kai mini duka yana faɗin bani da kishin yan uwana, wannan dalilin ya sa a ranar na juya zuwa Funtua ko Momi da na shiga gaishe ta ta fahimci na sha kuka da ta tambaye ni sai na ce kai na ke ciwo, ta yi ta yi na tsaya na kwana na ce gobe ina da fita wajen aiki. Baba Babban ma ban gan shi ba an ce ya shiga ciki ya ɗan kwanta nasan kuma duk damuwar furucin Mami ne, haka na koma gida ina cikin matsanancin damuwa, Baban Amra bai lura da haka ya fara mini wasu tambayoyin da ba su shafe sa ba wai me Baba Babba ya ce mana? Ko mganar rabon gadon ne? Tsabar haushi ko amsa shi ban yi ba sai ya fara faɗa wai ya fahimci yanzu na raina shi sai ya riƙa yi mini magana ina share shi tunda na ga yanzu ba shi kuɗi nike da shi ina masa hidima to ban isa ba har gobe yana matsayin mijina sannan ai kafin ni na fara yin hidima shi ya yi hidimar da ni ganin abin zai koma wata fitinar sai na bashi haƙuri saboda a halin da na ke ciki bana ma bukatar wata hayaniya amma shi ya kasa ganewa abin da ke gabansa kawai ya ke dubawa saboda ba shi da adalci.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Gabaɗaya ba ni da sukuni saboda duka suna bayan Mami da Ansari ne, ni ce kaɗai bana tare da su, shi ya sa suka ware ni jin daɗina ɗaya su Yaya Sulaiman sun kusa dawowa ina tunanin shi ne kaɗai zai taya ni wannan faɗan amma a yanzu kam Mami ta ja tun ga za a yi hatsaniyar da ba a taɓa yi ba akan wannan gidan gonar, ban san cewa shirin Mami ya fara fallasa ba sai da Ya Usman ya zo gidana ma'aikatarsu ta turo shi wani taron bita na kwana uku a garin a katsina shi ne ya kawo mini ziyara. Shi ne yake faɗa mini gida ba daɗi da na ke tambayan shi su Mami.
"Mami ta sauya Balki, ko ni kafin tahowata na shiga bangarenta na gaisheta tana ganina ta tashi ta shige ciki, abin ya ɗaure mini kai ahalin na san Mami ta fi kowa zama mu yi hira mai tsawo tare da ita."
Zuciyata ta amsa, abin da na ke gudu ne yake neman faruwa.
"Ayya ka san zafin rashin nan na Baba ƙarami ga kuma rashin lafiyar Ya Sulaiman duk sune suka saka ta zama haka."
Sai ya kalle ni kamar yana so ya fahimci wani abu ni kuma sai na yi saurin kauda wannan zance kar ya fahimci ƙarya na ke yi amma bai bar maganar ba, faɗa mini yake yi Ansari ma yanzu ba ya masa mgana sun haɗu kafaɗa da kafaɗa ya wuce bai gaishe shi ba sannan Momi ma ta ce ta kasa gane kan Mami irin shigan nan da take yi mata da yamma ta ɗan taya ta zama in ta shiga Mami take tashi ta bar mata falon sai dai in ta gaji da zama ta koma bangarenta ta kuma tambayeta ko ta yi mata wani abu ne ta ce mata ba komai.
"Maigado Wallahi gidanmu ya sauya. Ba daɗi shi kan shi Baba Babba sai rama yake yi a tsaye yau lafiya gobe ba lafiya."
Cikin tashin hankali na furta" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
Ya cigaba da faɗin" Tun bayan faruwan lamarin nan komai ya rikice, amma ina fatam idan su Abida suka dawo komai ya daidaita. Tun suna saka ran dawowa farkon wata mai kamawa Ya Muneera ma ta ce idan suka dawo za ta zo kasar sai a zauna gabaɗaya a tattauna domin magance matsalolin da suke tunkaro mu."
"Allah ya sa."
Na faɗa a fili amma zuciyata na rawa, na samu Ya Usman ya tafi ba tare da ya fahimci na san kan zancen ba, ina zance masa kan maganar gado ne, ina zan iya fada masa suna tuhumar mahaifinsu ne da ya yi musu rashin adalci wannan Magana tana da munin a ji daga bakin wani daga cikin mu.
Abin da na ke gudu ne shi ke yake faruwa. Maganganu har sun fara yawo kuma na tabbata Baba Babba shima mganar ta je masa Shi da Momi wataƙilama Yaya Usman har su Ya Asad duk ya sanarwa, kaina na dafe da na ke jin yana sara mini, irin wannan lamarin akwai sarkaƙiya duk yadda kaso ka warware shi cikin sauƙi ba zai warwaru ba. An samu matsala tun farko, an yi abin ba rubutu, idan sun aminta da junansu sun manta suna da mata da iyalai? Sannan sun manta akwai mutuwa, wata rana ƴaƴa za su taso su ɓukaci gadon mahaifinsu, su kuma gidanmu gadone kan gado tunda har na mahaifansu basu raba shi ba sannan ba su yi wani rubutu da zai iyakance ga na wane ga na wane ba, tabbas hakan babban kuskure ne shi yasa abin da Ubangiji ya ce a zarta gwara a zartar saboda gudun fitina.
Ni na ga ni a gidanmu da a ce sun raba gadon iyayensu da tun farko abin da ya faru bai faru ba sannan da ace sun yiwa dukiyar iyaka da rubutu da duk alamrin Bai cukurkude mana ba, kuskuren haka ya jawo mana gagarumin yaƙi, yaƙin da ya zo ya cinye gidanmu kaf, sannan wacce ta jagoranci yaƙin daga karshe ba ta ci moriyar kafiyarta ba.
Sai Allah ya kaimu Monday.
Ayi karatun Lafiya.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ni duk a tunanina satin da muka shiga su Ya Sulaiman zasu dawo kamar yadda muka ji, ashe an sauya Yaya Faruƙu ne kaɗai zai biyo jirgi ya dawo sakamakon likitoci sun tabbatar ba zasu sallami Ya Sulaiman ba sai ya fara takawa da k'afafunsa, ba taimakon sanda ko keke, shi yasa suka ce zasu sake riƙe shi nan da wata ɗaya.
Shi kuma ya ƙosa, ya matsu sai ya dawo gida amma tunda Ya Asad ya ji labari ya ce ya zauna ya bi dokokin likitoci domin samun ingantarciyar lafiyarsa. Ya ce Abida za a bari da shi, Yaya Faruƙu kuma ya dawo gida, ko Baba Babba dawo, ya d'an warware tunda dama Yaya Faruk din ne a gari. Anisa ta fad'a mini hakan da muka yi waya tunda ni kaina mun kwana biyu ban yi mgana da Ya Faruƙu ba bai k'ira ni ba, nima ban kira shi ba, ina jin kunya da nauyi domin ina tunanin maganganun da suka fita daga bangaren Ansari shima sun isar masa. Bayan na ji maganar a bakin Anisa ne na yi waya da Mami itama ta sake tabbatar mini da sun yi magana mgana da Ya Sulaiman a cikin satin nan Yaya Faruƙu zai dawo za a bar Abida a tare da shi, fatan samun lafiya na yi masa jikina a sanyaye, na ji daɗi da har muka gama waya Mami ba ta yi mini batun gadonmu ba, nima ban yi mata ba, saboda kwata-kwata ma bana son yin maganar domin ɗaga mini hankali al'amarin yake yi. Har Ansari ban yadda mun sake waya ba, ban kira shi ba shima bai k'ira ni ba, kuma ina da tabbacin haushina yake ji shi ya sa bai neme ni ba.
A bakin Momi da muka yi waya na ji labarin dawowar Yaya Farouk. Na kira ta na gaishe ta sannan na ji yanayin jikin Baba Baaba hawan jini ya rafke shi, likita ne ke jigilan zuwa gida yana duba shi na musamman da Ya Asad ya ɗaukan masa.
Jin ya dawo yasa na cire nauyi da kunya na kira shi na yi masa barka da dawowa, dama na tsammancin fiye da haka daga bangaren Ya Faruƙu domin shi karimi ne, haba haban da ya saba yi mini bai ragu ba, mun jima muna waya da shi na ji daɗin labarin da ya bani na Ya Sulaiman da cewa kaɗan ya rage kafar ta ƙarisa warke wa sai a kunce ɗorin wataƙila kafin ma su cike wata ɗaya za su iya dawowa, na ji daɗin bayanin nasa , na ji nutsuwa ta saukar mini,don ba almun ya samu labarin cecekucen da yake ta fita.
Kewa ta kama ni, kewar Abida, kewar wacce zan yi magana da ita na ji sanyi, ta kuma yi mini sassauci idan ta ga raunina ya bayyana. Sai dai duk yadda na matsu da dawowar Yaya Sulaiman haka nake cikin zullimin durowar Abida Funtua ta ji wannan bak'in labarin don kuwa na tabbatar Abida zata jagoranci y'an sashinsu wajen shata layi damu don a bayyane yake yadda Baba Babba ya jarabtu akanta itama haka take sonsa tare da kiyaye daarajarsa, na tabbatar aurenta da Sulaiman ba zai yi tasirin da zata gwada nata wulak'ancin ba.
A fili na furta "Allah mun tuba, Allah ka yafewa iyayenmu wannan gangancin da suka yi da sunan zumunta."
Tsorona Allah kar wannan fitinar da Mami take son jawowa ya yi silan baƙin cikin da zai iya kai Baba Babba k'asa, don kuwa mutuwar Baba ƙarami ta raunana Baba Babba matuƙa raunin da har a muryarsa ya bayyana, gangar jikinsa ya rasa k'arfi da kuzari gabadaya. Dan na rasa madafa sai na tsananta addu'a mussaman a cikin sallolina na dare ina adduar Allah ya daidaita komai kar sheɗan ya samu damar shiga gidanmu ya daidaita mana shi
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Ina Katsina ban koma Funtua ba, amma ina kiran waya ina jin halin da suke ciki.
A
Jin za su dawo ya sa nima na fara shirin tahowa Funtua na yi ko da sati ne, sai aka ci sa'a ina tambayan Baban Amrah ya ba ni izini ya ce sai mu je tare ya duba Ya Sulaiman shi sai ya dawo ni kuma na zauna. Sai kuma a ka ci saa a satin yara suna hutun mirdterm break, shi ya sa na yi tunanin tafiya da su gabaɗaya.
Ina ta shirina cikin farinciki ana gobe za su sauka gida Basma ta zo mini yini, mun sha hira sosai muna tuna rayuwarmu ta makaranta muna dariya, sai yamma Baban Abdul ya zo ya ɗauke ta, itama da alƙawarin bayan su Abida sun dawo za ta je har Funtua ta gaishe da mai jiki.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Daran ranar da su Abida zasu sauka a lagos kasa barci na yi, a ranar wata asabar da safiya Yaya Sulaiman suka sauka a filin saukan jirage na garin lagos, kuma Ya Asad ne da tawagansa suka je suka tarbe su, na ɗauka a ranar za su taho Funtua amma sai muka ji shuru, su Anisa da Yaya Hamida duk suna can Funtua a gida suna jiran isowarsu ni ce dai na jira idab sun sauka sai na taho, amma ba su taho a ranar ba sai washegari da safe. Yaya Asad ne ya ce sai sun kwana sun sake hutawa, da safiyar lahadi nima na isa Funtua ni da yara da Baban Amrah. Misalin k'arfe ɗaya na rana ko minti talatin ba muyi da sauka ba sai ga motocin tawagar y'an sanda tunda reshen jihar Kaduna, tunda daga airport suka tarosu. Muka cika harabar gidan cikin murna da farinciki Allah sarki Baba Babba sai ga shi da kansa ya buɗewa Yaya Sulaiman murfin mota yana fitowa da kafafunsa zai ɗukawa Baba Baaba shi kuma sai ya tarairayo shi ya rumgume shi har hawaye suna zirarowa ta gefe da gefen idanuwan Baba Baaba, muma sai kuka muna share ƙwalla shi kan shi Yaya Sulaiman ɗin hawayen yake yi. Baba Babba na sakinsa Mami ta rike shi tana hawayen farinciki.
"Ashe zan sake ganin ka a kan kafafuwanka Sulaiman?
Ta faɗa tana mai sake kecewa da kuka sai ya rumgumo ta yana faɗin" Alhamdulillah Mami. Allah ya sa ina da rabon sake rayuwa da ku."
Kowa ta kan Yaya Sulaiman ya bi, ni ce kawai na yi ta kan Abida, wacce na ga ta yi kiba ta sake fari da cika kamar ba wacce ta je jinya ba, rumgume ta na yi ga mamakina nima sai ta riƙe ni, ina kuka ina faɗin" Sannunki da ƙoƙari ya ke masoyiyar yar'uwata."
Dago ni ta yi tana share mini hawaye tana kuma yi mini murmushi, yara ma haka ta riƙa rumgumarsu da'ya bayan ɗaya, mun daɗe a harabar gidan kafin a dumguma zuwa falon Mami can kuma sai mutuwar Baba ƙarami ya dawo sabuwa, shi kuka mu kuka Yaya Sulaiman kuka Yaya Asad ne mai ba su ba da bakin a yi haƙuri, sai da aka natsa suka yi wanka suka ci abinci sannan aka sake zama har Video call a ka kira Ya Muneera itama ta yi magana da su Abida kowa kaga ni yana cikin sukunin dawowar Yaya Sulaiman akan dugagunsa. Zuciya ta samu salama daga cikin tararradi. Baban Amra Zaria ya wuce a ranar ya kwana, sai washegari ya koma Katsina. Ni kuma ina gida domin gidan ya d'an yi daɗi kad'an. Don ina ankare da Mami da Ansari nake kada su ballo wata magana, sai kuma aka ci sa'a ba su yi ba. Jama'a ana ta zuwa duba Ya Sulaiman da yi musu barka da arziƙi. Baba Babba ma jiki ya yi kyau kamar ba shi ba.
Yaya Asad bai kwana ba a ranar ya juya saboda aiki, zai shiga jirgin k'arfe shida zuwa birinin Ikko.
Kwana na biyar a Funtua lokacin har Abida ta koma bangarensu ita da mijinta, na samu nutsuwar zuciyata da ban ga Abida ta birikice ba, tabbacin bata ji komai ba, sai hankalina ya kwanta ina shirin haɗa kayana na koma gidan mijina saboda yara sun koma makaranta Baba Babba ya ce na dakata za a yi general meeting tun da na ji haka na firgice saboda ban san abin da wannan zaman zai haifar ba.
Zama ya haɗa mana dukkanmu har da y'an bangarensu Abida, Ya Muneera ce kawai ba ta a wajen, kowa da kowa ya hallata. A bangarenmu a falon Mami aka yi zaman ita lokacin ta fita daga takaba da kwanaki biyu.
Sai dai zaman har da limamin masallacin unguwar. Dattijon arziƙi ne sannan malami ne sosai masanin Qur'ani da hadisai, mai wadar zuci da fayyace gaskiya komin d'acinta. Bayan buɗe taro da addua da yiwa Baba ƙarami addua Baba Babba ya fara kora jawabinsa.
Ya fito da wasu takardu na shaidar rukinin filayen Ladi farm gabaɗaya mallakinsa ne babu sisin Baba ƙarami a ciki.
Sannan dabbobin rukunin, dawakai ne da talo-talo, da dawisu na Baba ƙarami, amma sauran duk dabbobin dake cikin Ladi farm mallakin Baba Babba ne, sai dai Baba ƙarami ya kasance yana kula da su, masoyin dabbobine kuma likitansu ne.
Amma bisa adalci Sai baba Babba ya ce za a raba amfanin gona kashi biyar shi kash uku, a bawa iyalin marigayi biyu duk da shi bai damu da noma ba, yafi son siyan dawakai da tsuntsaye.
[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Bayan ya gama jawabinsa liman ya ɗora da tasa nasihar kan rayuwa da muka mutuwa, sannan ya gangaro kan haƙƙokin raban gado da waɗanda Ubangiji ya hallata ma samun gado.
Ya yi maganganu sosai jikin kowa kuma ya yi sanyi falon ya yi shuru ana sauraransa, daga karshe ya nuni da ce wa Baba Babba ya yi daddako, ya yi zumunci, domin bisa adalci irin nasa ne ya sanya ya ce a raba guda biyar, amma an sani akwai tazarar sosai a tsakaninsu.
Sannan ko da ya ce ladi farm tasa ce ya fadi gaskiyar abin da ba nasa ba a ciki. Dan haka liman ya umarci a zagaya da takardan filin kowa ya ga ni a cikinmu da kwanan wata da komai sama da shekaru talatin baya
Kowa ya yi na'am da wannan tsarin amma Mami bata ce uffan ba tabbacin bata gamsu ba ke nan.
Ya Sulaiman da ni hankalinmu ya yi tashin gauron zabi.
Tare da adduar Allah ya hana ta ikon magana.
Mami ba nauyin kowa ta ce" Wallahi ban amince da wannan tatsuniyar ba".
Ta faɗa tana babu ko d'ar.
Ya Sulaiman ya mike yana mata magana amma ba ta saurare shi ba, kuka ta saka na sosai ganin haka ya sa Baba Babba ya sallami liman domin ba zai so a yi wannan hatsaniyar ta cikin gida a gabansa ba.
Momi hankalinta tashe ta mike tana faɗin" Haba Mami! Alhaji kuwa idan bai yi muku ba, ba zai zalunce ku ba. Menene Bai yi muku ba sai yanzu da aka zo gargada ne kuma zai ci amanar shak'kin
d'anuwansa?".
Mami ta kalle ta da jajayen idannuwanta kafin ta ce" Ba zan yi mamaki dan kin yi mini gori ni da ya'yana ba. Don mamakin yadda za'a danne mana dukiyarmu ta fi komai girma a idona!
Yaya Sulaiman cikin rawan jiki da na murya ya ce" Mami kin ga shaida kin ga cewa filin nan na Baba Babba ne ".
Tsawa ta daka masa kafin ta ce" Dalla rufe mini baki, mara kishin kansa, don anzo da wata takarda duk ta tsufa sai ace shaidar ke nan, ba zan yi shuru a cuce ni ba, daga nan har gaban abada kuwa"
Na miƙe jikina na rawa ina kuka ina kiran sunan Mami amma ba ta saurare ni ba, daga karshe ma tsawa ta buga mini tana faɗin" Zan ci miki mutumci Balkisu."
Sai na yi shuru na koma gefe ina kuka su kuwa Baba Babba da su Yaya Usman sun yi shuru kamar ruwa ya cinye su, ina tunanin Baba Babba ne ya dakatar da su daga yin magana. shi da kansa kansa na ƙasa ya kasa magana. Abida kuwa kai kawai ta ke girgizawa Yaya Usman na cije baki, Ya Faruƙu ma ya yi shuru kamar baya a wajen.
Mami kuka take yi tana rantsuwan ba zamu amince ba
Ansari ya miƙe yana faɗin" Ina bayan ki Mami.
Ganin haka yasa Abida ta miƙe itama tana faɗin"Muma mu nan akan ce wa ladi farm ta Baba Babba ce.
Yaya Usman ya miƙe yana marawa Abida baya bayan shima ya ce "Komai zai faru sun shirya masa.
Yaya Faruku ne