Author : Maman Teddy Category : Romance
tayi ƙasa da kanta, sau dayawa yakan bata kunya, don kuwa ko agaban Oummu ne idan yaso taɓa jikinta taɓawa yake babu ruwansa, murmushi Oummu tayi tare da dubansu cikin kulawa ta miƙowa Zieyaderh'n wani babban leda, inda tace "Ga tsaraba nan takaiwa ƴan maiduguri!" ɗan rusunawa Zieyaderh tayi tare da karɓan ledan, cikin jin daɗi tayiwa Oummun godiya.
Amotarsa suka nufi airport inda Babanta dashi ke zaune agidan gaba, itakuwa agidan baya take zaune, koda sukaje airport ɗin sun samu tuni jirgin yakusa tashi, Sooraj dinne yayi musu komai, inda baibar cikin airport ɗin ba saida yaga tashin jirginsu, daga airport din kuwa kaitsaye office dinsa ya wuce, yayinda zuciyarsa ke cike da kewar matarsa wacce ayanzu tazama sanyin idanunsa.
Basuwani jima suna tafiya acikin jirginba suka iso garin na Maiduguri, koda suka sauƙa a airport ɗin tuni suka samu wata mota na jiransu wanda itace zata kaisu har inda zasu, bisa kwatancen baban nata suka iso gaban wani makeken gida wanda aka ƙawata jikinsa da farin fenti, gidane me kyaun gaske yayinda wani tangamemen gate yazama shine ƙofar shiga gidan, cikin yanayi na mamaki Zieyaderh tafito daga cikin motar, ahankali take ƙarewa gidan kallo, Baban nata ne ya ƙwanƙwasa babban gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani maigadi yaɗan buɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate din tare da ɗan leƙowa, cikin mutuntawa suka gaisa da Malam Garba, nan Malam Garba yace yayi masa iso wajen Hajiya Mama, (Hajiya mama itace mamar Maryama wato mahaifiyar Zieyaderh)
Babu wani jimawa maigadin yace su shigo, koda suka shiga cikin gidan mamakine yasake bayyana akan fuskar zieyaderh don kuwa sosai cikin gidan yayi kyau, ko ina cike yake da shuke shuken flowers masu kyau, maigadin dakansa yayi musu jagora harzuwa cikin wani haɗaɗɗen falo, wanda da dukkan alama shine babban falon gidan.
Akan kujera suka zauna su dukansu daidai lokacin wata mata wacce aƙalla bazata wuce 30 years ba tafito daga cikin kitchine din dake cikin falon, idanu huɗu sukayi da Ziyada hakan yasa tray ɗin dake riƙe ahannunta ya suɓuce yafaɗi, kallonta Ziyada tayi cikin yanayi naɗan mamaki, muryar wata ƴar dattijuwar mata da taji abayanta yasata juyawa ta kalli matar, wata ƴar dattijuwace wanda aƙalla bazata wuce 53 years ba, ahankali matar ke sauƙowa daga kan steps, matar fara ce irin sol ɗinnan, duk da cewa ta tsufa amma da ka ganta zaka gane cewa shuwa arab ce, donko hausan dake bakinta ma wani iri ne,
haɗuwar idanun dattijuwan dana Ziyada yasanya gaba ɗayansu sukaji ƙirjinsu ya buga, cikin matsanancin mamaki matar wacce ake ƙira da Hajiya Mama ke kallon Malam Garba kana kuma saita dawo da kallonta ga Zieyaderh, wanda ko ba afaɗa mata ba taji ajikinta cewa matar itace kakarta wato uwa ga mahaifiyarta kenan, bazata iya jurewa ba sai kawai tatashi inda taƙarasa da gudu ta faɗa jikin Hajiya Mama, nan tasaki kuka, Aunty Ounnaisa dake tsaye bakin kitchine ganin cewa Ziyada tafaɗa jikin Hajiya Mama yasa taji hawaye sun cika a idanunta, da sauri ta ƙaraso cikin falon inda ta ɗago Ziyada daga jikin Hajiya Mama ta rungumeta, cikin muryar kuka Aunty Ounnaisa tace.
"Koda ba da mahaifinki na ganki ba, tabbas idan naganki zangane cewa kedin jininmu ce, tabbas naji hakan ajikina, naji ajikina cewa kece yarinyar da ƴar uwata ta rasu ta bari, kece wacce mukayi watsi da rayuwarki, bisa biyewa son zuciya!."
Hawayene suka wanke fuskar Ziyada, duk da cewa batasan wacece Aunty Ounnaisa'n ba, amma taji ƙaunar kyakkyawar matar da kamar ka latsa fatarta jini ya fito tsabar fari da hutu Acikin zuciarta.
Cikin karamci Malam Garba ya gaida Hajiya Mama, inda daganan ya kora musu bayani dakuma nuna musu Ziyada, inda yasanar dasu cewa ƴar Maryama ce, daga Hajiya Mama har Aunty Ounnaisa kuka suke, sosai suke kukan danasanin abun da suka aikata na shariya dakuma halin ko inkula da suka nuna, cikin zazzafan ƙaunar Ziyadan Hajiya Mama tajawota jikinta, hakanan takeji kamar ƴarta Maryama ne agabanta, kuka sosai Hajiya Mama tayi inda ta roƙi Ziyada akan tayafe musu watsi da ita da sukayi, haka Ziyada tayi kuka sosai, amma na tsananin farincikin ganin dangin mahaifiyarta, nanfa Hajiya Mama ta gabatar mata da Aunty Ounnaisa amatsayin ƙanwar mamanta, daganan kuma Hajiya Mama ta ƙira dukkan familynta inda tace dasu tanason ganinsu, aikuwa cikin mintuna kaɗan gaba ɗayansu suka hallara ababban falon nata, ita da kanta tagabatar musu da Ziyada, tabbas kamannin Ziyada dana ƴar uwarsu Maryama yayi yawa sosai, kusan kowannensu saida yayi kuka musamman ma Alhaji Ahmad Rufa'e wanda yake shine babba agidan, kuma hamshaƙin mai kuɗine, sosai yayi kukan tunawa da ƴar uwarsa, awannan rana sosai Ziyada taga gata irin wanda bata taɓa gani ba a iyaka tsawon rayuwarta, gaba ɗaya ƴan uwan mahaifiyarta ta sai nannan suke da ita, kowanne daga cikinsu burinsa shine ya nuna mata tsantsar soyayya da kulawa, koda yamma yasomayi nan suka fara haraman tafiya don jirgin 6 zasubi sukoma Abuja, sam ƴan uwan mahaifiyar nata basu so haka ba, sunso ace takwana, amma babu yanda suka iya, don Malam Garba yace dasu mijinta bai bata izinin kwana ba, wasu irin tsaraba suka haɗota dashi mai uban yawa, inda Alhaji Ahmad yace suma zasuzo su Abujan Insha Allah, Nan Ziyada ta rubuta masa adreshin su, gaba ɗaya ahalinne suka rakosu zuwa airport saida sukaga tashinsu sannan suka juyo zuwa gida.
Ƙafe 7 daidai acikin garin na Abuja yayi musu, wata jibgegiyar mota Sooraj ya turo dan a ɗaukesu, daga airport din kaitsaye gida aka wuce dasu, duk yanda Ziyada taso babanta ya bari ya kwana ƙin amincewa yayi, haka tanaji tanagani ya shiga mota driver ya maidashi gida.
Agajiye tayi wanka, koda ta fito daga wankan, kaitsaye jakan makarantarta ta ɗauƙo, nan tashiga haɗa takardun da zata karanta don gobe zasu fara zana waec examination inda daga ss 2 tayi tsalle zuwa ss3 don zana jarabawan waec kamar yanda Mah Love ɗinta ya buƙata.
Waya suka ɗan taɓa da Nasmah da kuma shukra don suma a ss2 din zasu zana jarabawan ta waec, daganan kuma sai suyi neco da jamb, akasalance ta aje wayan nata tare da ɗan juyowa, jitayi tafaɗa cikin jikinsa, idanunta taɗan zaro waje don sam bataji shigowarsa cikin ɗakin ba, hannayensa yasanya inda ya warware tawel ɗin jikinta, take towel ɗin ya faɗi yayi ƙasa, ganinta haka naked yasashi jan wani irin dogon numfashi tare da ɗan lumshe idanu, kana ya jawota ya mannata da jikinsa, kullum ƙara kyau take, yayinda yakejin skin ɗinta na ƙara laushi like cutting, ɗan rage tsawonsa yayi tare da ɗaura kansa akan wuyanta, cikin kasalan daya sauƙar mata lokaci guda tace.
"Mah Love am tired fa."
Saurin ɗago kansa yayi ya dubeta, tare da sakin wani murmushi, laɓɓansa ya cija kana ya riƙe waist dinsa yana kallonta, cikin muryarsa mai ɗauke da aji yace.
"Yaushe kika girma, da har kike ƙoƙarin yi min wayo?."
Dariya tayi harsaida fararen haƙwaranta suka bayyana, ahankali taɗan karyar da wuyanta gefe cikin salonta na shagwaɓa wanda akoda yaushe ke masifar ƙara mata kyau tace.
"Please ɗan kaɗan ko?."
Kansa yagirgiza, cikin silent voice ɗinsa yace.
"A'a dayawa."
Hannunsa ta kama inda ta zagayo ta bayansa, ɗan tsalle tayi tare da ɗalewa saman bayansa, kana ta ɗaura hannuwanta akan shoulder ɗinsa, cikin jin daɗin samun kanta akan bayansa tace.
"To kaɗan yi yawo dani please ko zan dainajin gajiyan."
Wata t-shirt ɗinsa dake aje kan gado ya ɗauka tare da zura mata ajikinta, goyonta yayi da kyau kamar wata ƴar baby haka ya nufi ƙofar fita ɗakin da ita, luf tayi abayansa tare da lumshe idanunta, kaitsaye ƙofar dazai fitar dasu a part ɗinnasu ya buɗe ya fita, da sauri ta buɗe idanunta, ganinsu a falon Oummu yasa tasoma ƙoƙarin sauƙa daga kan bayannasa, amma ina yaƙi bata daman hakan, cikin yanayi naɗan tsoro takawo bakinta daidai saitin kunnensa inda ta ɗana masa cizo, cikin yanayi na jin zafi yaɗanyi ƙara, tare da saketa ta duro ƙasa, dariya tashiga yi masa sosai, idanunsa ya zuba mata Musamman ma yanda yaga tayi masifaffen kyau da tana dariyan, kanta yayo da sauri ta soma ja da baya baya hannu yasa zai kamota aguje tanufi ƙofar falonsu, hartakai bakin ƙofar ya cafko hannunta inda ya juyo da ita, azafafe ya mannata ajikinsa tare da ɗaura bakinsa akan nata.
Da sauri Oummu da tun fitowarsu take kallonsu tayi saurin juyawa takoma cikin ɗakinta, don dama tsaye take asama hakan yasa basu ganta ba, tana shiga ɗaki ta sauƙe ajiyar zuciya, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Gobe goben nan zaku koma gidanku, bazaku ci gaba dayin iskancinku agabana ba, bansan ma yaushe kuka zama mararsa kunya ba sam!."
Sosai suke kissing ɗin juna hartakai ga tsayuwa naneman gagaransu, hakan yasa ya ɗauketa suka shige cikin falo, kai tsaye akan gado ya shumfuɗeta, rigar jikinsa danata ya zare, tare dayi musu light off na hasken ɗakin, haɗuwar naked skin ɗinsu waje ɗaya shiya ƙara zafafa matsanancin sha'awar juna azuƙatansu. Yau salon nasu ya banbanta dana kullum, hakan yasa gaba ɗaya suka manta duniyar da suke, cikin wani irin yanayi mai kama da shiɗewa take fusgar numfashi da ƙyar, ahankali ta buɗe bakinta yayinda idanunta suka cika da ƙwalla, yanayin yanda yake ƙara shigewa cikin jikinta da kuma yanda yake groaning su suka sanya hawayen dake cikin idanunta gangarowa, ita kanta batasan hawayen na menene ba saidai zata iya dangantasa da cewar yanayin da take ciki ne yasanyasu fitowa, hannunsa yasanya inda ya rungumota sosai, bakinsa daya kasa rufuwa tun ɗazun ya ɗaura akan nata, lokaci guda suka sake shiɗewa, ita kanta bazata iya misalta irin daɗin dayake jiyar da ita ba, wanda har yakai ga tanajin wani irin abu na yawo acikin kanta, shikuwa Sooraj kwata kwata nutsuwa da tunaninsa basa jikinsa, haka yakejinsa kamar yana swimming cikin kogin zuma, sai yaji yanason ƙyaleta sai kuma yaji sam bazai iyaba, kasancewar daɗin dayakeji ya zarce misali.
Sam bazata iya sanin yaushe kuma tayaya bacci ya ɗaukesu ba, haka sukayi bacci yana cikin jikinta, inda take ƙasansa shikuma yana sama, bacci sukayi cikin matsanancin soyayyar juna.
Washe gari da safe kuwa tunda wuri ta shirya inda, ta ɗauki duk wani abun buƙatarta wanda zata buƙata wajen exam din, shida kansa yabata break taci, kana ya ɗauketa suka tafi makarantar.
Awansu ɗaya da rabi acikin babban examination hall ɗin suka kammala zana jarabawar tasu ta Biology, koda suka fito daga jarabawan hira suka ɗan taɓa dasu Nasmah kafun daga bisani yazo da kansa ya ɗauketa, sosai tasha mamaki ganin sunnufi wata hanya daban bana gidan Oummu ba, maigadine ya wangale musu gate, inda ya tura hancin motar cikin gidan, ganinsu acikin gidan dasu Oummu suka taɓa kawota yasa ta ɗan zaro ido cikin yanayi na mamaki tace.
"Mezamuyi anan?."
Hannunta yakama suka shiga cikin gidan, saida suka kawo har tsakiyan falon kafun yasanya hannuwansa ya dafa shoulder ɗinta cikin kulawa yace.
"Mundawo nan gidan, nanne gidanmu, kuma anan zamuyi rayuwa, ko bakyaso?."
Murmushi tayi tare dayin hugging ɗinsa, ahankali tace.
"Inaso sosai"
Shida kansa yayi mata wanka inda ya samata wasu kaya marar nauyi. Gaba ɗaya wunin ranan atare sukayi inda sosai yake maida hankali wajen sauraran shagwaɓan da taketa zuba masa.
Tayaya zai misalta irin matsanancin son dayake mata? yanajin shaƙuwarsu acikin jininsa, sosai yake mata wani irin so da babu kamarsa aduniya, akanta zai iyayin komai, yanasonta fiye da yanda yakeson ransa.
***
Sosai zamanta dashi keyi mata dadi, yayinda kullum shike kaita exam yakuma dawo da ita, inda yau sukayi geography wanda kuma shine papern ƙarshe.
Tunda ya ɗaukota a school ɗin ya lura da cewar kamar batajin daɗi, hakan yasa yaketa tattalinta, maimakon ya wuce da ita gida, kai tsaye sai yawuce da ita, unguwar wuse zone 4 inda tuni yasayawa mahaifinta gida anan harma sun dawo, can yakaita daganan yakoma wajen aikinsa, haka ta wuni agidan tana dariyan Inna Ma'u, don kuwa duk jimawan Inna Ma'un agidan baisa tadaina halinnata ba, haka nan take kullum ci wannan sha wancan, bakinta baya taɓa zama shiru, inta ritsa apples saitaci guda biyar atake, sannan sai jarababben son kallon tsiya inta ɗaura idanunta akan tv, bata ƙaunar abun da zaisa ta kawar dasu.
Sai da akayi sallan isha sannan yazo ya ɗauketa.
Washe gari da safe kuwa mutanen Maiduguri sukayiwa gidan nata tsinke, sosai tacika da tsananin farinciki, haka Aunty Ounnaisa takawo mata kayayyakin gyara na shuwa masu masifar kyau da tsada, ita da kanta takaisu gidan Oummu dan su gaisa, sosai Oummu taji daɗin zuwansu, haka sukayi hira sosai, kwanansu ɗaya suka bi jirgi suka koma Maiduguri.
**
Alhamdulillah jikin Pharouk yanata samun sauƙi, inda yake samun kyakkyawar kulawa daga wajen doctors, harzuwa yanzu nadama ne cike fal azuciyarsa, tabbas yayi danasani mai tsanani, inda kuma yaƙudurta aransa cewa, koda yagama warkewa zai cigaba da zama a Germany bazai koma Nigeria ba, cikin ikon Allah kuma sauƙi nata samuwa masa, inda iyayensa suka yanke shawaran cewa dazaran yagama samun sauƙi zasu ɗaura masa aure da ƴar yayan mamansa, koda yaji shawaran nasu baiƙi ba donshi yanzu rayuwa takoya masa hankali.
Ina labarin Aneesa da Yasmeen masu buri da fatan mallakar SOORAJ? arayuwa dama ance ka shuka alkhairi saika girbi me kyau, gaba ɗayansu rayuwa tayimusu ƙunci, inda Mahaifin Aneesa yayi mata auren dole da wani mai wanke masa motoci, kasancewar yaga al'amuranta nason fin ƙarfinsa, ita kuwa Yasmeen yawon duniyancinta take ta bugawa don ta kasa samun mai aurenta, tuni idanunta ya buɗe inda ta gudu tabar Nigeria can America takoma da zama, tana iskanci da mazan turawa suna biyanta maƙudan kuɗaɗe, duk da cewa bajin dadin rayuwar take ba amma bata da zaɓi.
Bayan wasu watannu.
Acikin wasu watannin da suka shuɗe abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa harda auren Mas'oud da budurwarsa Aisha, da kuma auren Al'mustapha da ƴar kanwar Oummu me suna Jaminash,, inda su Sooraj da Ziyada suka taka rawar gani sosai abikin, acikin watannin da suka gabata ne kuma, sukayi neco da jamb, inda har result ɗinsu ya fito, sosai jamb ɗinta yayi kyau, hakan yasa kaitsaye Sooraj ya sama mata admission a Nile University Abuja, inda taci gaba da karantar science, don alƙawari ta ɗaukarwa kanta cewa zatayi karatu tuƙuru dan ganin tazama babban likitan mata.
Alhamdulillahi tafara karatunta cikin nasara inda komai ke tafiya mata ayanda takeso, wani babban al'amarin da ta soma lura dashi shine yanda gaba ɗaya jiki da yanayinta suka sauya, sosai taƙara zama babbar mace skin ɗinta yayi fresh harwani shinning yake, yayinda hips ɗinta suka ƙara girma sosai, gawani irin matsanancin kasala haɗe da yawan bacci dake damunta. Hakanan yau tatashi da wani irin zazzafan zazzaɓi, ganin haka yasa RAJ gaba ɗaya ya ruɗe, shida kansa ya kimtsata inda kaitsaye ya wuce Nizamiyye hospitall da ita.
Sosai sukayi checking ɗinta, kana suka fitar da result ɗin abun dake damunta, fuska ɗauke da murmushi likitan ya miƙawa Sooraj result din inda yayi masa congratulation, domin Ziyada na ɗauke da ciki har na tsawon 4 month.
Mamaki, farinciki, nishaɗi, sune gaba ɗaya suka cika zuciyar SOORAJ bazai iya misalta daɗin dayaji acikin ransa ba, idanunsa ya lumshe ahankali.yace.
"Allah Alhamdulillah! haƙiƙa baiwarka da buwayarka ta gagari misali, kaika ɗauramin lalura alokacin da kaso, kana kayayemin ita alokacin da kaso, yanzu kuma gashi ka azurtani alokacin da kaso!" hawayene suka cika cikin idanunsa, sai kawai yajawo Ziyada yayi hugging ɗinta sosai, wani irin matsanancin ƙarin ƙaunarta yakeji acikin ransa.
Tabbas itaɗin alkhairi ce acikin rayuwarsa, shigowarta cikin rayuwarsa ya basa farinciki mai yawa, saboda ita yafarajin kansa cewa shima mutum ne kamar kowa, cikin tarin soyayyarta ya ɗaura mata kiss agoshinta, ganin ƙwalla acikin idanunsa yasa itama nata idanun suka kawo ruwa, tabbas taji daɗi sosai, Allah Abun godiya, wai yau itace ke ɗauke da cikin SOORAJ ajikinta, mutumin da zuciarta ke matuƙar ƙauna da bege, wanda ko da wasa bata taɓa kawo cewar zai aureta ba ma, daga asibitin kaitsaye gidan Oummu suka nufa, itadai kunya takeji tana Allah Allah kada Sooraj yafaɗawa Oummu wani abu, saidai kuma tunowa da tayi cewar shiɗin bamai yawan magana bane yasanya, tabisa suka shiga falon Oummun kai tsaye, fuska ɗauke da murmushi Oummu dake tsaye a dinning table ta amsa musu sallaman da sukeyi, batare da zato ko tsammani ba taji Sooraj yayi hugging ɗinta sosai, kansa ya ɗaura akan kafaɗanta tare da lumshe idanunsa, dame zai godewa mahaifiyartasa wacce ita tayi sanadiyar samuwar farincikinsa? haƙiƙa Oummu tacika uwa ta gari data aura masa Ziyada, yana alfahari da mahaifiyartasa sosai, hawayene suka cika idanunsa harsuka samu daman ɗiga akan kafaɗan Oummu, cikin yanayi na mamaki Oummu taɗago kansa tare da dubansa, itama hawayen ne suka cika idanunta, cikin sanyi tace.
"Meyataɓa zuciar Jarumin ɗana hartakaisa ga zubar da hawaye?."
Murmushi yayi tare da ɗaga hannunsa yayi mata nuni da Ziyada wacce ke tsaye tana kallonsu, kallon Ziyadan Oummu tayi cikin, sanyin daya kasa ɓoye tsananin shauƙin dayake ciki yace.
"She is pregnant!"
Idanu Oummu tazaro.cike da matsanancin farinciki, sosai abun yazo mata amatuƙar bazata, hakan yasa tayiwa Allah Sujjada tare da gode masa, nanta rungume Ziyada wacce gaba ɗaya kunya ya hanata sakat.
Haka Oummu tayita nannan da Ziyada inda take taƙira Abba tasanar masa, faɗan irin farincikin da Abba yayi ɓatawa ne, nan Oummu tashiga ƙiran ƴan uwa da abokan arziki tana faɗa musu, kowa murna yake tayata sosai.
Tattali haɗi da kulawa ziyada ke samu daga wajen mijinta da kuma mahaifiyarsa, kowa ji yake da ita haka suke lallaɓata kamar ɗanyen ƙwai, basason duk wani abu dazai taɓa ta.
Sannu ahankali take renon cikin jikinta kana kuma take zuwa makarantarta, sam cikin nata baihanata duk wani hidiman mijinta ba, musmaman yanda Sooraj yazame mata kamar yaro ƙarami, koda yaushe yana liƙe ajikinta, ayanda ta fahimta kuma shine idan har ya shafe sama da kwana biu bai kusanceta ba to hakanan zata ga yadawo kamar wani marar lafiya, yamaida ita abinci kuma ruwan shansa.
Cikin ikon Allah yanzu cikinta yashiga wata tara harda ƙarin kwanki, ganin yanda cikin nata yayi girma sosai ne yasa Oummu ɗaukota ta dawo da ita gabanta, nanfa Sooraj shima ya tattaro yadawo gidan Oummun dan kuwa baya taɓa iya bacci idan baiji ɗumin jikin Sunshine ɗinsa ba.
Awata ranan larabane naƙuda ya tashiwa Ziyada gadan gadan tun tana daurewa hardai Oummu tafahimta haka suka ɗauketa suka wuce da ita asibiti,