tsawo ba ta sake haɗa mu ba, washegarin Baba Babba ya sake yiwa yaro huduba da sunan Sulaiman.
Addu'a sosai momi da baba Babba suka yi mini a lokacin da suka ga kayan da na kawo.
Baba ya ce "Faruk ma ya ce Ansari ya turo kud'i wai a sayi raguna guda biyu. Allah ya yi muku albarka."
Duk yadda Abida bata sakar mini jiki ba, ban tafi ba sai da aka yi walimar suna da ni. Duk da ba gayya aka yi ba, iyakacin matar Yaya Asad ne da iso ana gobe suna ita da iyalin ta, gabad'aya na ga mata ta sauya mazaunai da kirji sun cika dam, fatarta ta goge ta zama tamkar wata half-caste. Na shiga tunanin dama Anty zata yi Kiba ne? Ni da nasanta siririya doguwar mace sannan bata da manyan mazaunai haka nan kananun nono gareta. Amma tsabar kudi da daula ne ya sanya tashi guda ta zama haka ko kuwa surgery aka yi mata? Ni sai na ga har k'uruciya ta kara. Don ba zaka ce ita ta haifi manyan yanmatan mata, alhalin da har gulmar mijinta ya fita k'uruciya muke yi ni da Abida. Ya'yanta su Aysha sun zama manyan y'anmata sosai hatta Bilkisu mai sunan tana aji biyar a sakandire ta dinga murnar ganina don duk salla sai na aika mata kayan sallah masu tsadar gaske.
Kan dole na kunshe mamakina akan sauyawar matar Yaya Asad tunda abokiyar gulmar ba wani sakewa ta yi da ni ba. Daga matar Yaya Farouk da ta Yaya Usman shikenan sai ya'yansu sai ni da nawa yaran muka yi walimar sunan cikin nutsuwa. Abida bata yi wata kwalliya ba gabadaya ma bata da kuzari duk y'anuwanta da matansu kamar zasu hadiye ta tsabar nuna kulawa da soyayya amma gata nan babu walwala wanda kowa ya gane rashin uban danta ke nukurƙusanta duk da bata furta ba.
Ni dai addu'ata da fatana idan Ya Sulaiman na raye Allah ya dawo da shi gida lafiya.
Anty Rukayya matar Yaya Asad ta zata je ganin sabon gidansu da ake kan ginawa ta ce 'Na shirya mu je tare, duk da bana son zuwa amma haka na daure na bita ban watsa mata k'asa a ido ba a lokacin na fahimci kamar anty Rukayya da Abida babu jituwa a tsakaninsu.
Unguwar Asokoro muka je, duk yadda ake labarin kuɗin Yaya Asad ban zaci sun kai haka ba. Don kuwa mallakar gida k'arami a Asokoro ma ai sai manyan masu kudi bare wani rafkeken gida na garari. Na daga kai ina kallon ginin wannan kam zai yi hawa hud'u zuwa biyar.
"Dankari mankari"
Na furta a fili.
Muka nutsa cikin gidan da masu aikin suke ta faman aikinsu mafi yawa masu jajayen kunnuwa ne suke jagorantar aikin.
Na ce "Anty Rukayya ina miki fatan a lahira ma ki samu dandasheshen gida a gidan aljanna, don a duniya kam kin samu".
D'adi ya kamata ta murmusa ta ce "Ameen Maigado ke ma ya miki fiye da haka anan duniya da kuma lahira"
"Ameen yayata in sha Allah idan zaku dawo ki fad'a mini takanas zan zo a yi tariya da ni ".
Da sauri ta ce "In sha Allahu kuwa zan fada miki Maigado duk da sai next year zamu bar fatakot, amma dai zan sanar miki idan lokacin ya zo"
Ko fenti ba'a yi ba da saka kofofi gida ya fito ya yi ras ina idan ya sha fenti da kaya na alfarma?
Bayan shekara muka yi bikin Ansari tunda yana aikinsa yana kuma juya kud'insa. Funtua muka yi bikin dangin Mami sune suka zama gatanmu, don kuwa sun zo sun cika mana gida basu barmu mu kad'ai ba. Baba Babba da Ya Farouk sun zo daurin auren shi ya yi walicci tunda har Abuja ya je ya gaishe shi ya sanar masa. Momi ma da ita aka yi bikin amma ban da Abida ba ta zo ba, wai tana fatakot tunda watanni biyar Kenan Yaya Asad ya zama kwamishinan y'an sanda na jihar River's. An yi biki lafiya an tashi lafiya ni ce na zama kamar uwa a wajen tun da ba Ya Sulaiman sannan ita kuma Ya Hamida duk abin da ta ga na saka hannu sai ta zare jikinta a ciki, ina can Funtua Baban Amra ya kira ni da albishir ya samu aiki a jamiar da nake koyarwa ta marigayi UMARU MUSA Y'AR ADUWA. A matsayin non acadamic staff, dama na ji ana ta batun zasu ɗebi sabbin ma'aikata a wannan shekarar na yi masa murna sosai. Ina komawa Katsina na sake yi masa murna baki da baki.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ina ayyana yanzu sai ƴan'uwansa su daina k'ullata na, har gida suka zo taya shi murna ni kuma na yi musu girke-girke da kayan Snaack, sai habaici suke yi a fakaice ban biye musu ba domin ni yanzu irin matsalolin nan sun daina ɓata mini rai. Baban Amra ya yi farimciki da samun aikin har hakan ma ya nuna a saman fuskar shi ni kaina na taya shi murna a matsayin magidanci zama ba aiki ba bu daɗi sam.
Ɗan'uwan Baban Amra zai siyar da filinsa da yake jikin nasa sai ya kawo masa talla, shi kuma Baban amarah ba shi da kuɗin siya. Sai ya yi mini ta yin siyan filin ni kuma lokacin ba ni da kuɗi a hannuna sai dai kadarori. Shiyasa ban siya ba sai daga baya Baban Amra yake fad'a mini ai fili yanzu ya zama nasa tunda ya siyar masa da b'angaren Hajiya shi kuma sai ya bashi filin ya yi masa ciko, tunda filin yana da girma sannn unguwar ta yi daraja sosia shiyasa ma Baban Amra ya dage ya mallak. An yi rubutu da shaidu da komai kowa ya saka hannu tare da ajiye takardar shaida a wajensa.
Wani irin kwantar da kai ya fara mini a kwanakin nan ne, wani irin ji da ni Baban Amra yake yi, soyayyar da ko a farkon aurenku bai gwada mini irinta ba, hatta wanka ma sai ya ce tare zamu yi, ya cuda ni , na cuda shi. Duk dare ya cika ni da kalamai da ƙauna. A da sai mu yi wata wani abu bai shiga tsakanin mu ba amma kwanaki nan a akai akai sai ya nema abin nasa har mamaki yake ba ni, yana kokarinsa wajen ganin ya gamsar da ni. Hankalina ya Fara kwanciya nutsuwar da ta yi mini tustu na Fara samun sauki a zuciyata da gangar jikina. Sosai hankalina ya kwnaata har nake tunanin rashin samun attention din Sahal shine kan gaba a wajen wargajewar walwalata.
Wajen aikinmu daya amma Shi yawanci da safe yake fita yayin da ni ba kullum nake fita da safe ba sai idan ina da darasin safe. Idan mun fita tare shi yake ɗaukar mini jaka, idan na ce ya bari kar a fara ce masa mijin Hajiya.
Murmushi yake yi ya ce ai ya daɗe da zama haka, ni ko farinciki ya cika ni na samu kwanciyar hankali ana cikin haka ya bijiro mini da maganar ya kamata mu fara gina wannan filin muyi kyakyawan muhallin da zamu nuna, kuma mu k'arishe rayuwarmu da ya'yanmu a cikinsa. Da kalamansa da soyayyarsa ya yi amfani ya ruɗe ni, na siyar da filina guda guda biyu, ɗaya da shi aka zagaye filin kuɗin dayan kuma aka fara kafa foundaton ɗin gini da shi, sannan akwai ruwan kuɗi a cikin account ɗina duk na tattara na bashi, tunda mu zai yiwa ginin domin farincikinmu shi yasa ban ji k'yashi ko kokonton bashi ba.
Da haka aka fitar da gini, mai hawa uku ginin ne na alfarma na k'asaita aka kai linta aka zuba dakin aka dora sama aka sake zuba dakin aka dora Hawa na uku kaso saba'in da kudadena ake ginin. Tunda aka yi rufi sai ginin ya tsaya amma a hankali a hankali ana cigaba da aiki ni da shi duk kudadenmu anan suke ƙarewa, barin ma ni duk dukiyata da wasu kaddarorina sun tafi a wannan ginin gumin sana'anata da albashina sun tafi anan sannan har gobe ni ce nake ɗaukar nauyinmu gabaɗaya.
Komai ni nake yiwaa kaina da ƴa'ƴana ban damu ba. Don mantawa nake yi yana da aiki. Na sake shiriricewa da shi da na ga ya karbi car loan ana cirewa a albashinsa ya siyar da motarsa tunda ta tsufa ya sayi sabuwa mai kyau, sannan yana siyan wani abu a harkar gini dan haka nasan ba shi da wani kudi.
Sannu a hankali gida ya hattama fenti da tayals suak rage da kayan band'aki, murna muke yi sosai don kuwa yadda muka tanfatsa gini irin wannan munsan hucewar Ubangiji ce. Duk da muna ganin sauara ne kadan ya rage amma kafin a kammala din ba kananun kudi kudi zai sake had'iyewa ba. Sai dai kuma a hankali zamu yi har mu hattama.
Sannu a hankali sai nake ganin sauyuka tare da shi, ya fara kaffa kaffa da wayarsa, haka nan yana yawan wuce lokutan dawowarsa gida. Sannan ɗan soyayyar nan yanzu duk babu magana ɗaya biyu sai ya kulle bakinsa yafi mayar da hankali kan wayarsa. Tunda ya samu aiki sai muka yanke shawara ya dinga tafiya da Amrah tunda makarantar ta a hanyar makarantarmu take. Ni kuma na dinga kaisu Farha tunda Mafi yawa ba sassafe nake fita ba. Amma shi tun safe sai yammacin zai gama.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Dan haka sai yake tafiya da ita idan zai dawo sai ya daukota tunda itama sai yamma. Baya son ta dawo gida ita kad'ai . Duk sai runtsi ya daukota ya kawota sannan ya sake fita. Amma tunda ya k'ulla abota da waya da rashin zaman gida sai ya fara bata umarnin ta hau abin hawa ta dawo duk da ba kullum yake yin haka ba.
Sannan yanzu ungulu ta koma gidanta na tsammiya sai ya shafe satttika bai neme ni ba.
Kwata kwata hankalinsa da rayuwarsa, sun koma kan wayarsa na fara zargin akwai abin da ke ɗauke masa hankali.
Gabaɗaya na susuce na shiga damuwa, kuma ni daman damuwata na bayyana a saman fuskata.
Sannu a hankali na fara gasgata maganganun Abida. Na yarda da batun Basma a gare ni, da irin fadan da ta mini kamar ta dake ni lokacin da na ke faɗa mata duk kuɗaɗena sun k'are wajen ginin da muke yi, ta yi ta mini faɗan cewa ni ce zan ɗauki ɗawainiyar miji sannan na yi na ya'yansa, na yi masa ginin gidan da zai zauna, na ga hakan ya kamata?
A lokacin duk ban hangowa kaina matsala ba, sai ma ce mata da na yi" Ni ban Ga abin damuwa ko rashin dacewa ba. Ni da ya'yana ne fa kawai to menene ribata dan ban taimake shi mun yi rayuwa mai kyau ba?"
A lokacin kasa magana ta yi, sai yanzu da nake ganin abubuwa na lalacewa maganganunta suke dawo mini a cikin kaina, na shiga damuwa ba mai rarrashina ku'ncin zuciya suka haifar mini da ciwon kai da jiri sai da na je na ga likita faɗa ya yi mini da cewa jinina ya hau sannan ina saka damuwa a raina deperession na neman ya kamani zan kashe kaina, jin haka sai hankalina ya tashi, daga asibiti gidan Basma na wuce na je mata da kuka Sai Dai na kasa bayyana mata halin da nake ciki sai ita ce ta zargi kukan da nake yi bana komai bane na kuttun mijine.
Takaici ya kama Basma ta rufe da faɗa" Ai da man na faɗa ki, ba ki da wayo ba ki yi shawara da kowa ba kika kwashe dukiyarki ki ka narkawa miji yana kwance kina masa komai ai dole ya yi miki wulakanci yanzu ba ki san me gobe za ta haifar ba? Ni dama nasan ba zaku kwashe kalau ba."
Na shiga tashin hankali ganin haka yasa ta sassauta ta shiga lallashina hakuri zan yi domin koma mene ne ya riga ya faru, tun daga lokacin Basma ke kula da ni tana yawan zuwa gidana ta duba ni a cewarta in ta k'yale ni takaicin namiji zai iya sakawa na hadu da stroke, kuma gaskiya ta faɗa Sahal na neman gigita mini duniyata k'warai da gaske. Haka siddan kuma ya d'ora mata karan tsana idan ta zo gidan ya dinga kunci ke nan. Har ta kai ya fara fad'in bata nufinsa da alheri Nima kuma ba sona take yi ba tunda tana son kashe mini aure.
Munafukace tana son raba aure.
Wulakanci iri iri ba wanda ba ya yi mini, amma ba wulakanci na kai tsaye ba, a a wani irin wulakanci mai susuta zuciyar yaya mata. Ba ruwansa da na yi kwalliya ko ban yi ba, baya daukar damuwata da muhimmanci, idan na masa magana zai kula ni, idan ban masa ba yana tare da wayarsa cikin jin annushuwa. Tunda ya samu aiki ba zance ga ranar da ya shigo da wani abu a leda a matsayinsa na maigidanci ba.
Duk da haka ban tab'a k'alubalantarsa ba.
Kashe kud'insa ya k'aru akai akai zan ga an cire mini kud'i wanda a da hakan ba d'ab'iarsa ba ce. Idan har zai cire to sai abu mai muhimmanci.
Muna cikin haka kwatsam aka mini waya ta biyu da ta kid'ima ni ta tayar mini da hankali komai ya tsaya mini cak.
Tsananin tsoron Allah ya sake kama ni. Oh rayuwa babu tabbas, idona ya soye zuciyata ta bushe na dinga jin bugawarta fiye da k'ima Allahu Akbar! Ikon Allah kafi ga haka. Kafin nan hawayen tausayi da dimuwa ya goce mini.
✍️✍️✍️
*Surayya Dee*
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: 32
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Dan Allah ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.
Na sake dubawa na tabbatar Yaya Farouk ne ya ya mini waya.
Na zauna na zabura na mik'e.
Anty Rukayya ta rasu?
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
Na ambata da k'arfin gaske. Zuciyata ta dinga harbawa da k'arfin gaske.
Gabadaya sai yawo take mini, ba abin da ya dawo mini irin bara da na je haihuwar junior ta dauke Ni zuwa sabon gidansu da zasu tare.
Wata daya da ya wuce Allah ya ba ni iko na mata waya na gaishe ta, har ta had'a ni da Yaya Asad ya dinga mini gorin na zama yartsako samu ka k'i ii dangi. Har na dinga k'iranta amma shi bana k'iransa.
Ni kuwa fuskar da ta ba ni ne ya sanya nake girmamata. Yayin da shi ko na k'ira shi ba kasafai nake samunsa ba, yana kuma wahalar gaske ya neme ni dan kansa.
Na kalli agogon wayar na ga k'arfe shida saura kad'an.
Yaya Hamida na fara k'ira na sanar mata.
Ba wani alhini ta ce ", Ubangiji ya mata Rahma".
Murya ba amo na masa da amin. Na zarce da ce wa zamu tafi tare ne wajen ta'aziyar?"
Da azama ta ce "Ba zan je ba, idan kin je ki had'a ni da mijinta a waya. Uwata da rasu a waya ya mana gaisuwa dan haka nima zan yi masa ta wayar ya wadatar."
Na mararaice na ce "Haba Yaya Hamida baya k'asar ne fa. Kuma ai ba'a rama baƙi da baki. Ki duare mu je tare dan Allah ".
A harzuke ta ce "To uwar iya ni da bak'i k'irin zan rama! Ko momi ce ta kwanta dama ba zan yiwa Asad gaisuwa a zahiri ba."
Daga haka bata sake ce wa komai ba ta kashe wayarta tabbacin ta gama maganar ta.
Na k'ira Ansari na sanar masa ya ce 'Dazu ya ga N.T.A sun sanar mai dakin kwamishinan y'an sanda na jihar River's ta rasu.
Na numfasa na ce ya batun ta'aziya?"
Ya ce "Jibi in sha Allah zan bi jirgin safe na isa Abuja. Daga Maiduguri zuwa Abuja da tafiya ba zan iya zuwa a mota ba.".
Dad'i ya kama ni ganin na samu wanda zai je a cikinmu.
Na yi masa addu'ar ya iso lafiya.
Na kasa zaune na kasa tsaye tausayin Yaya Asad da na yaransa ya yi matuk'ar kama ni.
Yarana suna gidan Hajiya da yake a cikin hutu ake. Ban so aka tafi da Farha ba. Amma Amrah ta dage da ita zasu tafi ko su fasa zuwan suma. Kan dole na bari suka tafi da ita.
Sahal bai shigo ba sai goma saura na gabatar masa da abinci ya ce cikinsa a cunkushe yake.
Na ce "Rasuwa aka yi mana Baban Amra!.
Da hanzari ya ce"Waye?"
Murya ba amo na ce "Anty Rukayya Maman Bilkisu ".
Ya yi shiru da alamu nazarin wacece yake yi.
Da azama ya ce "Matar yayanku?"
Na ce "Ita fa Baban Amra. Ban ji tana ciwo ba sai mutuwa kawai na ji."
"Cike da alhini ya ce "Allah ya mata Rahma, ya shafe kurakuranta."
Cike da rauni nake amsawa da amin.
Ya shiga wanka ya fito ya yi shafa'i da wuturi.
Duk ina zaune ban iya motsawa ba.
Sai da ya hau gado ya zauna na tausasa harshe na ce "Baban Amra gobe nake son tafiya Abuja".
Ya yi shiru bai tanka ba. Tsawon lokaci ina dakon amsar sa.
Kafin ya ce "Ki yi mata addu'ar Allah yasa ta huta kawai. Amma gaskiya tafiya Abuja a yanzu bana so"
Na kalle shi sororo na ce zuwa ta'aziyar ne baka so na je?"
Ba ja in ja ya ce "Eh"a
Na rausayar da kai na ce "To kai zaka je a madadina?"
Ya girgiza ya ce "Ba zan sake na bi wannan hanyar ba don kuwa ina son