yi masa wulakancin da ni zata bari a cikii. Amma ga mamakina sau daya tak ta bari suka gaisa.
Sai da ta bari ranar da zata tafi, muna tafe zan kaita asibitin inda zasu hadu da abokan tafiyarta.
Ta kalle ni ta ce "Maigado duk yadda na so na makance na kuma kurmance daga rayuwar gidanki na kasa wannan jarumtar. Yanzu haka kika zabarwa kanki? Kullum ke ce kai yara sassafe ko da sai da rana ko yammacin za ki wajen aiki, shi kuma gogan ba inda za shi amma yana nade a gado! Haka nan tunda ya rasa aiki sai kika yi sanadin da ya rasa jarumtar zuci? Dole aikin gwamnati ne kadai namiji zai yi ya rike iyalinsa?
Wato ke kina da kudi zaki rike kan ki, ki rike y'ay'anmu, sannan shima ki rike shi da dukkan lalurarsa?"
Ta tambaya idanuwanta na kan fuskata da nake tuki sannu a hankali.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Na numfasa na ce "A a Abida ba haka bane, ke da kan ki kinsan sadda yake da hali ba abinda da bai yi ba, mai kokarin kyautatawa iyalinsa ne. Yanzu kuma sai nake ganin bai kyautu dan babu ta same shi na boye masa wadata ko na yi masa kwange ba. Mussaman da a kullum yake yaba mini tare da jadda ba zai taba mantawa da alherina ba, ba shi kuma da burin da ya zarta ya samu damar da zai jiyar da ni dadi ya kuma yi mini halacci".
A wannan karon murmushinta ta yi, tsawon lokaci kafin ta ce"A takaice dai na fahimci ke kika sanagarta shi gabadaya. Sannan kika kasa nuna masa komin kashin sana'a ya fita ya yi da ya zauna ki yi masa komai a gidansa. To saurara ki ji da kyau!
Allah da ya halicce shi yafi ki sonsa, ya kuma fiki tausayinsa, ya kuma fada mana a cikin alkuraninsa mai girma ce wa ba ya dorawa rai sai abin da zai iya. Haka kuma cikin hukunce hukunce da ya gindaya a cikin aure ce wa ya yi "Namiji ko shine yafi kowa talauci ya ciyar da matarsa gwargwadon ikonsa, ko da kuwa matar itace tafi kowa arziki a lardin! Dan haka idan dan Allah kike wannan hidimar to ki sani ba shi ya dora miki ba, asalima sarayar da hakkunanki masu yawa kika yi, yana kwance ke kuma kina tafe kullum a titi da sunan kai yara makaranta, da kuma kuma daukosu ko da ace ba zaki je wajen aiki ba, ya zame miki wajibi ki yi hakan, wannan ke kika dorawa kanki babu wata sakayya da Allah zai miki. Kazalika idan kina yi masa hidima da tunanin nan gaba idan ya samu dama zai miki halacci to ki yi maza ki farka daga barcin yaudarar kai da kika jefa kan ki a ciki don kuwa tabbas zai shayar da ke mamakin gaske, yadda bai wani girme ki da yawa ba, lokaci zai zo da zai ga sa'anin Amrah ne daidai da shi at that time kuwa komai zai kubuce miki ne sai an yi sa'a zai tuna da yanzu da kike ta wahala da rike masa gida ba tare da kin yiwa kan ki tanadin gobenki da ta y'ay'anki ba. Na taba fada miki wannan maganar, yanzu ma na maimaita miki and it will be the last time da zan sake furta miki. Time will tells you the real fact".
Daga haka ta fito da gilashinta ta saka ta hau dube dube a wayarta.
Duk da nasan ta riga ta kammala bayaninta zai yi wahalar gaske ta sake jan maganar. Na yi kundunbala na ce "Na gane Abida in sha Allah komai zai daidaita, zan gyara in sha Allah!
Na fada da wata kalar murya marar amo.
Tare da tunanin ta ina zan fara ce wa zan janye daga yin abubuwan da take korafinsu? Alhalin duk yadda yake yaba mini idan na kuskure ce mini yake dole ya ga komai tunda ni nake da dama a yanzu, ni kuma tashin hankalina ya furta mini wannan kalmar.
Tun watanni shida da ya yi zazzabi na hutar da shi kai yara da daukosu kafin ya warware shike nan ya sallama mini har yau bai karbe ni ba.
Ni gabadaya ma mamakinsa ne yake dabaibaye ni ta yadda kullum kullum kirkinsa da tausayina yake raguwa a maimakon ace ya ninka, saboda yadda nima ban gaza da dawainiya da shi ba.
*Contact me 08032773332* *what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.
Surayya Dee
✍️✍️
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Har muka isa inda na kaita bata yarda mun sake maganar Sahal ba. Da na matsa da son sai ta kula ni ma a gajarce ta ce "To ban da kina da mantuwa bana fada miki ba zan shiga shirginki da mijinki ba? Yanzu ma kasa jure wa na yi ta yadda kika k'arantawa kan ki tunani da hangen nesa. Amma Allah yasa ki gane tun komai bai gama kwace miki ba."
Kwanaki biyu ina ta bitar kalaman Abida, amma na kasa samun mafita don na kasa fad'a masa ya dinga kai yara makaranta ya kuma dinga fita ko yaya ne, tunda a farkon rasa aikinsa yana fad'i tashi yana samun ana daukarsa yana tsayawa masu rangwamen gata suna biyansa yadda zasu iya. Amma yanzu kam da muka yi shekaru daya da rabi da rashin abin yinsa ya daina fita gabadaya da sunan yin sana'a kullum yana gida a nad'e akan gado, ko kujera kamar wani hamshakin basarake in ji Abida.
Ban san me ya saka Sahal da Abida basa ra'ayin junansu ba har yanzu da muka kwashe kusan shekaru goma da aure. Don bayan tafiyarta da kwanaki biyu bana mantawa, na dawo daga office k'arfe uku na yammaci gajiya da yunwa suka sababa mini ciwon kai, a falo na zube iskar fanka na kada ni. Yayin da yake zaune kan kujera yana kallon labarai a tashar C.N.N.
Hankalinsa ya raja'a akan yak'in da Saudiyya take yi da k'asar Yamen. A gaggauce ya kalle ni ya tausasa ya ce "Sannu Billy, alamu sun nuna kin gaji".
A hankali na ce "Ga yunwa ga ciwon kai".
Ya mik'e ya ce "Bari na kawo miki cake da tea ki rage karfin yunwar, sai ki sha paracetamol Ki dan huta kafin la'asar."
Bai jira absata ba ya nufin kicin ya hado mini shayi mai kauri a katon mug din da nake sha, ya zubo mini cakes guda hudu a cikin bowl. Bai zauna ba sai da ya dauko maganin hade da pure water mai rangwamen sanyi.
A tausashe na ce masa "Thank you Daddy".
Bai amsa ba ya cigaba da kallonsa ni kuwa na tsani kallon wannan tashin hankalin, domin alamun ne na musulunci ya fad'a cikin garari da fitinar gaske. K'asa mai tsarki da duniyar musulmai suke kallonta a uwa wai itace ke yak'ar kasar musulunci ta Yemen. K'asar da Annabi ya yi nuni da sashen yankin da take ya ce imani na can, ya sake ce wa imani na Yemen!
Yemen din da kaso casa'in da tara na alummar musulmai ne. Har menene abu mai dadi wajen kallon wannan masifa da ta fadowa alummar musulmai bakidaya?
Na fara cin abinci na kammala na yi gyatsa, zufa ta yanko mini. Na balli maganin na sha. A wajen na kishiginda, k'arar bude kofar da ya yi ya fita zuwa masallaci ya saka na farka, na sani kuma bai tashe ni kaitsaye ba ya bari na dan huta ko kan zai sauka. Na zauna ina jin babu ciwon kan dama nasan yunwa tafi yawa don yau ban karya ba , ruwan Lipton kawai na sha a gurguje saboda yara zasu yi latti.
Sai da na yi wanka na saka guda cikin material din Malaysianfabrics don bana gajiya da sanyasu saboda da taushi da rashin nauyinsu, ga kyaun da yake mai daukar idon mai ganinsa07020695644 order ur Malaysiaanfabrics.
Sannan na tada sallah.
Ina idarwa na fada kicin na hau aikin abinci. Ba ni da mai aiki mace. Amma akwai almajirin da muka yi sabo duk safiya da yammaci zai zo ya share mini gida ya yi moping, ya gyara kicin, ya mini wankin kayan yara ya yi guga. Amma bana ba shi wanke wanke, wannan ni nake yin abina, na yi girki na gyara dakunan barcinmu da bandaki. Amrah kuwa tuni na koya mata wanke bandakinsu da panties dinta.
Har wajen biyar bai shigo ba, ga shi bana son na sake fita.
Ina ta wasiwasin dauko yara, ya shigo ina kwashe abincin daga tukunya zuwa filas.
Ya biyo ni kicin din ya tsaya daga bakin kofar ya ce "Sannu har an sheka mana girki haka?"
Na ce "Yanzu babu ciwon kan, shiyasa na yi girki kada su dawo babu abin da zasu ci".
Hakane to sannu da kokari".
Na tausasa harshe na ce "A gajiye nake ka daukosu mana"
Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Daure dai ki kwasosu ball zan kalla kin kuma sani biyar da rabi ake farawa".
Na girgiza kai na ce "Kallon k'wallone tafi hidimar ya'yanka? Me yasa kake son barina da dukkan nauyin da kaine wajibi a kansu, yanzu ace bana jin dadi ba zaka kwaso ya'yanka ba, saboda kallon kwallo?"
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya girgiza kai ya ce "Daga nan har wata guda komai za ki yi nasan ba ra'ayinki ba ne, tunda ta zo gidan nan ai dole komai na ga ni. Babbar godiyar da nake yiwa Ubangiji a lokacin da nake da dama ba abin da ban yi miki ba, kowa sha'awar ki yake yi. Idan har jarabawar da na shiga ne sanadin da zaisa ki raina ni, ko ki dinga neman yi mini iyaka a zamantakewarmu kawai ki bude baki ki yi magana" .
Nan da nan na ce "Dady me ya kawo wannnan maganar?"
Bakina har harde wa yake yi.
Ya zuba mini ido ya ce "Ke menene sanadin fadin na bar miki nauyinkan da nine a hakku na yi su? Kin sani, na sani daga bakin uwar iya wadannan kalaman suka fito ba a bakinki ba. "
A sanyaye na ce "Mu bar maganar haka nan, ban cika son idan muna magana ka dinga shigo da wata ko wani ba".
Ya juya yana fadin "Duk yadda nake dauke wa yarinyar nan kai sai ta kai ni bango na shata mata layi da shigo mini gida!
Haka na shirya na fita daukosu.
Ina mamakin daga ya yi jinya na karbe shi kai su da dauko su shike nan sai ya zame mini wajibi ni zan kai su na daukosu alhalin shi ba abin da yake yi? Kasan zuciyata na fara ganin k'amshin gaskiya cikin hasashen Abida. Amma da yake sonsa nake tsakani da Allah sai ban wani zurfafa ba na watsarke da tunanin na cigaba da hidimomin da nasaba.
Kwana biyu yana mini yar shariya kafin ya warware domin bai iya dogon fishi ba, tunda ni din zan yi ta takalarsa da magana har ya huce.
Akan dole na tattara komai na ajiye na cigaba da harkokina tare da adduar Allah ya cigaba da sakawa nemana albarka, kuma Alhamdulillah komai na taba sai Ubangiji ya saka albarka ya zama kudi sosai.
Lokacin biyan kudin hayar gida ya zo, na biya na shekara guda sabanin shi da yake biyan na shekaru biyu.
Abin farinciki da W.H.O. da nake aiki da ita ta sake kara mini wa'adin aikin da zan mata daga shekaru biyu zuwa shekaru uku.
Dan haka a cikin wadata muke sosai. Ga kasuwancina da yake ta habaka don yanzu ma'aikata ne da ni masu kama mini dan sosia ake yin snacks. Don ban cika ma yin dari ba sai dai ka ji ana fadin kowanne a yi guda dari biyar ko dubu.
Sai da Abida ta yi watanni goma sha hudu sannan ciki ya samu. Bana mantawa da murna ta kira ta ce mini "Bilki ki fara shirin tarban d'a ko diyarki nan da watanni takwas masu zuwa".
Da karadi na ce "Kai madallah da Abidan Baba! Allah ya raya ya sauke ki lafiya".
Ta amsa da "amin !
Har mun yi sallama ta ce "Kinsan Allah kada ki fadawa kowa nan duniya ke kadai kika sani har Yaya Sulaiman ma bai sani ba."
Dadi ya sake kama ni ina jin lallai ina da matukar muhimmanci a zuciyar Abida tamkar yadda take a tawa zuciyar.
Duk yadda nake cikin zumudi haka na kama bakina na tsuke ban fadawa kowa ba, tunda tafi so a ganta da shi. Na dinga yi mata addu'ar samun lafiya. Kullum sai na kira na gaishe ta, ta yi ta mini tsiyar ta gane nafi son unborn a kanta domin kafin hakan ai sai na kwana biyu ban neme ta ba, yanzu kuwa na fitine ta da yawa.
Dariya kawai nake yi ban kuma fasa gaishe ta kullum safiya ba. Idan abin ya ciyo ni ma har da yammaci sai na sake kira, da dukkan zuciyata nake jin son abin da Abida zata haifa mini.
Da yake a Katsina suke ba'a gane me take ciki da wuri ba, sai da cikin ya yi kwari, aka dinga murna da fatan alheri, domin itace kadai aka yi aurenta ta zarta shekara bata haihu ba.
Wani zazzabi da ta yi na je dubo ta na yini guda, na dawo da zullimin ko Abida zata iya cika alkawarin da ta yi mini a lokacin da take cikin shekarun kuruciya? Ga shi bata samu aure da haihuwar da wuri ba, har sai da aka fara jajensu. Ko Yaya Sulaiman zai amince a yadda ya sake ninka rawar kai a kanta?
Ina tafe ina wannan tunanin. Kasan zuciyata kuma sai tunani nake ban taba ganin Sahal a yanayin da nake ganin Yaya Sulaiman idan Abida na gabansa ba.
Na yi karamin tsaki tare da kore tunanin da ke son sababa mini Shubuha don kuwa nasan yana sona ai. Kawai he is not romantic ne yadda nake so da ace he is da na fi kowa dace. Duk da a yanzu ma kowa kallon daula yake yi mini a cikin ahalinmu. Abida ce kawai tasan hakinanin halin da nake ciki. Duk da taki bari na fada mata hakinanin matsalar da ta fi damuna a gidan aurena.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yau da gobe har watan haihuwarta ya tsaya cikin ikon Allah ta haifo yarinyarta lafiyayya mai kama da Yaya Sulaiman sak.
Cikin sa'a cikin hutun yara aka yi haihuwar kuma abin farinciki ranar birthday din Yaya Farouk wato ranar ya cika shekaru shida.
Kwana biyu da haihuwar muka isa, murna kan murna yake yi ya samu birthday mate kuma itace matarsa, ya ganta fara mai gashi. Kaitsaye yarinyar tafi kama da ni akan Abidan.
Daga ita, har jaririya lafiyarsu kalau Yaya Sulaiman sai kanzagi shiga goma fita goma sai ya leko ya mata sannu.
Na dauki yarinyar na tsura mata ido sonta na keta ni tamkar yadda na dinga jin son Amrah a ranar da na haife ta. Na dago da idanuwana da suka cika da kwalla na ce "Sannu Abida Allah ya baki lafiya ya raya mana ita akan sunna".
Ta murmusa ta ce "Ameen.
Can na numfasa na ce "Shin kyautar tana nan ko Abida? Wannan tawa ce ko?"
Ta murmusa ta ce"Annabi ya ce munafikine yake saba alkawari, Duk yadda na sha wahalar nakuda ba zai saka na fasa baki abin da tuntuni naki ba ne. Cikin dalilan da yasa na amince da auren Yaya Sulaiman har da ba ki kyautar da ba za'a kwace miki ko nuna miki iyaka ba. Don idan ba shi ba, ba lallai burina ya cika na ba ki kyautar halak malak ba."
Na matsa na rungume ta na kasa ce wa komai domin wani irin rauni ya shige ni, tare da wata irin soyayyar da ba abin da zai shafe ta ila yaumil kiyama.
*
Ranar suna Yaya Sulaiman ya sake shayar da mu mamaki da ya ce sunan yarinyar Bilkisu alhalin da ya ce sunanta Aisha. Sosai Abida ta yi murna tamkar sunan momi aka ce an saka.
Basma Maska aminiyarmu da itama cikin Katsina take aure, uwar Abdul, Ayra da Iman.
Da ita aka yi shagalin sunan Bilkisu. Yaya Salaha da Yaya Hamida sai fadi suke suna manya ba'a yi musu takwara ba sai ni?
Ga takwarata ta gidan Yaya Asad ta cika shekaru goma a jiya.
Yaya Munira kuwa ta what'sapp aka yi vedio called da ita ta dinga fadin yadda ta yi missing dinmu gabadaya, ta kuma ce ta gode da son kan da suka yi, domin kamata ya yi a sakawa jaririya Munira ba Bilki ba.".
A wannan lokacin nima dauke nake da karamin ciki na watanni uku. Gabadaya cikin ya zo mini a bazata ban so ba, mussaman da nan ba da jimawa zan karbi y'ata da Abida ta haifa mini.
Amma haka na hakura na yi godiya ga Ubangiji na fadawa Abban Amrah ya yi murna. Na dinga mamakin ikon Allah. Don na shaida samuwar cikin haihuwa ikon Allah ne kawai, ban da haka yadda Sahal yake Mr 2minutes sannan sai an dauki lokaci kafin ya bukace ni, dole na yi mamakin yadda ciki ya shiga, dariya ta kwace mini a dalilin na tuna abubuwa masu yawa a kansa sam ya gaza a wannan fannin na kasa fitowa na fada masa har lokacin. Kunya da tsoron fassarar da zai mini suka mini dabaibayi. Duk yadda nake cire kudi na siya masa magungunan k'ara k'arfi masu tsada da supplement bai sa ya gane manufata ba, bai kuma taba mayar da hankali wajen shan ba, da ya sha sau daya tak to kuwa sauran sum zama asara shiyasa na hakura na daina siya suna zame mini na takaici tunda da hannuna zan zubasu a shara komin tsadarsu kuwa.
Kwanci tashi har su Abida suka yi arba'in.
Ina kwance a dakina