Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   4 / 48

9K to 12K   out of 142.5K words

yi tare da yunƙurin ƙwace kanta amma riƙon da yayi mata bana wasa bane,  ɗan kwalin dake kanta ya fusge ya yi cilli dashi gefe, ganin haka yasa taƙara fasa ihu haɗe da turjewa, amma takasa ƙwacewa, hanunsa yasanya da iyaka ƙarfinsa ya ja rigan koɗaɗɗiyar atamfan dake jikinta, ɓesss kakeji rigar ta yage, dama tuni kayan sunyi laushi.  Ganin saman ƙirjinta ya bayyana afili, yasa samarin suka bushe da dariya, kowanne acikinsu jikinsa yaɗauki mazari, burinsu kawai shine suga sun farketa.    Wani irin ihu Ziyada tasa tare da kafa bakinta akan hanun wanda ke riƙe da ita ta sakarmasa cizo, awahalce yasaketa yana fidda wani irin ƙaran azaba, itakuwa aguje ta lula cikin jejin.   Ganin haka yasa suka rufa mata baya, gudu take sosai  suna biye da ita, sam batasan cewa takawo bakin titi ba,  aguje ta zo zata bi takan titin tasake faɗawa wani jejin... Kafun ƙiftawan ido wata mota da tataho aguje tayi sama da ita, tim haka ta faɗo ƙasa.   Amatuƙar razane yafito daga cikin motar yayo kanta,  waro kyawawan idanunsa waje yayi tare dasa hanu ya toshe bakinsa, lokaci guda jikinsa yaɗauki rawa ganin irin ɓarnar da yayi,  kwance take cikin jini ba ako iya gane kamanninta,  wani irin rawa jikinsa keyi kamar anjona masa shocking, hannayensa duka yasanya yaɗagota, buɗe motar yayi yasata agidan baya, yanashiga wajen driver ko gama rufe murfin motar baiyiba, ya figi motar da gudun gaske.   Samarinnan naganin abun daya faru sukayi saɗaf saɗaf suka bar wajen, cike da haushin rashin samun nasara da basuyi ba.

Gudun da yakeyi har ya wuce hankali, tamkar zaitashi sama, gaba ɗaya ya ruɗe, ganin yanda jini ke fita ajikinta.  Alokacin daya shigo cikin garin Kaduna, gani yake kamar motar tasa bata gudu, hakanne yasanya yaƙara gudun motar mintuna kaɗan saigashi a cikin asibiti,   amatuƙar ruɗe yaje yaƙira likitoti suka zo suka ɗauketa aka wuce da ita emergency room.   Ganin yanda kanta ke zubda jini yasa likitoti suka duƙufa akanta wajen bata taimakon gaggawa.

Shikuwa SOORAJ yana nan awaje yakasa zaune yakasa tsaye, hankalinsa amatuƙar tashe yake, tsoronsa ɗaya kar ace masa ta mutu,  wani irin gumi ne ke fesowa ta goshinsa, kowa yagansa yasan cewa yana cikin tashin hankali.

Aƙalla sama da awa ɗaya da rabi likitoti suka ɗauka suna bata taimakon gaggawa,  cikin ikon Allah Kuwa sun shawo kan lamarin, saidai bata farfaɗo ba, amma sun tsaida jinin dake fita daga goshinta dakuma gefen kanta da ya fashe.

Yana tsaye likitotin suka fito daga Emergency room ɗin.  Da sauri yataho wajen  Dr.Salees, baikai ga cewa komaiba Dr.Salees yasakar masa murmushi tare da sanya hanu ya dafa kafaɗan SOORAJ ɗin.   
"Karka damu SOORAJ munshawo kan matsalan, sai dai mujira farkawanta, muje office saina ƙarasama sauran bayanin"

Babu musu SOORAJ yabi bayan Dr.Salees zuwa office ɗinsa.

Suna shiga cikin office ɗin Dr.Salees ya nunawa SOORAJ wajen zama, kana shima ya zauna.

Sakeyin musabaha sukayi kafun Dr.Salees yacigaba da cewa. 

"Ka kwantar da hankalinka ba wani babban damuwa bane, buguwane  kawai, tabugu sosai gaskiya, amma dayardan Allah munshawo kan komai, saidai kuma bamusan awani irin yanayi zata buɗe idanuba, amma muna kyautata zato, Insha Allahu ma zata tashi lafiya, Allah dai yatsare na gaba"

Da "Ameen" Kawai SOORAJ ya amsa yana mai sauƙe ajiyar zuciya akai akai.

Bisa umarnin SOORAJ aka maidata wani special room,,,,   ahankali yaturo ƙofar ɗakin yashigo, sauƙe idanunsa yayi akanta, tana kwance flat kanta na kallon sama, gaba ɗaya rigar dake jikinta ta ɓaci da jini, kanta kuwa a ɗaure yake da farin bandeji (bandage) yayinda tulin gashin kanta ke watse akan pillow, ɗauke kansa yayi daga kallonta tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kan wata kujera yaje ya zauna haɗe da kai dubansa kan ledan ruwan da aka saƙalashi ajikin wani dogon ƙarfe, yana shiga cikin jikinta ahankali, kallonsa yakuma dawowa dashi kan agogon kamfanin Gucci dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.  Ƙarfe goma na safe daidai haka agogon yanuna masa,  hanunsa yaɗaura akan haɓansa haɗe da furzar da iska daga bakinsa,  miƙewa yayi tsaye tare da nufar ƙofar fita, haryaje bakin ƙofar kuma sai ya tsaya juyowa yayi ya kalleta, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta da kusan rabin breast ɗinta suke a bayyane, da sauri yakawar da kansa, wani irin bugawa yaji kansa yayi, kamar andoka masa guduma,   jacket ɗin dake jikinsa ya cire tare da nufar inda take kwance, saidai koda wasa baisake barin idanunsa sun kalli ƙirjinnata ba,   jacket ɗin nasa yarufa mata ajikinta, kana yafice daga cikin ɗakin.     Office ɗin Dr.Salees yaje ya biya kuɗi, aka tura nurses guda biyu wanda zasu tsaya akanta don bata kulawa, shikuwa motarsa yashiga yabar asibitin.     Direct gidansa ya nufa ransa ajagule, sam baiso haka takasance ba, yau yatsara tafiya Abuja, amma ga abun daya faru, zaman cikin Kaduna yakamashi dole harzuwa farfaɗowar yarinyar.

Wanka yayi kana yazo ya kwanta akan gado, lamo yayi yana tunanin yanda accident ɗin ya kasance, sai alokacinne ma mamaki ya kamasa,  ƙaramar yarinya irinta mai zai fito da ita awannan lokacin? da dukkan alamu kuma ba acikin hayyacinta take ba.  "To kodai mahaukaciya ce?" ya raya hakan azuciyarsa, da sauri ya kawar da wannan tunanin acikin ransa,  wayarsa yaɗauka ya kunna karatun Al'Qur'ani mai girma, yana cikin jin karatun bacci ɓarawo ya sace shi.....

(More Comment nd Vote more typing😝 kuyi haƙuri yau banyi editing ba...   Zan fara halina fa readers idan nayi update yau sai jibi kuma🤣😝 Allah yasa bazaku takura ba. )

         *🍇SOORAJ FANS GROUP🍇*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HFwwNXNTaW6HUbrbHjBHVM

*Idan kinsan Bazakina Comment ba kada kishiga, ONLY NOVELS kawai mukeso, bayan haka bamason kowani irin post.... Bamason Talla kona menene, idan kinyi zaki ganki a waje*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand ans succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

              *WATTPAD*
        @fatymasardauna

        *CHAPTER 6*

Tunda ya kwanta bacci bashi ya tashi ba sai da aka soma ƙiraye ƙirayen sallan Azahar.  Toilet yashiga yayo wanka.  Still riga da wando na jeans yasanya ajikinsa. Masallacin dake kusa da gidansa ya nufa donyin sallah.   Tun da yafita yin sallah baidawo ba sai ƙarfe huɗu na yamma, wanka yasakeyi.   Combat jeans ne ajikinsa baƙi sai kuma wata farar riga mai ɓaƙaƙen aninaye.    Yana tsaye agaban dressing mirror yana taje tulin sumar kansa, wanda yasha aski irin na zamani, screen ɗin wayarsa ya soma kawo haske, ɗan matsawa kusa da yawartasa yayi.   Sunan  Mas'oud ne ke yawo akan screen ɗin wayar, kasancewar ya sata a silent shiyasa batayi ƙara ba, ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa. 

 "Ina falo" Inji cewar Mas'oud.

 "Okay"  kawai Sooraj yafaɗa akasalance tare da aje wayartasa,   bai fita falon ba yaci gaba da taje sumar kanshi, saida ya kammala duk wani abu dazaiyi kana ya ɗauki wayarsa dakuma car key ɗinsa yafita zuwa falo.

Cike da takaici  Mas'oud ke kallonsa,  duk da yasan cewa halin Sooraj ne shanya mutane, amma kuma abun da yayi masa yauɗin yayi masa ciwo.  

"Inakuma zakaje?" Mas'oud yatambayesa yana me ƙare masa kallo.

"Asibiti"
SOORAJ yabashi amsa ataƙaice.

"Abiti kuma? Baka da lafiya ne?" Mas'oud yajero masa duk waƴannan tambayoyin alokaci guda.

Ɗan ya mutsa fuska yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kwantaccen sajen dake shumfuɗe akan fuskarsa.   
  "Accident mukayi, zanje na duba yarinyar dana bugene kota farfaɗo"  ya faɗi haka yana me nufar hanyar fita daga falon, kai kawai Mas'oud ya girgiza haɗe da miƙewa tsaye yabi bayan SOORAJ ɗin.   SOORAJ ne ke tuƙa motar yayinda Mas'oud ke zaune agefen mai zaman banza.  Tafiya suke babu wani wanda yace da   ɗan uwansa wani abu, ahaka har suka kawo asibitin,   sam Mas'oud baiwani damu da shirun da SOORAJ ɗin  yayi ba, because yasan hakan halinsa ne, bakoda yaushe yacika yawan magana ba, amma idan kafahimcesa yana da daɗin zama, dan bayashiga abun da babu ruwansa...

Atare suka jera suka shiga cikin asibitin.   Office ɗin Dr.Salees suka nufa, shiyayi musu jagora zuwa ɗakin...  dama yana shirin zuwa dubata kenan suka shigo.

Tananan har yanzu bata farfaɗo ba, wasu allurai Dr.Salees yayi mata,  juyawa yayi ya kalli SOORAJ dake zaune akan wata plastic chair....  "Zata iya farfaɗowa akowani lokaci da yardan Allah, Yana da kyau katsaya atare da ita." Inji cewar Dr.Salees.

Kai kawai ya iya jinjina wa Dr.Salees alaman yaji, fita Dr.Salees yayi daga cikin ɗakin. 

Kallon Mas'oud daya kafe yarinyar da idanu SOORAJ yayi, tsayawa yayi yana kallon yanda idanun Mas'oud ke yawo ajikin yarinyar ko ƙyaftawa ba yayi,  takaicin Mas'oud ɗinne yakamashi, sam shi kam baiga wata mace aduniya dazai tsaya ɓata lokacinsa wajen kallonta ba, yaga manyan mata da suka amsa sunansu mata baiji komai gamedasu ba balle wannan ta tsitsiyar yarinyar, inbanda ƙaddara ma maizai haɗashi da ita,  sam shi baya shiga sha'anin mata, saboda yasan menene matsalarsa, wannan ma don dolene kawai, amma dazaran ta farfaɗo zaisa amaidata inda ya ɗaukota.

"Tunda kana nan ni inaga kawai zantafi yau nakeso nakoma Abuja, please kakula da ita, idan tafarfaɗo tagayama garinsu saika maida ita!" SOORAJ yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye.

Da sauri Mas'oud ya kallesa cikin mamaki yace "Zaka koma Abuja kuma?"

Kai SOORAJ ya jinjina masa alamar "Eh"

"Hmmm lallai SOORAJ baka da imani, kabuge yarinya kuma katafi kabarta? wato nine marainin wayonka shine kakeso katafi kabarni da ita ko?"

Murmushin gefen baki SOORAJ yayi wanda yayi masifar ƙarawa fuskarsa kyau. 
 
"Mene matsalarka Mas'oud idan kakula da ita? Kasan inada abubuwan yi da yawa, banjin kuma zan iya ɓata lokacina akan mace" SOORAJ yafaɗi haka yana me kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

"Nima ai bazaman banza ne sana'ata ba, kai kabugeta kuma kai kake da alhakin tsayawa akanta kakuma bata kulawa harsai ta warke, saboda haka ni kaga tafiyata" Mas'oud yafaɗi haka aƙufule, don ya lura tsagwaran iskanci ne ke damun SOORAJ ɗin.

Still murmushin gefen baki yayi haɗe da bin Mas'oud ɗin da kallo harya fice daga cikin ɗakin.      Kan kujera yakoma ya zauna, yayinda ya juyawa gadonnata baya, wayarsa yaciro ya soma latsawa..

Ahankali take ware manya manyan oily eyes ɗinta masu kyau da burgewa,  dishi dishi tasoma gani, kafun daga bisani idanun nata suka soma washewa,    ɗakin tasoma ƙarewa kallo, yayinda ƙwaƙwalwarta ke tunano mata abubuwan da suka faru, amatuƙar razane ta ƙwalla ƙara..     "Wayyo Allah Nashiga Uku dan Allah karku cutar dani!!"

Azabure yajuyo jin ihunta abayansa,   yunƙurin tashi zaune tasomayi amma ina jin kanta take yayi mata wani irin nauyi, ga wani raɗaɗin azaba dake ratsata...

Tsuka yayi ƙasa ƙasa tare da maida kansa ga wayarsa yacigaba da latsawa, yatsani mutumin da baida nutsuwa.

Babu yanda ta iya haka takoma ta kwanta tana gunjin kuka, saboda kotafi kowa ƙoƙari ayanzu bazata iya tashiba.   Idanunta ne suka sauƙa akan bayansa, domin dama yabata baya.   Ganin namiji na zaune ya bata baya yasa taƙara volume ɗin kukanta,  jikinta na rawa tace "Dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni, nakoma inda nafito, wallahi nayarda ma ni Zan auri tsoho ɗan dashe'n, nidai kada ku cutar dani, wallahi ni marainiya ce, dan Allah ku ƙyaleni natafi!" kuka take tsakaninta da Allah tana zabga magiya da roƙo, amma ko motsi baiyiba balle tasaran zai juyo gareta, duk atunaninta shiɗin ɗaya daga cikin mazan da suka ka mata ɗazu ne. 

Ganin baijuyo gareta ba yasa tacigaba da kukanta,    yana zaunene kawai amma jiyake kamar ana hautsina ƙwaƙwalwarsa, kuka yana ɗaya daga cikin abun daya tsana,   wata tsuka yaja me ƙarfi haɗe da juyowa ya watsa mata wani irin kallo, idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna,  wani irin shock Ziyada taji acikin jikinta, lokaci guda ta haɗiye kukanta,  ɗauke idanunsa yayi daga cikin nata yaci gaba da latsa wayarsa.  

Ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, neman kukannata tayi ta rasa, sai jikinta daya ɗauki wani irin zazzaɓi mai zafi.   Idanunta na kallon bayansa, cikin wata irin murya mai sanyi tace.... 
"Kamaidani gidanmu kaji!"

Tsayawa yayi daga latsa wayar  da yake yayi shiru...  Bugun zuciyarsa ne ke ƙara tsananta, lumshe kyawawan idanunsa yayi, tare da sauƙe wata irin ajiyar zuciya.   Tashi yayi ya fice daga cikin ɗakin batare daya kalli koda ɓangaren da take ba.

Ganin yafita daga cikin ɗakin yasa  Ziyada fashewa da kuka. 

"Shikenan na mutu yatafi ƙiran sauran ƴan uwannasa, shikenan zasu zo su lalatamin rayuwa!" Cikin gunjin kuka take maganar.

Jin anbuɗe ƙofar ɗakinne yasa, tayi saurin kallon bakin ƙofar,  murmushi Dr.Salees yasakar mata haɗe da cewa
"Yauwa Patient kintashi ko? sannu, yanzu inane ke miki ciwo ?"

Kasa amsa masa tayi saima kafesa da idanunta dake ɗigan ruwan hawaye da tayi,  kamar yasan tunanin da take acikin ranta, murmushi yakumayi akaro nabiyu haɗe da cewa "Ki kwantar da hankalinki nan asibiti ne, ba wai wajen da za'a cutar dake ba."

Rumtse idanunta tayi da ƙarfi sai alokacin tatuna da cewa tana cikin gudu taji wani abu ya doketa har saida ta ɗagu sama, to daga wannan lokacin bata sake sanin maiya faru ba sai yanzu data ganta cikin wani ɗaki.

Hanu Dr.Salees yakai jikinta ya taɓa, zafi zau yaji ajikinnata,   alluran daya shigo dasu yasoma ɓarewa,  ganin allura ahanunsa yasa Ziyada sake fashewa da sabon kuka, murya adashe tace "Don Allah kayi haƙuri karkamin, wallahi bazan sake guduwa ba!"

Mamakine yakama Dr.Salees sai kawai yatsaya yana kallonta.  Dai dai lokacin SOORAJ yashigo cikin ɗakin.

Kallonsa Dr.Salees yayi haɗe da cewa. "Yauwa SOORAJ gwamma daka shigo ai, kaga wannan ƙanwartaka tsoron allura takeyi, kuma akwai zazzaɓi ajikinta dole sai anyi mata allura sannan zata samu relief, bayan haka kuma yakamata kanemo mata ko tea ne tasha, akwai yunwa ajikinta sosai"

"Okay, kayi abun daya dace kawai!" SOORAJ yafaɗa a gajarce, domin baison yawan surutu.

Kai kawai Dr.Salees yagirgiza aransa yana mamakin miskilanci'n SOORAJ.

Ziyada na kuka haka Dr.Salees yayi mata allura, SOORAJ kuwa yana zaune ko kallon inda suke baiyi ba, earpiece ma yasa akunnensa yana sauraran cool music.   Dr.Salees nagama aikinsa yafita daga cikin ɗakin.

Cusa kanta tayi acikin pillow tana kuka, hakanan taji haushin  mugun mutumin daya sanya akayi mata allura, dama ance mata turawa mugayene to gashi yau ta tabbatarwa kanta, domin kuwa tana da tabbacin  cewa shiɗin idan ba bature bane to kuwa balarabe ne, don wannan farinnasa ba'a banza ba. 

Yana zaune aka soma knocking ɗin ƙofar ɗakin. 
 
"Come in" yafaɗa da ɗan ƙarfi.  Wani matashin saurayine ya turo ƙofar ɗakin yashigo, jikinsa sanye da wata jar riga  wacce agaba da bayanta aka rubuta MUZAFAS HOTEL da manyan harufa.   Manyan ledodin dake hanunsa ya miƙawa SOORAJ cike da girmamawa,   kuɗi SOORAJ yaciro daga cikin wallet ɗinsa ya miƙawa matashin saurayin.     Kallon SOORAJ saurayin yayi zaiyi magana, SOORAJ yaɗaga masa hanu, haɗe da cewa
"No badamuwa jeka kawai"

Godiya Matashin saurayin yashiga yiwa SOORAJ cike da murna yafice daga cikin ɗakin.

Ɗaukan leda ɗaya daga cikin ledodin SOORAJ yayi, cikin Unigue Voice ɗinsa yace
"Tashi kici abinci!"  yanayin yanda yayi maganar ne yasata saurin juyowa takalleshi, saidai kuma yanda ya fusge, yasa tashiga raba idanu kozataga wanda yayi maganar, domin ayanda yasha mur bazaka taɓa cewa shine yayi maganan ba.   Aje mata ledan akan ɗan ƙaramin drawern dake kusa da gadon yayi,  juyawa yayi cikin takunsa na isa yafice daga cikin ɗakin.  

Tana ganin fitansa ta sauƙe wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, har acikin zuciyarta tsoronsa takeji.

Shiru yayi bayan yagama sauraran jawabin  dake fita daga bakin Dr.Salees.

Hanu yasa yashafi sajensa,  sam bayajin yiwuwar abunda Dr.Salees ɗin ke faɗi,  daransa da lafiyansa bayajin zai iya kwanan asibiti.  Tashi yayi tsaye yabawa Dr.Salees hanu suka sakeyin musabaha kana yafice daga cikin office ɗin bayan yasanya hanu acikin wata takarda.   Ɗakin datake kwance ya nufa, bayajin abunda zai aikata akanta daidai ne, amma kuma hakan shikaɗai ne mafita.   Yasan abun da zuciyarsa ke raya masa ba abu bane mai kyau, amma kuma baida wata hanyar dazai samawa kansa hutu sama da wannan, idan kuwa har maganar da Dr.Salees yafaɗa masa gaskiya ne, to yazama lallai ya aikata abun da zuciyarsa ke umartansa daya aikata, a wani ɓangaren baidamu da wani irin kallo mutanen duniya zasuyi masa ba, yasan kansa yasan ba irin sa mata ke ɓuƙata ba, kyawunsa da haɗuwarsa afili kawai suke, amma abaɗininsa yafi kowani irin namiji rauni....

*(My Wattpadians Vote ɗinkufa yana ƙasa😥 I swear ku ƙara yawan vote kokuma nata baku gajeren pages)* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

               *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           
              *WATTPAD*
        @fatymasardauna

      *CHAPTER 7*

A ƙalla yaɗauki kusan mintuna 4 ajikin ƙofar, yayinda hanunsa ke  kan handle ɗin ƙofar. Cije laɓɓansa yayi kana yatura ƙofar ahankali yashiga.

Duka hannayensa ya zuba acikin aljihun wandonsa yana kallonta cike da takaici. Kallonsa yakuma maidawa ga ledan daya aje mata, yananan ayanda ya aje, don ko taɓa ledan batayi ba.

Ƴar ƙaraman tsuka yaja, haɗe da sanya hanu ya ɗan bugi kansa.   "Wannan yarinyar da'alama itace ƙaddarata ta biyu!" yafaɗi haka cikin wata silent voice, sam bayason damuwa, gashi yafahimci cewa ita kanta Yarinyar Damuwa ce mai zaman kanta agaresa.   "Yanzu da tayi bacci, shine takeso ya ɗauketa ko kuma me?" yatambayi kansa cike da takaicinta.
Tsuka ya kuma ja kana yafice daga cikin ɗakin.

Mintuna kaɗan wasu nurses su biyu suka shigo cikin ɗakin, kasancewar alluran da Dr.Salees ya mata nada matuƙar ƙarfi bazata iya farkawa nan kusa ba, yasa Nurses ɗin suka ɗaurata akan wani gado wanda keda ƙafafun taya,   haka suka turota akan gadon har bakin motarsa, buɗe musu gidan baya yayi suka sanyata aciki.    Da wani irin gudu ya figi motartasa yafice daga cikin asibitin,    shikaɗai yaketa zuba tsuka, har ya iso makeken gidansa dake cikin unguwar Malali, yana gama daidaita parking ɗin motar tasa, yaɗauki goran ruwan dake gefensa,  ɓalle murfin yayi haɗe da kai goran bakinsa,   gaba ɗaya ruwan dake cikin goran yashanye tas, ko kaɗan bai rageba,   yanaganin wayarsa na ƙara amma yaƙi ɗagawa,  duk da bai duba sunan dake yawo akan screen ɗin wayarba, amma yasan wake ƙiransa, tunda yatafi yabarsa kuwa to shima bazai ɗaga ƙiransa ba, idan wulaƙancine shima ya'iya salo salo.

Direct

4 / 48