wheelchair, sannan wannan zaman har da Ya Asad aka zo, kamar ma wancan karon wannan ma lokacin kallon kallon kawai aka yi a tsakaninmu da ahalin Baba Babba kowa ya kauda kai, mu ma daga bangaren mu har da Hamida da Anisa, muka zauna a rukunin mu suma suka zauna a nasu rukunin Baba Babba duk ya rame ya lalace daga gani ya sha jinya yana zaune kan weelchair, gwanin ban tausayi, ni da man a raina ban taba jin za mu yi nasara ba har addua nake yi na ka da ya zama kotu ta bamu nasara ko yaya ne Baba Babba ya samu adalci.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Haka kuma ya faru bayan sake tattara hujojji da shaidu kotu ta tabbatar da Ladi Farm ta Baba Babba ce, fuskokinsu Ya Usman ya cika da farinciki .
Mami da Ansari kuwa kamar za su yi bindiga saboda bacin rai, jin an samu tabbacin gona ta Baba Babba ce a kotun Ya Muneera ta miƙe cikin sanyin muryanta ta ce" Alhamdulillah Allah mun gode! Cikin adalci kotu ta tabbatar ba'a zalunci kowa ba. "
Bisa adalci da zumunci had'i da biyayyar da marigayi Babanmu ya yiwa mahaifinmu mun sadaukar da Ladi farm da dukkan abin da yake cikinta ga iyalin marigayi Babanmu Alhaji Isa Funtua gonar da ake takaddama akanta halak malak. Mahaifinmu da ake k'ararsa ko mu ya'yansa bamu da alak'a da gonar Ladi farm ila yaumil qiyama."
Tana gama fadin haka sai da ta share ƙwalla ta kwashi takardun gabanta ta doshi mahafinsu.
Yayin da Abida da Yaya Usman suka yi kanta a harzuk'e, ganin duka zasu rufar mata da shi ya sanya Ya Asad ya shiga tsakani yana mai daka musu tsawa.
"Mene ne haka? A nan ne za ku yi mana haka? Kuma haka za ku yi mana?".
Ya fada idabuwansa sun yi ja sosai".
Ya Usman ya buɗe baki zai sake magana Ya Asad ya sake buga masa tsawa kafin ya ce" Usman ka yi shuru, mu ba dukiya ba ce a gabanmu gaskiya ne Munnera ta faɗa. Mutuwar Baba ƙarami da lafiyar Baba Babba ta fiye mana duniya da abin da ke cikinta."
Kalamansa suka sake sanyaya mana jiki, suma daga haka ba su sake ja in ja suka shisshige motoci suka bar haraban kotun aka bar mu cikin sanyin jiki, Mami ta yi sukuri ba magana amma ni na fahimci jikinta ya yi sanyi sosai.
"Mami kin ga ni? Mune ya kamata mu nunawa duniya cewa Baba ƙarami ya fiye mana duniya da abin da ke cikinta amma mun kasa. Sai ga shi su sun nuna mana karamci da dattako, sun bar mana gonar tunda mun nuna duniya ce a gabanmu ba mutuwar mahaifinmu ba."
Mami ta yi shuru kanta na kasa ta kasa mgana Ansari ma duk bakinsa ya kasa cewa komai.
Yaya Hamidaa ma cikin sanyin jiki ta ce" Wallahi na ji kunya. Na ji nadama ta shige ni."
Anisa ma ta amsa da cewa" Wallahi nima, sai na ji dama ba mu kawo ƙara, wannan fa shine sun watsa mana aniyar mu."
Mami ta saki gauron numfashi amma ta kasa mgana, wani abu ya yanke a kirjinta kamar nadama ne ya fara shiganta amma tabbas jikinta ya yi sanyi, kuma fuskarta ya bayyana haka, ni dai daga nan muka rabu da su suka kama hanyar Funtua sai da suka isa na k'ira Anisa take faɗa mini su Baba Babba gidan suka dawo amma sun ga ana ta haɗa kaya wataƙila ma har gidan gabaɗaya sun bar mana.
Ina sharan ƙwalla na ce" Sun yi daidai. Sun nuna mana idan kudi ne a gabanmu ga shi nan sun bar mana gabaɗaya."
Mami ma sun ce tunda suka koma jikinta yake sanyaye bata sake tayar da maganar ba. A raina na ce nadama marar amfani.
Baba Babba.
Murya a dakushe ya ce "Sannu Munira. Hakika Na gamsu da wannan shari'ar na kuma amince da hukuncinki da dukkan zuciyata na bar musu.
Allah ya rufa miki asiri Duniya da lahira.
Ina Usman, ina Abida?"
Ya fad'a muryarsa na rawa.
Suka amsa gamu Baba.
Ya ce "ku bude kunnuwanku da kyau, ku saurare ni, na amince da hukuncin Munira. Duk wanda ya tayar da maganar nan a cikinku lallai ni ya shirya yak'i da shi, kuma Wallahi idan na mutu wani cikinku ya tayar da maganar to lallai ban yafe ba".
Wannan kalamin shi ya sanyaya musu jiki suka hakura kann dole.
"Na fad'a miki ba za ki bisu Abuja ba Abida! Sulaiman ya fada cikin jarumta da son motsa mata kwanji.
Dariya marar nishadi ta yi masa tare da ce wa "Mutuwa kadai zata hana ni bin ahalina.
Ai tunda kuka kasa fadawa gyatumarku gaskiya ba sauran aminci ko Zama a tsakaninmu. Dama ni saboda kyautar da zan yiwa Bilki na aure ka, ba sonka nake yi ba. Yanzu kuma na gane had'a zuria ma da ku kuskure ne babba."
Ga mamakinsa sai ba hassala ainun ba domin zai Dade Bai ya abin da tayar masa da hankali ya Kona masa rai irin wakiar da take faruwa a gidansu.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya rasa mai zaice mata.
Ta sake ce wa "Ban yi zaton rashin kirkin mami ya kai kurewa ba. Tunda na gane nan duniya ba wanda ya isa da ita ai kuwa dole a guji hada zuria da ita. Yanzu haka ina da ciki na tabbatar a Germany na kwaso cikin nan wanda kaddara ce ta saka aka yi tarayyar. Sai dai ba zan haife ba, da ikon Allah sai na zubar da shi ya bi rariya"..
Ashe a lokacin ma bakinta dauke yake da maganin da ake sanyawa k'asan harshe wanda take tayar da nakuda bakatatan.
Karfin hali ya sanya take magana amma a cikin azabar ciwon mara take.
Ba zato kuwa ta fadi k'asa jini ya b'alle take ta suma.
Haka ya kwashe ta zuciyarsa ta bushe ga ni yake ma tamkar ya haukace tsananin bacin rai na dibansa.
Munira da Usman sun ga sadda ya fito da ita tamkar gawa ya saka a mota.
Dan haka suka fito sai dai tuni ya ja mota zuwa asibiti.
Haka aka bata taimakon gaggawa ta farafado aka daura mata ruwa da allurai na rage ciwo da zugi.
Kwanata biyu aka sallame ta.
Ta kuwa tubure sai ta bisu Abuja.
Shi Baba Babba tun jiya Yaya Faruk ya kai shi tunda zai ga likita washegari.
Munira kuwa zata bi momi ne daga nan ta shiga jirgi ta koma inda ta fito.
Kan dole suka tafi da ita. Sulaiman ya zuba mata ido don gabad'aya a rikice yake, hankalinsa ya rub'anya tashi akan kalamanta mussaman maganganun da ta fada akan mami sun masa tsauri na gaske a zuciyarsa.
✍️
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tafiyar Abida ta sanya Ya Sulaiman cikin ruɗani mai yawa, ya raunana duk da ya saka jarumtar dannewa da gudunmawa dakakkiyar zuciyarsa,amma abin da ke ɓoye a cikin zuciyarsa ya bayyana har a saman fuskarsa zuwa gangar jikinsa, a tsaye yake amma kana kallonsa za ka fahimci maza sun raunana sannan zuciya na ciwo.
A cikin zuciyarsa ya ƙullaci Ya Asad a matsayinsa na babba me yasa bai dakatar da Abida ba? Aure ne a kanta amma ta kama hanya ta bisu ba da izininsa ba, bayan ta gama faɗa masa munanan kalamai akan mahaifiyarsa, sannan har da Baba Babba ko da Abida ta bisu a lokacin da baya cikin sukunin da zai dakatar da ita, to a yanzu fa da ya warware yake samun saukin jiki da na zuciya? A ganinsa kamata ya yi su zaunar da ita, su sake jadadda mata daraja da ƙima irin ta aure, sannan idan har zasu yi masa adalci ai ba shi ya yi laifin ba, bai kuma kamata laifin Mami ya shafe shi ba. Mami uwa ce a gare shi ko akan bola take rayuwa ba zai guje ta ba, kuma tilas ne ya yi mata biyayyaa. Amma tsabar tsaurin ido har ta iya kallon idanuwansa ta kira sunan Mami ta jingina mata munan kalamai. Sannan mafi baƙin cikin abin da Abida ta yi masa shi ne ta yi sanadiyar lalacewar gudan jininsa, ashe bata son shi? Duk da yana ganin soyayyarsa a cikin idanuwanta. Amma tunda ta iya cewa had'a zuria da uwarsa abin kaico ne! Lallai dole ya nuna mata kuskurenta don bai yi lalacewar da zata furta masa wannnan k'azamar kalmar akan idanuwansa ba, sannan ta fi a iska. Cire masa ciki da ta yi ya sake harzuk'a shi tare da alwashin ko sonta ne ajalinsa ta yi kad'an ya neme ta da sunan sulhu. Haka nan ba zai sake ta ba, amma idan ta nemi ya sake ta da kanta, to la shakka take yanke zai sake ta din. Yanzu ma idan zata shekara dubu ba zai bi bayanta da sunan biko ba. Kuma ko sun dawo da ita matukar ba ta yi tuba kan kalamanta ba to kuwa babu ita babu sake jin dadinsa matuƙa da aniya ta ɓata masa rai kuma ya ƙullase su kwarai da gaske. A ransa yake ta sakesaƙe, me ya rage masa a wannan duniyar yanzu? Babu Baba ƙarami, babu Baba Babba da iyalansa, sannan babu mata babu ƴaƴa, ƙannensa kuma matan ne kawai. Ansari ya juya masa baya. Mami bata sauraransa to shi me ya rage masa a wannan duniyar ne? Ya so ana gama shari'ar nan ya zubawa Mami ido ta yi komai yadda take so sai kuma ya kasa ganin ta yi sanyi sosai kamar ba Mami ba, maimakon abin da take fata na mallakar ladi farm ta yi farinciki amma ba ta yi ba sai ma yake ganin ta cikin rashin sukuni kamar dana sani da nadama suka yi mata k'awanya amma ta kasa furtawa kowa. Shi kansa Ansari duk ya yi sanyi ya daina cika baki, tunda ga dukiyar ga gidan gabaɗaya an bar musu amma kuma sun kasa farinciki. Saddiqa da yaya Hamida dama tun ranar zaman kotu sun furta nadamarsu. Mami da Ansari ne ba su yi magana ba amma ko basu furta komai ba yanayinsu kawai ya isa ya bayyana suna cikin damuwa da nadama.
Ganin komai ya 'kare, dukiyar da Mami take haƙilo ta dawo tasu, to me za a jira kawai sai ya samu Mami ya ce a raba gado a ba wa kowa nasa kason.
Mami ta shiga tashin hankali cikin damuwa ta ce" Saurin me kake yi haka Sulaiman? Ka bari ko zuwa nan gaba idan mun sake samun natsuwa."
Kai tsaye ya ce" Wata natsuwa kuma Mami? Ai gidan nan tuni mun yi sallama da natsuwar zuciya har da ta gangar jiki. Gwara a raba a sallami kowa tunda dukiyar muke so kuma ga tanan an bar mana."
Mami ta kasa magana da Ansari ya zo ta faɗa masa shima dai bai ce komai ba, illa iyaka ayi abin da Ya Sulaiman yake so a raba a bawa kowa nasa kason sha'anin gado da komai ma ya ƙare.
Mami ba ta da cewa dole ta amince aka haɗa dukiyar waje ɗaya Ya Sulaiman ya gayyato malamai aka zauna aka raba gado daidai yadda Addini ya hukunta ya tanadar.
Wurin da Ya Sulaiman yake zaune ya fito a nasa kason, sannan bangaren Mami ya fito ana Ansari. Mu kuma matan sai muka yi mubaya'a zasu fitar da mu a wasu gidajen na wasu garuruwa, ni na samu gida mai kyau a garin Katsina. Saddiqa da Anisa anan garin Funtua suka samu na su gidajen.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: In da ace Baban Amra yasan yadda na ke kwana na tashi da ƙunar zuciya kan rashin Abida da bai ce haka ba amma sanin ba zai gane komai ba yasa ban tsaya yi masa bayani ba ina cikin damuwa, damuwar da ta ke cin zuciyata sannan yana kassara gangar jikina amma shi duk bai lura da haka.
Kwanaki kadan sai ga sako wai kaninsa da muke zaune a bangarnasa zai fara gyaran wajen don aurensa watanni uku suka rage, a kuma wajen zai zauna. Hankalina ya yi tashin gauron zabi tare da tuna lokutan baya muna Kano da na dinga yiwa Sahal nacin ya sayi gida ko na rainawa ne ya zuba haya. Ga irin ranar da nake guje masa ta zo. Yanzu ina muka dosa ke nan? Don ko giyar wake muke sha ba zamu bawa Hajiya notis din tashi tamkar yadda k'aninsa ya bamu ba.
Na sake kutsawa cikin nazari tare da tunano Sahal bai ajiye komai ba ban da k'aton fegen da ya siya shekarun baya. Tabbas wajen ya zama unguwa mai daraja a yanzu. Tare suka siya da yayansa da shine babba a dakinsu. Dan haka filayen biyu a jere suke manya na sosai.
Shi kansa hankalinsa ya tashi, tunaninsa ya kulle. Ya shiga damuwa kullum da zullimin inda zamu koma yake kwana da tashi. Da na ga ya shiga rudani ainun sai kawai na yi masa tayin mu koma gidana da ya fito a gadona a maimakon mu je mu kama haya. A farkon kamar ba zai amince ba, amma da ya yi nazarin ba shi da mafitar da wuce hakan sai ya amince mini. Dad'i ya kama ni, dama a matuk'ar takure nake da zamana a cikin gidansu mussaman idan sister's dinsu sun zo. Ba k'aramin takaici suke guma mini ba, mussaman Yaya Tourai bansan me na tsare mata ba.
Da labarin komawarmu gidana ya iske su kuwa ba abin da basu ce ba. Ai yanzu zan sake d'agawa da izza. Na cinye masa arziki, nawa yana ta habaka. Amma da yake na gama da shi ya kasa fahimtar ni din ba alheri ba ce, don a lokacin da yake cikin arzikinsa ai a jere na dauko haihuwa saboda na tara magada. Amma tunda na tsiyata shi na kulle bakin mahaifa na k'i haihuwa. Dan kuma na nuna musu isa na dauko yar riko babu neman amincewar miji bare ta uwarsa. A sa'ilin da na ji suna furta wadannan kalaman murmushi kawai na yi, domin tashin hankalin da ya faru a gidanmu ai ya wuce ƙaramin abu ya zauna yana damuna.
Amma da Baban Amrah ya dawo na sanar da shi, na ce masa Idan bai gamsu da shawarar komawarmu gidana ba, to ya kama mana haya babu damuwa. Jin na ce haka ya yi maza ya ce shi ba shi da matsala yasan halina duk abin da na mallaka ai kamar nasa ne, kar na damu da masu magana. Yasan ni rufin asirinsa ce. Ashe shima yasan ƴanuwansa suna ta yamididi akan batun. Hajiya ma da na shiga gaishe ta sai da ta yi mini maganar komawarmu gidana na ce mata ina son mu koma ne tun da ko bamu zauna ba y'an haya zamu saka, sannan muma hayar zamu kama, to gwara mu koma ɗin. Ta ce "hakan na da kyau, ganin Baban Amra ya amince shi da Hajiya sai na fara shirin tarewa, bayan mun je mun duba gida lafiyayye ne, sai ɗan gyaran da ba za a rasa ba Baban Amra na barwa bangaren gyare-gyaren gidan, na kira Ya Sulaiman na faɗa masa ya ce hakan da na yi daidai ne. Mami ma da na kirata ba ta ce komai ba, yanzu ba ta cika doguwar magana ba, ni tsorona kar a ce haƙƙin Baba Babba ne ke bibiyar Mami, saboda yanayin da take ciki ya yi tsawo. Ya kamata a ce ta saki jikinta zuwa yanzu, amma kuma lamarin nata sai ƙara lalacewa yake yi, ba wanda yasan meke damunta amma mu munsan ba zai wuce nadama da girman haƙki ba.
Shiryen -shiryen tarewarmu na mayar da hankali, duka duka lokacin wata ɗaya ne da rabon gadonmu, har mun fara parking din kaya tun da gidan an gama gyara komai ya yi fes kamar sabo, wata ranar jumma'a da asuba wayar Yaya Sulaiman ta tashe ni, wayar da ta tafi da numfashina na wani lokaci, wai faɗa mini yake yi na taho gida mun rasa Mami!
Mami fa, mamin da ko jiya da daddare na kira ta mun gaisa har ina jin daɗin ta saki jiki mun yi hira har na bawa yara suma suka gaisa da ita, ita ce wai Ya Sulaiman yake faɗa mini ta rasu? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Na faɗi kasa ina kuka, ina birgima ina faɗin na shiga uku na lalace! Baban Amrah ya kasa iyawa da ni sai da ya je ya kira Hajiya ita ta zo ta zauna da ni tana lallashina.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Bilki bar kuka, mamaci ba ya buƙatar wannan kukan na ki, addu'arki kawai take bukata a yanzu, ki yi hakuri, ta shi, bari na shirya, kai Sahalu shirya yaran yanzu mu kama hanya."
Kuka kawai nake ina faɗin "Na rasa Baba ƙarami, na rasa Mami, na rasa Abida na rasa Baba Babba na rasa kowa ina zan saka raina."
Lallashina kawai take yi tana ce mini ina da Allah na yi shuru kar na yi saɓo. Har muka kai Funtua kuka na ke yi ban sake tsinkewa da lamarin duniya ba tabbas ba sai da na ga gawar Mami lulluɓe cikin likkafani, a lokacin na sake tsinkewa da sha'anin rayuwar gabad'aya. Tabbas duniya zancen banza ce, yau ga dai Mami ta tafi inda Baba ƙarami ya tafi bayan duk faɗin tashin da ta yi akan dukiya yau itama ta mutu ta barsu ko sisi bata ci a ciki ba. Wallahi duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya yi kaico a rayuwarsa, mutuwar Mami izina ce sannan wa'azi ne ga mai hankali. Mutuwar kwatsam, da daddare Ya Sulaiman ya ce ya shigo bangarenta suka yi hira ta ce mai za ta sha magani kai na sara mata suka yi sallama ta shiga ciki, da asuba ne ya kasa natsuwa kafin ma ya kai ga zuwa masallaci ya shiga bangarenta tuni mai ikon rai ya yi ikon shi sai dai ya tarar da gawa har ta fara sandarewa alamun ta jima da rasuwa wataƙila tun farkon dare. Allahu Akbar rai baƙon