Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   13 / 37

36K to 39K   out of 110.8K words

za ki iya haƙuri da shi ba? Kar ki manta shi kansa Baba ƙaramin nan da ya tara dukiyar da guminsa yau ina yake? Ba shi a duniya ya tafi ya barki, ya bar mu ya bar kowa na shi da duka dukiyarsa ba domin baya so ba, sai don wa'adinsa ya yi ba shi da yadda zai yi Mami."

Sai ya ga ta dukar da kanta ƙasa har a lokacin ba ta ce komai ba.

"Mami ki yi hakuri, ki sake yin hakuri, ki yiwa zumumci kara, ki sake kallon karamci da kirkin Baba Babba a gare mu. Mami ba kya tunanin wata rana duk tafiya zamu yi inda ya tafi? Me kika nema ne a duniyar nan? Me ya rage miki ne? Yau ko da a ce ba a bamu ko sisi daga cikin gadon Baba ƙarami ba, ba zamu tagayyara ba Allah ya rufa mana asiri, mene ne ba zamu yi miki ba? Ina aiki, Bilkina na aiki Hamida na cikin rufin asiri, haka Anisa, Saddiqa Nurse ce, sannan ga Ansari yana harkokinsa yana samun rufin asiri sai godiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Mami mene ne ba za mu yi miki ba? Wanne jin daɗin duniya kike bukata wanda ba za ki samu daga bangarenmu ba? Dan Allah Mami daure ki yi mana kawaici cikin zumuntar gidanmu.! Ko da ma cutarmu ya yi, Ubangiji ne alkali mafi adalci. Sannan albarkar da za ki dinga sanya mana kadai ta ishe mu arzikin duniya da lahira. Kada ki bari mu shiga cikin tarihi, kada ki janyo mu tozarta ki yi hakuri, ki k'ara hak'uri da sannu Ubangiji zai miki kyakkwan sakamako."

Ya ɗauka ta saduda ya dauka maganganunsa ya shige ta yadda ya ga ta yi shuru ba ta yi mgana ba ya ɗauka nasihar ya ɗauki kusan awa ɗaya yana yi mata tare da kalaman jan hankali sun shige ta ashe ba haka bane domin yana gama magana ta ɗago ta kalle sa sannan ta girgiza kai kafin ta ce" Sulaiman ke nan. Duk abin da za ka yi ba zan bar haƙkina ba. Cutarmu fa za su yi muna ji muna gani fa Sulaiman? Ko Annabi da kansa ya ce kar ka yadda a danne maka haƙkinka har sai idan lamarin ya fi ƙarfin ka, ni kuma bai fi ƙarfina ba shi yasa na tsaya kai da fata akan sai an ƙwato mana haƙkinmu."

"Mami!

Sulaiman ya kira sunanta cikin sarewa, sai kawai ta ɗaga masa hannu kafin ta ce" idan har kana so ka yi albarka kar ka sake zuwa dakina da wannan maganar. Wallahi Tallahi bazan janye wannan ƙarar ba sai alƙali ya kwato mana haƙƙinmu, su da suka yi zaluncin ba su yi nadama ba sai mu ne da suka danne wa haƙƙinmu? Ko kuwa haƙilon da kuke yi kai da Bilki na kar a ɓata musu, su kun ga suna yin haka akan ku? Sun fi ku wayo, domin kansu suka sani kafin ku. Idan ma za ku dawo cikinmu ku dawo, ni ɗin nan dai ni ce na kawo ku duniya ba Momi da Alhaji Babba ba"

Ta fada cikin sake jadadda masa, cewa ita ce fa mahaifiyarsu kar su manta da haka.

Cikin ƙasƙantar da kai Sulaiman ya ce" Mami ba kya tunanin yadda rayuwata za ta ƙare? Tunda na dawo ban sake samun natsuwa ba. Abida ta yi nesa da ganina, ba kya tunanin bayan yankewar zumunci har da taɓarɓarewar aurena da Abida a cikin yunkurinki?

Kai tsaye Mami ta ce" Sai dai in ba ta sonka. In tana son ka za ta zauna da kai ko da zumuncin ya yanke. Ko da yake ta fi ka sanin ciwon kanta za ta zaɓi ahalinta ne sama da kai. Kaima sai ka yi irin yadda ta yi."

Kasa magana ya yi, rauni ya mamaye shi hawaye sun kawo a ƙwarmin idanuwansa amma bai bari sun zuba ba, ya yi saurin mayar da su, haka ya miƙe yana layi kafin ya ce" Shike nan Mami. Shike nan ba zan sake ce wa komai ba."

Daga haka ya fice daga ɗakin nata ta kara shi da harara tana mai faɗin" Sakarai kawai dama nasan akan shedaniyar yarinyar nan kake wannan kai kawon to sai Dai auren naku ya lalace a hakan. Ja'irar yarinya mai bakar fuska da bakar zuciya".

Fitarsa haraba ya haɗu da Ya Usman da Muneera zasu fita a mota ya yi ƙokarin yiwa Usman Sallama amma bai amsa shi ba sai Muneera ce har ta wuce sai ta dawo.

Yaya Sulaiman ya ƙarfin jikin?

A sanyaye ya amsa mata da ya ji sauƙi, sai ta kaɗai kafin ta ce" Allah ya kara lafiya."

Yana so ya yi magana amma ba ta tsaya sauraransa ba ta yi gaba Usman ya daɗe da barin wajen, ya daɗe a tsaye yana nazarin rayuwa har sabo ya yi zuciyarsa na kitsa masa me yasa ya dawo kasar? Ko me yasa ya rayu shima bai mutu kamar Baba ƙarami ba? Da ace bai rayu ba da yau bai ga wannan baƙin cikin da tashin hankali ba, yana jan ƙafa ya karisa bangarensu shi da Abida da ya kasance fanko tunda jiya da yau ma ko kwanan bata zo ta yi ba.

Yasan wace ce Abida ba zata tab'a sauraransa ba yanzu wataƙila sai an gama wannan shariar sai ta yanke hukunci. Kuma hukuncinta dai dai da yake da rabuwa da shi, in dai Abidar da ya sani ce mai tsauri da ra'ayin rik'au ce.

Bai san yana hawaye ba sai da ya ji suna sauka daga saman fuskar shi, ashe wai kuka yake yi, kukan rashin Baba ƙarami, kukan rashin bango kamarsa, komai ma ya yi masa tsaye cak ya kuma rasa tunanin da zai yi, ya riga ya gama sarewa da lamarin Mami tun da ta sake rantsewa to tana nan akan bakanta. A ranar ma lauyan da suka ɗauka ya zo gidan shi da Ansari sun yi magana da Mami ba fashi ranar 20 ga wata za a yi zaman farko kamar yadda aka rubuta a takardun ƙaran.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Sai kawai ya sare ya yi saranda da cewa Mami sai ta cika muradinta kuma gashi ta ɗauki hanyar cikawa, ya daina mata magiya ya yi shuru da bakinsa ya koma zura musu ido ita da Ansari kamar yadda ya ce shike nan ba zai ƙara mganar haka ne ya faru bai sake ce musu komai ba.

*Dakin Baba Babba.*

Daga shi sai Munira zaune suke tsawon lokaci bai ce komai ba, duk da shi ya bukaci ta shigo har cikin dakin barcinsa, ya kuma ce da Momi ta basu waje. Munira kuwa bata ce komai ba, tana zaune tana dakonsa zuciyarta cike da tausayinsa, ta tabbatar yana cikin rudani da rashin sukunin zuciya mai yawa.

Da matukar rauni a zuciyarsa ya ce "Abin da tashin hankali Munira. Ace ni zan yi shari'a da ya'yan Isa? Hakan kuma bai isa ba sai na sake ba ki damar ki ba ni kariya su kuma ki barsu?".

Hawaye ya k'wace musu gabad'aya. Ya ce "Kaf ya'yan da muka haifa daga ku har su Bilki babu wanda Baba karami ya ja a jikinsa irin ki hatta sunanki shi ya zaba miki. Kin sani kin girma sosia bai daina yawo da ke ba. Yanzu da kika tafi wata k'asa duk taron da zamu yi shi yake tunowa da ke ya ce a lalubo ki a waya, a gaishe ki. Ko ya'yansa idan ya haifesu baya tab'a tsayawa wajen me za'a yi tunda yasan zan yi komai. Amma haihuwarki ba rawar jikin da bai yi ba. Dan haka ni ba zan je kotu ba, balle ki saka rigarki da rabin ilimin da ya ba ki damar sanyata daga aljihunsa suka fito.

Ta numfasa ta ce "Baba dole zaka je kotu domin a k'aida idan an yi k'arar mutum har kotu ta kawo masa sammaci sai ya girmama kotu ya je idan ya so sai ya gabatar da uzzirinsa sannan ya janye daga k'arar ".

Ya numfasa ya ce "To ku dauko wani lauyan Munira, bana son ki ba ni kariya bisa son zuciya, bana son iliminki ya yi mini amfani ni kadai ban da Babanku ".

Ta yi k'asa da kai domin tausayin mahaifinsa ya mata dabaibayi k'warai da gaske don kuwa jarabawar rashin Baba karami kadai idan an bar shi da ita ta ishe shi radadin zuciya bare kuma wannan bala'in da ya gitto.

A tausashe ta ce lokacin daukar wani lauyan ya k'ure, gobe ne zaman.

Ka kwantar da hankalinka komai za'a yi bisa gaskiya da k'aida, ina maka alakawarin abin da zai biyo baya wanda zaka gamsu ne".

Ya kada kai ya ce "Allah dai ya shiga lamarin kawai amma al'amarin ya b'aci. Sai dai na fahimci kuskuren da muka yi ne Allah ya bawa shaidan damar shigowa cikin zumuntarmu.16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Katsina.

Ranar ashirin ga wata ta kama ranar da za a yi zama akan shari'ar a babban kotun dake cikin garin Katsina. Tun asuba wayar Mami ta tashe ni daga barci faɗa mini take yi yau ne ranar shiga kotu na tabbatar da na samu hallata, ba ni da yadda zan yi na amsa mata.

Baban Amra dama yana sane da ranar tun da suna wayar da Ansari tun safen ya yi mini magana ban dai ce masa komai ba tunda ko na hana shi zuwa yasan hanya zai iya zuwa shi yasa ban ma tsaya b'ata wa kaina lokaci wajen yi masa bayanin ba sai ya je ba.

Na kira Ya Sulaiman a waya ya tabbatar suna hanyar tahowa Katsina shi da Mami da Ansari, sai na ji nima na gama sarewa dole kanwar naƙi na shirya bayan yara sun tafi makaranta na shiga bangaren Hajiya na yi mata sallama na ji tana mini zancen shariarmu da za a fara yau.

"Bilki ashe kuma haka gida ya rikice! Sahal ya faɗa mini na ce lamarin dai bai yi daɗi ba "

Sai ga ni zaune gaban Hajiya ina ta faman yaƙe, shi yasa ban so Ansari ya saka Baban Amrah cikin maganarmu, ga shi nan ya zo ya barbaɗamu wa ma ya sani ma ko duka ƴan'uwansa, sun ji labari tun da dai ga shi a bakin Hajiya.

"Allah ya kyauta na gaba. Amma shi ma dai wan baban naku ya so kansa duk uban gidan gonar nan da ake labarinta a garin Funtua da jihar Katsina gabad'aya ya ce tasa ce shi kaɗai? Yin shari'ar ma yana da amfani saboda a fiddo muku da haƙkinku"

Ni dai ba baka sai kunne, na kasa mgana kaina na kasa kunya duk ya kama ni ke nan komai da komai na sirrinmu Baban Amrah ya gama barbaɗa mu a gari amma ba laifinsa bane, laifin ƴan'uwana ne su suka jawo mini wannan tozarcin.

Bayan na yi mata sallama zan tafi ta bi ni da faɗin" Allah ya ba ku sa'a Bilki. In sha Allahu kune da nasara."

Ta san ranar za mu fara zaman kotu ashe, ni ina can ina arowa kaina jarumta da sunan kar dangin mijina su fahimci akwai matsala ashe aikin banza na ke yi Baban Amrah ya gama kwance mini zani a kasuwa ban sani ba.

Tare muka tafi da shi, shi yasa ni ko magana ban yarda ta haɗa mu ba, shine yake ta maganganunsa yana faɗa mini In sha Allahu mune da nasara ya san lauyan da muka ɗauka Barrister Jibril Hadi, senior din su ne a makarata guri ne yasan kan aikin shi kuma ai muna da hujoji ni dai kala ban ce masa saboda a lokacin jin kaina na ke yi kamar ba ni ba komai, na duniyar nan baya yi mini daɗi, har muka isa cikin kotun nan da misalin goma da rabi na safiya lokacin su Mami ba su iso ba sannan ana gudanar da wata sharia ne, wanda daga shi sai tamu shari'ar, muna haraban kotun motar Ya Usman ta fara shigowa bayan ta kuma ta Yaya Faruƙu ce. Kafafuwana sun kasa ɗaukata daga in da nake sai da na jingina da bangon wajen.

Baba Babba tare da Momi da Abida a motar Ya Usman. Ya Muneera da take sanye da rigar ta lauyoyi a motar Ya Faruku. Babu Ya Asad watakila bai samu zuwa ba, sun ganni nima na gan su, ina son na ƙarisa na je na gaishe da Baba Babba amma kunya da nauyin sun k'i barina kuma ma kafafuwana ba za su iya ɗaukata ba rawa suke yi, Abida ma ta ganni ta ɗauke kai ta gabanmu suka bi suka wuce kamar ma ba su taɓa sanina ba. Baban Amra ba ya wajen yana can gefe suna mgana da wani lauya, shigar su ba daɗewa sai ga motar Ansari ta shigo wajen Mami da Ya Sulaiman suka fito. Mami fuskarta ba damuwa ita da Ansari Ya Sulaiman ne kamar ni mun yi zuru zuru. Wai ashe lauyan da Baban Amrah ke magana da shi lauyan da su Mami suka ɗauka ne sai da na ga sun k'ariso wajen ya gaishe da Mami yana sake gabatar da kansa.

"Barista. Kana da tabbacin za mu yi nasara?

Mami ta tambaya tana mai kallon Barista, ya karkace da rigar shi ta lauyoyi yana fadin" In sha Allahu Hajiya. Ai muna da hujojji masu k'arfi, kuma ma shari'ar bata da tsawo ba za ta ɗauke mu lokaci mai yawa ba."

Mami ta jinjina kai Ansari ya dafa kafadanta yana mai ce wa" Ba ki da matsala Mami Barr Jibril ya san kan aikin shi."

Ni da Ya Sulaiman muna gefe kamar ruwa ya cin ye mu, lauyan ya fara shiga ba daɗewa aka sallami masu ƙara na ciki sai ya fito ya ce mu shigo mu ne akan layi, gamu ga su Abida amma ba wanda ya nuna yasan kowa a cikinmu sai dai ana kallon kallo kowa ya ɗauke kansa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: A wajen zaman kowa da rukuninsu, bayan an karanto k'ara da gabatarwa ga lauyoyin masu k'ara da masu karewa aka fara shari'a, ni tun da aka fara na ke shatatan hawaye ina kallon Baba Babba ma yana ta sharan k'walla da haɓan babban rigan shi, tun ballatana da Lauyan mu ya gayyace shi tsayuwa a ɗan akwatin nan na masu ba da shaida, ya yi masa tambayoyi akan dukiyarsu da take haɗe da ta Baba ƙarami. Nan ma ya yi duka jawabin komai kamar yadda yake a farko, yadda lauyan ke jifan Baba Babba da cuta garemu ya sake kunyata ni sai da Ya Muneera ta mik'e ta yi mgana sannan alk'ali ya dakatar da Barr. Jibril, an gabatar da dukkan hujojji. Sannan yaya Muneera ta gabatar da takardun shaidar cewa filin Ladi farm ta Baba Babba ce, mu ma daga bangaren mu Lauyanmu ya gabatar da cewa komai na dukiya tare ne, kuma har Baba k'arami ya rasu bai taba ce wa ladi farm babu guminsa a ciki, haka Mami ta ce da Lauya ya gayyace ta, bayan gama haɗa duka shaidu a waje ɗaya sai ya ce ya ɗaga sake saurara ƙara zuwa 21 ga watan gobe kuma zai zama ranar ƙarshe da za a yanke hukunci.

Har aka tashi zaman kotun nan kuka na ke yi, a gaban idanuwanmu su Abida suka shisshiga mota suka bar haraban kotun amma da alamu kamar Baba Babba jikinsa ya tashi, domin Yaya Faruƙu da Momi na riƙe da shi lokacin da zai shiga mota, daga kotun muka rabu da su Mami.

Ni da Baban Amra muka koma gida ina shiga gida na rufe kaina a ɗaki ina ta faman kuka. Na shiga dimuwa mara misaltuwa, na shiga tashin hankali da yasa bana iya barci komai nawa ya tsaya cak, duk na rame na lalace saboda zullumi da tunani.

Ya Sulaiman ma a can Funtua komai ya dak'ule, domin ya sanar da ni cewa Baba Babba ba lafiya suna dawowa gida a ranar da aka yi zaman kotu yana zaune a kan kujera ya ƙame dumfara ta dinga fita ta bakinsa tare da karkacewa. An kai shi asibitin cikin garin Funtua kwana ɗaya ya yi Ya Asad ya iso suka ɗauke shi zuwa speacialist hospital Abuja.

Ni dai ba abin da nake yi sai Allah ya yayyafawa matsalar wuta. Ya huci zuciyarsu Abida, don kuwa a bayyane yake ita da Usman a shirye suke a yi yak'in basasa.

Ranar har sai da Baban Amrah ya farka jin ina cewa Allah ya sassauta fushin Abida!

Tsaki ya yi kafin ya ce" Mtsewww, ke yanzu ba ki damu da damuwar Mami ba sai na wata can Abida? An ya Bily haka Abidar nan ta bar ki? Ita fa bata ko damu da ke ba, ta bi bayan ƴan'uwanta amma ke kina nan kin kasa sukuni saboda su."

Har ya gama maganarsa ban ce masa komai ba, ai tun da ba gidan su yake faruwa komai ma zai iya cewa, tun da ba zuruan Hajiya ba ne suka tarwatse ba ai ya ce haka, ba zai taba gane yanayin ba tun ba bashi ne a cikin tashin hankalin da nake ciki ba, daga karshe ma ɗakin na bar masa ban sake yarda mun yi wata mgana da shi ba, ni kunyar fita ma na ke yi sai na ke ganin kowa yasan abin da ke faruwa za a dinga nuna ni a matsayin wacce mahaifiyarta ta tayar da hargitsi saboda gado.

A can ma Funtua an ce gari ya ɗauka ana ta mganganu marasa dadi tun da labari ya zaga ko'ina da cewa mun kai k'arar wan ubanmi saboda gado, kowa na kallon mu a waɗanda ba su kyauta ba wasu kuma suna ganin cewa ba a yi mana adalci ba ne shi ya sa abin ya kai zuwa gaban alƙali. Dama yanzu kowa albarkacin bakin shi zai faɗa, tunda sanin gaskiyan sai Allah sai kuma mu da muka san mafarin komai.

Har ranar zaman kotu ta zagayo ban sake barci cikin salama ba, daga Abuja su Abida suka taho Baba Babba a kan

13 / 37