Abida tunda dai kad'an ya rage ki cika shekaru hud'u a dakon dawowarsa kawai ki yi gaiba idan kin samu miji ki yi aurenki tunda har kika furta mini kin gaji na tabbatar kin kai k'ololuwar gajiya ne tabbas".

Takaicinta ya shake Abida a zafafe ta ce "Ce miki na yi ina marmarin wani rijalun ne bare ya biya mini nasa littafin ra'asin? Yaya Sulaiman din nake kewa kuma gangar jikina take mararinsa ba waninsa ba. Kawai idan za ki taimake ni, ki taimake ni, idan kuma ba wani taimakon da za ki iya yi mini to yaune rana ta k'arshe da za ki ce na yi gaiba don kuwa daga nan har mahdi ya bayyana zan jira shi ".

Ta fad'a cikin kuka na sosai.

Maigado ta kasa ce wa komai don sosai Abida ta bata tausayi Duk yadda take danne al'amura a ranta tare da jin kai matakin Yaya Sulaiman ya yi matuk'ar bugunta ta yadda ta fara sauke al'amura masu yawa. Ta tabbatar saukowar da ta yi take mu'amala da ita da kyau har da soyayyarsa da son sanin inda zata gan shi ko ta samu wani bayani gamshasshe.

Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru.

Tsawon lokaci suna zaune jugum jugum don sosai suka shiga alhini.

A sanyaye Abida ta shiga bayi ta wanko fuskarta ta fito ta shafa hoda sannan ta fita dan gaida Yaya Asad. Suna gidan aka yi sallar magariba da isha.

Basu bar gidan ba sai da Bilki ta damkawa duka yaran tsarabarsu kowa da ledarsa tunda ga kan Amal har zuwa kan Noor. Yan aikin gidan mata ma duk ta bisu da turare.

Abida kuwa gwangwajeta ta yi da haddun materials din Malaysianfabrics....07020695644

Wanda take ta yi mata nacin tana so saboda kyaunsu da rashin nauyinsu.

Suka tafi baba da Momi suna ta saka musu albarka.

A hanya ya kalli yadda ta takure ta kasa sukuni.

Ya tausasa harshe ya ce "Sarauniyar shaiba ya dai?"

Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi shiru don ya riga da ta gane ta idan ta shiga yanayi irin haka tafi son shiru.

Maimakon ya sake yi mata magana da baki sai kawai ya kunna musu karatun alkur'ani suratul Maryam ta fara tashi da muryar sheik Afif.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: https://youtu.be/hzVPVzqlXVo?si=F6LxKyPrNjaT2TvZ

*D'INGISHIN KWAD'O*

*Book 4*

*Na*

*Surayya Dee*

*Marubuciyar*

*HALIN YAU*

*SABO DA KAZA*

*BAK'AR TA'ADA*

*LITTAFIN KUDI NE PAY 1K VIA* 2384876855

*Surayya Ibrahim*

*Zenith Bank*

*08032773332*

*DAN ALLA MASOYANA A JE A MINI LIKES A YOUTUBE GASA NA SHIGA DA WANNAN LABARIN NAKU. KU TAIMAKA DA LIKE'S DAN LABARIN YA KAI GA MATAKIN NASARA*.

*ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI*.

Jikinta ya yi sanyi ainun. Ta rasa yadda zata yi a kan dole ta ce "To".

Ya dinga yi mata godiya har ta ji wani iri. Don sai ya bata tausayi yadda ya kwantar mata da kai tamkar ba babban dan sanda ba.

Ganin ya shawo kanta ya sanya ya ce "Bari na bar ki, ki yi barci Maigadona, zamu yi magana da asuba in sha Allah stay blessed and I do love you dear '.

Daga haka ya katse wayar ba tare da ya jira amsawarta ba.

Sai dai ya yi matuk'ar tura sak'o mai nauyi a zuciyarta kalaman nasa sun saka ta cikin nishadi da nutsuwar hakura ta karbe shi a matsayin mijinta. Ta yi shiru tana tunanin yadda zata kasance a matsayin matarsa.

Yayin da shi kuma ya kasa kwanciya. Tabbas da aiki a gabansa tunda a bayyane k'arara iyalin Baba k'arami suke gaba da shi. Sannan dukkan fishinsu akansa suka d'ora. Zai yi komai dan ya auri Bilkisu don hakan ne kad'ai hanyar da zai daidaita shi da su dari bisa fari don idan tana hannunsa dolensu su yi mu'amala da gidansa sabanin idan watace ko da sun shirya ba lallai su zo gidansa ba, sai da kwakkwaran dalili.

Da k'yar barci ya sure shi. Da asuba yana idar da salla ya k'ira ya dinga tarayyarta da rarrashi da maganganu masu nauyi kafin ya k'yale ta bayan ya tabbatar jikinta ya tsumu da manyan kalamansa.

A daren ranar Baba ya sake zama da Asad tare da Farouku.

Ya kaurara murya ya ce "Na yi magana da Bilkisu ta kuma ba ni tabbacin ta amince da batun aurenku! Amma ka saurare ni da kyau. Duk cikinku kai ne babba, ba sai na maimaita abin da ya faru na rikicin da ya gitta a tsakaninmu ba. Na yi faricinciki da Ubangiji ya k'ulla wannan alherin a tsakaninka da ita, dan

kuwa a duniya ba abin yake saurin yafe gaba irin auratayya. Yana daga cikin dalilan da Annabin Rahma ya auri mata daban daban daga kabilu mabanbanta, duk kuma kabilar da ya auri y'arsu gab'ar da suke yi da musulunci tana zagwanyewa.

Dan haka ka yi iya k'ok'arinka ka daidaita zumuncinku da ya yi rauni da y'anuwan Bilki. Ka buda musu k'ofar da zasu zo gidanka su sake, haka nan ka yi iya kokarinka wajen ganin kun sake hadewa kuna zumunci ko da bana raye. Sannan ka cigaba da bincike akan Sulaiman. Kana ganin dai yadda Abida take zaune bata kaunar ayi mata maganar ko zata yi gaiba, a haka ta kwashe shekaru kusan hud'u babu shi, babu alamarsa ga ya'yansa nan basu san shi ba!

Baba ya yi shiru a dalilin kuka na neman kubuce masa.

Sai da Asad ya dinga ba shi hak'uri sannan ya dan nutsu.

Ya numfasa ya ce "Bilkisu ta ce 'Na sanar maka da d'iyarta d'aya zata zo gidanka da kuma Alti".

Mamaki ya kama shi ya murmusa ya ce "Baba ka fad'a mata idan wad'anccan na Katsina ma Babansu zai ba ni to ta zo mini da su zan rikesu gabad'aya".

Dad'i ya kama Baban ya dinga yi masa fararen addu'o'i tare da tunasar da shi Bilki yarinya ce a kansa dan haka ya yi hak'uri mai yawa akan sha'aninta.

Ya rufe maganarsa da ce wa tunda bazawara ce ka tambaye ta sadakin da zaka bata, sai kawo. Sannan ka nemo wanda zai karɓa maka auren dan kuwa nine waliyyin Bilkisu matuƙar ina doron k'asa."

"Baba ni ga Babana nan Faruku. Sai kawai ya karba mini auran."

Ya fada yana kallon shi gabadaya suka fashe da dariya, har da Momi da ta shigo falon yanzu.

Baba ya ce" Shike nan Faruku ssi ka karɓa masa auren ya zama d'anka tunda Bilki ta nuna kai ne ubanta."

Suka sake saka dariya mai bayyana suna cikin farinciki. Abida da ta dawo ta ji labari abin da ya wakana ta dinga dariya tana tsokanan Ya Faruku da Baban Ya Asad shi kuma ya ce duk ya dau girman.

Baba Babba ya saka daurin aure sati daya ranar jumma,a in an sauko daga masallacin Jumma'a.

Tunda Abida ta ga biki ya zo, ga babu lokaci.

Haka ta siyowa Bilki package din amarya daga Bojuwa herbs Kano.

Sanyi flusher ta sha babu gardama don tasan tasirinsa da ingancinsa. Sauran kayan k'ara niima ne take yi musu yawon Ki. Amma dai Abida ta tisa ta a gaba ta cinye ciccibin garari na matan da suka haihu ko suka taba yin aure Sauran kaya kuma ta adana mata ta ce ta san da kanta zata bukace su.

08032773332 ga masu son sanyi flusher da dukkan kayan gyara masu kyau da tsabta.

Farouku ya samu Bilki a gida da yamma bayan ta dawo daga aiki, ya dinga yi mata godiyar karrama Shi da ta yi tare yi mata alk'awarin yana tare da ita cikin kowanne bigire na rayuwa sannan duk matsalar da zata taso wacce ba'a fata to ta shi zata tuntuba kaitsaye.

Idonta cike da k'walla ta ce "To a takaice.

Jikinsa ya yi sanyi domin gabad'aya ya fahimci sadaukarwa ta yi akan batun kwamishina amma ba soyayya ba.

Ya ce "Ni zan biya masa sadaki sarauniyar shaiba nawa zan ba ki? Baba ya ce sai an tambaye ki".

Kanta na k'asa ta ce "Tunda daga aljihunka kudin zai fito ka bada Dari biyar".

Ya yi gajeriyar dariya ya ce "To da ba ni Zan biya masa ba fa Bilki?"

Ya tambaya cikin mamakin yadda ta matse akan dubu dari biyar zai bata.

Ta ce da shine milyan zai bayar tunda an ce ba kyau tsananta sadaki".

Ya kwashe da dariya sosai yana ganin shegantakarta kullum sake bayyana take yi.

*Katsina*.

Daren alhamis Sahal zaune a falon kasa yana kallon labaran kasa kwatsam ya ga ana sanarwar d'aurin auren da ya yi matuk'ar dukan kahon zuciyarsa . Ya zabura ya mike tare da k'ara volum don dai ya tabbatar da abin da yake ji da Ga ni.

Tiryan tiryan kuwa ake sanarwa a madadin rundunar y'ansanda ta birinin tarayyar k'asarmu tana sanar da dukkan alummar tare da goron gayyatar y'an uwa da abokoan arziki zuwa daurin auren kwamishina Asad Musa Funtua da amaryarsa Bilkisu Isa Funtua.

Daidai nan ya kashe talabijin din gabadaya tare da safa da marwa cikin rashin sukunin zuciya. Dama da gaske yaran suke yi da suka fad'a masa mahmansu zata yi aure?

Wani irin tashin hankali ya rufar masa mai tsananin gaske. Ya dinga tuhumar kansa me yasa ya sake ta alhalin yasan Asad na sonta tun filazal? Me yasa ya ba shi damar da zai aurar masa matarsa uwar ya'yansa? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Yake furzarwar da k'arfin gaske wanda ya ja hankalin Hawwa da take samanta wanda itama ta ga sanarwa tunda ya koya mata kallon labaran k'asa.

Amma Amrah da Faruk tuni suka yi barci dan haka basu ji hirjinsa ba.

Gulma da son ganin halin da yake ciki ya sanya Hawwah gangarowa a sukwane.

Sai dai yanayin da ta ganshi yana ta sa'a'i tare da suratai ya yi matuk'ar sanyaya mata jiki don kuwa muraran tashin hankali ne ya bayyana masa.

A sanyaye ta ce "Baban Amrah nutsu ka zauna mana kada ka Fadi ka hadu da jinya fa".

A matuƙar gigice ya ce "Idan Har irin wannan suyar mata suke ji idan mijinsu zai kara aure to la shakka sun cancanci a yi hak'uri da su a kuma rarrashe su iyakacin rarrashi. Hawwah so nake na mutu ko na huta da azabar ciwon da k'irjina yake yi mini. Da ace nasan haka Bilina ta dinga jin radadin aurenki da na yi a zuciyarta da ban auro ki ba, bare ki zmaa sanadin rabuwata da masoyiyyita ta gaskiya ".

A zafafe Hawwah ta ce "Hala dai bayan kishi da yake yagalgalaka har Kanka ne ya tabu? Menene nawa a cikin rabuwarku? Wuka na saka maka ko bakin bindiga akan sai ka sake ta?"

Cikin fitar hayyaci ya ce ", Aurenki ne dai sila. Kullum zuciyarta na zafi da turiri Aman ban kula ba, ban rarrashe ta ba, Sai ma danne mata hak'kin tare da fifitaki akanta da ya'yanta. Ga shi na rabu da lu'ulu'u na kama azurfa".

Bak'in ciki mai tsananin gaske ya shak'e Hawwah da muryar kuka ta ce "Ni ka misalta da azurfa ka kwatanta wacce take shirin Zama matar gabjejen jarumin Dan'sanda irin Asad Funtua da lu'ulu'u? Ta nisa ta had'iye kukan ta ce "Ina tabbatar maka sai Anty Bilki ta ga banbancinka da sabon angonta fiye da banbancin da ka ga ni a tsakanina da ita. Don kuwa shi ba zai yi mata butulci ya yaudari budurwa da dukiyar da take mallakinta ce ba, a dalilin shi gabjejen attajirine ba da kudin mace ya yake tutiya ba.

Bak'in ciki kan bak'in cike ne ya dinga k'wamushe shi. Ga wani irin azabben ciwon da yake barazanar fasa masa k'irjinsa ya yi masa k'awanya. Take Jiri ya kwashe Shi ya fadi yaraf kan kujera.

Yayin da Hawwa ta ja tsakai mai tsananin gaske ta wuce zuwa samanta tana fad'in "Idan aka wayi gari da kai lafiya to tabbas soyayyarja bata cika ba don kuwa kamata ya yi ka bak'unci lahira kafin wani ya fara sukuwa akan matar da kake ƙirarin kana sonta".

A wannan dare Sahal ya gane me kira da nisan dare don kuwa ya Ga tsayinsa matuk'a gaya. Sannan shine dare Mafi tsaurin a dukkan rayuwarsa. Wani irin Kishin Asad da tsanarsa ne suke ta walagigi da shi. Ya dinga addu'ar Allah ya gajartawa Asad kwana Bilki ta yi masa takaba ta dawo masa shi da Ya'yansa.

A masallacin juma'a na k'asa na birnin tarayyar Nigeria aka sake daura auren Bilkisu a karo na biyu da sadaki mai k'ololuwar daraja.

A lokacin da ta ga alert din kudi mai nauyi a asusunta daga kuma Yaya Farouku. Murmushin da babu nishadi ya k'wace mata domin so ta yi ace shine da kansa ya bata sadakin ba waninsa ya biyawa ba.

Bata ce komai ba don sosai alhini ya kutso mata.

Abida ta dinga yi mata d'an bikin ta yi daraja da yawa.

Ba wani shiri Bilki take yi ba Abida ce ta ce sai sun yi walima ta kuma karbi kudade a hannun Ango, na kwalliya da gyaran jiki, masu nauyi.

Ango kuma bakin shi har kunne a wajen yin hoto yana ta kama Balki tana bige masa hannu amma shi bai damu ba, a ransa yake fad'in an daura dai hankalina ya kwanta.

An sha walima a gidan zuwa biyar aka kai Amarya kayattacen gidan Ya Asad bayan Baba Babba ya yi mata nasiha sannan ya damkawa Baba Faruku ita ya ce ya kai ta gidan mijinta, tare da fad'in "ko na mutu ka tsaya mata Farouku!.

Abida da Saddiqa da Momi, da matar Ansari suka bisu a baya.

Yaya Hamida dai ta ce zata zo bayan biki, don kuwa ta ji haushi da Bilki ta auri Asad mutumin da bai zo musu gaisuwar mami ba.

Ba su wani jima ba suka tafi bayan Abida ta yiwa Bilki raɗa.

"Saura ki matsewa yayana cinya".

Bilki ta ture ta tare da fad'in "Abin da yake ranki ke nan ko?"

Abida ta kyalkyale da dariya tare da fad'in "ke kika koya mini irin wadannan zantukan, dan haka gobe da azahar zan zo na ji bayani".

Bilki ta yi mata k'aramin tsaki tare da fad'in ki zo sassafe ma Abida ".

Ta yi dariya ta fice ta samu sauran a falo suka tafi suka bar amarya ita kad'ai.

Tana tunanin yadda zasu kwashe da angon nata da yake ta rawar jiki tamkar ya yi shekaru goma babu mace tare da shi.

Tasan yau dai kam ba zai daga mata k'afa ba

Rawar k'afar da yake yi kadai ya isa ya nuna ya matsu.

*Surayya Dee*

✍️

37 / 37