da Momi suka taimakawa Baba Babba ya mik'e suka bar mana falon Ya Sulaiman zai bi su Mami ta ce "Dawo! Ko kuma na yafe musu kai".
Wannan kalaman sune suka dakatar da shi daga bin bayan Baba. Amma yadda suka fita hankalinnsu a tashe sannan su harzuƙa sosai daga kalaman Ya Usman da Abida, amma bai saka Mami ta saduda ba sai ma ta cigaba da mganganu ita da Ansari suna yi ma su Aneesa famfo akan su mara musu baya, akan akilo da suke yi na ganin ba'a cucemu ba.
"Haba Mami don Allah ki bar mganar nan haka nan. Yau ko Baba ya dawo duniya Wallahi ba zai yi alfahari damu ba".
Ya Sulaiman ya fad'a murya babu amo, shi yana kwalla ni kuma ina faman kukan sharbe, abin da na ke ta gudun faruwarsa ne ya faru, kuma ina hango kafiyar Mami kan iya haifar da hargitsin da ba mu taɓa tunani ba.
"Ki yi haƙuri don Allah Mami ki bar mganan nan haka don Allah ba don halinmu ba."
Na fad'a ina kuka Mami ta kalle mu ta sake kallonmu kafin ta koma ta zauna tana jijjiga k'afa ta ce" Na rantse da wanda raina yake hannunsa ba zan maganar nan ba. Sai na yi sharia da duk wanda zai tauye mini haƙkina ni da ya'"yana"
Ansari na gefenta ya ce" I support the motion Mami."
Anisa ma ta ce tana bayan Mami haka ma Yaya Hamida sai ya kasance daga ni sai ya Sulaiman ne a ware.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Mun kasa ce wa komai saboda kalaman Mami sun girmi tunaninmu ban sake tsinkewa da cewa Mami ta yi nisa ba sai da ta furta wata magana mai nauyi.
Wai ba ta yarda da hatsarin su Baba Ƙarami ba ma, tana zargin maƙarƙashiya aka shirya saboda a kashe Baba ƙarami da Ya Sulaiman
Tana faɗin maganar jikina ya tsuma tashin hankali. Ya Sulaiman kam a tsawa bude murya ya yi sosia ya ce
"Mami! Na roke ki kada Ki sake furta wannnan mummunar kalmar ko da a zuciyarki ne "
Ta zaro masa ido kafin ta ce" Ai ba ƙarya na yi ba. Ka yi lissafi da kanka me ya sa bai faru da Faruƙu ba sai kai? Haba da akwai ayar tambaya akan wannan lamarin."
Ansari ya jinjina kai kafin ya ce" Uhm ni fa na daɗe da tunanin haka Mami kawai dai ban yi mgana ba ne domin ba ni da wata hujja."
Ina kuka da muryata a buɗe na ce" Haba Mami yanzu sai ki bari zuciyar ki na faɗa miki Baaba Babba zai iya yin wani abu na cutar da Baba ƙarami? Me yasa Mami? Me ya sa kike so ki jawo abin da bamusan iyakacin inda zai tsaya ba?"
"Kin ci uwarki Balki. Na ce kin ci
ubanki!
Mami ta faɗa a harzuƙe har tana yi mini daƙuwa.
Ansari ya kaɗa kai kafin ya ce" Dama kin kai mata hannu Mami kwata - kwata Bilki ba ta kishinki sannan mu ma y'an uwanta ba ta kishinmu"
Mami na huci ta ce" Idan suka ce za su kware mini baya sai dai na yafe su Wallahi. Kuma idan na yafeku ba zaku taɓa yin albarka ba idan kuma haka kuke so to ku bada himma."
Tana gama faɗin haka fuu ta bar mana falon Yaya Sulaiman ya bi bayanta yana kiran sunanta..
Ni kuma suka bar ni da Ansari yana ta gaya mini maganganu wai ba ni da kishi ni sakara ce mara wayau Abidan da na ke kuka saboda ita, ubanta zata kare, amma da ya ke ni sakara ce ba san nawa ba tamkar Dai ba nice gaba da shi ba.
Ina kuka na ce" Ansari kar ka runtse idanuwanka ka manta da mu Ahali ɗaya ne. Kar ka manta Abida matar Ya Sulaiman ce fa?"
"To sai me? Sai ya sake ta tun da abin na su ba adalci a ciki.'
Cewar Anisa sai na fahimci gabadaya yanzu suna bayan Mami ne, ba wanda zai iya saurarata ballana ya gane ina manufata ta dosa.
Nima falon na bar musu na shige ɗaki ina ta kuka, mutuwar Baba ƙarami ta dawo mini sabuwa mutuwa ce ta kawo mu wannan bigiren yau da Baba ƙarami na raye, ba mganar gado ballanta asan asirin da suka rufe shi da Baba Babba.
Ranar haka gidan nan ya kwana ba lafiya, da safe da na je gaishe da Mami ƙin amsa gaisuwata ta yi, shi ya sa jiki a sanyaye na fita zuwa bangaren Ya Sulaiman saboda na kasa shiga bangaren su Abida. Sun yi tsit kamar ba su a gidan sai dai ina zuwa bangaren Ya Sulaiman na iske
Shi kad'ai wai ta je asibiti.
Kawai na jine amma ba wani asibiti. Baba ya hanata zama ya sata ta dawo gidanta akan dole shine sassafe ta fice da sunan zuwa asibiti. Nasan Abida za'a fafata don kuwa ba mai sassauci ba ce irin Yaya Munira.
"Balki, na yi iya bakin ƙoƙarina amma Mami ta ce tana kan bakanta ta saka Ansari ya nemo musu lauya za su shigar da k'aran Baba Babba."
Kai na dafe ina faɗin" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.
Idona ya soye hawayen ya kafe, kirjina ya yi nauyi ainun.
"Bilki muna cikin Tsaka mai wuya(Janafty )Mami ta ce idan muka bijere mata za ta yafe mu. Ya za mu yi?
Shima yana magana cikin k'unar rai, bamu da wata mafita Mami mahaifiyarmu ce idan ta tsine mana zamu bi duniya mu lalace, idan kuma muka goya mata baya dai dai yake da mun saka wuka mun gille zumunta.
Ya numfasa ya ce "Ga yarinyar nan ta murde, na ga take takenta ita zata jagorancin bangarensu wajen sake watsa zumuncinmu.
Muka gama zaman bamu samu mafita ko dabara ba.
Haka muka fito babu matsaya, kaitsaye muka yanke muje mu gaida Baba Babba.
Zamu shiga muka ci karo da Ya Usman ya rako likitan da yake duba Baba Babba ke nan jikin na shi ya tashi saboda hatsaniyar da ya faru jiya, jikina ya sake sarewa lokacin da na ga na gaishe da Ya Usman ya yi wucewarsa kamar bai ganni ba.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Jikina kamar ba nawa ba na ƙarisa shashen Baaba Babba Momi ce kaɗai a falo itama da na gaisheta sau ɗaya ta amsa daga nan ta tashi ta bar falo na yi tsaye ina kukan zucci da na sarari amma ba motsin kowa, kamar zan taka ɗakin da Baaba Babba yake sai na ji kamar muryan Ya Faruƙu sai na fasa na juya zan nufi ɗakinmu muryar Abida na ji tana waya.
"Ya Muneera sun ce za su kai Baaba Babba ƙara a kotu. Tunda bamu muka fara ba, to ba za mu juyawa yaƙinsu baya ba."
Ta yi shiru tabbacin tana sauraronta ne.
Sai Kuma na ji ta cigaba da magana cikin d'aga sauti ta ce "Na rantse da wanda raina yake hannusa Yaya Munnera za mu yi sharia da su kuma sai mun tabbatar da adalci ga Baba Baaba sannan za mu dakata."
"To Idan kinsan ba za ki kwafsa ba to sai ki zo ki tsaya masan".
Ban ji me Ya Munnera take faɗi ba, saboda yadda jikina ke rawa yasa bansan na k'arisa ƙofar ɗakin namu ba, kofar a buɗe ta bar ta.
Murya ba amo na shiga dakin bakina dauke da sallama.
Ta juyo tana ganin ni ce ta sake haɗe rai, itama idanuwanta sun yi luhu luhu alamun ta sha kuka.
"Zan kira ki Ya Muneera."
Ta faɗa sannan ta katse wayar ganin ta nufo ni sai na yi ƙoƙarin shigowa ɗaki amma Abida ta yi maza dakatar da ni daga bakin kofar dakin wanda hakan alamace na bazan shiga dakin ba ke nan.
Nan da nan na ji na muzanta idona ya ciko da kwalla.
Tana kallona ina hawaye ita ko saboda taurin zuciya ban ga kukanta ba akan fuskata Abida ta bugo mini kofa ta bar ni da radaɗin zucci da sarari, ina kuka wiwi da gudu na koma bangarenmu sai ɗakin Mami tana zaune gefen gado tana magana a waya a yanayin yadda take mganar na fahimci da Ansari ne domin faɗa masa take yi cikin satin nan take son ta shigar da kara kan Baba Babba.
Gabanta na faɗi ina kuka na riƙe kafafunta ina faɗin" Don Allah Mami ki yiwa zumunci kara, ki yiwa Baba ƙarami alfarma ki yiwa Yaya Sulaiman karamci ki janye mganar nan don Allah"
Fizge kafarta ta yi, kafin ta miƙe tana fadin" Wallahi Balki yadda na ke jin takaicinki zan iya yi miki baki."
Na kalle ta ina kuka amma bai saka Mami ta saduda ba, cikin dakiyarta ta ce"idan kika sake ce wa tak a kan wannan mganar sai na yi miki Allah ya isa. Sannan zance ba za ki yi albarka ba Balki."
Kaina ya sara na durƙushe ina faman gunjin kuka ba ni da wani kalami da zan sake furtawa haka na ja jikina na fito, ranar a ɗaki na yini yarane ma suka debe mini kewa suna ganin ina kuka suka fara tambayata Mahma me ya faru da ke? Dan haka na hadiye kukan dan na Samar musu da nutsuwa.Tun jiya rabo na da waya komai na duniya baya yi mini daɗi Anisa da Yaya Hamida da safiyar nan suka koma gidajen mazajensu, tun ina tunanin Mami za ta sauka har na yi sarandar da ce wa bata fara domin ta daina ba. Gidanmu ya rikice gabadaya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ba zato ba tsammani kawai sai ga takardan sammaci daga babban kotun katsina, sammaci daga iyalan Marigayi Alhaji Isa Funtua(Baba karami) zuwa Alhaji Musa Funtua.(Baba Babba).
Wannan takardan sammacin ta yi silan ɗaga hankalin Baba Babba da ahalinsa, ashe dai Mami da gaske take yi, ashe Mami duk abin da take faɗa har zuciyarta ne? Hankalin Baba Babba yafi na iyalansa tashi, yana kuka yana faɗin" Bazan iya sharia da ƴa'ƴan ɗan'uwana ba, ba zan iya shari'a da iyalan Isa ba, bayan ƙasa ta shafe idanuwansa ba."
Momi ma hankalinta ya kai maƙura wajen tashi, tana kuka Baba Babba na kuka, bata taɓa tunanin Mami zata yi haka ba, ta ɗauka duk barazana ce ashe ita da gaske take yi? Wannan wani irin lalacewa ne ace saboda gado ƴaƴan Baba ƙarami zasu yi shari'a da Baba Babba itama tana goyon bayan Baba Babba shi ya janye, ya ba su duka gidan gona in dai haka Mami take so, zai fi mutumci da kuma yi ma zumunci kara, akan ayi ya yamimidin yana shari'a da ahalin k'aninsa bayan k'asa ta shafe masa ido.
Ga shi kuma zaman kotun ranar 20 ga watan da muke ciki ne, yau kuma biyu nan da kwanaki sha takwas ke nan masu zuwa.
Shi dai Baba Babba ba nan yake hango matsalan ba, shi ba zai iya sharia da ya'yan d'an'uwansa lamarin ne yake saka shi kuka da tunanin mutuwa ce duk ta jawo wannan tonon sililin yau in da ace Baba ƙarami na raye da duk haka bai kasance ba.
Gabad'aya komai ya ɗakule masa, a cikin zuciyarsa yake jin wani irin zafi zafin da ya kasa misalta misalinsa, tun bayan rasuwarp Baba karami yake fama da nauyin zuciya ga wannan rigimar da ta taso. Shima yana ji dama ace shi ne ya rasu ba Baba ƙarami ba, da yau bai fuskanci wannan tashin hankalin da damuwar ba, da shi ma ya huta kamar yadda Baba ƙarami ya huta da kwaramiyar duniya mai cike da rudani.
*
39
Ina katsina Ansari, ya kira ni yana faɗa mini za a fara sauraran ƙara ranar 20 ga wannan watan da muke ciki, na shiga ɗimuwa da tashin hankali Mami ba zata saduda ba, Mami da gaske take yi ke nan? Ya kuma sake ba ni tabbacin tuni takardar sammaci ya isa ga Baba Babba da iyalansa, na sake firgita nasan Mami da kafiya kuma tun da ta kafe sai ta cika muradinta, ba tare da shawara da kowa ba na yiwa Kawu Bala waya na sanar da shi halin da ake ciki ina kuka ina roƙon shi su zo su sami Mami wataƙila in suka yi magana ta ji su ta kuma janye kuɗirinta.
"Ashsha abu bai yi daɗi ba! Sai dai ba zan saka kaina a sabgarta ba, don kuwa kunsan yadda muma muke ciki da ita".
Kukana ya tsananta na kasa Magana.
Jin yadda nake kuka ya saka ya ce "Tausayinki ya kama ni! Share hawayenki zamu zo mu same ta Allah ya sa ta ji. Tunda kunsan halin uwarku muma ba jin dad'inta muke yi ba."
Cikin shassheƙan kuka na ce" Kawu ku taimaka ku daure, ku tursasata ta janye, wanne irin masifa ta had'a mana haka?"
Ya ce "Zamu yi Mata magana da nasiha Idan ta amince shike nan, amma ba zancen tursasa ta tunda bamu da kudade masu nauyi. Yanzu ma saboda ke da nema muku masalaha da mutunci ya saka Zan yi karfin hali na jarraba tunkarar ta. Don na yi alƙawarin daina shiga sha'anin mahaifiyarku saboda halinta. Amma tunda har lamarin ya kai ga haka zamu zo mu sameta idan ta ji nasiharmu shike nan, idan bata ji ba sai na ce Allah ya bata sa'a. Duniyace wanda ma ya tara dukiyar ai ya tafi ya barta. Itama bata fi ƙarfin Allah ya ɗauke ta a wannan yanayin ba."
Haka muka rabu da Kawu Bala bayan ya bani tabbacin zasu je har Funtua su samu Mami da maganar ni kuma a gida ina ta fata da addu'ar Allah ya
sa zuwansu ya zama alheri.
Kwana biyu tsakani ina ta fama da zullumi, na sake kiran wayar Kawu shi ya fada mini a jiya suka je suka yi magana da Mami kuma ta nuna ta ji nasiharsu amma dai bata ce musu komai ba, hankalina ya ɗan kwanta a tunanina an samu nasara da karfin gwiwata na kira wayar Mami sai dai tuni ta ranfo ni ce na kai k'ararta wajen yayyen nata, ko gaisawa ba ta bari mun yi ba ta fara mini faɗa tana zagina.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Sakarya marar kishi, ai nasan dama ke ce kika kira su Yaya Bala kika kai k'arata. Bilki kina daukar lamarina da wasa? To bari ki ji na rantse da Allah bazan bar maganar nan ba sai an kwato mini haƙkina da na ƴaƴana gwara ma ki yi shuru da bakinki. Duk kuma wanda za ki turo kin daɗe ba ki turo su ba amma ina nan akan matsayata babu ja da baya."
Tana gama faɗin haka ba ta saurara ni ba, ta kashe wayarta na yi ta k'iranta daga baya ba ta ɗaga kirana ba. Na k'ira wayar Ya Sulaiman, shima ɗin ya ba ni tabbacin sun zo amma ko bayan tafiyar su Mami ta sake jadadda masa da ce wa tana kan bakanta ba kuma irin ban baki da nasihun da bai yi mata ba amma ta ce, babu gudu ba ja da baya, Ansari kuma yana bayanta tun da har shige da ficen, ƙaran ma Ansari ne ya yi a Katsina ya shigar da karan sannan ya ɗauki ƙwararan lauyan da zai tsaya akan sharian yanzu haka ma suna ta haɗa hujojinsu ranar shiga kotu kawai suke jira. Hankalina ya rub'anya tashi gabaɗaya duniyar ba ta yi mini daɗi har zazzaɓi ne ya kama ni da nake yinsa a tsaye saboda zullumi da tashin hankali.
*
Funtua.
Kwanakin shiga kotu, suna ta kara matsowa, duka duka saura kwanaki hud'u ne a fara zaman farko. Hankalin Ya Sulaiman ya tashi ganin har Ya Muneera ta samu Visa ta iso. Hakan ya alamta mana ita ce zata tsayawa Baba Babba.
Abubuwa sun sake ƙwabewa don kuwa barci kad'ai ke kawo Abida shashinsu Hakan ma yasan turo ta ake yi akan dole. Duk juyin da zai yi kuma bata yarda ta ce masa uffan. Gaba ta k'ulla a tsakaninsu mai tsananin gaske duk da itama fama take yi da zazzabi da rashin kuzari wanda take ganin bacin rai ne ya sababa mata.
Gari na waye wa take fice wa zuwa bangaren momi, tamkar akan k'aya take, da yake a cikin rudani yake sai Bai tsananta ba, don Shi tashin hankalinsa ba akan fishin Abida bane, gabad'aya hankalinsa da tunaninsa yana kan ya samu damar da zai hana yin wannan shari'ar da take k'aratowo, tun ba'a shiga kotu ba, gaba ta fara k'ulluwa a tsakaninsu da ya'yan Baba Babba. Ko Muneera da ta iso garin ba ta zo b'angarensu ba kuma bai ga laifinta ba, a irin abin da Mami ta yi musu suna daidai da irin hukuncin da suka ɗauka a kansu.
Ya kudire zai sake tuntubar mahaifiyarsu a karo na k'arshe ko Allah zai sa zuciyarta ta yi laushi ta sauko a janye k'ararta tunda lokaci bai kure ba. Hakan yasa yau tun asuba bayan ya dawo daga sallar asuba a bangarenta ya sauka shima duk ya rame ya lalace ,shi da ya dawo daga jinya ya kamata ace ya samu natsuwa da hutu amma ina tun bayan dawowarsu bai samu natsuwa ba sannan bai samu hutu cikin salama ba tun da zuciyarsa babu sukuni.
Duƙurshewa ya yi a gabanta yana sake bata baki da lallashi nasiha yake yi mata cikin dubara wanda ba cin fuska ko raini a ciki.
"Haba Mami har kin manta mutuwa? Har mene ne a duniyar da ya fi miki Baba ƙarami? Wani daɗin duniya ne ya fi miki Baba ƙarami Mami? "
Shuru Mami ta yi ba ta yi magana ba, amma da alamu kamar jikinta ya yi sanyi ganin haka yasa ya sake gyara zama yana ƙara tusa mata mganganu domin zuciyarta ta raunana ta saka Ansari ya janye ƙarar Baba Babba da ya shigar.
"Amsar ita ce Babu Mami, ba wani daɗin duniyar da ya fi miki Baba ƙarami, kuma kin rasa shi kin haƙura! To mene ne a dukiya ko gona da ba