ta fita ba, ba za mu manta ba, don da yanzu ina tunano abubuwan da suka faru amma ina jin kamar a yau ne muka rasa Baba ƙarami. Mutuwa tana da d'açi, sannan mutuwa mai tonon asiri mutuwar Baba ƙarami ce ta yi sillar ta tarwatsewar gidanmu, kaina na saka a cikin tafukan hannayena duka biyu na sake fashe wa da kuka ina jin wani irin nauyi a samam k'irjin irin nauyin da na riƙa ji lokacin da gidanmu ya hirgitse, Ubangiji na ke fata da roƙo ya daidaita kan ahalina
Na cigaba da hakaito rayuwarmu washegari muka koma gidajenmu cikin sukuni da salama, sannan yanzu muna mgana da su sosai, barin ma Yaya Faruƙu yana yawan kirana saboda har gobe Yaya Faruƙu nawa ne, ina girmama karamcinsa a gare ni. Abida ma muna waya sosai sannan Yaya Sulaiman ma suna haɗa mu da shi, kuma jikinsa sai godiya yana ta samun sauƙi.
Ya Asad sati ɗaya ya yi ya juyo zuwa gida Nigeria. Abida da Yaya Faruƙu za su cigaba da zama tare da shi har sai an sallame shi, Abida ko an ce ta dawo ba za ta yarda ta dawo ba. Baba Babba ya ce a barta ta zauna ta samu ladan jinyar mijinta, ban ɗauka haka Abida ke son Yayana ba sai a wannan lokacin aikin ta ta ajiye ta ta tafi jinyar Yaya Sulaiman kuma da aknsa ya faɗa mini da jikinta da zuciyarta take wahala da shi, kusan ita ke yi masa komai sai na ji tausayinta ya kama ni, shi da man Yaya Faruƙu Ladi farm ne kuma ba matsala akwai masu kula da wajen shi ya sa ba shi da wata matsala.
Gabaɗayanmu mun koma bakin aikinmu tunda hankula sun kwanta ni kuma a gida na cigaba da karɓan aikin snacks sannan a bangaren aikina na W.H.O, mun cigaba da wayar waa da mata kai wajen kula da cikin da raino da kuma muhimmancin yin rigakafi ga yara bayan haihuwa.
Ba tare da shawara da kowa ba Baba Baaba ya fara tattara dukkan wata dukiyarsu shi da ɗan'uwansa idan a baya ba wanda ya san shiga da fitar dukiyarsu, yanzu mutuwa za ta yi sillar fallasar komai. Idan a baya dukiyarsu tana haɗe ne a waje ɗaya ba wanda yasan tsakaninsu yanzu dalilin mutuwa yasa dole komai ya bayyana, ya shiga har bangarenmu ya yi magana da Mami da Ansari tun da Yaya Sulaiman baya kusa.
Ya ce 'an fara tattara dukan abin da Baba ƙarami ya mutu ya bari idan an gama tattarawa lokacin su Yaya Sulaiman sun dawo za a zauna a raba gado domin a sauke masa nauyi, wannan maganar rabon gado, wannan gadon shine silar dambarwan da ta faru a gidanmu dambarwar da ta yi silar da na rasa Abida na rasa Ya Munnera.
Bansan da mganar ba Mami ta kira ni da kanta a waya tana faɗa mini abin da yake faruwa.
Sai na ji hawaye ya goce mini, yanzu shike nan mun rasa Baba ƙarami, har ga shi ana mganar rabon gado Allah sarki rayuwa Allah ya kyautata makwancinsa ranar yini na yi kamar marar lafiya. Baban Amrah yana can bangaren Hajiyarsu sai da ya shigo ne ya ganni zaune a falo na shiga zurfin tunani ban san ya shigo ba sai da na ji hannunsa a saman kafaɗata sannan na dawo hayyacina.
"Lafiyarki kuwa?
Ya faɗa yana kallona cikin kulawa, na sauke ajiyar zuciya idanuwana suka kawo ƙwallah, gidan da ma ya yi mini shuru yara sun tafi islamiya, Basma ce ta ce mini za ta shigo to ta kira ni ta ce ta fasa zuwa Baban Abdul ya yi baƙi sai dai zuwa gobe.
"Na sha faɗa miki ki daina zurfafawa kanki tunani. So kike na rasa ki na shiga uku?
Kalamansa na ƙarshe yasa sai da na yi dariya, kusa da ni ya zauna ya ɗan rumgumo ni da sigan lallashi yana ɗan buga bayana.
"Komai mai wuce wa ne, Allah ya jiƙan Baba,. Shi kuma Yaya Sulaiman da ikon Allah sun kusa dawowa"
Na gyaɗa masa kai cikin gamsuwa domin na yi lamo a jikinsa na kuma karɓi lallashinsa, ban san me yasa ba sai gani ina bashi labarin wayar mu da Mami, ina ƙoƙarin mai da hawayen da suka cika mini ƙwarmin idanuwana, amma ga mamakina sai da ya ɗago ni cikin nuna murnarsa kamar na ba shi labarin wani abin daɗi.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: "Ma sha Allah."
Ya faɗa yana kallona, na yi kasaƙe ina kallon sa, faɗa masa fa na ke yi mutuwar mahaifina ta dawo mini sabuwa saboda an yi maganar rabon gado, amma yana kallona da farinciki a muryansa har ya bayyana a saman fuskarsa.
"Gaskiya Baba Babba ya yi tunani kuma ya cika ɗanuwa na gari, gwara a raba a bawa kowa haƙƙinsa haka addini ya tanadar"
Ni dai har ya gama magana ya tashi, ban sake wani motsi ba me ya sa yake murna? Saboda na ce za a raba mana gado, a kullum al'amuran Baban Amrah mamaki yake ba ni, ba ya gyarawa kuskuransa sai ma ƙoƙarin sake wasu yake yi, ajiyar zuciya na sauke amma abin da ya yi ya tsaya mini cak a zuciyata sai dai ban iya faɗa wa kowa ba sai washegari da Maman Abdul ta zo, ban yi mata wata magana ba, saboda na
san ko na faɗa mata sharhi da magana kawai zan jawowa kaina ita da Abida har gobe ba sa iya boye adawarsu akan Baban Amrah shi yasa na yi shuru da bakina amma dai na ji daɗin zuwan ta mun yini tare muna hira kuma ta saka ni na saki jikina har na manta damuwata.
Tun daga lokacin da na yi ma Baban Amrah maganar rabon gado ya dame ni bini-bini sai ya tambaye ni wai ya ake ciki ne har yanzu ba a kiramu ba? Tun ina mamakinsa har na daina na gama fahimtarsa kuɗin kawai yake hange, tun da ranar ma muna karyawa a gaban yara yake ce mini." Kai gaskiya za ku sha kuɗi Balki, ko gidan gonar nan kaɗai ai sai ta yi miliyan dubu da doriya."
Kawai sai na saki baki ina kallonsa, au shi da man ya kwanta ne da gidan gona yana lissafin zan samu kuɗi ya sake komawa ya naɗe hannu ni kuma na sakin masa kuɗi ina masa hidima shi da ƴaƴansa da iyayensa, tun da na riga na sabar masa, a lokacin ban ba shi amsa ba sai da ya sake yi mini zancen kai tsaye na faɗa masa gaskiya.
"Gidan gonar da kake mgana ba ta Baba ƙarami ba ce shi kaɗai, duka dukiyar tare ne da na Baba Babba. Ko mu y'ayansu bamu san yadda dukiyar su take ba."
Tun daga nan na kashe masa baki amma duk da haka bai daina tambayata har yanzu Baba Babba bai kiramu ba?Ranar da daddare har mun kwanta ya sake yi mini mganar na harzuƙa na miƙe ina faɗin" Bai kiramu ba, don Allah Baban Amrah ka ƙyaleni da wannan maganar. Mu fa ba gado ba ne a gabanmu mutuwar mahaifinmu ta fi yi mana ɗaci, sannan lafiyar Yaya Sulaiman ta fi damunmu fiye da tunanin wani gado."
Ganin na buɗe masa wuta ina masifa sai ya yi ƙasa da murya yana faɗin" Sorry ni ma ai mutuwar tafi damuna amma ina so na ga an sauke ma Baba ƙarami nauyi, ai Allah ne ya ce a raba ko Bilkis? Kuma ke matata ce duk abin da ya shafe ki ai ya shafe ni."
Saboda haushinsa da ya kama ni ko magana ban yi masa ba na koma na kwanta na juya baya ya san ya yi laifi shi ya sa ya mirgino ta gefena yana kiran sunana, ta gefen kunina da dama yana yi mini raɗa, da ya ke ya iya kalamai sanyaya zuciya Idan ya so, tuni ya shawo kaina da azama muka tallafi juna sai dai kamar ko yaushe bai wani daɗe ba, ya matsa gefe ya fara barci ni kuma ya bar ni kwance cikin hawaye, na daɗe ina kallon shi ina tunanin wai haka sauran maza suke? Ba su damu da damuwar matansu ba sai kan su? Ban gane komai ba amma ba ni da yadda zan yi haka na ja jikina na shiga tiolet na yi wanka na tsarkake jikina na zo na sauya rigar barci na raɓe ta gefensa na kwanta ina tunanin makomar rayuwata, shike nan ni a haka zan ƙare, ba zan iya ɗorar da komai akan jin daɗin aure ba, a wajen ana mini kallon mace a cikin sahun matan da suka yi dacen samun gwarzon miji, kyakkwa Kuma marar hayaniys, ni kuma a cikin gida ni kaɗai na san inda ɗakina yake yi mini yoyo, na daɗe kafin barci ya kwashe ni cikin tunani da zullumi.
Tun da muka yi haka da Baban Amrah ya kiyaye ni da maganar rabon gado, nima jin Mami ba ta sake yi mini maganar ba, sai na cire abin a raina sai kwanaki biyu tsakani Ansari ya kira ni a waya yana faɗa mini wai Baba Babba shiru har yanzu bai ce komai ba? Takaici ya kama ni amma sanin da na yi Ansari da Mami bakinsu ɗaya akan komai shi yasa ban ɗora komai ba amma sai na ce masa" Mu yi hak'uri mu ba shi lokaci watakila bai gama tattara dukiyar..."
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Kawai sai Ansari ya tare ni da ce wa" To dukiyar me? Abu ga shi nan a bayyane ai ba a bukatar wani dogon zama."
Mamakin kalamanshi suka hana ni magana ban gama mamakin ba ya sake kwabo wata maganar.
"Wallahi idan ya sake ya cucemu ba za mu yi shuru ba, mun san komai babanmu na da kaso mai yawa a cikin dukiyar nan Mami ma ai ta faɗa.'
Ina jin ya ambaci Mami nasan daga bakinta maganar ta fara fitowa. Na yi maza na kame bakina tare da fadin "Allah ya kyauta "
Da azama ya ce "Malama saura a zo batun rabon gado wata magana ta taso ki waremu ki je kina marawa bare baya Wallahi kika yi kuskuren yin haka zamu cire ki a cikin jerin ƴan'uwanmu. Tunda ba ki da wayo ko kadan"
Ni dai ban ce komai ba har muka gama wayar jikina a sanyaye abin da na yi ta gudun faruwansa shi ne ya zo ya faru daga ƙarshe.
*Na ce kuna karatun nazari ko kuwa iya na nishadi kuke yi?*
*Wannan labarin gabadaya fa ban gina shi dan nishadi ba!*
*Dan haka a yi hakuri a nutsu a gane me nake son a fahimta.*
Na daɗe ina tauna maganganun Ansari a cikin zuciyata amma ban iya mgana da kowa ba Yaya Sulaiman ne zai taya ni ga shi kuma ba ya kusa duk da yana ta samun lafiya. Har an kunce karayarsa guda ɗaya muna saka ran dawowarsu nan da wata ɗaya. Amma ni kaɗai ba zan iya ba da Mami ba, balle ga Ansari shima ba shi da sauƙi in dai ga lamarin yan gidanmu ne. Mami dama tun Baba ƙarami na raye take da wannan adawar, bata samu ikon fitowa da ita bane. Ballatana yanzu da ba ya raye zata iya aikata komai, ina ta tsoro amma sai na dake, nake ta adduar Allah ya kaɗe fitina duk wata guguwar da za ta taso ta dumfari zuru'armu Allah ya yi kare mu da ita. Ashe ba zamu tsira daga wannan guguwar ba.
Ana cikin haka ne gutsiri tsomar ƴan'uwan Sahal a kaina ya fara isa ta, yanzu har ta kai a kan fuskata ake shaguɓa mini magana da ce wa na babbake komai, na sakawa d'anuwansu mutuwar zuciya, kamar ni ce na hana shi ya fita ya nemi aiki, shi ya zaɓarwa kansa zaman gida, amma ni ba ruwana a ciki. Daga baya har Hajiyarsa ma na ga ta sauya mini idan na shiga gaishet a bayan gaisuwa ba ta sake ce mini komai saɓanin a baya zamu zauna mu yi ta hira. Na fara fahimtar ta fara ɗaukan zugar ƴaƴanta akan ni ce sillar rasa aikin ɗanta yana zaune a gida, sun manta Allah ne meyi, gutsuri tsomarsu bai bai dame ni ba, don ban fasa fita aikina da uzurorina kuma ban fasa hidima da gidana da yara na ba, tunda saba ya ma zame mini jiki. Na lura burinsu ya samu aiki ya ƙaro aure, don na gane ban gama da shi ba, ni ko a raina na ce ai ba zai iya rike gida biyu ba, gida ɗayan ma ba iya rike shi ya yi ba ballantana biyun amma su duk ba zasu san haka ba, tun da wani sirrin a lulluɓe yake ko an bayyana ba kowa zai iya fahimtar haka ba.
Wayar da Ansari sati ɗaya ne tsakani Baba Babba da kan shi ya kira ni ya ce na nemi izini wajen megidana na zo Funtua ko kwana ɗaya ne yana son ganina. Hankalina ya tashi amma tunda ya tabbatar mini da komai lafiya sai na samu natsuwa, in tambayan Baban Amrah ya amince washegari ni kaɗai na taho funtua har Farha a gida na bar ta tare da Baban Amrah, sai da na isa gida na fahimci dukkan ƴan bangaremmu ne Baba Babba ya kira ba makawa akan maganar gadonmu ne, ilai ko haka ne, a falon Mami ya tara mu gabaɗayanmu, daga Yaya Hamida da a lokacin sun koma Kano da zama, sai ni da Ansari ne manya a wajen. Ko Momi bata shigo wannan zaman ba daga mu sai mahaifiyarmu sai Baba Baaba.
Bayan zama da addu'ar Rahma ga Baba ƙarami. Baba Babba ya fara jawabi kan dukiyarsu da take haɗe a dunk'ule.
Baba Babba ya sake tunasar damu basu raba gadon mahaifinsu ba, sannan ba su raba na mahaifiyarsu ba sun cure su waje ɗaya suna kasuwancinsu tare a lokacin kuma yarda da zumumci hadi da aminci ba su yi tunanin yin komai a rubuce ba, basu kuma taɓa tunanin wata rana mutuwa za ta gifta da har za a bukaci haka ba, to bayan zama da kuma ƙiyasun duka dukiyarsu ya yanke shawaran kawai za a
rabata gida uku ne, shi ya ɗau biyu tun da kason shi ya fi yawa a cikin duka samun su, sai sauran kashi ɗaya a barwa Baba ƙarami a rabata Ga iyalinsa.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sannan kuma gidan da muke ciki bangaren da muke halas malak ya zama mallakinmu shi kuma zai riƙe bangaren da suke ciki sannan ladi farm kuma za ta fito a cikin na shi sauran kaddarorin ne a matsayin na Baba ƙarami.
A wajen sai da Mami ta ce ba ta gane ladi farm zai tashi a na iyalan Baba ƙarami ba, ni ce na riƙa taɓa kafarta sai ba ta ƙara magana ba Ansari ma bai yi magana ba saboda ƙwarjinin Baba Babba, daga ƙarshe ya cr za mu jira dawowar su Sulaiman kafin a sake zama, kafin lokacin zai yi magana da wasu lauyoyi da malaman addini da zasu yi kiyasin dukiyar sai a taru waje ɗaya a raba komai cikin adalci. Baba Babba na fita daga bangarenmu Mami ta mike ta ce ba zai saɓu ba.
Ansari ma ya miƙe yana faɗin" Haba ji wata tsatsuniya Mami, yana nufin saboda zalunci mu fitar da mu za a yi daga ladi farm? Wannan ƙatuwar gidan gonar ne zai ce tashi ce ita kaɗai wannan ma ai ƙarya ne'
Mami na kaɗa kafa ta ce" Daman na san za a rina. Ai zalunci ya shirya dole ya ce haka. To wallahi Tallahi bai isa ba ko da za a yi sharia ne bai isa ya mallake wannan gidan gonar ba.."
Ansari ya kaɗa kai kafin ya ce" Tabbas Mami, sai dai a yi sharia har mahadi ya bayyana amma ba za mu yi shuru a cuce mu ba."
Ina zaune gefe na yi tagumi gabana na tsananta bugawa, ina tsoron kar wannan mganar ta kawo mana rabon kai a gabana Mami da Ansari suka gama yiwa sauran yan'uwana famfo suka hau suka zauna, nima kuma Mami ta dawo kaina ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"Shashasha na san daman ai ba za ki yi mgana ba. To ko za ki mutu wannan karon ba zan yi shuru a cuce ni a cuci ƴaƴana ba. Tun da suma dangina sun ware ni ba ni da kowa sai ku gwara ma ku haɗe kai domin mu taru mu yaƙe su mu kwato dukiyarmu."
Sai kawai na fashe da kuka kafin na ce" Haba Mami, haba don Allah wannan abin da kike yi sam bai dace ba."
A lokacin hannu ta saka ta bige mini baki tana faɗin" Za ki ce haka tunda an taɓo ubanki da danginsa, to bari ki ji yadda shima bai yi abin da ya dace ba mu ma kar ya yi tsammanin za mu yi abin da ya ce. Idan yana son gaskiya a raba komai gida biyu ya ɗau na shi kason ya bamu namu kason shike nan sai a zauna lafiya.
"Faƙat"
Ansari ya faɗa sauran ma suka mara masa baya ni ko cikin sharan hawaye na ce" ku tuna fa mahaifinmu ne ya rasu Mami ko takaba ba ki fita ba amma kina hayaniya da faɗa kan dukiyar? Dukiyar da shima wanda yatara ta yau ya tafi ya barta, kar ku manta in da ya tafi yau ko gobe cikinmu wani zai iya tafiya, kuma tsakani ga Allah munsan cewa Baba Babba ya fi Baba ƙarami kuɗi to ba zai zama dukiyarsu an yi raba dai-dai ba in har za mu yiwa junan mu adalci Mami"
Na karishe faɗa cikin ƙanƙantar da kaina amma bai sa Mami ta gane ba sai ma zagina da ta hai yi tana ce mini da ace ba a gida ta haife ni ba sai ta ce Momi ce uwata tsabar yadda bana ƙishinta a matsayinta na uwata. Ansari kuma kamar ya