Author : Maman Teddy Category : Romance
suka sa dariya, har acikin ransu su mamakinta suke na yanda gaba ɗaya tabi ta takura kanta.
Acan Ƙauyen Saminaka kuwa Tuni Abba sun gana da Malam Garba baban Zieyaderh, inda yayi musu karɓa ta mutumci, babu laifi kuma sun yaba da halin karamcin daya nuna musu, nan suka zauna suna me sake fahimtan juna, sam su Abba bada wasa suka ɗauko maganan auren ba hakan yasa lokaci guda suka gama magana inda Malam Garba ya shaida musu cewa ya basu auren ƴarsa Zieyaderh, Alhaji Maham ɗaya daga cikin aminan Abba shi ya ciro wasu kuɗi dake cikin aljihunsa inda ya miƙa amatsayin sadakin auren Zieyaderh, naira dubu ɗari ne cas, cewar da sukayi basason bikin ya ɗauki lokaci ne yasanya Malam Garba cewa suyi haƙuri suɗan bashi lokaci zuwa nan da kwana huɗu zai sanar dasu kowani lokaci ya yanke, shikuwa yayi hakanne don yanason tattaunawa da Zieyaderh akan batun auren, domin tun da aka fara batun auren baiji ta bakinta ba kuma itama tana da haƙƙi, cikin mutumta juna su Abba sukaiwa Malam Garba sallama inda suka kama hanyar dawowa cikin garin Kaduna.
..........
15 minute da tashinsu a school kenan amma har zuwa yanzu Kamalu driver baizo ɗaukarta ba kamar yanda ya saba, waige waige taɗan somayi wai kozata hangosa amma babu ko me kama dashi, gashi gaba ɗaya ƴan makarantar sun soma watsewa don tuni su Shukra ma sun tafi, ahankali take takawa harta isa bakin gate ɗin fita daga makarantar, tsayawa tayi daga ɗan gefe kaɗan tana me ƙarewa motocin da keta hada hada awajen kallo, wata haɗaɗɗiyar blue car wanda taji black tinteck ne ta tsaya adaidai gabanta, kallon motar Zieyaderh tayi amma ganin bata iya ganin wanda ke cikin motar ya sanya ta ɗauke kanta gefe,tare da cigaba da kallon hanya, ahankali ya shiga zuge glass ɗin motar, fuskarsa ɗauke da murmushi yace "My ƴar kyakkyawan budurwata!" jin muryarsa acikin kunnuwanta yasanya tayi saurin ɗagowa ta kalleshi, hakanan taji gabanta ya faɗi amma sai tasaki murmushi, da hannu yayi mata alaman da ta taho, samun kanta tayi da kasa musa masa sai kawai taɗan ƙarasa jikin motar, daga ciki yasanya hannu ya buɗe mata murfin motar, duk da cewa ƙirjinta na dukan uku uku haka ta daure tashiga cikin motar saidai bata rufe murfin motar ba, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kama ƴan yatsunta tana wasa dasu, shikuwa Pharouk ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙiran sunanta murya asanyaye. Jin yanda yaƙira sunannata yasanyata ɗago da kanta ta kalleshi, gani tayi gaba ɗaya murmushin dake kan fuskarsa ya kau, zuwa yanzu damuwane shumfuɗe akan fuskarta sa, kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saidai kuma ba cikin idanunsa take kallo ba, tunowa da tayi cewa jiya tabarsu da Almustpha batare da tasan me Almustaphan ya faɗa masa ba yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, jitayi idanunta naneman kawo ruwa, ahankali yasanya hannunsa ya ɗago haɓarta, hakan yasa suka jefa idanunsu cikin na juna, cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa yace "Kinason aure'n?" gabantane ya faɗi dajin tambayar tasa amma kuma saita samu kanta da kasa amsa masa, fuskarsa yasake mareraicewa tare da cewa "Da gaske kenan aure za'a miki? me yasa kika amince da hakan? kinyarda arabani dake kenan ko?" yaƙare maganar yana me matuƙar nuna rauninsa akan fuskarsa.
Hawayen dake kwance acikin idanunta ne suka samu daman gangarowa batare da ta shiryawa hakan ba. Ganin hawaye akan fuskarta ya sanyashi lumshe idanunsa tare da matso da fuskarsa gaf da tata har suna iya jiyo hucin numfashin juna, jin sauƙan numfashinsa akan fuskarta yasanya azabure tayi saurin buɗe idanunta , shima buɗe nasa idanun yayi wanda suka kaɗa sukai ja, wani irin kallo daya mata ne yasanya tayi saurin jan jikinta baya tare da ture hannunsa dake kan haɓan ta, kuka ne yake neman cin ƙarfinta hakan yasa ta juya da sauri ta fita daga cikin motar, dai dai lokacin kuma motar da aka saba zuwa ɗaukanta dashi wanda kamalu driver ke ciki ya tsaya adai dai ƙofar shiga gate ɗin makarantar, da ɗan sassarfa taje ta buɗe murfin motar tare da faɗawa ciki kana ta jawo murfin ta rufe, kanta ta cusa acikin cinyoyinta tare da sakin kuka me sauti, Ko bi takan Kamalu driver dake bata haƙurin rashin zuwansa da wuri da yayi bata biba, kuka take sosai tana me kakkame jikinta, wani irin zafi zuciyarta ke mata, Me yasa har izuwa yau baice komai ba? me yasa ya hanata ganinsa har na tsawon kwana uku? tanajin zafi acikin rai da zuciyarta, safe, rana, dare, duk shine acikin rayuwarta me yasa takejin hakan? Kukanta taci gaba dayi wanda babu me rarrashi, zuwa yanzu harta soma jin haushin kanta, musamman yanda tamaida kanta wata wawiya akansa.
Ganin tashin motarsu yasanya Pharouk sakin wani murmushi wanda shikaɗai yasan ma'anarsa, key ɗin dake jikin motar yaɗan murza, tare da cilla motar tasa kan titi, yayiwa kansa alƙawarin matuƙar shine Pharouk to SOORAJ bazai taɓa samun Zieyaderh amatsayin mata ba.
SOORAJ
Ahankali yake matsowa jikinta yayinda takeja baya shi kuma yana me ƙara matsota, wani irin numfashi yake fitarwa me zafi, kasancewar takawo jikin bango hakan yasa ta tsaya cak, hakan kuma yayi daidai da ƙarasowarsa gareta, ganinsa adaf da ita yasanyata lumshe kyawawan idanunta tare da sakin wani sassanyar ajiyar zuciya, kyakkyawan fuskarta yake kallo yayinda idanunsa ke lumshewa ahankali hankali, numfashinsu ne ya cakuɗa dana juna, yayinda ƙamshin turarensu ya haɗe waje guda, hakan yasa wani irin ƙamshi mai daɗi ke fita ajikin kowannen su, fuskarsa ya manna da tata fuskar yayinda ya sauƙe hannayensa akan faffaɗan waist ɗinta, cikin wani irin yanayi ya ɗaura lips ɗinsa akan nata tare ɗan kama lip ɗinta na ƙasa ya ɗan tsotsa, wani irin abune yaji ya zirga masa har cikin tafin ƙafansa, sake kama lips ɗinnata yayi yashiga tsotsa ahankali yayinda yake fitar da wani irin numfashi, ahankali cikin rufewar ido yake ƙara tsotsan laɓɓanta, wanda hakan yasanya taɗan buɗe bakinta, ahankali ya tura bakinsa cikin nata yayinda harshenta ya faɗa cikin bakinsa, wani irin abu yaji yatsarga ajikinsa yayinda yaja wani irin numfashi tamkar wanda zai shiɗe, azabure ya farka daga baccin da yakeyi, tare da buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, wani irin zufane ke ketowa ta jikinsa yayinda gaba ɗaya gashin jikinsa suka mimmiƙe, jijiyoyin jikinsa ne suka fito raɗa raɗa, tashi zaune yayi yana ne ƙoƙarin jawo numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwacewa, yayinda yakejin tamkar ana buga masa guduma acikin kansa, wani irin ƙara yayi tare da dafe kansa wanda yakejin wani irin azababben ciwo acikinsa, hannayensa yasanya ya dafe kunnuwansa tare da rumtse idanunsa, duniyarce gaba ɗaya take juya masa.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 41*
Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, tare da rumtse idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja tamkar waƴanda aka watsawa garin barkono, hannayensa ya sanya ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa, wani iri yakeji acikin kansa tamkar ana doka masa gudu ma, cikin ƙarfin halin daya aro ya dasawa kansa ya miƙe tsaye tare da soma binbango yana neman hanyar da zai sadasa da toilet, zuwa yanzu ko gani sosai baya iyawa, wani irin duhu ne ke neman mamaye ganinsa, sunan Allah Yashiga ambata acikin ransa yana me tafiya ahankali, ƙafafunsa ne sukayi masa nauyi, haka yakeji tamkar an ɗaure masa su da kaca, aninayen dake jere reras agaban rigarsa ya soma cirewa, tare da sanya hannunsa ya kunna shower take ruwa yasoma zuba ajikinsa, duka hannayensa ya sanya ya dafe bango tare da rumtse kyawawan idanunsa, yayinda ruwa ke dukan naked skin ɗinsa, still ambaton Allah Yaketayi acikin ransa, ahankali yakejin nutsuwar daya rasa na dawo masa, yayinda yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, zuciyarsa kuwa har yanzu fast fast haka take bugawa, sake lumshe idanunsa yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa, ko ka ɗan bayason tuno mafarkin da yayi wanda tunda yake bai taɓayin makamancin irin saba, bayan hannunsa yasa yaɗan naushi bango tare da kashe shower'n, wani white towel ya ɗaura akan waist ɗinsa tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel yashiga goge jiƙaƙƙiyar suman kansa, koda ya fito daga toilet ɗin, zama yayi akan dressing mirror tare da ɗaukan body lotion ya shiga shafawa jikinsa, yana gamawa ya feshe jikinsa da wani irin body spray me daɗin ƙamshi, black pencil crazy jeans and white t-shirt ya sanya, kasancewar anyi ruwa sannan akwai sanyi sosai agarin yasanya shi ɗaura black leda jacket akan rigan, wayoyinsa ƙiran Samsung galaxy S20 da kuma iphone 11 pro max ya zura acikin aljihun jacket ɗin nasa, wasu irin combat shoe yasanya masu kyau da tsada, ahankali ya ƙarasa gaban mirror tare da ɗaukan facing cap white colour ya sanya akansa, baƙaramin kyau shigan yayi masa ba, yayinda sajen dake kwance akan fuskarsa keta shinning. Farfumed ya fesa ajikinsa kana ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ahankali yake sauƙowa daga kan haɗaɗɗen matattakalan da zai sadasa da wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa, yana ƙarasowa cikin falon yanufi wajen wani haɗaɗen fridge wanda yake na glass, gaba ɗaya kana iya hango duk wani abu dake ciki, buɗe fridge ɗin yayi tare da zaro gwangwanin malt, ɓalle murfin yayi tare da kai bakinsa jikin gwangwanin, 8 minute kacal ya shanye gaba ɗaya malt ɗin, tare da wurga gwangwanin cikin dustbin. Cikin takun dake nuna tsantsar aji da kuma nuna cikakken zarransa na ɗa namiji, ya fito daga cikin ƙawataccen hotel ɗin, wanda anan yake da zama tunda yazo Singapore, hotel ne mai kyaun gaske don yana ɗaya daga cikin manyan hotels ɗin da akeji dasu a ƙasar Singapore, tafiya yake da ƙafafunsa yayinda yashiga cikin ƴan ƙasar yasaje dasu sak, kasancewar kalan fatarsu iri ɗayane danasa yasanya bazaka iya banbanceshi da suba, babu wani ɗaya acikinsu da zaice ya ɗarasa hasken fata, wani ƙaton club yanufa inda maza masu aji ke zuwa, kowa dake cikin club ɗin harkan gabansa yake babu ruwan kowa da kowa, wasu suna shaƙatawane da ƴan matansu yayinda wasu keshan wine, wasu kuwa rawa kawai sukeyi, kan wata kujera da take ita kaɗai ya zauna tare da zaro wayansa don yanaso yayi vedio call da Mas'oud, ɗaya daga cikin masu aiki a club ɗinne ya tambayashi tsakanin Alcohol da wine wanne yake da buƙata. kansa ya girgiza tare da cewa ya basa drinks kawai, hakan kuwa akayi inda ma aikacin ya cika masa gabansa da drinks kala kala, nan ya maida hankalinsa ga wayarsa tare da dannawa Mas'oud ƙira.
Nigeria
Kasancewar Yau asabar babu makaranta hakan yasa bata tashi da wuri ba sai wajen 9, kasancewar yanzu sam bata aikin gidan Oummu ta ɗebi wadatattun ma'aikata wanda sukeyin girki da komai, fitowanta a wanka kenan zama tayi agaban mirror tare da shafa mai ajikinta, sama sama ta shafa powder akan fuskarta tare da ɗan goga man baki abakinta, wata doguwar riga na black lace ta sanya, sosai rigan tayi mata kyau, tsayawa tayi tana me kallon kanta a madubi, ita kanta tasan tayi wata ƴar rama wanda bakowane zai gane hakan ba har sai in wanda ya lura, tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali ne aka turo ƙofar ɗakin nata, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta cikin yanayi na girmamawa tace "Barka da safiya Oummu!"
"Yauwa barka, fatan kintashi lafiya!" Oummu ta tambayeta cikin kulawa.
"Lafiya ta amsa tana me ƙoƙarin sunkuyar da kanta ƙasa.
"Masha Allah, to maza zo muje yau kina da babban baƙo yana falon Abbanku, nasan da ace kinsan da zuwansa to tabbas da tun 7 zaki tashi" Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin kamo hannunta. Jitayi gabanta ya faɗi, tsorone ya kamata don gaba ɗaya tunaninta ya bata cewa Pharouk ne ya kuma dawowa. Haka tabi Oummu jikinta asanyaye, suna sauƙa daga kan steps ɗin Oummu ta miƙo mata wani tray wanda samansa ke ɗauke da kayan fruits. "Ungo ki kai masa tun ɗazu ke yake jira yace yana sauri zai koma"
Jikinta na rawa haka ta amshi tray ɗin ta fice daga cikin falon, ƙirjinta na dukan uku uku haka ta nufi ɓangaren da zai sadata da falon Abba. Ahankali taturo ƙofar falon bakinta ɗauke da sallama ta kutsa kanta ciki, tarwal idanunta suka sauƙa akansa, koda wasa bata taɓa tunanin ganinsa awannan lokacin ba, muryarta narawa tace "Baba!!" murmushi Malam Garba yayi tare da yi mata alama da hannunsa akan taƙaraso, da sauri ta ƙaraso cikin falon tare da ƙarasowa gabansa ta aje tray ɗin, idanunta ne suka kawo ƙwalla cikin muryarta dake rawa tace "Baba sannu da zuwa!"
"Yauwa Zieyaderh sannu ya makarantar?"
"Alhamdulillah!" tafaɗa asanyaye tana me kallon mahaifinnata.
Ganin haka yasanyashi sakin murmushi tare da sanya hannu ya dafa kanta, cikin kulawa yace "Kina mamakin ganina ko Ziyaderh? karkiyi mamaki ni mahaifinki ne kuma ina ƙaunarki amatsayinki na tilon ƴata, haƙiƙa nasan banzama mai kyautawa agareki ba, duk irin abun da nayi miki banyi miki shi ason raina ba, nakuma ɗauki hakan amatsayin ƙaddara da babu wanda ya isa ya guje mata, kiyi haƙuri ki yafemin Zieyaderh haƙiƙa na cutar da rayuwarki na bari kinyi rayuwa cikin wahala da rashin gata, nasan ban kyauta miki ba amatsayina na mahaifi agareki...." Kuka tasanya me sauti tare da kifa kanta akan ƙafafunsa kana ta sanya hannayenta duka biyu ta rungume kafafun nasa, wani irin kuka takeyi mai ban tausayi yayinda agefe guda kuwa wani irin nutsuwa ke shiga zuciyarta.
"Nibakamin komai ba Baba, kaine zaka yafemin, duk da cewa bansamu ƙauna daga gareka ba, amma baka koyar dani tarbiyan banza ba, na saɓa tarbiyana na gudu na barka batare da neman izininka ba, kayi haƙuri Baba kayafemin!!" Tafaɗa tana kuka sosai. Idanunsa ne suka cika tab da ƙwalla ahankali ya ɗago kafaɗunta cikin son ya rarrasheta yace "Nayafemiki Zieyaderh, najima da yafemiki Allah yayi miki albarka, kema kuma inaso kiyafemin haƙƙin ki dake kaina wanda bansauƙe miki shi ba!"
Hawayen dake gudana akan fuskarta ta share tare da yin murmushi cikin jin daɗin ganinta gata gashi tace "Najima da yafe maka Baba!"
Murmushin jin daɗi shima yayi tare da shafa kanta cikin soyayya irin ta ɗa da uba yace "Allah Yamiki albarka!" da "Ameen" ta amsa tana murmushin jin daɗi, kamar ba itace tagama kuka yanzu ba, tray ɗin da ta shigo dashi ta miƙo mai tare da cewa "Baba kasha fruit" Murmushi yayi tare da girgiza mata kansa cikin halin dattako irin nashi yace "A'a Zieyaderh naƙoshi, bakiga har abinci sun kawomin ba!" yafaɗa yana meyi mata nuni da kulolin dake jere saman table. Cikin jin daɗi Zieyaderh tashiga bubbuɗe kulolin wanda aka shaƙe cikinsu da abinci na alfarma. "Baba to ai bakaci ba!" tafaɗa aɗan shagwaɓe tana kallonsa. Murmushi yayi tare da cewa "Dawo kizauna kusa dani" cikin jin daɗin sabuwar kulawan da tasamu daga mahaifinnata ta dawo ta zauna akusa da ƙafafunsa.
"Zieyaderh" yaƙira sunanta cikin kulawa.
"Na'am" ta amsa masa tana me dubansa.
Gyara zamansa yayi tare da cewa "Nasan ko ada can baya ke me hankali ce da nutsuwa, sannan kuma ke yarinyace me biyayya, bansan ko akwai soyayya atsakaninki da wanda ake ƙoƙarin haɗaki aure dashi ba, amma haƙiƙa na amince da karamci da kuma mutumci irin na waƴannan mutanen, saidai kuma duk da haka bazan yi gaggawan yin gaban kaina ba, duk da cewa na amince musu batare danaji ta bakin ki ba, sannan sun kawo sadaki suna me neman asanya musu lokacin aure amma banyi musu na'am ba nadaice su bani nan da kwana huɗu, bazan hanaki abun da kikeso ba Zieyaderh, bakuma zan tilastaki yin abun da bakya so ba, idan har bakyason aurennan karkiji ɗar ko shakka ki sanar dani, nikuma zan maida musu da sadakin su zan kuma basu haƙuri"
Shiru tayi tare da sunne kanta ƙasa, wasa da hannayenta tashiga yi cikin sanyin daya zame mata sabo tace "Na'amince musu Baba!"
Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa cike da tausayin ƴartasa yace "Allah yamiki albarka Zieyaderh, tashi kije idan yaso sai ki sanar da Ummantaku ni zan wuce!" "To" tace dashi asanyaye kana ta miƙe tsaye tana cewa "Baba kaɗanci abincin ko kaɗanne dan Allah!" murmushi kawai yayi harta fice bai sake ceda da ita komai ba. Zieyaderh kuwa tana fita daga cikin falon aɗan corridor ɗin dake barandar falon ta tsaya, bayanta ta jingina da jikin bango tare da sanya hannu ta sharce hawayen daya silalo kan ƙuncinta, kanta ta girgiza tare da ɗan cije laɓɓanta, ita kaɗai tasan meke zuciyarta,wanda bazata kuma iya furtawa kowa ba, gefen mayafinta tasanya ta goge idanunta sosai sannan ta nufi ɓangaren Oummu. Afalo ta samu Oummu hakan yasa ta ɗan rusuna tare da gaya mata saƙon Baban nata, murmushi Oummu tayi tare da miƙewa tsaye mayafinta ta ɗauka kana tafice daga falon, Zieyaderh kuwa kitchine ta wuce inda ta haɗawa kanta tea, domin ayanda take batajin wani abu bayan tea zai iya samun gurbin zama acikinta.
Jin abun da Malam Garba yace yasanya Oummu yin murmushi, batakai ga cewa komai ba muryar Abba dake shigowa ya karaɗe cikin falon inda yake cewa "Karka damu Malam Garba ae danan dacan wajenku duk ɗayane awajen mu, kuma kamar yanda kuke iyaye awajenta, haka muma muke matsayin iyaye awajenta"
"Ƙwarai kuwa kuma insha Allah zata samu kyakkyawan kulawa awajenmu, idan kace takoma wajenka kafun bikin makarantar ta zai iya samun matsala, amma idan tananan baza a samu wani matsala ba muna shirye shiryen mu kuma tana zuwa makaranta!" cewar Oummu wacce sam batason Baban Zieyaderh'n ya kafe akan ta koma wajensu, so take tayiwa zieyaderh gyara na musamman, kana kuma tayi mata auren gata.
Ganin sun haƙiƙance ne yasanya Malam Garba, janye maganarsa na cewa yanason tafiya da Zieyaderh, dole tasa ya haƙura yayi musu bankwana bayan sunyi shawara da Abba sun kuma yanke lokacin biki nan da sati biyu masu zuwa, duk yanda Malam Garba yaso ya shiga motar haya ya koma Abba ƙiyawa yayi nan ya kafe akan dole saidai driver ne zai maidashi gida, sam bayason jayayya dasu hakan yasashi amincewa bayan Oummu ta