yo siyayyar kayan jarirai da su pampers kamar za a bude shago.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni kaina sai da na ga kayan sun yi yawa Abida kuma na siya mata super wax da leshi mai tsada da mayafinsu masu tsadar gaske, ko ba za ta amsa ba ni dai na sauke haƙƙi da nauyi a matsayina na uba tunda ina makwafin yaya Sulaiman ne, tunda ba inuwarsa a wajen kuma babu wanda zai maye gurbinsa sai ni shi ya sa ban ji na sare ba.
Da na koma gida shi kan shi Baban Amrah da ya ga yawan kayan sai da ya yi magana, ni kuma na sake ba shi amsa da fadin "Abida ce ta haihu sannan d'an Ya Sulaiman ne, komai zan yi musu ban biyasu girman ƙaunar da suka nuna mini ba".
Jin na faɗi haka yasa sai ya yi shuru bai yi mini sharhin nasa ba".
Washegari tun safe muka d'au hanya, azahar muna Zaria salla kawai muka yi sai abinci da muka ci, ya kai mu tasha muka shiga mota cikin sa'a gurbin mutum biyu ya rage dan haka muka biya wajen ni da yara. Nan da nan muka kama hanyar Abuja ni da su Faruk, muka bar Amra da Babanta a Zaria sai washegari za su koma Katsina. Ni kuma dama na ce masa zamu dan yi kwanaki, daɗin da na ji, jiya mun samu hutun mid semester.
Sai da muka sauka a garin Abuja sannan na kira wayar Ya Faruku na ci sa'a ya daga k'iran ya sha mamaki da na ce masa ga ni a Abuja, addreshin gidan Baba Babba zai ba ni. Ya shanye mamakinsa, ya turo mini adreshin, mai taxi ɗin da na tare na nuna masa ya ce ya san wajen tunda fitattaciyar anguwace ta masu hali.
Danƙareren gida Ya Asad ya saka iyayensa a ciki, har sai da na saki baki ina kallon gida.
Ba kowa a gidan daga Baba Babba sai Momi sai Abida, sai ma'aikata.
Kawai suka ganmu kwatsam kamar daga sama, tunda da na isa bakin gate din gidan Yaya Farouk na k'ira ya yiwa maigadin magana ya bude mana bayan ya kinkimi kayana.
Ya ce mu shigo zai dawo ya shigo mini da sauran kayan.
Momi ce a falo tare da Baba Babba.
Dukkansu bakinsu ya kasa rufuwa na murna da mamaki.
Momi ta miƙe tana faɗin" Lale marhaban Maigado ke ce tafe?"
Ina murmushin jin daɗi na ce" Ni ce Momi."
Su Farha suka nufe ta ta tarbesu cikin farinciki. Ni kuwa gaban Baba Babba na ƙarisa na rusuna ina gaishe shi.
"Barka da zuwa, lale da Bilkisu yayar Abida!
Nan da nan idanuwana suka kawo ruwa domin na tuna shekarun da suka shud'e a lokacin da muke hade, muke rayuwa cikin jin dadi da kaunar juna.
Kaina na kasa da rawar murya na ce " Sannu Baba mun same ku lafiya?"
Ya amsa da lafiya k'alau yana tambayata sauran yaran da sauran ƴan uwana duk na amsa mishi da muna nan lafiya.
'To Alhamdulillah sannu mai gado. Allah ya yiwa rayuwarki albarka.'
Na amsa da "Amin"
K'wallah na taruwa a kwarmin idanuwana farinciki da alhini sun kewaye ni kamar na fashe da kuka haka nake ji.
'Sai kika ji yar uwar taki ta haihu ko?'
Baba Babba ya katse mini tunani.
"Ban ji ba Baba. Sai shekaranjiya ne Ya Faruku ya kira ni ya faɗa mini."
Ya jinjina kai kafin ya ce" Da ya ke sai jiya aka sallamo ta daga asibiti wataƙila ba ta samu natsuwar kiran ki ba ne maigado "
Ina kallon Baba Babba a cikin zuciyata sai ayyana har yau Abida ce raunin Baba.
"Maigado har yanzu baku samu labarin Sulaiman ba?
"E, Baba bamu samu labarinsa ba har yanzu."
Ya jinjina kai kafin ya ce" Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin aminci"
Na amsa da Amin kasa kasa sai falon ya yi shuru, tunda Momi ta ja yaran zuwa ciki, ta gefen ido nake k'arewa Baba Babba kallo ya warware sai dai bai mayar da jikinsa ba haka nan tsufa sosai a tare da shi alamun har lokacin zuciyarsa bata nutsu sosai ba.
Mamakin Baba Babba nake yi a kullum shin wanne dalilin ne ya sanya ya zubawa Abida ido ta zauna a gida har hakan ya taimaka wajen b'acewar Yaya Sulaiman?
Duk da dai nasan itace rauninsa, amma duk da haka ina mamakin yadda ya iya zuba ido Abida take zaune a gabansa, idan a lokacin ba shi da lafiya ai daga baya ya ji sauƙi ya kamata ya mayar da Abida d'akin mijinta tunda bai sake ta ba. Bai kuma yi laifin da za'a kashe masa aure ba.
"Maigado tashi ki shiga wajen y'aruwar ta ki, ku gaisa ki yi salla ki ci abinci ki huta."
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Muryarsa ta katse mini tunanina, na amsa masa da to na tashi na shiga dama kayan da na zo da su tuni Momi ta shigar mini da su.
A bedroom ɗin farko na iske Momi da yara ta zuba musu abinci suna ta mata hira tana dariya.
Nan na fara shiga na duk'a har k'asa na sake gaishe ta.
"Lafiya lau Maigado, ya mutanen gidan ina me gidanki da amaryar Alhaji?"
Na amsa mata da duk suna lafiya, mun barta a Zaria tare da Babanta.
Na daɗe a wajenta muna hira itama sai da ta tambaye ni labarin Ya Sulaiman na ce mata ba wani labari cikin damuwa ta ce "Oh Allah ka bayyana wannan yaron alfarmar Annabi."
Na amsa mata da Amin.
"Za ki fara yin salla ne ko sai kin ƙarisa wajen y'aruwar ta ki?
Na ce bari na je can wajenta sai na yi, ita ta nuna mini dakin da Abida take ciki na shiga ciki na iske ta zaune a gefen gado tana shan tea ga Baby a cikin showel a gefenta yadda ta kalle ni na gane ba zan wani samu karbuwa daga gareta ba.
Ba ta yi mini mgana ba tun bayan da na yi sallama ta amsa mayafin jikina na yaye ina faɗin" Sannu "Abida."
Kai tsaye da muryata cikin dakewa ta ce" Yauwa Bilki"
Na kalle ta itama ta kalle ni, hawaye suka kawo mini amma ban bari sun zubo ba, itama ina ganin rauni a cikin idanuwanta sai dai ta yi saurin kauda kanta daga barin kallona.
Ganin haka yasa na ƙarisa wajen jariri na ɗauko shi zuwa jikina a gefen gadon na zauna, ina mai kallon yaron sai da na yi kabbara a cikin zuciyata yaron nan kamar ni ce na haife shi tsabar kammanina da ya debo, ni kuwa dama kaf ɗakinmu na fi kama da Ya Sulaiman hawayen da nake tarewa suka zubo har saman kumatun jaririn na saka hannu na share masa sai barci yake yi.
"Kai ma mu ka biyo?"
Na faɗa murya babu amo kamar shi da Farha a bayyane ba tantama, wannan jinin Ya Sulaiman ne! Da sauri na rungume jaririn ina mai fashewa da kuka har yana fidda sauti. Abida na gefe tana kallona amma ba ta yi mini magana ba sai da na sha kuka na k'oshi na share hawayena amma ina ƙankame da jaririn a hannuna zaman sama da mintina ashirin ba mu tanka ma juna ba sai ita Abidan ce da ta gaji da kanta ta kalle ni tana faɗin.
"Ina yaran ko ke kaɗai kika zo?"
Ina shirin bata amsa sai ga su Farha Momi ta kawo su Faruk ya nufi Abida yana ganinta, ta rike shi a jikinta tana faɗin" Yayanmu akwai ƙauna ashe baka manta da ni ba? Ta faɗa tana shafa kumatunsa shi kuma yana dariya.
Jaririn da yake hannuna ta nuna masa tana faɗin" Je ka kaga k'aninka? Kana son shi?
Da sauri ya ce" E Ammi ina son shi."
Don kaf yarana Ammi suke kiran Abida, wajena ya nufo yana faɗin na ba shi jaririn na ce ba zan ba shi ba Momi ta ce ya zauna sai na rike masa haka ko aka yi jikin shi har rawa yake yi.
"Mahmah da shi za mu tafi?
Ina shafa kan shi na ce" A a Faruk a wajen Ammi za mu bar shi."
Abida kuma na ta kallon Farha itama tana ta kallonta kamar ta gane ta, kamar ba ta gane ta ba, sai ta miƙa mata hannu tana faɗin"Farha zo mu gaisa."
Ta mik'a mata hannu Farha ta tafi zuwa gare ta, ta riƙe ta ta daɗe tana kallonta kafin ta shafa kumatunta tana faɗin" Farhan Bilki ta girma!
✍️
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: *Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini later domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zata iya zuba kudi ta saro masu daraja irinsu ba*.
*Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
Na kalle ta ina mai murmusawa, duk yadda soyayyar ɗa da uwa take Abida ta yi jarumtar bar mini abin da ta haifa shi yasa nake yi mata uzziri don ta nuna mini zahirin soyayyar da ta shafe dukkan iyashegenta a zuciyata. Nan duniya na shaida Abida na cikin jerin masoyana na haƙika. Duk da tana kawaici amma yanayin yadda take kallon Farha zaka san akwai soyayya irin ta uwa a idanuwan Abida.
Ta sake tambayar Farha da 'Ina yayarku?'
Farha ta ce "Mun barsu a Zaria tare da Dady".
Ganin har biyar ta gota ya sa na mike na kwantar da jaririn a saman gado, ganin na mike yasa Farha ta saki hannun Abida ta nufo ni tana faɗin" Mahma ina za ki?"
Ina kallonta na ce" Ba inda zan je Farha salla zan yi "
Ta sake ni jin ba tafiya zan yi ba.
"Je ki zauna wajen Ammmi ku kalli Baby kafin na idar da salla."
Ta gyada mini kai, ta tafi wajen Abida ni kuma na shiga tiolet.
Abida ta sauke ajiyar zuciya, tabbas a shaidar da ta yiwa Bilki ta san zata so Farha kuma zata fifita ta fiye da su Amrah ko da kuwa ba Sulaiman ne ubanta ba.
Sannan ganin Farha tsab cikin kayan alfarma ya sanya ta sake jin ba ta yi nadamar yiwa Bilki kyautar abin da ta haifa ba, sai ma take ganin yadda Balki ke kula da Farha inda tana hannunta ba lalle ma ta samu irin wannan kulawar daga gare ta ba.
Inda na barsu nan na iske su Farha da Faruku suna ta faman yiwa Abida surutu, ni na ɗauko sallaya da kaina na shimfida. Abida ta nuna mini gabas na tada salla ina idarwa Mami ta kawo mini abinci na ci kaɗan saboda cikina ya cushe, yaran kuma sun fita sun koma ina ga wajen Momi ne, kayan da na siyawa Abida da Baby na ɗauka na kai har gabanta na miƙa mata ba ta tambaye ni ba ta karɓa ta ajiye a gefenta.
"Abida sunan yaro Sulaiman" Na furta hakan cikin jarumta.
Ta kalle ni kafin ta ce" Baba Babba ya zaɓa masa suna tuni."
"Wanee suna?"
Na tambaya a hankali.
"Sunan Baba ƙarami. Isa."
Da sauri na ce" A a ba sunan Baba ƙarami zai amsa ba, sunan sa Sulaiman saboda Anisa ta haihu kwanaki kuma sunan Baba Ƙarami aka sanya masa."
Nan ma bata yi mgana ba tana ta dai kallona ni kuma ganin haka yasa na cigaba da faɗin"Sunan yaro Sulaiman. Allah ya raya mana shi. Shi kuma Ya Sulaiman idan yana raye Allah ya bayyana mana shi."
Sai kawai na kece da kukan da nake ta danne shi da k'arfin gaske saboda ba ni da ƙwarin gwiwa indai akan mganar da ta shafi Ya Sulaiman ne.
Jikin Abida ya yi sanyi ta yi sukutum tana jina amma ba ta yi magana ba.
Amma daga ga ni itama ta shiga tunani mai zurfi.
Dama ace, dama za ta iya mayar da hannun agogo baya.
Ikon Allah ne yasa ta rabu da cikin nan lafiya a sanadin Bp ɗinta ya hau fiye da k'ima ta kuma tabbatar saboda rashin ji daga Ya Sulaiman ne. Kamar yadda ya faɗa menene na shi? Mami mahaifiyarsa ce ko akan bola take ba zasu guje ta ba.
Ta kuma tabbatar sanadin barinsa k'asar nan saboda ita ne, ta tabbatar ya nemi ya yi nesa da sune a dalilin ba zai nemi sulhu da ita ba, duk yadda take tak'ama da jin kanta ya dame ta ya shanye, ta san halinsa ba ya daukar reni ko kad'an abin da zai biyo bayan takaddamansu ba mai sauƙi ba ne, da a ce ba ta je gaisuwar Mami ba, da nadamar ta yi mata yawa domin da farko cewa ta yi ba za ta je ba. Baba Babba ya matsa mata akan sai ta je. Da a ce ba ta je ba da yanzu kunya da nauyin sun ishe ta, da ba ta je musu ta'aziya ba da yau ba ta san da wani ido za ta kalle su ba.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni dai ina ta kuka, tana zaune gefe tana kallona ta kasa lallashina har sai da na gaji na share hawayena.
Sannan na sake kallonta ina faɗin" Allah ya raya mana mai sunan Ya Sulaiman."
Abida ta amsa a sanyaye amma ba fara'a a saman fuskarta.
Tana so ta ware su yi hira da Bilki, tana so komai ya wuce amma da zarar ta tuna yadda ta ga su Balki a kotu da yadda suka dunk'ule wajen kalubalantar mahaifinsu sai ta ji komai ya k'wace mata.
Ganin mun yi jugum jugum yasa na miƙe ina faɗin" Bari na je wajen Baba Babba."
Ta gyaɗa mini kai na fice na barta tana mai bina da kallo.
Mamakina take yi wai nice da wannan jarumtar? Yadda na ce sunan yaro Sulaiman ya bata mamaki sosai don tasan yadda nake kaffa kaffa da ita. Sannan na nuna a bangaren uba nake.
Ina fita falo na samu Baba Babba na zauna a gabansa ina fadin Baba ashe ka yiwa yaro huduba da sunan Baba Karami?"
A sanyaye ya ce"A tun ranar da aka haife shi".
Na yi k'asa da kaina cikin girmamawa na ce "Don Allah Baba ina neman alfarma a saka sunan Ya Sulaiman a kuma tayamu da addu'ar idan yana raye Allah ya dawo da shi gida lafiya."
Jikin Baba Babba ya yi sanyi, yana ta lallashina da ce wa" ki yu haƙuri Bilki. Allah zai bayyana shi. Sunan yaro kuma Sulaiman kamar yadda kike so ".
Na ce "Na gode Baba! Daga na zarce da fadin abin da yake cina a zuciyata.
"Bamu da kowa a yanzu Baba.
Baba ƙarami ya tafi ya barmu, mami ma haka, sannan ga Ya Sulaiman bak'in ciki da maraici ya saka ya fantsama duniya yana raye ko ya mace sai Allah!
Ga haihuwa an yi masa bai sani ba bare ya rungumi yaron ya yi masa addua irin ta uba. Ahalin Baba k'arami muna rayuwa cikin bak'in ciki tare da tunanin bamu da inda zamu dosa da matsalarmu."
Hankalin Baba Babba ya sake tashi, cikin karaya ya ce"Maigado haka kuka dauka?"
Na jinjina kai kafin na ce" E Baba. Abubuwa da dama sun faru da ya kamata ka tsawatar amma ba ka ce komai ba. Ana kallon Abida ta dawo gida aka zuba mata ido ta zauna alhalin ba sakinta mijinta ya yi ba. Na kuma san baku mana irin wannan tarbiyar ba. Ina tuna Yaya Salaha da Yaya Hamida sun sha tahowa gida idan sun samu matsala da mazajensu a ranar kake sakawa a mayar da su, ba don ba kwa sonsu ba, sai dan ku nunawa mazajensu daddako da kara. Amma ace Abida ta taho gida a barta ta zauna haka siddan. Yaya Sulaiman ba shi da wata alfarma ke nan?"
Na fada ina sharan hawaye.
Cikin sanyi Baba Babba ya ce" Ba ni da lafiya Maigado ba zan iya komai a lokacin ba. Da na ji sauki kuma na kyaleta ne dan zuciyoyi su sake hucewa kada a zo a samu sabani mummuna.
Na gyada masa kai shi kuma sai ya cigaba da faɗin" Abin da ya ba ni mamaki shi ne me ya sa Sulaiman bai zo ba? Da ya zo mun zauna da wataƙila an samu masalaha.
" Duk da haka Baba bai kamata a zubawa Abida ido ta zauna a gida haka ba, ba wannan tarbiyar kuka bamu ba, lokacin yaya Asad ai yana nan bai kamata a barta ta yi yadda take so ba."
Baba Babba ya jinjina kai cikin gamsuwa kafin ya ce" Na aminta da maganarki Maigado. Hakika kin hasko mini kuskuran da ni na kasa ganewa. Alokacin Abida ta nuna mini so take yi ta samu natsuwa idan ta zauna a can za a samu matsala tsakaninta da Mami da Sulaiman, ni kuma sanin halin zuciyarta ya
sanya na fahimceta na ce ta zauna har a samu natsuwa ban ɗauka lamarin zai lalace kamar haka ba Mai mgado. Sannan k'arfin barinta don na bawa cikin jikinta da yake kokarin faduwa kariya.
Na fahimci Baba Babba ba shi da laifi lamarin ne ya kwace masa, ya yi ta addu'ar Allah ya bayyana Sulaiman cikin aminci na yi ta amsawa da Amin Amin.
Mun daɗe muna hira mai dad'i har sai da aka k'ira sallar mangariba.
Sannan na koma ciki na iske Abida da su Faruku suna ta mata hira, toilet na shiga na dauro alwala na yi salla bayan na idar na jawo jakata na kira Baban Amra da na ga ya yi ta kirana wayar na jaka, mun gaisa har ya ba ni Amra muka gaisa, ta ce Na bata Ammi. Na mika mata wayar. Ta saki fuska da murya ta yi hira da Amra sosai.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Yara tare da Momi suka kwana ni kuma a dakin Abida amma magana mai