Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   23 / 37

66K to 69K   out of 110.8K words

da d'a mai ido kan yaranta ba ta sauko ta dawo tana kai su, ko tana cikin makaranta ne idan suka tashi za ta je ta dauka.

Ta so ta hada shi da Hajiya sai kuma ta fasa kamar za ta kauda kai amma ta ji ta kasa rashin adalci kiri kiri fa yake nuna mata, ya koma direban amaryansa amma ya'yansa ba zai musu ba, ita bata damu ya mata ba ma, amma ya yiwa ya'yansa mana.

Wani dare suna kwance ta sassauta murya cikin tausasawa ta fara yi masa magana amma ya taso da fada wai ita ba ya'yanta ba ne? Da sai ta jira ya yi musu abu, da ba ke kike kai sun ba? Me ya sa yanzu za ki fito da tsirfa?

Aikin da na amince ki yi ba alfarma na yi miki ba? Ai ba duk namijine zai yarda iyalinsa kullum tana sintiri a waje ba. Ya ya hakane za ki dinga fitina ta?".

"Saboda na ga alaman kai ba ka da adalci, kai azzalumi ne Sahal "

Ta ba shi amsa kaitsaye.

Ya mike a fusace yana nuna ta da yatsa.

"Ni kike kira Azzalumi Bilki? Dama tuni kike son faɗa mini wannan maganar sai yau kika samu dama"

A zafafe ta ce "Na faɗa kai azzalumi ne sannan ba ka da adalci. Ka san ba a gidan wahala ko babu ka dauko ni ba. Duk wata gwagwarmaya da babu a gidanka na santa na kuma koyi juriya da hakuri hadi da sadaukarwarka don na rayu da kai. Tare da yi maka kyakkwan zaton kasan alheri, zaka saka mini shi da alheri, ashe ba haka bane, ban karance ka daidai ba".

Ta kammala maganarta idanuwanta na kallon shi ido cikin ido, domin yau ta kai makura wajen shakiyancin da yake yarfa mata.

Ya tunbatsa da fushi yana ayyana lallai zai mata hukuncin da sai ta nemi shi guiwarta biyu a k'asa idanuwanta cike da k'wallar nadama tana neman afuwarsa da son ya cigaba da rik'e ta tunda bata da wajen zuwa . Wataƙila ta manta da hakan amma a yau zai ankarar da ita bubuwa masu yawa.

Ya zuba mata ido ya ce "Tabbas ban dauko ki a gidan wahalar rayuwa ba, sai dai na kwaso ki ne a gidan masu son zuciya da take umarnin Allah. Na d'auko ki ne a ahalin da suka yi shari'a da junansu akan dukiya, na dauko ki a cikin mutanan da abin duniya zai saka su k'i junansu, suka rabu dutse a hannun riga kowa na fatan Allah wadai a tsakaninsu. Ban da rabon haihuwa mai zafi mai ya kai ni wannan kasassabar, don bansan yadda zan ji ba, idan na bude ido na ga Amrah da Faruk na shari'a da gaba da juna akan abin duniya ba."

Kuka mai ciwo ya k'wace mata. Ta dinga kururuwar bak'inciki tare da fatan Allah ya sauko mata da ajalinta take yanke.

Amma duk da haka cikin jarumta ta ce "Tabbas baka yi mini karya ba kalamanka akan turba suke. Amma wataƙila baka da wayo lokacin da zuriar'ku ta haustine da guda daga cikin iyayenku maza ya yi d'ab'iar nan ta k'uda baka haram akan d'iyar wansa uwa daya uba d'aya ".

Ya muzanta ya razana ya ce "A gidan uban wa kika ji wannan batun?"

Hawaye na malala a dukkan idanuwanta ta ce "A kundin tarihin da ba zai gogu ba. Duk inda aka kai da boye shi kuwa. Dan haka mu tarihinmu iyayenmu basu yi abin kunyar da ya yi ajalin guda cikin iyayensu ba. Har abada kuma ba za'a samu irin haka ba tunda gado ne. Dan haka ka shirya zaka ga hakan a ya'yan Hawwah don ya'yantane zasu yi wannan gadon, a gidanka tarihi zai maimaita kansa, kamar yadda ka yi fatan shari'ar da aka yi a gidanmu ta maimaitu akan ya'yana."

Tashin hankalinsa ya bayyana b'aro b'aro a fuskarsa da gangar jikinsa gabad'aya. Ya zuba mata ido yana mata kallon tsana, yana ayyana tamkar ya shak'e ta ko ya yi mata dukan da zai lalata mata kyakkwar surarta, yadda ba mai kwasarta.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai dai ya tabbatar dukanta ba k'aramin bala'i zai rakitowa kansa ba domin duk yadda ya mata gorin ahalinsu sun dare sun tarwatse bata yi arahar da zai saka hannunsa a jikinta da sunan duka ya kwashe kalau a hannun ahalin nata ba. Duk tak'amarsa kuwa.

Tana da yaya kwamishinan y'an sanda (Asad) wanda tun asali yasan bai so aka ba shi aurenta ba. Tana da Usman soja ne wanda shima matsayinsa ya fara nisa a gidan soji. Tana da tantiri irin Ansari kuma mai d'amara ne. Bayan haka ga Farouk da yake da kud'i a hannunsa ya tabbatar zai kashe ko nawane akan Bilki. Haka nan tana da darajarta ta daban kasancewarta tsohuwar ma'aikaciyar kungiyar lafiya ta duniya (W.H.O) Wanda suke had'akar ayyuka da hukumar kare hak'kin d'anadam(Human rights). Bayan haka Munira babbar Lauya ce da take aiki da kotun duniya reshen k'asar da take zaune, sannan jamiar kare hak'kin ya'ya mata ce. Ga uwar iya Abida. Ga Yaya Hamida mijinta babban alkali ne a kotun shari'ar musulunci. Ga Basma yar karare da zata yi zugar da dukkan ahalinsu Bilki zasu yi masa d'aurin talala.

Dan haka a fusace cikin isgili ya ce "Don iyayenki masu son zuciya ki je na sake ki saki biyu, ba don uku tashi guda sakin jahilai ne ba, da na cike miki, shasha mai bak'ar zuciya da bakin k'ishi. Ki je, idan kin samu adalin da ya fini wanda ba azzalumi ba, sannan ba mai gadon abin kunya ba sai ki aura Hakima Bilkisu Isa Funtua!

Yana gama fad'in haka ya fita ya bar mata falon.

Ita kam sai ta ji kanta na juya mata kalaman Sahal na mata kuwwa a kunnenta har ma kwakwalwarwarta bakidaya.

"Ki je dan iyayen ki na sake ki saki biyu"

Tirk'ashi!

Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.

Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.

Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

End of book 2

Muje ga book 3

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BVkUYEzJHcEAhYoST77vEH?mode=ems_wa_t

*Wannan littafin na kudine*

*1k via 2384876855*

*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*

*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*

# 08032773332#

# 09069067488#

*Littafi na d'aya ya zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku suke zuwa a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO 3*

*BY*

*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*

*HALIN YAU*

*SABO DA KAZA*

*BAK'AR TA'ADA*

*Barar addu'arku*

*A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata*.

*Ina barar addu'arku da ku taya ni yi mata addu'o'in smaun rahamar Allah*.

*Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko*.

*Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad'aya*.



Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.

Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.

Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.

Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had'iyewa a gabansa.

Da murmushi ta dinga fad'in "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba".

Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d'aya.

Gabad'aya jikinsa ya sake ya yi tub'us.

Yayin da ita ta kasa fahimtar komai.

Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba.

Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya'yanta addu'ar Allah ya tsare mata su ya kuma k'addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya.

Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne?

Sai yanzu ta fahimci girman k'alubalen da yake gabanta.

Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu'a.

Sai da aka fara k'iran assalatu ya farka.

Ya shiga bayi ya d'oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi.

Sai da ya idar ya ce "Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je".

Bak'in ciki har mak'oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak'incikin da ya taso mata.

Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d'ab'iar mace kamila mai ilimi ba ne.

Dan haka ta yi masa bakam.

Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba.

Ya tafi masallaci yana fad'in "Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo.

Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta.

*Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu"*

Zuciyarta ta buga da k'arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k'arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad'ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak'uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata?

Ta girgiza kai tana fad'in "Ko duk zuri'armu sun k'are ba zan sake zama k'arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne.

Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri.

Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa.

Amma a yanzu fa?

Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida?

Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k'arkashin wani take.

"Ina zan tafi ni Bilki?"

Ta fad'a cikin rawar murya irin ta kuka.

Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad'ai zata zauna ba. Take ta tuno da d'aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y'an haya a k'asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud'e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud'e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za'a sake karɓa a bata kudi da daraja.

Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad'in "Hajiya da fatan dai lafiya?"

Murya ba amo ta ce "Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?".

Da girmamawa ya ce "An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba'a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan."

Ta ce "To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. "

"To za'a yi hakan Hajiya da ikon Allah. "

"

Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d'aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d'ebo mata kullum.

Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d'aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu.

Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?"

Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya'yanta.

Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya'yanta yana matuk'ar tayar mata da hankali.

A haka ya dawo ya tarar da ita.

Ya zauna a gefen gadon. Ya ce "Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k'wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d'akinki.".

Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce "A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k'are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faɗawa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk'atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo".

Da iyakacin gaskiyarsa ya ce "Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha'awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha'awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha'awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k'arfi bukatar al'amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki".

Na goge hawayen na ce "Zaman ne ya k'are."

"Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab'a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?"

Ya fad'a a zabure.

Cikin nutsuwa ta ce "Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak'uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za'a zagi iyayena yayin da za'a sake ni sannan na bada hakuri ba. "

Ya mike yana fad'in"Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za'a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d'anta ko kuma na y'anuwanta shakikai".

Bata kula shi ba don bata da abin fad'a kuma.

Ya sake zama ya sassauta ya ce "kin yi nazarin ya ya rayuwar ya'yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?"

Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce "Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi".

Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab'a masa.

Ta numfasa ta ce"Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya'yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y'ay'anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka."

Daga haka kuka na sosai ya k'wace mata.

Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce "Bilki ki zauna na mayar da ke".

Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik'e tare da fad'in"Wannan kuwa shine gangan Sahal!

" Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al'arshi zama ni da kai ya k'are ila yaumil k'iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari'a sai dai tunda shari'ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni ".

Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya ce "Idan ba za ki zauna saboda ni

23 / 37