Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   28 / 37

81K to 84K   out of 110.8K words

zasu sanya ta walwala a guje kuntata mata. Bayan haka a dinga kokarin hana ta zama ita kad'ai na tsawon lokaci.

Abida ta taka muhimiyar rawa wajen dawo da tunanin Bilki daidai.

Don komawa ta yi ma d'akinta kacokan. Hakan kuma na tunowa da Bilki rayuwarsu ta baya mai dad'i kafin komai ya cakalkale musu.

Ana haka Yaya Asad ya biyawa Bilki da Abida umrah.

Ya yi hakan ne don zuciyarta ta sake daidaita.

Ba Bilki kawai ba, hatta Baba Babba ya ji dad'in hakan.

Suka shirya suka tafi aka bar junior a wajen Momi. Don kuwa ana faɗawa Bilki zasu tafi Saudi ta ce Da Farha zata tafi. Tunda a satin zata fara zuwa makarantar da za'a saka ta. Idan sun dawo sai ta fara zuwa.

Ba musu aka yi mata yadda take so.

Haka suka tafi su uku. Sati biyu suka yi suka dawo.

Sosai Bilki ta dangana. Ta cire hankalinta akan komawarta Katsina tunda Farha har ta fara zuwa makaranta. Wani lokacin ma Farha ce ke damunta da batun yaushe zasu koma gidansu ne? "

Katsina.

Hawwa ta haihu sati biyu da suka shud'e, daidai lokacin Bilki na umrah. Iya k'arfin iyakarsa ya yi mata hidima. Sai dai ita bata yaba ba don kuwa ta dauke shi maikudine sosai. A yanzu da zaman nasu ya fara nisa ta fahimci ba shi da komai illa albashinsa. A ciki zai yiwa uwarsa da y'ay'ansa da kuma ita da abin da ta haifa.

A lokacin ta fara gane duk arzikin da take ga ni a gidan Bilki ce. Tunda ta bar gidan ta gane ta tafi da abubuwa da yawa tunda ba shi da mai yi masa.

Bayan haka tana zargin Bilki ta yi asirin da zai so y'ay'anta fiye da k'ima, tunda ai farkon zuwanta ba haka yake mu'amala da yaran ba. Asalima shi da kansa ya ce "Amrah ce zata dinga yi mata aikin shara da wankewanke. Amma a yanzu saboda kada a saka ta ya dauki mai aiki. Iya dakin barcinta da band'aki kawai take gyarawa. Sai ko wanki da guga da take yi musu ita da k'aninta. Suma idan kayan masu nauyi ne da kansa yake wanke musu ya dauraye su kuma su shanya. Bata sake hassala ba sai da ya ce mata zai sakawa jaririya sunan Bilki. Ta yi tsalle ta dire akan bata yarda ba, don kuwa ba zata sha azabar nak'uda sannan a sakawa yarinyarta sunan kishiya ba.

Bai zafafa ba amma a gabanta ya k'ira Amrah ya mik'a mata jinjirar ya ce "Ki zaɓarwa kanwarki sunan da kike so a saka mata ".

Hawwa ta ji tamkar ta rufe su da duka daga shi har d'iyar tasa.

Yayin da farinciki ya kama Amrah.

Da murmushi sosai ta ce "Na gode Dady! Na zaba mata sunan Hajiyarka".

Ya taya ta murmushi ya ce "Allah ya raya lubabatu".

Farouk da yake gefe ya ce "Ameen."

Sai lokacin Sahal ya ce "A a yayan Mahmah matso kusa da ni kai kuma ka zabar mata sunan da za'a dinga fad'a mata tunda Yaya ta sanya mata sunan da ba za'a dinga gyatsa shi ba."

Ya girgiza kai ya ce "A a Dady ta zabo inkiyar ma dan kuwa nima idan aka sake haihuwa ni zan zabi sunan da nake so."

"Oh dabararka ke nan?"

"To Allah ya kawo masu albarka".

Daga haka ya karbi yarinyar Amrah tana fadin "Tunda ni Amrah ita kuma Ifrah kawai".

Hawwa a ranta sai ayyana k'arfin halin da aka gwada mata take yi. Yarinya ce zata zaɓarwa y'arta suna tsabagen an shiga an fita an juyar da hankalinsa kansu?

Kan dole ta yi shiru amma matuƙar ta tafi gida yawon arba'in itama sai ta nemo taimakon da zata karkato hankalinsa kanta da d'iyarta.

Duk da idan an tambaye ta menene baya yi mata, idan har gaskiya zata fada babu ce amsar.

Kawai matsalar ta ba kudin facaka a hannunsa yanzu sannan mu'amalarsa da ya'yansa na matuƙar mintsininta har ta dinga jin ina ma uwarsu ta nan?

Haka dai rayuwar take tafiya kowa yana hak'uri da yadda aka zartar masa rayuwa. Alhamdulillah, Allah ka saukaka mana gabadaya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai da ya yaran suka fita ta dauko robar hadaddiyar gumbarta da ta siyo a Kano unguwar rijiyar lemo.

Tun tana amarya take son gumbar dan ta ga aikinta tunda cikinta ya fara tsufa ta daina ci.

Yanzu da ta dauko ta bata yi komai ba. So take a yi suna ta Ga nawa zata samu ta karbi abinsa zai bata ta sake order gumbar da ciccibin a wajen Hajiya Halima Mai..............

Sannan ta ga robar sanyi flusher da robar kazar sababi na Bojuwa herbs a kicin din Bilki ta tabbatar ingantattun kayane tunda ta gansu wajen Bilki. Tuni ta kwafe lambar a wayarta Sai ta shirya zata yi order din maijego package.

*Abuja*.

Bayan watanni uku.

Zuwa yanzu Bilki ta kammala iddarta. Ta ajiye tunanin komai tana zaune lafiya. Tana shan magani sai dai guda d'aya tak. Gabadaya an sauke ta daga kan sauran.

Daidai wannan lokacin aka yiwa Yaya Asad sauyin aiki an dawo da shi Kwamishinan Y'an sanda na birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.

Gabadaya gida ya kaure da murnar cigaban da ya sake samu tare da murnar zai baro fatakot gabadaya.

Amal da Noor sune kananu a gidan Momi suke, makarantarsu aka saka Farha.

Aysha babbar diyarsa barista ce bana ta kammala bar school ta Enugu.

Khadija da take biye da ita tana London tana karantar aikin had'a magunguna Phamarcy.

Hafcy ce a jamiar skyline ta Abuja tana ajin farko tana karantar aikin jarida.

Bilkisu yanzu zata kammala sakandire.

Ranar da ya bar fatakot da wuri ya sauka a Abuja bai je gidansa ba, kaitsaye gidan da muke ya dira. Ya gaida iyayensa.

Suka yi masa murna da fatan alheri.

Baba Babba ya ce "Yanzu a haka za'a yi bikin alherin da ya same ka babu iyali a tare da kai Abubakar?

Yanzu wa zai saka maka tauraron?"

Da murmushi ya ce "Baba hakuri zaka yi ka ara mini Momi ga kuma amaryarka Aysha shike nan ita da Momi sun wadatar."

Baba ya kaurara murya ya ce "Ka mayar da hankali akan batun aure. Iyayen matarka sun zo nan ya fi sau uku akan sun baka kanwarta ka ce sam kallon diya kake yi mata.

Nan makwabtanmu yarinyarsu ta nan ta kammala masters mahaifinta da kansa ya ce mini idan ba ka yi magana da wata ba, ka neme ta zai baka. Na yi maka magana ka ce na dakata kana cikin uzziri, yau kusan wata takwas da maganar amma ka k'i mayar da hankali."

Ya sunkuyar da kansa ya ce "A kara hak'uri Baba zan yi ne in sha Allah, a cigaba dai da yi mini addu'a."

Momi ta ce "Addu'a kam muna yi, daura niyyar auren ne baka yi ba. Kuma duk mukamin nan naka haka ake kallon ka fanko tunda baka da mace. Aure ai shine cikar darajar d'anadam ".

Haka dai suka yi ta yi har suka gaji dan kansu. Ya basu hakuri kamar yadda yake musu kullum.

Bilki ita kad'ai a d'aki don daga Abida har Farha da junior basa nan, yara na makaranta, Abida na asibiti tunda a specialist hospital Abuja take aiki.

Ta yi wanka tana sanye da material din Malaysianfabrics ta yi Fes da ita Sai tashin k'amshi na alfarma take yi.

Alti ta turo kofar d'akin tare da fad'in "Mahmah in ji momi ki zo ku gaisa da yayanku".

Bata tambayi waye a cikin yayin nasu ba.

Don tun jiya ta ji Abida na fad'in Yaya Asad yau zai dawo Abuja gabad'aya.

Ta mike ta bude wadirof ta dauko k'aramin mayafin da ake sakawa da gown, wanda ya dace da material din.

Falon Baban ta dosa kaitsaye don tasan suna can.

Tana shiga idanuwansa suka fad'a cikin nata, tunda yana zaune a kujerar da take fuskantar mai shigowa.

Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta rasa yadda zata yi kamar ta juya ta koma d'akinta saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki. Gabadaya ya sake yi mata kwarjini.

Bata san ya aka yi ba kawai sai ta tsugunna har k'asa tana fad'in "Ina kwana Baban Bilkisu?"

Ya kasa amsawa domin bai so ta yi masa irin wannan gaisuwar ta k'ololuwar girmamawa ba. Yafi son irin wacce suke yi masa a dan risinar da kai kadan a gaishe shi, amma yanzu ta wani zube tamkar wadda take gaida Baba Babba ko wani tsohon dattijo.

Murya ba amo ya ce "Maigado ya jikin dai?"

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ta amsa masa da fad'in "Da sauk'i". Kanta na k'asa.

Baba Babba ya ce "Ah ta warke ita da take batun a samo mata aiki ta gaji da zama haka ".

Yaya Asad ya ce "Ah lallai Maigado ta warware na ji dad'in wannan batun.

Ɗauko mini duka takardunki, idan na nutsu sai mu ga yadda za'a yi."

Ta mike ta koma d'akinta dan ta taho da takardunta tunda da zata baro gidan Sahal a cikin akwatin ta sanyasu, a cikin akwatin kuma Alti ta hado mata kayan da taho da su nan.

Ya bita da kallon k'urillah, haka yake son mace ta bude ta k'asa. Duk da ya ga yanzu ta tsiyaye ba kamar yadda ya santa ba.

Ta dawo ta sake durk'ushen sannan ta bashi hannu biyu. Ya sake jin babu dadin yadda take yi masa.

Amma ya karɓa ya ajiye a gefensa.

Daga haka ta yi masa sallama sannan ta mik'e ta basu waje.

Da Abida ta dawo ta bata labarin Yaya Asad ya karbi cv dinta za'a samo mata aiki.

Abida ta ji dad'in don hakan alamace Bilki ta yi hak'uri ta bi hukuncin Baba na ba zata koma Katsina ba.

Yaya Farouk da shi ba maaikcin gwamnati ba ne kullum sai ya zo gidan ya taya ta hira. Suka sake shakuwa sosai. Duk sadda zai zo sai ya siyo mata abun da zata ci ko na amfani kuma mai tsada.

Idan ta zauna tana yawan tambayar kanta to shi a ina yake samun kudi ne? Tasan Ladi farm nan ne wajen aikinsa, yanzu kuma da bata hannunsa me yake yi ne?"

Rannan suna falo suna hira shi da ita da Alti don kuwa sosai suke dasawa shi da Alti.

A sanyaye ta ce "Yaya Farouku fad'a wai sana'ar me kake yi ne yanzu?"

Ya yi dariya ya ce "Bilkisu tawa! Ba cima kwance bane ni. Harkar crypto na yi, kinsan farkon harkar an samu kudi da dala, ina cikin wadanda suka yi harkar a farko suka samu alheri. Yanzu kuma Sai nake yin harkar canji.".

Ta murmusa tare da fad'in "Alhamdulillah na ji dad'i sosai, Allah ya taimakemu gabadaya ".

Ya ce "Ameen Maigado ".

Daga haka Alti ta tashi ta shiga kicin don d'ora sanwar dare don tunda ta zo ita take girkin gidan don kuwa Ubangiji ya yi mata baiwar iya girki."

Bilki ta kalle shi ta ce "Yaya Farouku akwia kayayyakina masu muhimmanci a Katsina. Sannan na bar motata, ina son na kwashe kayana a gidan dan a zuba y'an haya tunda dai ka yi zugar da Baba ya hau kai ya zauna ya hana ni komawa".

Ya yi dariya sosai ya ce"Kada ki damu sai Alti ta je su hadu da Anisa tunda yanzu ta koma Katsina da zama su hada miki kayan.

Mota kuma ki bar mata ki ce in jini, ke kuma ki zabi wacce kike so sai na siya miki".

Ya murmusa ta ce ", Allah yaya Farouk ka kama k'asa da yawa amma sai a yi ta dorawa Yaya Asad nauyi da yawa".

Ya kwashe da dariya sosai ya ce"Wa ya ce ya zo a farkon? Maigado yau d'ansanda kike karewa ki bar ni? Ba damuwa!

Ya fada yana jijjiga kai sosai.

Alamun ya yi fishi. Tana dariya sosai ta ce "Afuwan Yaya Farouku ai kasan ni da kai bata b'aci.".

Suka cigaba da hirarsu.

Wata d'aya da karɓar takardunta ya kawo mata upper ta samu aiki da hukumar tantace abinci da magunguna wato (Nafdac). Sosai ta yi murna. Ta fara zuwa wajen aikinta cikin nutsuwa sosai, komai ya daidaita mata dan yanzu ma an daina taya ta kwana daga ita sai Farha suke kwanciyarsu.

Kawai abin da ya takura ta d'aya ne, rashin mota a hannunta. Kullum da Abida suke fita ta ajiye ta.

Idan ma Abida ba morning zata yi ba, haka take tashi ta kaita wanda tasan k'arfin hali take yi domin tun farko Abida bata son a takure ta. Amma yadda Abida ta yi laushi take yi mata kirki abin har mamaki yake bawa Bilki, tausayinta take ji ko kuwa menene? Sannan ta lura Abida ta d'auki son duniya ta dorawa junior. Kowa ya lura da hakan Momi har fad'a take yi mata akan ta rage yadda ta makale shi a ranta.

Bilki dai tasan kowa na son d'anta amma abin Abidan babu sauk'i sai take ganin ko dan bata rayu da Farha bane ya sanya ta ɗorawa yaron dukkan soyayya. Don kuwa ko kad'an bata shiga al'amarin yarinyar tsakaninta da Farha kamar yadda take mu'amala da sauran ya'yan y'anuwa. Amma ko kusa ba ta jinginawa kanta ita.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai ta yi kamar ta fad'awa yaya Farouk batun motar da ya ce zai siya mata, tunda ya saka ta bayar da tata, har Anisa ta k'ira ta yi masa godiya. Sai kuma ta fasa tare da tunanin bai manta ba.

Rannan wajen karfe d'ayan dare ta tashi ta yi fitsari, ta fito a band'aki sai ta ga wayarta na haske. Sai da ta kwanta sannan ya dauki wayar ganin wasu lambobi a jere iri d'aya ta gane layine na mussaman.

Ta ajiye bata dauka ba.

Kafin ta yi tunanin waye mai layin, k'iran ya sake faɗowa wayarta.

Ta saka hannu ta amsa tare da kangawa a kunnenta.

Murya ba amo ta yi sallama.

Ya amsa ba alamun barci a muryarsa.

Gabanta ya buga Yaya Asad zai bugo mata waya da tsakar dare?"

Kafin ta samu amsar tambayarta.

Ta ji cikin wata irin ya ce "Maigado na tashe ki ko?"

A sanyaye ta ce"Ba komai".

Ya numfasa ya ce "Ya yanayin aikin ba kya samun matsala ko?"

"Ba wata matsala".

Ta ba shi amsa a takaice.

"Ya ce "Ma sha Allah! Dama zan tambaye ki ne wacce irin mota kiki so , don bana so ki dinga tahowa a taxi ba idan an tashi tunda na ga Abida ke kai ki da safe ko?"

"Eh ita ce, amma mun yi magana da Yaya Farouku zai siya mini. Ka bar ta na gode".

Ya sake tausasa harshe ya ce "Ga shi kuma na yi niyyar yi miki alheri Maigado. Shike nan sai ki had'a biyu, ko ki ce masa ya siya miki wani abin amma mota kam ni zan siya miki".

Abin alheri ya yi mata amma ko kusa bata ji dad'in alherin ba. Don kuwa ta tabbatar akwai abin da zai biyo ba.

A takaice ta ce"To na gode, Sai da safe ".

Ya sake yin k'asa da muryar ya ce "Ko za ki daure na turo miki hotunan motocin ta what'sapp ki zaba so nake a kawo miki da wuri "

Har cikin zuciyarta sai da ji nishin da ya yi kunne a kunnenta.

A kidime ta ce "To" tare da katse kiran zuciyarta na bugawa sosai.

A fili ta furta "Duk masifarka bana sonka, ba namijin da zan sake sa shi a zuciyata idan ba Yaya Farouku ba."

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Tsabar kidimar da ta shiga ya sanya bata bude what'sapp din ba. Sai da ta ga yana k'iranta ta what'sapp din sannan ta katse ta duba.

A zabure ta tashi ta zauna ganin motocin gararin da ya turo mata da zasu lashe millions of naira wai ta zabi wacce take so.

Ta murtsuke idanuwanta sosai dan ta sake gasgata ita Bilki ake yiwa tayin ta zabi guda cikin wadannan motocin?

Ta tabbatar dai ba gizo ba ne .

Sai ta rubuta masa wadannan duk sun yi mini yawa. Waɗanda basu kai wannan ba ta isa.

Ya ce "Amma tunda ba rokona kika yi ba, bai kamata na ce ga yadda nake so, ke kuma ki ce yadda kike so za'a yi ba ko?"

"Hakane"

Ta fad'a a takaice domin ta ji tamkar ya ji haushi ne.

"Kawai ki zabi kalar da kike so".

Ya fad'a cikin sigar umarni.

Maimakon ta yi masa voice irin yadda yake yi sai ta sake rubuta masa "Farar".

"Yauwa Maigadona! Na gode miki sosai Allah ya saka da alheri".

Tana mamakin jin godiyar da yake yi tamkar ba shine ya kamata ta yi masa godiyar ba. Ta jijjiga kai tana fad'in komai ma kake nufi ba yiwuwa zai yi ba dan ba kunyar wadda zaisa na k'wari kaina.

"Wai Maigadona!

Ta furta a bayyane.

Ta juya tana gyarawa Farha kwanciya.

Ta saki tsaki tare da fad'in "Ko ta ina na zama tasa?"

K'ira ya sake fadowa wayarta. Ta rasa yadda zata yi haka ta dauka akan dole.

"Maigado kin yi barcine?"

"A a Farha na gyara ta kwanta kan hannunta ".

"Sannu da kokari to"

Ta share tamkar bata ji ba.

Ya nisa ya ce "Maigado barci kike ji ne?"

Murya ba amo ta ce "um"

"To bari na k'yale ki haka nan, zamu yi magana da safe. Stay blessed".

Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo cikin sake mamakin sabbin hallayar da yaya Asad ya tsiro da shi zuwa gare ta, sai take jin wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara. Ita fa ba yarinya ba ce ta san manufarsa akanta kuma sai dai ya yi haƙuri ba zata taɓa sonsa ba, ba ruwanta da kuɗinsa balle muƙaminsa ya je wani waje ya nemo matar aure dan kuwa ita bai mata ba.

Tunda ga ranar yaya Asad kullum da daddare sai ya kirata yana kashe mata murya, tare da hilatarta. Ita dariya ma yake ba ta ɗauka

28 / 37