Alti har Yaya Farouku k'walla ce dam a cikin idanuwansu.
Murya ba amo ta ce ",To yayana, ka fad'awa yaya idan baku jini a waya ba ku k'ira layin Ammi ko na Alti"
Ta shafa kansa ta ce "Allah ya tsare mini ku, ya yi muku albarka".
Sai lokacin hawaye ya k'wacewa yaron. Ya mik'a mata hannun Farha ya ce "Watarana zan zo Farha".
Farha na kuka Bilki ta danna a mota Farouk ya rufe kofar.
Sannan ya doshi wajen mai Sunansa ya duka ya gaishe shi. Gabadaya jikin Yaya Farouku senior ya mutu murus ya kamu da ciwon tausayin Bilki da ya'yanta.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya ciro kudi da yawa ya ba shi ya ce ka kaiwa yayarka ku ajiye. Ku dinga siyan abin da kuke so a hankali.
Idan na ji ba kwa yin kuka, to da kaina zan zo na tafi da ku a jirgi idan an yi hutu."
Haka suka ja mota suka bar yaron yana daga musu hannu.
Sai dare suka shiga Abuja.
A gajiye.
Sun samu kyakkwar tarba don Baba Babba da kansa ya rik'e hannun Bilki ya kaita d'akin da yake makwabtaka da na Abida.
Haka momi ta dinga ina ka saka da su.
Y'an aiki suka baibayesu da abinci.
Amma me gabad'aya Bilki ta sake rikicewa ko da gari ya waye ta sake komawa yanayinta na farko. Ba um ba umum sannan ba cin abinci. Ta fi son a fita a barta ita kad'ai. Ga ba cin abinci.
Yaya Asad ya zo gidan da hantsi ya ganta sosia hankalinsa ya tashi da ya ga yadda ta koma.
Ya kalli Abida da take kanta ya ce "Da alamun fa ba'a hayyacinta take ba."
Yaya Farouku ya ce "Tahowar nan da aka yi da ita ne ya sake haustina ta. Kai! ni kaina ban yi barci ba, kwana na yi ina nadamar yaron nan Farouk! Dan har ta fara samun nutsuwa, daga jiya komai ya sake k'wacewa ".
Abida ta numfasa ta ce "Depression ne ya damke ta da kyau idan ba'a bita a hankali ba kuma yana iya zama saikatiric ishus.
Yaya Asad da bai san aurenta ya mutu ba ya ce "To menene damuwar Maigadon da zata hadu da ciwon damuwa irin haka.?
Ya juya ga Yaya Farouku don jin k'arin bayani.
Ya fad'a masa sun rabu da mijinta ta kuma bar masa ya'yansa.
Jikinsa ya yi sanyi don ya san zafin rabuwa da abin da ake so. Ya tuna tashin hankalin da ya shiga a lokacin da ta yi aure. Yanzu kuma shi kad'ai ya san yadda yake ji a dalilin rashin matarsa uwar ya'yansa. Shi kad'ai yasan yadda yake jin tausayin ya'yansa a dalilin suna rayuwa babu uwa. Yasan yadda Bilki take ji a zuciyarta.
Ya kalli Abida ya ce "Wai ya ya ciwon damuwar nan yake ne Dr?"
Abida ta d'ago kanta ta ce "Da yake ba a fannin na k'ware ba, bari na yi maka bayani daidai gwargwadon yadda na fahimta da yadda zaku fahimta."
Ta muskuta ta ce "Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.
Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa!
A kan yiwa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko kuma wasu ma su ce rashin haƙuri ne, ko rashin tawakkali ke haddasa ta ga wanda ya gamu da ita."
Ta numfasa ta zarce da fadin
"Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba dangane da cutar shi ne damuwa cuta ce kamar kowace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum!
Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa, da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kai."
Yaya Asad ya ce Sannu Dr Abida. Amma menene alamomin cutar?"
Dr Abida ta ce "Alamomin da ya yawa sannan ya banbanta daga wasu zuwa wasu. Amma manyan alamomin da likitoci suka bayyana sune kamar.
*TSANANIN BAK'INCIKI*
"Babbar alama ga mai fuskantar matsananciyar damuwa ita ce tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili.
Mai fama da wannan cuta ka iya tsintar kansa a kodayaushe cikin ɓacin rai da rashin walwala.!
Za ka ga kwata-kwata mai wannan cutar ya rasa farin ciki. Abin da zai sa sauran mutane farin ciki, shi zai iya ƙara masa ɓacin rai har ma ta kai mai cutar ga son ƙebewa daga jama'a.
*KEBEWA DA K'IN SHIGA MUTANE*
Dakta Abida ta ce "bayan samun ɓacin rai ga mai cutar, wata alamar da ake ga ni a masu wannan cuta ita ce keɓe kai.
"Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a ɗaki shi kaɗai, sannan zai rage walwala.
Ko fita za a yi gaba ɗaya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida."
*ƊAUKEWAR BARCI KO YAWAITARSA*
Dr Abida ta cigaba da fad'in "yana ɗaya daga cikin alamomin matsananciyar damuwa yawan barci ko ƙarancinsa.
"Yawanci masu fama da cutar damuwa za ka ga ko dai barci ya yi musu ƙaranci ko kuma su yi ta barcin ba ƙakkautawa".[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *RASHIN SON CIN ABINCI KO YAWAN CINSA*
"Yana ɗaya daga cikin alamun matsananciyar damuwa tsananin cin abinci ko rashin cin sa, inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba."
Ta nisa ta cigaba da ce wa
"Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sannan akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai yake iya magance ta
Sakamakon tsananin ɓacin rai da keɓewa daga jama'a, masu fama da cutar kan yi tunanin rayuwarsu ba ta da amfani, saboda haka sai su nemi mafita - wato kashe kai.
Kisan kai al'amari ne mai sarƙaƙiya wanda yake faɗowa mutum a tunaninsa a matsayinsa ne mafita.
Ko kuma mutum ya yi tunanin ce wa shi ne zai kawo ƙarshen wahalar ko matsin da suke ciki a rayuwa!
Duk da ce wa yana da wuya a fahimci dalilin da zai sa wani ya yi yuƙurin kashe kansa, mutanen da ke wannan yunƙurin kaɗai suka san me yake faruwa a cikin zukatansu."
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "61" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c14e6f82315f17460a4c92
"Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart."
Abida ta faɗa tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta.
"Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?"
Ta faɗa tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka.
Abida mai taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi.
"Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?"
Bilki ta faɗa itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci ɗaya.
"Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faɗa mini inda Ya Sulaiman yake ida kin sa ni. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faɗa mini in dai kin san inda yake Bilki.".
Abida ta faɗa cikin karyewar zuciya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "62" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1534d82315f17460a990d
"Lalle Babban yaya alama da zafin sa ya kutso. Mu yara sai mu mu yi baya "
Bilki ta ji zafin maganarsa sosai ta ɓata rai tana kallon shi kafin ta ce" Ya Faruku abin da za ka yi mini ke nan?"
Kana nufin abin da nake ga ni a idanuwanka wannan karon ma iska zai bi?"
Ya kasa bata amsa sai kawai ya tafi babu sallama.
Zuciyarta ta yi kunci bata yi zaton zata sake son wani namiji kwana kusa ba. Amma tabbas son Yaya Farouk ya kutso da k'arfin gaske daga inda ta sakaye shi a zuciyarta.
*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "63" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c157b482315f17460ae55c
"Idan kana son Bilki to ka nemi yardarta idan ta amince, nima na amimce kasan yanzu ba yarinya ba ce tana da wannan damar sannan kar ka manta ko da suke yara ban yi musu auren dole ba bare yanzu tana da y'ancin ta yiwa kanta zaɓin da take so. Idan ta amince da kai to zan fi kowa farinciki zan kuma taya ka da addu'a Allah ya tabbatar. Idan har hakan ya faru komai zai daidaita, waki'ar da ta nisantamu da juna zata gushe a zukatanmu. Ƴan'uwanta za su samu damar zuwa gidanka su yi zumunci kai ma naka za su je, daga nan komai da ya faru na rashin jituwa a baya zai wuce ba na fatan na mutu na barku a cikin wannan halin, Sulaiman ya tafi ba mu san inda yake ba, idan yana raye Allah ya bayyana shi. Idan kuma tana san inda yake ta boye, idan ta zo hannunka kana hillatarta duk za mu ji komai."
Yaya Asad ya ji ƙarfin guiwar tunkarar Bilki a wannan gabar tunda ya samu amincewar Baba Babba da Abida. Dama Abidan yafi ji da Usman amma tunda Abida bata botsare ba yasan Usman ba zai samu tallafi ba. Mamakin yadda Abida ta huce ta yi sanyi akan ahalinsu Bilki yake yi.
Da Bilki ta dawo ba wanda ya yi mata zancen zuwan Asad shi yasa ba ta san ya zo gidan ba. Shi kuma tun tafiyar shi kullum da safe zai tura mata sakon gaisuwar safe da asubar fari. Da daddare ma akwai na mu kwana lafiya. Ga k'iran waya akai akai, yana kashe murya yana yi mata kalamai irin na jirwaye duk da ta fahimci manufarsa amma sai ta nuna masa bata gane komai ba. Kuɗade masu nauyi yake turo mata akai akai, idan ta ce sun yi yawa ko ya daina. Ce mata yake yi idan Sulaiman ne ya tura mata kuɗi ai karba za ta yi ta gode masa, ba ta ce bata so ba jin haka yasa jikinta ya yi sanyi, bata sake ce masa komai ba, idan ya tura mata kuɗi sai dai ta yi godiya amma a cikin zuciyarta ta kudire yayaa Asad ba zai iya siyan soyayyarta da kuɗi ba. Kuma tana jiran ranar da zai gaji da ƙumbiya kumbiyarsa ya fito fili ya faɗa mata, daga ranar za ta fada masa ya daina wahalar da kansa don kuwa bata ra'ayinsa.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "64" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1c4cd006c2321ccbf267b
Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zaawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in.
Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu.
Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce ",Amma ina na Abida kasana tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce".
Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba."
Ya kammala fad'a yana shafa kansa .
"To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan."
Ta faɗa tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa.
"Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki tayani shawo kanta."
Ya fada cikin jin kunya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: I just published "65" of my story "DINGISHIN KWADO"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c1c583006c2321ccbf30fa
Bilki ta fara kuka mai sauti tana fadin" Ya Farouku me ya sa ba kai ba?
Me ya sa ba ka ce kai ne za ka aure ni ba ? Kana cutar da ni. Tun ina budurwan kasan ina son ka, kai ma na san kana sona amma saboda wani banzan dalili ka haramta mna9 cikar burinmu. Yanzu kuma bayan na dawo ka daɗa ja na a jiki ka sanya mini son ka da mararinka, ina ta tunanin wannan karon zan same ka mu yi rayuwa tare. Zuciyata tana girmamaka tana sonka, shi ne za ka zo mini da wannan maganar alhalin ina jin nauyinka. Ni dai gaskiya tunda ba sona kake yi da gaske ba, to kawai mu bar shi a hakan, ka bar batun mutumin can".
Ta gama fada tana kuka wurjajan kamar wata karamar yarinya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Na gode da addu'o'inku Ga mahaifiyata, wanda suka yi mini ta pc da Wanda suka yi a group dan Wanda suka yi ban Sani ba*
Na gode Allah ya karba ya jiƙan dukkan magabatanum*.
*Allah ya bada lada ya bar zumunci*.
*"Amma mene ne makasudin da yake janyo cutar tsananin damuwa?"*
Yaya Faruk ya yi tambayar a nutse.
Dakta Abida ta ce "cutar tsananin damuwa na iya kama kowanne jinsi na mutane, sannan ana ganinta a manya da yara duka.
Sai dai an fi ganin ta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga.
Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne yake shiga halin tsananin damuwa, kamar rasa wani makusanci, karayar arziki, ko kora daga wajen aiki, ko haihuwa mai cike da tangarɗa, da dai sauransu."
Dakta Abida ta cigaba da fad'in "yanayin halittar ɗan'adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.
Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba!
Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba shi iya jure jarrabawa. To irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa.
Sai dai wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta."
*"Ana warkewa kuwa dr?"*
Yaya Asad ya sake tambayar Abida.
Ta ce "ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya dace!
Idan aka lura alamomin wannan cutar sun bayyana ga wani ko wata, abu na farko shi ne a kai shi asibiti kaitsaye. A guji camfi ko jinginawa jinnu don yin wasarere da jinyar na iya sakawa ya koma ciwon hauka!
Yaya Asad ya sake tambayar
"Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.?"
"Muna ba da magunguna, sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wannan cuta kewa, da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu."
Sannan ta ce "makusantansu su riƙa jan su a jiki, da nuna musu kulawa.
Waɗannan ne suke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya."
Yaya Farouku ya ce "Sannu da kokari Abidan Baba. "
Yayin da Yaya Asad ya ce "Gaskiya ina fama da wasu alamomin dan haka nima ya kamata na ga likita. Zan bincika asibitin da suke da kwararrun likitan da ya k'ware a fannin wannan matsalar sai ku dinga zuwa tana ganinsa."
Yaya Farouk ya numfasa ya ce "Tunda debe kewa na kan gaba wajen samarwa da mai lalurar sauki to ya zama wajibi mu taru mu dinga sanyaya mata zuciya. Sannan ke da kike gida ki tabbatar kin gyara mu'amalarki da ita. Duk abin ya faru a baya mu bar shi ya wuce, mu yi ta addu'ar kada a sake jarrabarmu da rikici a tsakaninmu."
A sanyaye Abida ta ce "To".
(Maitama clinic) Anan Bilki ta ke ganin likita bisa rakiyar Abida da Alti.
Ta taimakon Allah da kulawar mutanen da suke zagaye da ita aka samu ta fara komawa hayyacinta.
Mussaman da take ganin yadda Abida ta damu da halin da take ciki. Baba Babba da kansa kullum sai ya zo d'akinta ya duba ya yi mata nasihar ta kwantar da hankalinta ta bi yaranta da addu'a, tare da bata misalai daban daban,. Y'ay'a nawa ne suke rayuwa basu taɓa ganin mahaifiyarsu ba? Ya'ya nawa ne suke rayuwa babu uwa ba uba gabad'aya. Hakan kuma ba zai hana su cimma dukkan nasarar rayuwa ba.
Annabin Rahma (S.W.A) da Allah ya bar shi a maraya ya kuma daukaka shi a cikin kafatalin bayinsa kad'ai ayace da dukkan mai imani zai sake k'arfafa imaninsa.
Don kuwa Allah shine mafi kulawa da rayuwar bayinsa.
Ire iren bayanin da yake mata ke nan a kullum. Da kuma mutanen da suka shahara a yanzu amma kuma sun rayu ne a gidan ubansu babu uwa wala mutuwa ta yi ko kuwa auren ya mutu aka barsu suna yara.
Damuwar da Bilki ta ga ahalinsu sun yi da ita ya yi matuk'ar rage damuwar da ta tsinci kanta a ciki.
Dama matsaloli biyu ne suka ankarata.
Yaranta da kuma yadda Sahal ya ce mata bata da inda zata je. Da ganin tana zaune ita kad'ai din, amma a yanzu ta saduda ta hak'ura da batun yara mussaman da kullum sai sun yi waya ko a layinta ko a na Abida.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tunda Amrah ta shiga s.s1 aka siya mata waya tunda haka tsarin makarantarsu take.
Don akwai darussan da dole sai da bincike a yanar gizo.
Dan haka kullum da daddare suke yin waya don da safe bata tashi da wuri.
Sannu a hankali ta wartsake gabadaya har likitoci suka rage mata magungunan da take sha, suka bada shawarar a yawaita mata abubuwan da