yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba.
Shi ya yi jarumtar ce wa "To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su."
Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah."
Ya ce "Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d'aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana."
Ba ja in ja ta ce "Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad'ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk'awarin zata dinga zuwa hutu wajen y'anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad'ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita."
Ta fad'a hawayen tausayin ya'yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad'ai yana matuƙar d'aga mata hankali.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ya share hawayen idonsa ya ce "Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k'ok'arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba.
Ya mike tsaye ya ce "Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci."
Ta zuba masa ido ta ce "katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k'are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka".
Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad'an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak'kinta kad'ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama.
Ya tausasa harshe ya ce "Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had'amu da alheri ya shirya mana zuri'armu da ya bamu".
A hankali ta ce "Ameen.
Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice.
Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k'ira Alti d'aki ta fad'a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak'uri a yau kukan ta taya Bilki sosai.
Da k'yar suka hak'ura.
Alti da Alawiyya suka fara had'a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had'a wadanda zasu iya.
Sai da daddare ta zauna da ya'yanta cikin hikima ta fad'a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne.
Amrah ta ce "Mamah kun rabu ne?"
Ba boye boye ta ce "Aurenmu ne ya k'are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba".
Hawaye ya k'wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo.
Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad'in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?"
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Da k'yar ta shawo kanta ta nutsu ta yi shiru. Ta dinga yi musu nasiha.
Farouk ya ce "Yanzu mu kad'ai zamu zauna a nan side din Mamah?"
A tausashe ta ce "A a tare da Dady sannan Antin ma zata dawo nan din".
Ya yi shiru amma ba haka ya so ba. Can ya ce "Amma ki fad'awa Dady kada ta ce zata dinga takura mana. Sannan Mahma if possible ki bar mana Alti".
Bilki ta shanye tausayinsu ta ce "Ku zauna lafiya da Antinku, kada ku yi mata rashin kunya.
Duk abin da ta ce ku yi, to ku yi mussaman ke Amrah."
Amrah da take kuka sosai ta kasa magana.
Farouk ne ya ce "Mahma to ki bar mana Alti please ".
Sai lokacin Amra ta ce "Maimakon ka bata hak'uri ta zauna da mu sai ka ce ta bar mana Alti?"
Kaitsaye ya ce "Ba zan bata hak'uri ba. Kullum fa sai na ga ta yi kuka duk yadda bata son mu gane.
Kullum Dady ne ya kai anty school da duk inda zata je a mota. Amma when last ya dauki Mamah a motarsa ko kuma mu?Kina ganin Dady yana siyo abu a leda ya kawo side din nan? Amma kullum sai na ga ya kaiwa ta sama abu a leda. Kawai Mahma ki je inda ba za ki dinga kuka ba." Ni fa tuni na gaji kawai dan ba ni da kudin da zan siya mata gida ne. Duk ranar da na je Abuja zan faɗawa uncle Farouku senior ya siya mata gidan tunda uncle Sulaiman ba dawowa zai yi ba"
Wannan karon Bilki ta kasa jarumta danne kukanta. Ta fashe da kuka ainun yayin da Amra da Farha suke kukan suma amma da yake namiji tun yana k'arami zuciyarsu mai taurice Farouk bai yi kuka ba. Amma idanuwansa sun yi tsilli tsilli tabbacin yana cikin damuwa sosai.
Gabaɗayansu har Alti sai da kukan ya k'wace musu don kuwa duk abin da ya fad'a gaskiya ne. Sannan basu yi zaton Faruk yana ankare da komai ba.
Shi kad'ai ne idonsa babu hawaye.
A hankali ya ce "ku daina kuka ai ba mutuwa za ki yi ba. Shi kuma Dady sai ya cinye gidan ".
Da sauri Bilki ta bige masa baki tare da galla masa harara da manyan idanuwanta da suka yi ja tsabar kuka.
Ya mik'e ya fice yana gunguni. Bilki ta bishi da kallon mamaki da tsoro. Baya rikici da Hawwa shi, asalima da Amrah kawia yake fad'a a gidan. Amma yanzu kam ta ga alama idan ta tafi shine zai fi bawa mutanen gidan matsala ba Amrah ba. Ko da yake Amrah ma ba shiga shirgin Hawwah take yi ba. Kawai ita ce take ce wa Amrah ta raina ta ko ana sakawa ta yi mata rashin kunya. Amma ta lura shi Farouku laifukan ubansu ne danƙare a zuciyarsa.
Ta fara lissafin adadin shekarunsa nan da watanni uku zai cika shekaru goma sha uku. Lallai zata tafi ta bar baya da kura don yanzu shekarun balaga zai fad'a, shekarun da idan ya'ya suka farawa kaiwa sai iyayensu sun kara hak'uri da juriya akan sha'aninsu bare kuma ace suna hannun yarinyar da shekaru kawai ta basu dan shakaru biyar ne tsakaninta da Amra.
Washegari a salube yaran suka tafi makaranta.
Suna tafiya mai kula da gidajensu Bilki wanda tun ma kafin a raba a basu nasu gidajen shi yake kula da su gabad'aya. Don har na baba Babba duk shine wakilinsu.
Ya iso da masu k'atuwar motar d'iban kaya. Dama kuma tun jiya masu kunce gado sun zo sun warwaresu an jingine su, duk kayan kicin dinta masu daraja sun hadesu a kwali wasu ta sake k'arawa Alawiyy akan siyayyar da ta yi mata.
Kayan yara kuwa ba abin da ta dauka illa gadon Farha. Kuma ta bar musu duk abin da tasan zasu bukata na amfani.
Sai lokacin Hawwah ta fara ankara da gidan nasu akwai abin da yake faruwa. Gabadaya Sahal ya susuce ya rasa kuzarinsa ta yi tambayar Har ta ga ji da amsar da ya bata na babu komai.
Bilki bata bar gidan ba sai wata washegarin sassafe a dalilin bata son ta tafi akan idon ya'yanta. Duk da sun fara girma sun wuce a yi musu wanka ko wankin kashi, amma tashin hankalin da suke ciki ba kad'an ba ne. Ita Farha da aka ce da ita za'a tafi bata daina kukan a wajensu zata zauna ba.
Babban zullimin Bilki akan yaranta maganar abincinne da harkar makaranta.
Amma ba yadda zata yi, ta barsu a hannun Allah.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tare da Alti suka hau saman Hawwah. Ta karbesu ba yabo ba fallasa. Cikin mutuntawa ta ce "Hawwah zuwa na yi takanas na yi miki sallama zan tafi don Ubangiji ya k'arar da zamana a gidan nan. Bayan haka kuma na damƙa miki yara a hannunki. Na sani rikon d'an da ba naka ba akwia wahalar gaske. Sai dai idan aka yi dan Allah aka yi hak'uri za'a ci riba a gaba.
Ga yara nan ki yi hak'uri da su, ki sake ninka juriyarki idan sun miki ba daidai ba, ki gyara musu ta yadda zasu fahimce ki. Idan kuma abin yafi k'arfinki ki faɗawa Babansu.
Allah ya sauke ki lafiya ya ba ki hak'urin zama"
Daga haka ta mik'e tana fadin"Allah ya sadamu da alheri."
Jikin Hawwah ya yi sanyi sosia ashe abin da ya kwantar da Sahal ke nan a kwanaki biyun nan?
Ta tabe baki. A k'asan zuciyarta tana jin dad'in yadda zata mamaye gidan ita kad'ai. Don kuwa falon Bilki zata mayar da falon yin dabdala ita da jama'arta.
Tana kallo suka fice amma ta rasa kuzarin yi musu rakiya.
Yayin da Sahal yake kwance tunda ya yi sallar asuba ya koma bai tashi ba.
Ba barci yake yi ba, wani irin zazzabi ne yake nukurƙusarsa.
Bilki da kanta ta ja motar tare da Alti suka tafi ta bar Alawiyya sai an tashi zata je ta ɗauko Farha sai su same su a gidanta.
Tunda suka isa gidan ta shige d'akin da aka shirya mata gadonta da kayanta.
Kwanciya ta yi, ita ba barci ba, ita ba ido biyu ba. Komai ya k'wace mata, ita da kanta bata san hak'ik'anin matsalarta ba. Amma dai tunanin ya'yanta yafi komai dagula mata lissafi.
Har yamma tana kwance mussaman da fashin salla ya same ta a safiyar nan.
Alti sau uku tana lek'o ta. Amma ganinta a kwance idanuwanta a rufe sai ta fice a zatonta barci ta samu tunda kwanaki biyu basu yi barci ba.
Sai da magariba ta kawo kai sannan Alti ta sake shiga ta ce "Mahmah kwanciyar zata yi miki yawa. Ke ba azumi ba amma tun safe ba ki saka komai a bakin ki ba."
Da k'yar Bilki ta bude idanuwanta da suka yi ja sosai ta ce"Ina Farha?"
Alti ta ce "Tana can tare da su Amrah ta k'i yarda ta biyo Alawiyya".
Murya ba amo ta ce "Dan Allah Alti ki je ki dauko mini ita komin kukanta ".
Cikin rarrashi ta ce"A a mahma rabu da ita. Ai kinsan yadda take ƙulafuncinki da kanta zata neme ki. Amrah zata kula da ita."
Kan dole Bilki ta hak'ura. Sai dai duk kokarinta na ta ci abinci hakan ya ci tura don kuwa tana yin loma d'aya ta ji komai ya cushe mata.
Kwanaki uku Bilki na cikin wannan yanayin ba cin abinci sannan kullum tana d'aki. Wanka kawai take yi. Hankalin Alti ya tashi k'warai da gaske. Ta tura Alawiyya gidan Basma akan ta taho da ita sabon gidan da suka dawo tunda Bilkin ta kashe wayoyinta gabad'aya ta adana su.
Basma bata yi jinkiri ba, don tare suka iso gidan Bilki a motarta.
Tun yammaci take gidan amma har magariba Bilki na kwance uffan bata ce ba.
Kan dole ta hak'ura ta tafi gidanta. Amma washegari kafin ta je wajen aikinta ta biyo ta d'auki Bilki da Alti kaitsaye asibiti ta kaisu ta ga likita ya rubuta Mata maganin da zata dinga barci da cin abinci don ya ce stress ne da damuwa suka yi mata k'awanya.
Akai akai Basma take zuwa sai dai kullum a sanyaye take tafiya a dalilin yanayin Bilki kullum babu cigaba sai sake cabewa.
Gabadaya yanayinta ba na lafiya ba ne amma kuma ba ta ce bata jin dad'i ko ba lafiya ba. Abin da ya damu Alti da Alawiyya yadda take kwana ta yini a kwance kuma ba cin abinci.
Ranar da suka yi kwanaki takwas su Amrah suka zo gidan. Babansu ne ya kawosu, Farha suka rako a dalilin ta fara kukan wajen Mahma zata. Sai ya taho da su gabad'aya tunda weekend ne ya barsu akan zai dawo ya dauke su da daddare.
Ganinsu cikin rashin damuwa sosia bai sanya Bilki ta ware yadda Alti ta yi tsammani ba. Don haka hankalinta ya rub'anya tashi tare da tunanin uwardakinta ta had'u da lalura basu fargaba.
Cikin kwanaki goma sha biyun da suka yi a gidanta sun yi ne cikin mawuyacin hali don al'amarin na Bilki kullum ba sauki. Idan har ta bude baki ta yi magana to kuwa Farha ce a kusa da ita. Ban da haka sai dai ta rufe idanuwanta ko ta yi k'uri tana kallon gefe d'aya. Alti da Alawiyya ba abin da suke yi sai kuka.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan tafi son zama ita kad'ai.
Wani zuwa da Basma ta yi juyin duniya ta yi da Bilki ta bude baki ta fadi inda ya jefa wayoyinta amma uffan bata ce musu ba sai ido kawai take binsu da shi.
Ta yi wata irin rama ta farat d'aya.
Ta birikice sosia tamkar ba Bilki sola ma'abociyar kyan fuska da zati ba.
Basma bata da lambar Abida yanzu. Ga shi bata da ta Yaya Hamida.
Ta kalli Alti ta ce "Ban Ga wayarta bare mu shaidawa wani nata halin da take ciki.
Da hanzari Alti ta ce "Ina da lambar Farouk da Saddiqa."
Nan da nan Basma ta ce "Ba ni ta Yaya Farouku ".
Alti ta mik'a mata wayarta ta ce "Duba za ki ga Faroukun Mahma".
Basma ta lalubo layin bugu biyu ya dauka ya ce "An buga an bar ki Altin Bilki".
*
Ya fadi hakan a zatonsa Alti ce.
"Ba Alti ba ce Ya Faruƙu. Basma ce kawar su Abida"
Shima da ya ke ya santa nan da nan ya gane ta suka gaisa.
Cikin hawaye Basma ta ce"Ya Faruk za ku bar Bilki ta mutu ne ba wani a kusa da ita?"
Cikin tashin hankali Ya Faruku ya ce" Subhanallahi wani abu ne yake faruwa da Bilkin?"
Basma ta karɓe da ce wa" Abubuwa da dama sun faru. Aurenta ya mutj sannan kuma tana kwance cikin mawuyacin hali ".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Tun yaushe?"
Ya tambaye ta a sukwane .
A sanyaye Basma ta ce "kwanaki sha shida ke nan".
"Subhannallah ya furta a takaice".
Ya numfasa ya ce "Yanzu a ina take ?"
Tana gidanta na unguwar Alkali".
Ya ce "Zan zo in sha Allah. Allah ya bata lafiya."
Ta amsa da ameen a sanyaye.
Washegari wajen azahar kamar daga sama sai ga yaya Faruku a gidan Bilki. Ganinsa da Bilki ta yi ya sanya kukan da ya kafe mata tunda ta shigo gidan ya k'wace mata. Ta dinga yinsa tamkar zata hadiye zuciyarta.
Gabadaya ya rikice ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen yi mata magana.
Komai ya tsaya masa cak domin ya ganta cikin mawuyacin halin da duk dakiyar zuciyar mutum sai ta motsa.
Da ƙyar ya bude baki ya ce
"Bilkisu ki yi hak'uri, ki daina irin wannan kukan! Duk abin da ya samu bawa mukaddarine daga Allah. Bawa kuma ba ya wuce k'addararsa."
Bilki ta tsananta kukanta ainun wanda ya sake jagula zuciayar Yaya Farouku. Ya tausasa harshe ya ce "Fad'a mini damuwarki na magance miki ita Maigado"
Ta kasa ba shi amsa saboda kukan da take yi. Sai da ta numfasa don kanta.
Cikin kuka ta ce" Ba ni da matsala, ina kukane saboda jiya aka fad'a maka halin da nake ciki, amma yau ka yi asubanci ka bar komai ka taho tunda ga Abuja don ka ga halin da nake ciki. Ko na rasa komai a duniya na tabbatar ba zan rasa ka ba yaya Farouku".
Karon farko da ta bude baki ta yi maganar da bata shafi Farha ba.
Tausayinta ya yi matuk'ar kama shi, don ya fahimci ta yi amannar ta rasa duk wanda yake da muhimmanci a duniyarta. Dawowarta gidanta alamace na ta gamsu ta rasa dukkan muhimman mutane a duniyarta da zata zauna a kafaɗarsu. Ya sunkuyar da kansa idonsa ya cika da k'wallar alhini. A ransa yake fad'in zumuncinsu bai yi lalacewar da Bilki zata yi zaman kanta a shekarunta ko da kuwa babu Baba Babba a duniya ba.
Ya tausasa harshe ya kalle ta da kulawa sosai ya ce "da yau zan juya don ban yi zaton aurenki ya mutu ba. Amma tunda hakane zan kwana kafin su Alti su shirya miki kayanki tare da ke zan tafi".
Ba ja in ja ta ce "Na gode sosai na kuma tabbatar zaka yi mini komai a rayuwata, ban tankwabar da kokarinka ba. Amma bana son na kawo maka hargitsi a gidanka. Ka yi hak'uri duk abin da zaka yi mini, ka yi mini ina da ga nan".
Tsawon lokaci suna muhawara amma fir Bilki ta kafe ba zata bar Katsina ta gode da k'ok'arinsa.
Alti ta kyafta masa ido fahimtar hakan ya sanya ya yi shiru, yayin da Bilki ta runtse idanuwanta a zuwan barci take yi.
Daidai lokacin Alawiyya ta kawo masa abinci.
Ya zuba ya ci abinsa suna hira jefi jefi da Alti.
Ganin haka ya sanya Bilki jan bargo ta lullube jikinta har fuskarta.
Da ya kammala ya yi mata magana amma babu amsa kan dole ya