duniya sai ga ƴanuwan Mami da ta rayu akan cewa ba sonta suke ba, take adawa da su, sune suke zagayemu da ita gabaɗaya, muna kukan rasa uwa, su kuma suna kukan rasa y'aruwa. Mutuwar Mami ta kassara sauran kuzarina ta kuma tafi da kaso mafi girma daga cikin yaƙinin rayuwata.
Kafin a kai gawar Mami kushewa su Baba Babba suka iso, bawan Allah nan mai yakana ne da yiwa zumunci kara, kaf ɗin su suka zo har da Abida da na ga ta yi wani kiba fuskarta ta kumbura ta zurma wani babban hijabi da na kasa gane wani yanayi take ciki. Ya Asad ne kawai bai zo ba, na ji Baba Babba na faɗawa Kawu Bala ce wa ba ya k'asar ne.
Baba Babba da Momi da su Ya Faruƙu har gaban gawar Mami suka ɗuka suka yi mata aduua.
Baba Babba ya kallemu kafin ya ce" Ku daina kuka, ku yi mata addu'a domin a wannan lokacin ita ta fi buƙata, Allah ya jiƙanki Habiba Allah yasa kin huta. Allah ya shaida na yafe miki, babu kullinki a zuciyata. Allah yasa ki shiga a sa'a."
Ya kammala fadin hakan hawaye na kawo masa, ya warke kamar ba shi ba, daga ganinsa yana samun kulawa sosai, yana hawaye, muna kuka sai na ji kamar na tashi na je na faɗi kan kafafunsa na fashe da kuka amma ba hali. Abida ta mini gaisuwa amma a takaice duk da na ga mutuwar ta buge ta ainun. Momi ta zauna tare da mu da kuma yanuwan Mami anan falon bayan an tafi kaita. Abida ma tana tare da mu sai wajen azahar sannan ta tafi bangaren momi ta kwanta kana ganinta kasan bata ma da cikakkiyar lafiya wataƙila ma akan dole ta zo. Duk da ina cikin zafin mutuwa sai nake ganin kamata ya yi ta bude bangarenta ta zauna ko dan hankalin mijinta ya samu daidaito. Gabad'ayanmu a firgice muke sosai da mutuwar nan ta mami. Amma Ansari ne kan gaba wajen firgici gwanin ban tausayi tunda Mami ta rasu yake zabura yana neman hanyar gudu kamar ya zare, mutuwar ta gigita masa tunani fiye da tunanin kowa, to ai dole. Ansarin Mamine. Shi ne abokin sirrinta duk wani abin da ta aikata da sahalewarsa, dole ya gigice gabaɗaya ya zare kamar wanda haukan dare ɗaya ya same shi. Aan dawo daga kai Mami an zauna ana karɓan gaisuwa. Baban Amra da Hajiya kwanan su uku suka juya da yara. Baba Babba da iyalansa kwana daya suka yi suka koma gabaɗayansu. Da za su tafi sun shigo har bangaren Mami sun yi mana sallama amma ban da Abida, ban ganta ba sai da na raka su haraba na ganta a cikin mota, ya Usman sabe da Farha ya leka ta bangaren da take zaune. Ina jin yana ce mata "Ko kina son tafiya da yarinyarki?"
Gabana ya buga da k'arfin gaske don kuwa raba ni da farha a lokacin ba karamin gigicewa zan sake yi ba. Nan da nan na ga ya Sulaiman ya zuba musu ido cikin hassala irin wacce na jima ban ga ya yi ba. Kafin mu yi magana, muka ji Abida ta ce "A a Ai ba yarinyata ba ce ta Bilki ce, munafikine mai yin alk'awari ya sab'a. Mik'a mata d'iyarta".
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A sanyaye ya dire ta, yarinya kuwa ta nufo ni. Na rike mata hannu ina ta hamdala don da ace sun yi gangancin ce wa zasu tafi da ita tabbas Yaya Sulaiman da Yaya Usman zasu yi kare biri jini sai dai idan Baba ne ya tsawatar. Don Yaya Sulaiman ya fuskata da su sosai. Haka aka shiga sallama da fatan Allah ya sauke su lafiya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya Sulaiman da Baba Babba suka yi maganar da ban ji me suka ce ba, sai su Ya Faruku da suka yi musabaha. Har suka tafi magana ta fatar baki ba ta haɗa shi da Abida ba, tun ranar da ta zo ta ce masa ya hakuri a cikin bainar nasi, shike nan ta'aziyar da ta yi masa. A tunaninsa ma a bangarensu zata sauka har su samu sulhu ashe ita da gaske take bata sonsa, ta kuma shirya rabuwarsu har zuciyarta. Duk yadda ya ƙullace ta, amma sai ya ji ya damu da yanayin da ya ganta na rashin lafiya da rashin kuzari. Amma ya riga ya kudire ba zai neme ta ba tunda dai bai mata laifi ba, bai kore ta ba. Sannan rashin ware shi ta yi masa ta'aziyar mahaifiyarmu cikin mutunci da tausayawa, ya sake tsananta fishinsa a kanta tare da lasar takobi lallai rigima yanzu aka fara tsakaninmu da ahalin Baba Babba tunda akan idon Baba da na Yaya Asad Abida take yi masa wannan rainin da kuma wulakanta masa aure amma basu taka mata burki ba, ya fahimci inda matsalar take akwai sauran jidali kuwa. Idan har zuba ido suka yi suna dakon ya je bikonta to kuwa ila yaumil kiyama ba zasu gan shi a gabansu akan batun Abida ba.
Daga ni sai Ya Sulaiman muka yiwa su Baba Babba rakiya. Ya Hamida har tana zagina wai ba ni da zuciya uwarmu ce fa ta rasu amma sun zo sun kwana ɗaya tal Abida ma saboda wulakanci tafi ƙarfin ta yiwa mutane magana. Ni dai ban ce komai ba ganin rasuwar Mami ta saka Ya Hamida ta koma masifafiya sannan ta gasgata yamididin da ake yi a gari cewar Baba Babba ne ya yiwa Mami Yasin shiyasa ta sururuce sannan dare d'aya ta yi bindiga ta mutu. Gabadaya Yaya Hamida ta tsanesu da gaske. Ni dai bana um bare um um. To ni me zai dame ni ballatana na kulata, bayan na rasa komai, duka duka kwanan Mami hud'u ne da rasuwa W.H.O ta turo mini saƙon sun sallame ni daga aiki sakamakon contract ɗina da su ya ƙare, dama shekaru uku ne, na yi biyu a Kano na zo Katsina na cike d'ayar.
Shi yasa har muka k'are zaman makoki, ban yarda na biye mata ba. Har ce wa ta yi ita da Asad har gaban abada tunda bai zo mana ta'aziyar uwarmu ba. Duk da Baba Babba ya hadamu da Shi a waya ya mana ta'aziyar smma hakan bai yi mata ba.
Ansari ne mai baki a baya amma yanzu ya yi sanyi tun bayan rasuwar Mami mutumin da sai da aka haɗa masa da rokon Ubangiji tare da ruwan rubutu. Tun lokacin Ya Hamida ta ɗauki ragamar nuna tsana ga ahalin Baba Babba da ni, kuma haushinta yafi yawa a kaina tunda ta ce ni ce ban daina ƙulafuncinsu ba. Ni dai ban biye mata ba, kwana goma na yi a Funtua na tattara na koma Katsina. Amma gangar jiki da zuciya sun raunana gani nan ne dai kamar wata mara lafiya sai da na koma gida ne Baban Amra ya san contract din aikina da W.H.O ya k'are yanzu sai dai na koma zaman gida. A wannan gab'ar Baban Amra ya tausaya mini ya kuma tsaya tsayin daka shi da Hajiya wajen kula da ni da lallashi, shi ya sa ko wani takaicin ya tusa mini idan na tuna da wannan karamcin nasa, sai na ji na yafe masa. Shi da Hajiya sun yi ƙoƙari a kaina ba don su ba da tuni depression ya kama ni.
Sannan Ya Sulaiman ma ya yi ƙokari a kaina shi ya sa har yau ban daina kuka idan na tuna da shi ba, da a ce yau yana nan da wataƙila kewa ba ta yi mini k'awanya da yawa ba. Saboda yanayin da na ke ciki ya sa maganar komawarmu gidan nan ya sha ruwa saboda ba na cikin natsuwata.
Ko wata ɗaya Mami ba ta yi a k'asa ba Ya Sulaiman ya ce za a raba gadon duka dukiyar da Mami ta mutu ta bari, saboda ba ya son a sake samun wata baraka daga bangaren gado, shi ya yi tsaye akan komai ga ruwan kuɗi ga kaddarori, kuma ya ce ba zai riƙe kudin kowa ba, dukkanmu ya damƙa mana haƙkinmu a hannunmu. Kayan Mami kuma an fiddo su an ce idan muna som wani abu mu ɗauka idan kuma bama so za a sadakar da shi da amincewarmu tun da haƙƙinmu ne gabadaya. A cikin kayan sai na ga wata sarkar azurfa da na taɓa siya ta nuna tana sonta na cire na bata, ina son sarkar nan sosai,ita kaɗai nake so a ciki kayanta. Na ɗauka na ce "ina son wannan Ya Sulaiman".
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya ce na ɗauka Ya Hamida ta taso tace itama tana so, ni ko da naga na riga ta ɗauka sai na ce ai na riga ki, Aman ga wata na nuna mata wata ta azurfar wadda tafi wacce na dauka din ma girma. Nan da nan ta fara sababi tana faɗin na dai riga kai hannu amma dama ta faɗawa su Saddiqa sarƙar take so. Raina ya ɓaci na ce " sakarkar fa dmaa tawa ce, ganin ta nuna tana so me ya sanya na bar mata. Yanzu don na ce ina son kayata sai ya zama jidali ? Haka kawai na ambata Ya Hamida ta fara kuka tana faɗin na yi mata gori don na ga Mami da Baba ƙarami basa raye, dama tuni ta fahimci na fi son su Abida a kansu, to na je tunda su na riƙe itama ta zare hannunta daga mu'amala da ni, daga wannan lokacin zumumcin mu ni da Ya Hamida ya samu tawaya, tawayar da har yau bai koma daidai ba.
Kalubalen da ake fuskanta akan matsalolin rabon gado masu girma ne, faɗa tsakanin y'anuwan juna, faɗan tsakanin yan ɗaki ɗaya, faɗa akan kuɗi ko wani kadara, sannan yanzu gidan gandu da yawan mutane son rasa hakkunansu saboda haɗaka da rashin rabawa. Sai bayan sun rasu ƴaƴansu sun taso, sun nemi hak'kin iyayensu rigima ta taso da za ta yi silar rabuwar zumunci. A bar katon gida ba'a raba kowa ya yanki waje ya yi Gini ba tare da iyakance hak'kin kowa ba. Sun manta cewa bayan su akwai ƴaƴan su da za su taso. Mata na fuskantar k'alubalen rashin raba hak'kin gidan mahaifinta da ita, za ta yi aure a wani gidan idan aka tashi rabon gado masu tsoron Allah me ke fitar da ita da kudi ko Sa wani fili, amma galibi ƴanuwa maza da ahalinsu ke babakere a gidan. To idan aka bari aka cigaba da tafiya da sha'anin gado yadda Malam bahaushe yake yi to la Budda an dinga samun baraka a cikin zumuntarmu. Gidajen gandu a a k'asar Hausa yana wahalar gaske a iya raba shi saboda yadda ake zaune kara zube.
Ko babban wa ya yi babakere akan dukiyar k'annensa duk kuma wanda ya fito ya ce a bashi hak'kinsa sai ya zama abin tattaunawa abin zunde a kuma ware shi ace yana son tada fitina.
Muna rayuwane da mutanan da basu dauki dukiyar gado da tsantseni ba. Alhalin cikin abin da Annabi ya yi ta jan kunnenmu tauye hakkkin magada na kan gaba, tare da yi mana gargadi mai tsananin gaske don kuwa hadarin cinye dukiyar magada tamkar kana d'urawa kanka wutar jahannama ne a cikinka.
Sulaiman..
Shi kaɗai kawai ya ke tunanin yanzu me ya rage masa? Ba shi da uwa ba shi da uba, haka nan ba shi da mata ba shi da ƴay'a y'anuwansa da zumunci ya haɗa su sun tarwatse me ya rage masa a halin yanzu? Shi kaɗai ya fara wani tunani, tunda ya gama sauke nauyin gadon dukiyar Mami kuma ya damƙawa kowa nasa kason to lokaci ya yi da shima zai nemawa kansa mafita. Ansari an samu ya dawo hayyacinsa ya ɗau dangana. Saddiqa da Anisa suna cikin rufin asiri haka ma Hamida.
Bilki ce abin tausayi yanzu ba ta da kowa a kusa da ita duk da sun zama attajirai saboda yawan kuɗin da gado ya samar musu. Balki ta fi zama abin tausayi kuma marainiya ta sosai a wannan gab'ar, ga rashin aikin da yake rage mata damuwa. Da a ce za ta samu wani aikin da ya ɗebe mata kewa, matuƙa yana jin tausayinta ganin ba Abida a kusa da ita, don shine shaida Bilki da dukkan zuciyarta take son Abida, duk da ya gasgata Abidan ma na sonta. Babban abin da yake sake sa shi jin tausayinta shima zai yi nesa da ita na wani lokaci. Ga mijinta shima ba shi da wani aikin hi rayuwarta akwai tausayi a ciki, kuma idan ba'a kai mata dauki ba komai nata zai kare ne tunda yasan yadda zuciyarta take komai fitowa zata yi da shi su saka a gaba.
Shi kaɗai ba tare da sanin kowa ba ya fara fafutukan nema mini aiki, ni dai ya kira ni ya saka ni na tura masa duka takarduna, kuma cikin ikon Allah lokacin ya yi daidai da n'ada Baban abokinsa Salim Buba da suka yi karatu a Germany tare sabon V.C na jamiar dama y'an jihar Katsina ne a garin Mashi. Da taimakon Salim ya samo mini koyarwa a jami'ar Umaru musa y'ar aduwa.
*MalaysianFabrics*
*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*
*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*
*7020695644.*
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu."
Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki!
Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne.
Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami.
"Yayw Sulaiman waɗanan mganganun fa? Ina za ka je?"
Na faɗa cikin damuwa da tashin hankali
Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haɗuwa."
In jin ya ce haka na fara kuka ina faɗin" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni."
Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki"
Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta.
Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi.
Na ce ya ɗan jira su Farha sun kusa dawowa.
Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaɗai sauran yaran fa?
Na yi shuru ban yi mgana ba.
Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita".
Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"
Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da