Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   23 / 48

66K to 69K   out of 142.5K words

fesa acikin ɗakin take ko ina yaɗauki ƙamshi,  kayan shafansa ta jere masa akan mirror sannan ta ninke bedsheet ɗin dake ƙasa ta ɗaurasa akan gado,     saida ta maida komai dake cikin ɗakin nead kafun ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa wanda bashi da sanyi sosai,  audugan da ta gani acikin drawer ɗinsa ta ɗauko,  ahankali taƙaraso jikin gadon tare da zama daɓas akan carpet ɗin daya kewaye gadon,  dayake hannun nasa me ciwon ba'akan gadon yake ba hakan ya bata daman sanya hannunta ta kamo nasa hannun,  ruwa ta ɗiga ajikin auduga sannan tashiga goge masa busashshen jinin dake hannunsa, ahankali takeyi kuma cikin nutsuwa gudun kada ta tashesa.
Ahankali yaɗan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, cute face ɗinta ya kalla da kuma small lips ɗinta, maida idanunsa yayi ya rufe yana mejin yanda take lallaɓa hannun nasa tamkar wanda aka bawa ajiyan ƙwai,       sam batasan da cewa ya farka ba,domin gaba ɗaya tabada hankalinta  ga aikin da takeyi,     tas ta goge masa jini har ya zamana tana iya ganin yankewan da yayi,  wani irin tausayinsa ne taji ya kamata, tasan dole idan ya farka sai ciwon yayi masa zafi, wata ƙila yanzu ma yanayi masa zafi, tunowa da haka yasanya taɗan sunkuyo da kanta, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta adaidai kan ciwon, tayi hakanne saboda ta sama masa sauƙi, kasancewar idan taji ciwo in tana hurashi baya yi mata zafi, hakan yasa  tashiga yi masa.

Wani irin sanyi yakeji na ratsa jikinsa, duk da cewa ciwon bayayi masa wani zafi sosai, amma hakan da tayi masa ya sanya ya samu relief, don har wani sabon bacci  yaji yana fusgarsa, luf yasakeyi akan gadon tare da sake lumshe idanunsa.  Sai yanzu yakejin ya dawo cikin sense ɗinsa, sai yanzu abubuwan da yayi ɗazu ke dawowa cikin brain ɗinsa,     shiru yayi yana mejin yanda zuciyarsa ke bugawa,  tabbas  SHI BA NAMIJI BANE  yau ya sake tabbatarwa kansa da hakan,  duk da cewa tuntuni yasan yana da rauni ta ɓangaren mu'amala da mace amma baiyi tunanin matsalartasa takai har haka ba,  bazai taɓa iya biyawa wata mace buƙatarta ba, sannan bazai taɓa iya alfahari da kanshi amatsayin cikakken Namiji ba,  baisan menene Sha'awa ba, bai taɓa jiba bai kuma san ya akeji ba, baisan ya Sex yake ba bai kuma san ya daɗi da rashinsa yake ba.  Tabbas shi gwanine akowani ɓangare amma awannan ɓangaren shi rago ne.  Zuwa yanzu ƙwaƙwalwarsa takusa daina aiki domin kuwa tunani na neman  illata ta, Meyasa bayajin Sha'awar mace? Me yasa bazai taɓa iya yin sex da mace ba? Me yasa bayajin wani abu na musamman ajikinsa dan gane da kowacce mace? Waƴannan tambayoyin sunjima suna barazanan tarwatsa zuciyarsa wajen neman amsarsu amma har yau baisamu amsan ba, hakan yasa ya rufe sirrinsa yabar abun amatsayin ƘADDARA me girma agareshi. Ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe, tare da rumtse idanunsa da ƙarfi, shi LOOSER ne, amma duk da haka  baya fatan ci gaba da zama looser akoda yaushe, saboda haka ayanzu baijin zai baiwa hawayen dake cikin idanunsa daman fitowa......

(Kowani bawa da irin ƙaddaransa, haka kuma kowani labari da irin yanda aka tsarashi, tabbas nasan nan gaba kaɗan zanzo wajen da bazai taɓa yi muku daɗi ba,  bakuma zanzo wajen ason raina bane ba, labarinne yazo ahaka, sai ansha gwagwarmaya, sai anfuskanci ƙalubale, sai kuma anjure ake kaiwa ga daɗi,   tabbas wasunku nasan bazasu iya juran wannnan wajenba, nasan ƙorafe ƙorafen ku zaita iskeni, nasan zakuyi challenge's ɗina,  wasunku zasu faɗamin magana mai daɗi, wasunku kuwa zanji saɓanin haka daga bakunansu, tun ayanzu ina fuskantar challenge's daga wajen  wasu, tabbas  nice me labari kuma nice me rubutu, idan asonane ako da yaushe nayi abun dazai faranta ranku, wannan shine kullum fata na, watarana inada important abun da zanyi amma haka nake squeesing nayi typing duk dan nafaranta muku, shin me zanji araina idan kuka jefeni da magana marar daɗi? kunaga zanji ƙarfin guiwa da farincikin sake yi muku wani fejin da zaku karanta? Tabbas nasan kuna ƙoƙari sosai sosai,musamman yanda kuke mini votes da comment, har acikin raina ku na dabanne My Wattpadians people, acikinku wasu ke faranta raina akuma cikinku wasu ke disturbing ɗina, amma nidai ina muku son so, nasan wasu mutane dagangan suke faɗan wata maganan duk dan su ɓata raina, amma babu damuwa dukanku ni inasonku.... Ni mutumce me ƙaunar duk wani maisona.... Please! Please!! Pleaseeeee!!! Idan kinsan nan gaba kaɗan zaki fito kiyi challenging ɗina akan labarinnan don Allah ki haƙura da karantawa wannan roƙo ne nayi muku masu challenge's ɗina.  Love You all and Son So My lovely fans❤*

*Vote and Comment*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

            *WATTPAD*
        @fatymasardauna

#romance

                *Chapter 34*

A hankali idanunta ke lumshewa da alama bacci takeji, amma kuma har izuwa wannan lokacin bata daina hura masa iskan dake bakinta ba.   Ahankali yake  fitar da numfashi, yana mejin sanyi na sauƙa acikin zuciyarsa, juyo da kansa ɓangaren da take yayi tare da sauƙe gajiyayyun idanunsa akanta,   itama ɗago manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, hakan yabawa idanunsu daman sarƙewa acikin na juna,  wani irin mimmiƙewa gashin dake jikinta sukayi, take tsikar jikinta ya shiga zubawa, tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi,  ba komai ya haifar mata da hakan ba kuwa, face arba da sexy eye balls ɗinsa da tayi,  wanda suke lumshewa ahankali tamkar na mejin bacci.  ƙasa tayi da idanunta, batare da ta sake hannunsa dake cikin nata ba,  ƙofar ɗakin aka buɗe hakan yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli ƙofan, Almustapha ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama,  da sauri tatashi daga zaunen da take tare da sakin hannunsa ta koma gefe.   Ƙarasowa cikin ɗakin Almustapha yayi yana me ƙare mata kallo, cikin muryarsa me sanyi yace. "Ya tashi ne?"

Kai kawai ta iya gyaɗa masa alamar "Eh" Raɓawa tayi tagefenshi ta fice daga cikin ɗakin.   Binta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Sooraj wanda ko motsawa baiyi ba.

"RAJ" Almustapha yaƙira sunanshi.

"Ummm!" Sooraj ya amsa masa akasalance yana meƙoƙarin tashi zaune.

Kallonsa Almustapha yayi sosai sai kawai yayi murmushi tare da cewa.  "Ya jikin naka?"

"Wani yace maka banida lafiya ne?" Sooraj ya faɗa yana me ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon.

"No ni ne kawai nake tunanin baka da lafiya, ko dai mutanen naka ne suka motsa?" Almustapha ya tambaya yana me ƙoƙarin gimtse dariyan dake bakinsa.

Hararansa Sooraj yayi baice dashi komai ba ya nufi hanyar da zai sadashi da bathroom, sarai yasan iskancin Almustapha yawane dashi, yanzu idan ya tsaya yadinga ɓata ransa kenan.

Dariya Almustapha yayi tare da jawo laptop ɗin Sooraj ɗin yashiga amfani dashi.

Luf tayi akan gado tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai,  ƙwayan idanunsa ne keta yiwa nata idanun gizo,  lumshe idanunta tayi tare da sakeyin hugging pillow'n dake hannunta, hancinta takai kan hannunta wanda tariƙeshi dashi, sosai hannunnata ke ƙamshinsa, wani irin kasalane taji yana sauƙa mata, tabbas ayanzu tayarda da cewa shiɗin na musammanne, kamar yanda komai da ya shafesa yake na musamman. 


Tari yake sosai acikin toilet ɗin, wanda har hakan yaɗauki hankalin Almustapha dake zaune akan gado,  ɗan tsayawa yayi ajikin ƙofar toilet ɗin, tare da cewa "RAJ are you Okay?"  shiru baiji ya amsa masa ba, hakan yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin,  da sauri ya ƙarasa wajen Sooraj dake tsaye agaban sink yana goge bakinsa da tissue. 

Idanu Almustapha ya zaro tare da duban tissue ɗin dake hannun Sooraj hankalinsa amatuƙar tashe yace
"RAJ jinin mene wannan?"

Hararansa Sooraj yayi cike da ƙosawa yace
"Amma dai ban gayyatoka ba ko?"

Fuskar Almustapha babu alaman wasa ko tsokana yasake cewa. "RAJ jinin menene wannan? please tell me dama baka da lafiya sosai har haka ne?" Gaba ɗaya Almustapha ya ɗaga hankalinsa.

"Bakina ne ya fashe!" Sooraj yafaɗa ataƙaice yana me sanya ruwa ya shiga wanke bakinsa. 

Kamar statue haka Almustapha ya tsaya yana kallon Sooraj, sam bai yarda da cewa wai bakinsa ne ya fashe ba, cikin yanayi me ɗauke da tsananin damuwa yace

"Shi kuma tarin da kake fa?"

"Uhhhhhh! am tired, please Mustapha leave me alone!!" Sooraj yafaɗi haka yana me dafe forehead ɗinsa, sam bayason irin wannnan tambayoyin da Almustapha keyi masa.

Jiki asanyaye Almustapha ya juya ya fice daga cikin toilet ɗin, saidai har cikin ransa yasan wannan jinin daya gani abakin Sooraj bana lafiya ba ne.

Almustapha na fita Sooraj ya sanya duka hannayensa ya riƙe weast ɗinshi,  iska ya fesar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa, shikansa yasan bai taɓayin tari yaga jini ba sai yau,  sai alokacin ya tuna da cewa sam bayashan maganinsa.  Wanka yayi kana ya ɗauro alwala, towel ɗaure a weast ɗinshi ya fito, black jeans and black t-shirt ya sanya, duk Almustapha na kallonshi, ganin zai fita baice dashi komai ba yasanya Almustapha tashi da sauri ya bishi, atare suka tafi masallaci..... 

Saturday.

Kasancewar yau ba makaranta hakan yasanya tun tashinta tashige kitchine, zuwa yanzu ta iya abubuwa da dama na dangane da girki, saboda haka kafun Ummu ta sauƙo ma ta kammala kusan rabin aikin,  ɗauke da murmushi Ummu ta shigo cikin kitchine ɗin.

"Zieyaderh!" Ummu taƙira sunanta.

Barin aikin da takeyi tayi tare da juyowa, cikin ladabi tace " Ummu ina kwana"

"Lafiya lau" Ummu ta amsa mata tana me ƙarasowa cikin kitchine ɗin.  

Atare suka kammala aikin, kamar koda yaushe Zieyaderh ne ta jere duka abincin akan dinning,   Ƙamshin turarensa ne yafara sanar da ita zuwanshi, hakan yasa ta kasa ɗaga idanunta.  Shine agaba Almustapha na biye dashi abaya haka suka nufo wajen dinning ɗin, Ummu naganinsu tasaki murmushin jin daɗi.

"Morning Maaa!" Sooraj ya faɗa agajarce yana me ƙoƙarin zama akan kujera.

"Morning" Ummu ta amsa tana me ɗan shafa kansa.

Rungumeta Almustapha yayi tare da yimata kiss a forehead ɗinta cike da kulawa yace.
"Good Morning Ummuna!" Murmushi Ummu tayi tare da shima da shafa kansa tace.
"Morning My Son"

Tana ɗago idanunta suka faɗa cikin na Almustapha hakan yasa ta saki murmushi tare da cewa "Ina kwana"

Murmushin shima yayi mata haɗe da cewa "Kintashi lafiya?"

"Lafiya" ta amsa tana me ƙoƙarin serving ɗinsu. 
Ɗan satan kallon Sooraj tayi, taga gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa, cikin sanyi tace.
"Yayah Ina kwana!"

Shiru yayi kamar bazai amsa ta ba sai kuma ya amsa mata da "Lafiya" acan ƙasan maƙoshinsa. 

Kamar yanda tasani kuma taga bashida wani abun sha daya wuce fruit salad, hakan yasa ta ajiye wani glass bowl wanda ke ɗauke da fruit salad agabansa. 

Serving ɗin kanta tayi sannan ta zauna, Ummu da Almustapha ne kawae keta hira, itakam dama mezatace acikin hirarsu, shikuwa SOORAJ dama kowa yasan ba magana yake ba.... Jin hirar su Ummu na damunsane yasanyashi miƙewa tsaye yabar wajen, da kallo Ummu tabisa har ya shige ɗakinsa.
Ahankali Zieyaderh itama tamiƙe tsaye don dama tuntuni ta ƙoshi da abincin, damar tashi kawai takejira. Sunanta da Ummu taƙira yasanyata dakatawa daga yunƙurin barin wajen da takeyi.

"Zauna inason magana dake" Ummu tafaɗa tana me ƙokarin aje kofin tea din dake hannunta.

Ƙirjinta ne yashiga bugawa lokaci ɗaya taji gabanta ya faɗi, aɗaɗare ta koma ta zauna akan kujera, miƙewa tsaye Almustapha yayi tare da ɗaukan kofin tea dinsa yabar wajen.

"Zieyaderh!" Ummu taƙira sunanta.

Bata iya amsawa ba saidai ɗago kai da tayi ta kalli Ummun jiki asanyaye.

Ummu bata wani damu da rashin amsawannata ba tace "Nayi magana da Mas'oud saidai abun da yafaɗamin akanki ya matuƙar girgizani, inaso kifaɗamin gaskiyar wacece ke? sannan kuma inason sanin ina mahaifanki suke da har zaki nesanta kanki dasu, karkimin ƙarya don banason ƙarya, Inajinki!" Ummu tafaɗi maganar tana me maida gaba ɗaya attention ɗinta ga Zieyaderh.

Ƙirjinta ne ya buga take idanunta suka cicciko da ƙwalla, bakinta na rawa tace. "Banda mahaifiya tun ina ƙarama ta rasu, natashi agaban Mahaifina da kuma matarsa sam bansan wani abu waishi soyayya ba, kullum cikin ƙunci da kaɗaici nake rayuwa, babu wani wanda yadamu da farinciki ko jin daɗi na, bansan kowa daga cikin dangin mahaifiyata ba saboda naji Babana yace ita ba ƴar garinmu bace, ban kuma san inane garinsu ba, tun ina ƙarama nayi sabo da wahalwahalun rayuwa, duk wani rashin gata ya ƙare akaina, sam babana bai ɗaukeni ƴa wacce ya haifa acikinsa ba, bansan daɗin mahaifi ba" Kuka ta fashe dashi tare da kifa kanta ajikin table, saida tayi kuka sosai sannan ta ɗago kanta hawayenta ta share kana ta cigaba da bawa Ummu labarinta, kama daga kan zancen aurenta da tsoho ɗan dashe har izuwa yanzu da take tare dasu, durƙusawa tayi akan guiwowinta cikin kuka tace "Ummu ki gafarceni saboda ni Ya Mas'oud yayi miki ƙarya."

Hawaye ne suka cika idanun Ummu, tabbas yarinya ƙarama kamar Zieyaderh bai kamata ace an banzatar da ita har haka ba, ya kamata ne ace anbata kyakkyawan kulawa.
Kafaɗunta Ummu takama ta ɗagota cike da kulawa tashiga share mata hawayen dake kwaranya akan fuskarta.

"Ya isa daina kukan haka nan, naga kanki yayi datti ɗauko mayafinki muje shagon saloon!" Ummu tafaɗi haka cike da kulawa.

Jiki asanyaye haka Zieyaderh ta haura sama don ɗauko mayafinta. Da kallon tausayi Ummu tabi bayanta, bawani jimawa sosai sai gata ta dawo sanye da hijab ajikinta.

Ko amota shirune ya biyo baya tsakaninsu, dan kowa da abun dayake saƙawa acikin ransa. Ummu kam tuni tagama yanke shawaran abun dake ranta, wayarta ta ɗauka ta turawa Almustapha da Sooraj text akan tanason ganinsu, daga haka ta aje wayarta.

Sosai aka gyarawa Zieyaderh dogon gashinta, lokaci guda ya ɗauki ƙamshi da walwali, daga shagon saloon Super market suka wuce, sosai Ummu ta sai mata kayan kwalliya dana sawa masu kyaun gaske, daganan suka ɗauko hanyar dawowa gida.

Tana sanya ƙafarta acikin falon idanunta suka sauƙa acikin na Almustapha wanda yasha kyau cikin baƙaƙen kaya. Da sauri tayi ƙasa da kanta, don har acikin ranta batajin daɗin irin kallon da yakeyi mata, kai tsaye ta haura sama nan tabar Ummu afalon.

Ummu na zama akan kujera Ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito, sanye yake da army 3 guater jeans da kuma black t-shirt, fuskarsannan babu alaman farinciki ko sakewa akanta, haka yaƙaraso cikin falon, akan kujeran dake facing na Ummu ya zauna tare da ciro phone ɗinsa daga aljihun wandonsa yasoma dannawa.

Gyara zama Ummu tayi cikin yanayi na kulawa tace "Banƙiraku nan don na faɗa muku wasa ba"Kallon Almustapha tayi cikin kulawa taƙira sunanshi, da "Na'am ya amsa mata tare da ɗagowa ya kalleta.

"Nasan banice na haifeka ba, amma kuma kana mini biyayya tamkar yanda zakayiwa mahaifiyarka, haƙiƙa amatsayina na yar mahaifiyarka inada ƴancin dazan iya zartar da duk hukuncin da naso akanka, kasani tamkar yanda nakeson ɗan cikina Sooraj kaima haka nake sonka, saboda haka na zaɓa maka matar da zaka aura ina fatan bazaka watsamin ƙasa a ido ba?"

Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannuwansa ya kama na Ummu. "Bazan taɓa iya bijirewa umarninkiba Ummu, ke uwace agareni saboda haka ina maraba da duk wani zaɓinki"

Murmushin jin daɗi Ummu tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa cike da ƙaunarsa tace "Nagode sosai Almustapha Allah ya maka albarka!"

"Ameen Ummu, amma wace me sa'ace haka tayi gamdakatar ɗin samuna?" cike da zolaya yayi tambayar.
Dariya Ummu tayi tare da cewa "Kanason sani?"

"Sosaima" Almustapha yabata amsa cike da zaƙuwa.

Duk abunda suke yanajinsu yana kuma kallonsu, amma ko uhummm baice ba, azahirin gaskiya wayarsa yake dannawa abaɗini kuma gaba ɗaya hankalinsa na garesu.

"ZIEYADERH itace wacce na zaɓama kuma itace wacce zatayi daidai da rayuwarka!"

Maganar Ummu data faɗane yasanyashi ɗago da kansa ahankali ya kalleta..

"Zieyaderh!"Almustapha ya maimaita sunan abakinsa, kansa ya sunkuyar ƙasa fuska ɗauke da murmushi yace
"Na'amince!"

Tsaida duk wani abu da yakeyi yayi yana kallonsu, hakanan yaji tamkar ruwan jikinsa na ƙonewa.


(fever na damuna so banajin daɗin jikina please kuyi manage, wannan ma da ƙƴar nayi muku, idan naji sauƙi gobe Insha Allah zakujini🙏🏻)
Naziphi Yarima:
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

              *WATTPAD*
           fatymasarduna
#romance

              *Chapter 35*

Sunkuyar da kansa ƙasa yayi tare da ɗan ciza laɓɓansa, idanunsa ya mayar kan wayansa,  samun kansa yayi da kasa cigaba da amfani da wayan, ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi weak.

"SOORAJ!" Oummu taƙira sunansa.

Ɗago kansa yayi ya kalleta batare daya amsa mata ba, itama bata nemi amsawar nashi ba taci gaba da cewa  "Kaji abun da muka tattauna akai, amma bakace komaiba, sannan kuma inaso na yaba maka game da namijin ƙoƙarin taimakon da kayiwa Zieyaderh, insha Allah, Allah Zai baka lada!" Oummu tafaɗi maganar tana murmushi.

Ko Uhumm  baice ba, sai ma kallon Oummu'n daya keyi, ganin damuwarta dana Almustapha zasu kasheshi yasanyashi tashi gaba ɗaya yabar musu gidan.

Kwance take luf akan bed ɗinta, biscuit ne ahannunta tanaci da kaɗan kaɗan, turo ƙofar ɗakin da akayi ya sanyata tashi zaune da sauri,   ganin Oummu yasanya tasakin murmushi tare da cewa       "Barka da shigowa Oummu"

Murmushi Oummu tayi tare da zama akan wata kujera,   cike da kulawa tace.  "Magana nazo muyi dake Zieyaderh!"

Gaban Zieyaderh ne ya faɗi, amma saita dake tare da cewa "To"

Murmushi Oummu tayi tare da dafa kafaɗun Zieyaderh'n tace  "Inaso kishirya ƙarshen wannan week ɗin zamuje ƙauyenku dan inason naga mahaifinki!"

Dummm haka ƙirjin Zieyaderh ya bada wani irin sauti,  hawaye ne suka cika idanunta alokaci guda,  bakinta na rawa tace "To!"
Murmushi Oummu tayi don tafahimci cewa tsoron zuwa ƙauyen Zieyaderh keyi, cikin son kwantar mata da hankali tace "Kar kisanya tsoro aranki idan munje bazan barki ahannunsu ba zandawo dake nan, kawai dai naga ya kamata ace mahaifanki susan inda kike ne!"

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kanta

23 / 48