Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Adventure

Chapter   16 / 37

45K to 48K   out of 110.8K words

Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Baban Amrah ya dawo na nuna masa upper ya yi murna ya ce shima ya yi interview a makarantar tunda v.c din dan Mashi ne abokin Baban Zaria ne.

Kwana huɗu da zuwan Ya Sulaiman gidana ya turo mini saƙo da cewa ya yi nesa da mu na wani lokaci amma kar mu damu idan da rabo wata rana zai dawo.

Ashe ba ni kaɗai ya turawa saƙon ba dukkanmu ne, sai ga wayoyin su Ansari cikin tashin hankali. Ansari ya bani tabbacin Ya Sulaiman ya kwashe komai nasa kamar ma ya bar k'asar ne gabad'aya sanin inda ya nufa a yanzu sai Allah. Mun shiga matsannacin tashin hankali Ya Hamida ta k'ira ni a waya ta zage ni tas tare da cewa na ji daɗi wacce na ke karewa ga shi nan ta yi sanadiyar tafiyar Ya Sulaiman uwa duniya ina kuka ina so na kare kaina amma bata ba ni damar haka ba ta kashe wayarta.

Tafiyar Ya Sulaiman da rashin sanin inda ya nufa ya sake rauna ni, na shiga matsanancin damuwa. Baban Amrah ya samu lasisin zagin Abida tare da kusheta.

Duk halin da na ke ciki bai saka, ya hadiye abin da yake cinsa ba fada mini yake yi "Ai dama kallona kawai yake yi na hana shi ya je kotu ya karemu, saboda ba na so na yi laifi wajen Abida da Ya Muneera to ai ga shi nan sun nuna mini matsayina, daga karshe su sun cure kansu waje ɗaya mu kuma sun samu nasaran tarwatsa mu, tunda ga shi Ya Sulaiman ya shiga duniya ba a san in da ya tafi ba, kuma yasan har da bak'in cikin Abida da ubansu ne ya sanya ya fantsama duniya. Ban da ma kaddara me zaisa Sulaiman kallon yarinyar nan da Sunan soyayya? Ta gama yin kwantai ta samu ya rufa mata asiri shine har take jin kanta ita wata tsiya ce. Kallon shi kawai na ke yi ban iya shuru ba sai da na ce masa" Baban Amra ban da karfin halinka ina ruwanka ne da zaka ce zaka shiga shari'ar gidanmu?"

Faɗin haka sai ya sake jawo mini ya dinga jefa mini maganganu da ce wa dama ya ga taketakena tunda na yi kuɗi na fara masa wulakanci to kar na manta shi ɗin garkuwata ne. Bak'in ciki ya turnike ni wai fashe masa da kuka ba tare da na sake ce wa komai ba. Ganin kukana ne ya saka ya sauko ya shiga aikin lallashina da nuna mini ya damu da ni shi yasa ya damu da damuwata.

Ni ko na ce idan har ya damu da damuwata kar ya sake dago mini wannan maganar, ya ce ya yi alƙawari.

Da gaske kam ya bar maganar domin kwana biyu haka ya shiga ririta ni, har wanka ma da taimakonsa nake yi. Gidanmu na Funtua ba kowa a ciki gida ya zama kango, ita kanta Ladi farm din Ansari ya ce ma'aikata na ta sallaman kansu, ba kula abubuwa dai duk sun lalace a gidan gonar tun barin Yaya Farouk garin Funtua.

Idan na zauna ina hakaito lamarin gidanmu sai na ji kamar zan yi hauka saboda baƙin ciki da takaici, da zaran na tuna sai na samu kaina cikin kuka, kuka mai karfin da bana sanin ma lokacin da na ke zunduma shi da iyakacin k'arfina.

Tabbas mun yi rashi, gidanmu ya ruguje ya zama kango.

Mami da ta gama yaki akan dukiya ta mutu ta barta, mu kuma muna ji muna ga ni gidanmu na Funtua ya zama kango.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu."

Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki!

Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne.

Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami.

"Yayw Sulaiman waɗanan mganganun fa? Ina za ka je?"

Na faɗa cikin damuwa da tashin hankali

Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haɗuwa."

In jin ya ce haka na fara kuka ina faɗin" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni."

Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki"

Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta.

Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi.

Na ce ya ɗan jira su Farha sun kusa dawowa.

Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaɗai sauran yaran fa?

Na yi shuru ban yi mgana ba.

Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita".

Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"

Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Ganin ya ruɗe yana ta wasu surutai yasa na s lalubo jarumta na yi ta masa nasihan da jan hankalin cewa tunda mutuwar Mami ta zame masa wa'azi ka da ya karaya, ya yi haƙuri ya cigaba da harkokinsa kowa iya kwanakinsa zai yi a duniya ya ɗauka ita Mami kwananta ne ya ƙare, da irin kalaman da na yi amfani kenan na lallashi Ansari ya bar kuka ya samu natsuwa.

"Allah ya jikan Mami da Baba ƙarami Allah ya sa sun huta."

Ya faɗa cikin karaya, na amsa mishi da Amin ina mai ɗauke hawayen da suka zubo mini da yatsun hannuna.

"Ya Sulaiman har yanzu ba labarin shi Ansari??

"Wallahi babu, na bincika duk in da ya kamata da wajen abokansa da suka yi karatu tare a Germany amsar duk iri ɗaya ce basu san in da yake ba sannan suma ba ya magana da su."

Ansari ya amsa mini cikin damuwa a muryansa.

"Shike nan. Idan yana raye Allah ya tsare shi a duk in da yake. Idan da rabon mu gana Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri."

Na faɗa ina jin kamar na fashe da kuka Ansari ya amsa da Amin mun daɗe muna tattaunawa kafin mu yi sallama bayan mun gama wayar na zauna a ɗaki ni kaɗai na ci kuka na ƙoshi sannan na faɗa bayi na wanke idanuwana, haka nake yi idan na tuna da yau ba Mami ba Baba ƙarami, sannan ba iyalan Baba Babba. Ga Ya Sulaiman ya yi nesa damu sai na ji ina kuka wanda banma san ina yi ba, ƙarfin zuciya ne da tasirin musulunci ke rike da ni amma matuƙa zuciyata da gangar jikina sun raunana, ƙarfin hali ne kawai da karɓar kaddara tunda rubutattaciya ce daga littafan kaddarar rayuwarmu, kuma cikar kowani musulmi karɓan kaddara mai kyau ko akasin ta.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi haka nan bawa yake zirga-zirgarsa na yau da kullum tunda akwai rai har da lafiya mun godewa Allah. Ba laifi ina samun ƙudi sosai tunda gidajen da na samu duk haya na saka, sannan ga sana'ata ta snack ta karɓu sosai da dukkan zuciyata da jikina nake yin aiki tuƙuri domin idan tuna maganar Ya Sulaiman ta ƙarshe a gare ni akan na zama jarumace na tsaya akan ƙafafuwana saboda ni uwa ce domin zama garkuwan ƴayana wata rana. Bana ko tsayawa jiran Baban Amrah domin ɗaukan laluranmu ta riga ta zame mini jiki komai ni nake yi, mantawa ma nake yi nauyin hakan na kan Baban Amrah ne, tun kuma da hakan ta faru ban sake komawa Funtua ba, saboda ko na je wajen wa zan je? Gida na can a kulle babu kowa shi yasa ko marmarin zuwa ban taɓa yi ba. Ansari da ya dawo ya zo kwanaki da ya shigo garin kan harkokinsa duk ya rame amma ba laifi tun da ya kwantar da hankalinsa ya fara ɗaukan dangana, ya sanar mini ya samu aikin amma an tura shi Maiduguri babban birnin jihar Borno. Jikina ya yi sanyi tare da zullimin yadda Ansari zai yi nisa Ga shi a lokacin garin Maiduguri na fama da ta'adin yan tada k'yar baya. Amma na daure na yi masa kyakkwar adduar alheri. Ya mini sallama akan gobe zai tafi. Tafiyar Ansari ya sake kassara ni don gani nake yi tamkar shima ya tafi kenan. Da k'yar na hak'ura na cire al'amarin a raina amma bansan me yasa nake ji a jikina ƴaƴana kad'ai suka rage mini. Shi yasa na rike aikina da sana'ata da muhimmanci don duk ƙokarina da wahalata sabo da su ne, domin na ingata musu rayuwa ko da wata rana bana tare da su.

*BAYAN WATA SHIDA*

Bayan watanni shida da tafiyar Ya Sulaiman, ba wanda ya sake jin labarinsa, yana raye ko ba ya raye ba wanda ya sani sai Ubangiji.

Ni dai addu'ata kullum shi ne idan yana raye ubangiji ya karkato da hankalinsa gida idan kuma ta Allah ta kasanance da shi Ubangiji ya haɗa mu a darussalam.

Ashe Abida ta haihu ban sani ba, kuma ba na tunanin wani a cikinmu ya san da batun haihuwar nan, nima Ya Faruƙu ne ya k'ira ni kwana uku da haihuwar ya sanar da ni, sai na ji abin kamar a mafarki tambayar kaina na ke yi dama Abida na da ciki ne? Mamaki da al'ajabi suka sake mamaye ni da jin ikon Allah! Yafaɗa mini namiji ta haifa da uwar da abin da aka haifa duk suna lafiya.

[9/16, 3:19 PM] Salma Muhammad: Duk da C.S aka yi maa Abidan a dalilin ba zata iya haihuwa da kanta ba, ban sani ba, sam bansan Abida na da cikin Ya Sulaiman ba wato shi ya sa da rasuwar Mami na ganta wani iri ashe lokacin ma tana cikin laulayi ne? Allah sarki! Kwalla ta zubo mini a dalilin na Kara fahimtar ya'yan Baba Babba gabaɗayansu sun rufe ni daga ganin status dinsu koma share lambata suka yi oho! Ya Faruƙu da na ke ganin yana yiwa zumunci kara bana ganin status dinsa Sai dai ina masa zaton bai share lambata ba, amma na gode masa domin ba dan shi bazan ji labarin haihuwar ba. zumunci ya riga da ya lalace gyaruwarsa zai zama wani abu ne mai wahalan gaske.

Amma na dinga mamakin yadda Baba Babba bai fada mini ba don kuwa ni ban daina gaishe shi ba, a kai akai ina k'iransa a waya na masa gaisuwar juma'a tare da tambayar jikinsa da iyalinsa gabad'aya.

Ni na kira su Saddiqa na faɗa musu haihuwarAbida suna ta mamaki, Ya Hamida ce sai da ta dama ta ɗaga kirana da nafaɗa mata haihuwan Abida ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Ta baya ta rago kenan. Ta yi nasaran koran shi daga k'asar gabaɗaya, sai ta zama uba da uwar abin da ta haifa."

Daga haka ta kashe wayarta sai na sake kiranta.

A fusace ta ɗauka tana faɗin" Wai lafiya kike ta kirana Bilki?"

N tausasa harshe na a ce" ko za ta shirya mu je Abuja mu ga Abida da abin da ta haifa?"

Kawai haka na fad'a Ya Hamida ta fara zagina ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce ita kam ba in da za ta je idan ni zan je Allah ya raka taki gona tunda ban san kishin kaina da na y'anuwana ba.

"Ba haka ba ne Ya Hamida, kar ki manta ba saboda ba Abida za mu je ba. Saboda Ya Sulaiman ne."

Ko saurarena ba ta yi ba ta sake katse wayarta tana faɗin sai kuma na yi, tun da na ji haka sai na zare ta a ciki a raina na kudiri niyyar ni kaɗai ma ya isa zan je na duba ta saboda zumunci da kuma Ya Sulaiman. Na kira Ansari mun yi magana ya ce shi Wallahi nauyi yake ji da ya raka ni amma na fara zuwa shima daga baya zai je, ko dai bai je ba magana ma mai daɗi sadaka ne na ji daɗin mgana da shi. Baban Amrah na dawowa na tare shi da maganar haihuwar Abida.

"Wace ce kuma Abida?"

Ya tambaye ni yana kallona, bai wani ba ni mamaki ba sanin dama ba ya son duk wata magana da ta danganci Abida yake yi ba.

"Abida dai tawa da ka sani y'aruwata"

Na ba shi amsa a takaice kuma a dake.

Ya jinjina kai kafin ya ce" ikon Allah, dama tana da ciki ne?

Na amsa masa da ce wa "ni ma ban sani ba sai da ta haihu."

Tabe baki ya yi bai yi magana ba, ni kuma ganin haka saboda bana son mu sake wata mgana daga baya da sauri na ce" Ina so ka yi mini izini na je Abuja na duba su."

Ya ɗaure fuska kafin ya ce" Me yasa za ki je?"

"Saboda ya kamata!

Na amsa mishi kai tsaye, tuna Ya Sulaiman da na yi yasa kawai sai na fara hawaye ina faɗin" Baban Amra ka yi mini izini na tafi, zan je ganin abin da aka haifawa Yaya Sulaiman wanda ba mu san ko yana raye ba, ni ina ji a jikina wataƙila ba ya raye, domin idan yana raye ba zai kai wannan wattanin bai neme ni ba, k'ila ma a inda ya je ya haɗu da tsautsayi na ajali."

Na ƙarisa faɗa ina mai fashewa da kuka. Jikinsa ya yi sanyi ya taso zuwa gare ni ya rumgume ni yana lallashina.

"Daina kuka, in sha Allahu Sulaiman yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya."

Ya furta hakan murya babu amo.

Na ɗago daga kan k'irjinsa ina faɗin" To idan yana raye yana ina. Me ya sa har tsawon wannan lokacin bai neme mu ba?

Na faɗa hawaye na sake kece mini! Shi ya share mini hawayen yana sake rumgume ni, a daran ya yi ta lallashina da kalamai sai ga shi na saki jikina tun ballanta ma da ya ce ya amince na je amma shi ba zai samu zuwa ba, za su je Zaria shi da Amrah su duba mai sunanta.

Na ce masa sai na tafi da Faruk da Farha. Ya ce to sai mu tafi gabaɗaya idan muka duba Maman Zaria ni da sauran yaran mu ƙarisa Abuja.

Da wannan shawaran muka tsaya washegari kasuwa na shiga na

16 / 37