Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   26 / 37

75K to 78K   out of 110.8K words

hak'ura ya yi musu sallama.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Alti ta bi shi k'ofar gida ta ce "Yaya Farouku kada fa ka yi fishi da Mahma gabad'aya fa ba a hayyacinta take ba. Sannan ba zata yarda ta bar Katsina ba, ba don komai ba sai don ya'yanta."

Ya girgiza kai tare da fad'in "Ko zata mutu kuwa sai ta bar Katsina. Su mata basa tunanin komai da kowa sai ya'yansu? To idan ya'yan suka mutu suka bar ta sai ta fasa rayuwa ke nan? Ko kuwa idan ita ta mutu ya'yan suma mutuwa zasu yi?"

Alti ta yi shiru don bata da ta ce wa akan sha'anin, amma itama kam da za'a samu a raba Bilki da garin da tafi son hakan tunda zullimin da take ciki kada mijinta ya ce ya mayar da ita don bata yiwa Bilki fatan komawa hannun wannan mutumin.

Ya ce "mu je na sake yi mata sallama ko zata amsa"

Suka shiga har d'akin suka tarar har lokacin tana lullube ruf ya kaurara murya ya ce "Maigado!

Ta bude fuskarta sannan ta bude idanuwanta ta zuba su akan fuskarsa.

Ya numfasa ya ce "Zan je na bincika asibitin da ya dace Ki dinga ganin likita. Gobe da safe ki shirya da wuri zan zo na d'auke ki da Alti zuwa asibitin".

Kai ta daga masa tabbacin ta ji.

Ya numfasa ya ce "Za ki je ai ko?"

Nan ma sake gyada masa kai ta yi alamun zata je din".

Daga hakan ya ce "To na tafi sai goben".

Ta d'aga masa hannunta na dama alamun bye bye.

Ya fita a matuk'ar sanyaye don ba zai yaudari kansa ba. Bilki ta samu matsala.

Har mota Alti ta raka shi tana ta yi masa fatan alheri mai yawa.

Tunda ya tafi yake ta nazarin asibitin da zai kai Bilki.

Karshe dai ya ya make shawarar ya kaita babbaan asibitin gwamnati don yafi son kwararren likita ya ganta.

Sai yamma ya samu nutsuwa bayan abokinsa da yake pharmacist ne a cikin asibitin ya ba shi tabbacin Su zo karfe tara na safe zai had'asu da likitan da zai duba ta.

Washegari kuwa k'arfe takwas a gidan Bilki ta yi masa. Ya tarar Alti na fama da ita ta kurbi ko ruwan shayi ne amma ta k'i.

Haka ya ɗebe Su zuwa asibiti.

Basu sha wahala ba suka ga likita. Ya yi dube dubensa tare da tambayoyi wanda sau d'aya Bilkisu ta amsa Duk Alti ke ba shi amsa.

Ya kalli Farouku ya ce "Depression ne ya shige ta!

Don duk alamomin cutar sun bayyana a tare da ita. Zan d'ora ta akan magani sannan a dinga samar Mata da nutsuwa tare da yi mata abubuwan da zai ɗebe mata kewa tare da sanya nishadi."

A sanyaye Yaya Farouku ya ce"Za'a kiyaye Dr. Ya mik'a masa hannu suka yi musabaha, ya yi godiya sannan suka tafi. Mota ya bude musu suka shiga, shi kuma ya wuce ya siyo magungunan sannan ya yiwa abokinsa godiya.

Tunda suka hau titi ya tausasa harshe ya dinga yi mata nasiha da muhimmancin yarda da k'addara.

Ba zato suka ji ta ce '"Na gode sosai Yaya Faruku. Zuwan da ka yi Katsina don ni ya tabbatar mini ina da sauran gatana".

Idanuwansa suka cika da k'walla amma ya sanya jarumta bai bari sun zuba ba.

Da suka isa gidan ya ce "Maigado ki daure ki ci abinci don na tabbatar kin ji dad'in zuwana da gaske."

Ta yi k'asa da kanta.

Ya ce "A zubo miki?"

A hankali ta ce "Eh."

Da azama Alti ta zubo mata kunun gyada da ta yi mata tun dare ya zuba a flask amma bata sha ba.

Ta karba ta kafa kai ta shanye nan da nan ta mik'a mata kofin.

Dad'i ya kamasu sosai. Alti ta ce "To ke fa? Rashin cin abincin ma ai jinya ce babba."

Ya numfasa ya ce "Bilki ina son na tafi da ke Abuja kuma tare da Alti zamu tafi ta cigaba da kulawa da ke ".

Nan da nan idanuwanta suka cika da k'walla ta dinga girgiza kai tabbacin ba zata bi shi ba kenan.

Ganin zata sake rikice wa ya sanya ya ce "To Shi ke nan ki zauna a nan din amma ki dinga shan maganinki akan kari. Idan lokacin komawa asibitin ya yi zan dawo da kaina na mayar da ke".

Murya ba amo ta ce"Ubangiji ya fini yaba maka Yaya Farouku ".

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Kafin tafiyarsa sai da ya tura mata kudi masu nauyi ta asusunta, kudin da suka ba ta mamaki ainun. Da za ta yi masa godiya ya bata rai tare da ce wa "Kada ki ce komai fatana ki kwantar da hankalinki, ki dinga cin abinci da magani ".

Ya yi musu sallama ya tafi yana ayyana al'amura masu yawa a kanta.

Zuwan Ya Faruku ya tafi da kaso mai yawa daga cikin damuwarta, mussaman da su Amrah suka zo sau biyu tana ganinsu ba'a yanayin tashin hankali ba. Sannan ga Basma ko da yaushe tana tare da ita, idan ba ta zo ba, za ta kira wayar Alti ta tambayi jikin Bilki.

Sahal tare da iyalinsa. Hawwa a gaban mota zai kaita asibiti awo. Yayin da Amrah da Farouk suke baya sanye cikin uniform dinsu. Dama can Amrah ita ta ke yi musu wanki a injin wanki, sai idan Farouk ya yi mata rashin kunya take ware nasa ta bar masa ya yi da kansa. Amma wankinsu ita da Farha ita take yi, ta kuma zauna ta goge musu tsab. Uwarsu da zata tafi cikin abubuwan da ta bar musu har da injin wankin. Da k'aramin firij, da k'aramin gas da kuma kettle da iron. Hatta tv sai da ta bar musu karama ta cikin d'akinta. Ta ce su dinga kallo.

Fes suke tunda mamarsu ta bar gidan basu yi fada ba. Komai Amra ta ce ya yi baya yin musu yi yake yi, sannan komai tare suke yi. Dan haka itama take yi masa komai. Babansu ya tattaro ya dawo b'angaren Bilkin, ba ya yarda ya hau saman sai idan da rana ne ko yammaci.

Hawwa ta yi fishi da b'acin rai amma bai canja ba. Ya kafe ba zai bar ya'yansa su dinga kwana su kad'ai a k'asa ba.

Kan dole ta ke biyo shi ta kwana tare da shi.

Ban da kwana komai a samanta ya ce ta dinga yi, kasa na yaransa ne.

Makarantar su Farouku ce ta fi kusa dan haka shi aka fara ajiyewa. Ya sauka Amrah ta mik'a masa lunch box d'insa tare da fad'in "Allah ya bada sa'a yayan Mahmah".

Ya karɓa yana murmushi amma bai ce 'kala ba".

Tunda babarsu ta tafi baya yiwa kowa magana sai Amrah. Idan safiya ta yi ya gaida Dady da anty to ba zai sake bude baki ya yi musu magana ba sai ta k'ure ko idan su suka yi masa. Sahal ya fahimci yadda Farouku yake kama da y'an gidansu Bilki haka ya dauko rashin warginsu. A ransa yake ganin Abida ce tafi dacewa ta zama uwarsa ba Bilki ba. Sannu a hankali yake rikidewa yana zama tamkar Sulaiman ne ya haife shi dan haka sosai suke kama da Farha.

Ya zama marar son hayaniya.

Sahal ya ce "Yaya me kika yi muku ne yau?"

A hankali ta ce "Muna da samosa da meat pie a fridge, su na soya mana. Mun karya da golden morn kuma".

Ya ce "Da kyau amma Amrah ba kwa tinawa da Dady. Kinsan yadda nake son snacks din Mahma kuma yanzu da take baku ai sai ki dinga tunawa da Babanku".

Ta dan yi gajeran murmushi tare da fad'in "Idan na dawo zan soya maka to".

"Yauwa uwata Allah ya yi miki albarka ".

Daidai lokacin suka isa makarantar su Amrah.

Ta sauka tana ce musu a dawo lafiya.

Hawwa da take zaune gaban mota ta cika ta yi fam tunda ta shigo motar uffan bai ce mata, ya'yansa kawai yake kulawa.

Tun ba'a je ko ina ba, murnarta ta fara komawa ciki bisa dalilin hankalinsa yanzu ya koma yaran sabanin lokacin da uwarsu take nan hankalinsa kacokan na kanta.

A da ita kad'ai yake ɗauka a mota suna tafe yana mata hirarraki masu dadi da saukar da kunya. Haka idan zasu dawo, ya dinga tarayyarta da siya mata abubuwan ciyeciye. Amma yanzu idan ya daukosu ba abin da yake yi sai hira da yara. Sannan ya ce d'akin Bilki ya koma na Amrah. Dakinsu Amrah kuma ya rufe shi. Sannan kicin din Bilki ma yaran ne zasu dinga amafani da shi tunda uwarsu ta bar musu kayayyakin da zasu buk'ata. Dakin Farouku kuwa yana nan a nasa.

Gabadaya ya rikice yana jin hak'kin Bilki kad'ai ya isa ya damalmasa lissafi. Amma sai ta shayar da shi mamaki ta ce ta yafe masa. Shi kuwa tunda ta yi masa hakan zai yi iya k'ok'arinsa ya ga ya'yanta basu wulak'anta ba.

*

Hakan nan baya musgunawa Hawwah don har y'ar aiki ya daukar mata amma ba mai kwana ba, zuwa take yi da safe ta yi shara da moping, sai ta yi girki. Shikenan sai ta yi tafiyarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sun ajiye Amrah ba jimawa ta ce"Yanzu dai dear baya ta tawa".

Ya ce "Ko d'aya ba wannan batun kawai ina jan yaran a jikina ne dan kada du shiga damuwa da yawa."

Ta langwabe kai ta kalle shi cikin wani irin yanayi ta ce "Ka raina yadda nake kula da su kenan?"

Ya dan yi murmushi kad'an ya ce "Ban raina ba my sweet baby".

Ta ce "Ina son mu dinga zama muna hira da su, amma Farouku sam ya bijire, ya kuma hana yayarsa ma. Da na k'irata ta hawo samana minti k'alilan zai ta k'walla mata k'ira ta zo ta ga wani abu. Shi kuwa idan har ya zo inda nake to gaisuwar safe ce bayan haka duk juyin da zan yi ina k'iransa ba zai nuna ya ji ba bare ya amsa, ya samo wata ear pies kullum yana mak'ale da ita a kunne."

Sahal ya numfasa ya ce"Kin san maza tun muna yara bamu da mu'amala irin taku ta mata. Ni kaina ai kin ga ba wani shige mini yake yi ba. Ki dage ku k'ulla abota da Amrah idan ya ga kina son yayarsa zai sauko. Sannan kada ki yarda ki nuna masa kin gane baya ra'ayinki".

Ta yi shiru tana ayyana ita kam bata ga ribar da ta ci da Bilki ta bar mata gida ba. Mijin hankalinsa yanzu yafi karkata kan ya'yanta. Sannan gidan da take ganin zata mamaye shi ita kad'ai ya ce "Na ya'yansa ne. Bata da alak'a da k'asan idan ba kwanciya barci ba, tunda a d'akinsa na wajen Bilkin suke kwana bisa dalilin ya'yansa yara ne ba za su kwana su kad'ai ba".

Gabadaya yanayinta ya fara sauyawa don da uwarsu ta na nan baya wannan kaffa kaffar da su. A ranta tana ayyana bari ta haihu ba zata yarda da wannan abin da ya b'ullo da shi ba.

Ranar wata asabar tun safe Farha ta dasa kukan ita dai a kaita gida wajen su yaya Farouk.

An yi rarrashin an yi hilar amma ta k'i yin shiru. Bilki ido kawai take binta da shi. Ta rasa me yake mata dad'i.

Alti ta ce "Ga Alawiyya ta tafi bare ta rakata su yini.

Kafin Bilki ta bude baki suka ji ana hawa saman a guje sannan suka ji ana kwnakwasa k'ofa. Da sauri Alti ta bude don tasan babu mai hawa a guje haka sai su Farouku.

Ilai kuwa sune d'in. Farha ta tafi a guje ta rumgume Farouku tamkar jiya basu hadu a makaranta ba. Amran da ta dade bata ganta ba, ba ta yi mararinta kamar yadda ta ke yin ta Farouku ba.

Hankalin Bilki ya dan sake nutsuwa ganin yaranta basa cikin matsala.

Farouk ya rik'e hannunta ya ce "Mahmah kin zama y'ar karama fa! I thought idan ba kya wanccan gidan za ki daina kuka kullum. Ko anan din ma ana saki kuka ne?"

Ta yi jarumta ba ta yi kukan ba. A hankali ta ce "Bana kuka Yaya Farouk. Ya ce "Yauwa ki dinga cin abinci, tunda kika taho nan ba mu yi fad'a da Yaya Amrah ba. Komai ta ce na yi ina yi ko Yaya?"

Ya tambayi yayar tasa.

"Hakane"

Amrah ta tabbatar da jawabansa.

Bilki ta dan murmusa kad'an ta ce "Allah ya yi muku albarka gabadaya ".

Basu tafi ba sai washegari lahadi da daddare lokacin da ya zo daukarsu tuni Farha ta yi barci dan haka lafiya lau suka tafi.

Ganin da Alti ta yi an fara samun cigaba a lafiyar Bilki ya sanya ta roke ta akan ta kunna wayoyinta.

Haka kuwa ta kunna kiran Yaya Hamida ne ya fara shigowa ta dauka suka gaisa cikin k'arfin hali ta fad'a mata halin da take ciki.

Hankalin Yaya Hamida ya tashi ainun amma ta dinga bawa kanwarta hak'uri tare da k'arfafa mata guiwar komai zai wuce tare da yi mata fatan alheri.

Ta kuma bata tabbacin zata zo a karshen sati in sha Allah.

Haka Ansari da su Saddiqa da Anisa duk sun ji halin da take ciki dan haka kullum sau biyu suke yi mata waya suna jin lafiyarta, za kuma su zo dubata a cikin satin da zai kama. Ansari kam takanas ya taho ya gaishe ta. Ganin ta samu sauki ya ce "Ta koma aikinta hakan zai sake rage mata damuwa.

Ta karbi shawararsa amma ta ce "Sai ta koma asibiti, sannan zata cigaba da zuwa makaranta.

Farha sosia ta makale masa ya dinga mamakin hakan a ransa ya ce tasirin jinin mahaifinta take ji a jikina.

Gabadaya ta juye sak Bilki haka da ya ga k'aninta junior sak Bilkin sai dai da za'a ga Sulaiman sai a ce sak shi.

Amma dai ba wanda zai ce Abida ce ta haife su, basa kama da ita.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *

Baba Babba da Yaya Farouk da babban d'ansa Ammar da yake aji biyu a jamiar Abuja da kuma Momi suna falon Baban a zaune.

Ya ce "Anya Farouku lafiyar Bilki k'alau kuwa? Duk juma'ar duniya sai ta gaishe ni amma yau juma'a ta hud'u ke nan ban ji daga gareta ba.

Yau tunda na dawo masallaci nake k'iranta amma layin a kashe yake."

Ba kuzari Yaya Farouk ya ce "Wallahi Baba ban fad'a maka ba ne. Bilki bata da lafiya an k'ira ni sati biyu da suka wuce. Ya yi masa bayanin komai.

Hankalin Baba Babba ya yi tashin gauron zabi ya ce

"Yanzu Farouku kasan da wannan al'amarin ka sakaye mini?"

Cikin girmamawa ya ce "Lokacin kana ta fama da zazzabi Baba ga shi jininka ya d'an hau sai na ji tsoron kada ya yi tashin da zaka jigata, amma na je na kaita asibiti na yi duk abin da ya kamata"

Baba Babba ya ce "Me ka yi Farouk? A ce d'iyar Isa tana zaune a gidanta ba kuma zaman aure ba? Ina da raina, sannan ku ma da ranku? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tabbas Bilki ta yi gaskiya da ta ce "Su yanzu ya'yan mahaifinsu basu da wanda zai tsaya musu. "

Daga Momi har Yaya Farouk hak'uri suke ba shi akan ya kwantar da hankalinsa.

Murya na rawa ya ce "Hankalina ba zai taba kwanciya ba kuwa matuƙar Maigado tana Katsina tana zaune ita kad'ai ba a gidan aure ba. Ga Abida tana gabana alhalin aurenta ba mutuwa ya yi ba. Lallai na ci amanar zumunci!

Ya fad'a hankalinsa ya kai k'urewar tashi.

Da k'yar aka samu ya daidaita ya daina kuka.

Ya ce " Farouku jibi nake son na ga Bilki a gabana."

Ya ce "Wallahi Baba na yi iyakacin kokarina akan na taho da ita, k'i ta yi, to ganin so nake lafiyarta ta daidaita tunda damuwa ce ta yi mata k'awanya ya sanya na rabu da ita. Kasan mata da y'ay'a.".

Baban ya ce "Har ya'yan ya bar mata ke nan?".

Yaya Farouk ya ce "A a suna wajen Babansu".

Baban ya numfasa tare da fad'in "Ka je ka taho mini da ita umarni na baka. Sannan idan uban ya'yan zai bata su, to ku taho tare da su zan rik'esu gabad'aya."

Kwanaki biyu a tsakani ya tafi Katsina. Ya ji dad'in yadda ya ga ta samu sauk'i.

Dan haka ya zauna ya yi mata bayanin abin da Baba Babba ya ce.

Ta yi shiru tana tunani gabad'aya kanta ya kulle. Yaranta fa da suke zuwa suna ganinta tana jin dad'i suma su na ji?

Aikinta fa, sannan ya zata yi da Alti da bata da kowa sai ita?

Amma bata isa ta ja da umarnin Baba Babba ba don kuwa ta sa ni tun mahaifinsu yana da rai Baban ne mai zartar da komai. Sannan ba zata iya kallon idon Yaya Farouku ta ce ba zata ji maganar mahaifinsu ba.

Kan dole Alti ta shiga had'a mata kaya amma iya na sakawarta don kuwa ta ce zasu dawo. Zuwa zata yi ta bawa Baban hak'uri tare da fahimtar da shi muhimmancin zamanta a Katsina.

Washegari sai da suka je asibiti ta ga likita ya canja mata magani a cewarsa akwai sauyi akan farkon zuwansu. Sai dai ya ga alamun bata samun barci don idanuwanta sun yi tsilli tsilli wanda daga jiya zuwa yau ne ta zama haka, ba dan komai na sai don umarnin da aka bata na lallai ta je Abuja in ji Baba.

Daga asibitin kaitsaye makarantarsu Farha suka je suka dauke ta. Yayin da Farouk junior ya yi tsamo tsamo jin Mamah zata tafi Abuja.

A sanyaye ya ce "Mahmah can za ki zauna ko za ki dawo nan?"

Da rishin kuka ta ce "Idan Baban ya bar ni zan dawo"

Ya rik'e hannunta ya ce ",Idan ya ce "Ba za ki dawo ba, to ki yi zamanki. Ni da Yaya bama fad'a kuma muna cin abinci idan an yi hutu zamu zo".

Daga

26 / 37