Author : Maman Teddy Category : Romance
iya ƙaryata Shukra ba, domin itama zuciyarta ta gamsu da hakan... "Menene amfanin wannan son? menene amfanin son wanda baisan kanayi ba, meyasa zuciyata tayi mini haka, tabbas idan nasoshi na so kaina dayawa saboda ba ajina bane!" Zieyaderh ta faɗa murya araunane.
"So baruwanshi da aji ko rashinsa Zieyaderh, kiyi fata wata ƙila shima ya soki!" Shukra tafaɗa cikin son ƙarfafa mata guiwa.
"Soyayyata bata da amfani Shukra, saboda ɗan uwansa zan aura, wani riba zan samu idan naci gaba da sonsa Shukra?" hawaye har sun cika idanunta.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da cewa "Kicire sonsa azuciyarki Zieyaderh, haka shine samun sauƙin kai da zuciyarki"
Hawayen dake cikin idanunta ne suka gangaro ahankali tasa hannu tashare, "Nayarda inasonka, amma zan barwa zuciyata ita kaɗai, zan jure duk wani zafi da ƙunci, idan har soyayyarka zata zauna azuciata bazata fice ba, ko ba komai watarana ita zata tausheni" maganan da takeyi acikin zuciyarta kenan... Haka taƙare gaba ɗaya wunin ranan cikin damuwa, sam walwalanta ya ragu babu wani jin daɗi atattare da ita. Koda aka tashi amakaranta data koma gida aɗaki ta zauna, ko abinci bata fito taci ba, damuwar SOYAYYARSA ne kwance aƙasan ranta.
Tun ɗazu yaketa juyi akan makeken gadonsa, shikansa baisan tunanin me yake ba, yasan ƙaddara tana iya sauyawa ako da yaushe amma baya fatan tasa ƙaddaran ta sake sauyawa, saboda zai iya jure komai amma banda sabon baƙon yanayin dayake samun kansa aciki kwana biyun nan, yasani shi mai rauni ne ako da yaushe... Kansa ya cusa acikin pillow tare da sakin wani numfashi me zafi, baitaɓajin ciwon ƙaddaransa ba sai ayanzu, yanaji ajikinsa cewa zuciyarsa nason wani abu, to amma metakeso? shine abun daya kasa sani, sau da dama yakanjinta awani ɓangare ne na zuciyarsa, amma asannu sannu sai yakejin gaba ɗaya ta mamaye zuciyarsa, kowani bugun numfashin da zaiyi da fargaba yake tafiya, ada baisan wani damuwa da zafin zuciya ba, amma asannu yanzu duk ta dalilinta yasansu, yana da buƙatar sanin me hakan yake nufi, baisan mezai kira abun ba, amma wani lokaci yakanji dama ace bai santa ba kwata kwata, yakanji inama da ace baizama silan taimakonta ba wataƙila da bata shigo rayuwarsa ba, akullum ji yake kamar an rubuta wani abu daya shafeta acikin ƙirjinsa, saidai babu wanda zai sanar dashi me hakan ke nufi. Idanunsa da suka kaɗa sukai ja ya ware tare da ɗaukan wayansa ya turawa peter saƙo, akan yayi masa booking flight, kallon agogo yayi yaga ƙarfe 7 na dare, ahankali ya sauƙo daga kan gadon tare da ƙarasawa gaban drawer ɗinsa, wata black trolly ya jawo tare da buɗe sip yashiga ɗebo kayansa yana zubawa acikin trolly'n, yagama sawa aransa cewa acikin waƴannan satuttukan bazaiyi zaman Nigeria ba....
***
Dariya sosai Yasmeen keyi wanda hakan ya matuƙar harzuƙa Aneesa, cikin yanayin fushi tace "Wallahi indai ina da rai bazan taɓa barin SOORAJ ba dole sai na koyardashi yanda zaiyi ya zama namijin gaske!"
Gimtse dariyan da takeyi Yasmeen tayi tare da cewa "Bakida hankali Aneesa, ko kin manta nice wadda nafara son SOORAJ acikin zuciyata? Ke Sha'awar SOORAJ kawai kikeyi Aneesa nikuma ba iya sha'awaba sonsa nakeyi, bandamu ba don kince shiba Namiji bane, ni indai zanna ganinsa akusa dani akullum zan iya jurewa, please Aneesa kibarmin SOORAJ dan Allah Ina burin kasancewa dashi"
Tsuka Aneesa tayi tare da cewa "Duk da cewa shiɗin bashida amfani amma duk da haka inajin sha'awarsa, aranannan naso ace dagaske fyaɗe zaimin, tabbas nasan danaji daɗin da wata mace bata taɓajiba, don hakan ni awajena bazai zamanto fyaɗe ba, hmmm amma haka guy ɗinnan yatafi yabarni da yagaggen riga ko breast ɗina bai iya taɓawa ba!!" Aneesa taƙare maganar cikin yanayi na ƙufula.
Dariya Yasmeen tasakeyi tare da cewa "Bazan hanaki ba Aneesa, amma inaso ki sani bazan janye daga son SOORAJ danake ba saidai mu duka biyun Allah Yabawa me rabo sa'a"
***
Kasancewar Yau Abba zaidawo hakan yasa Oummu tun safe take ta shirye shiryen dawowarsa, tsaye take a kitchine tana ƙoƙarin harhaɗa abincin da tayi akan tray... Almustapha ne yashigo cikin kitchine din fuskarsa ɗauke da ɗan damuwa. Kallonsa Oummu tayi cike da mamakin ganin yanayinsa tace "Almustapha lapia kake kuwa?"
Murmushi yayi tare da cewa.
"Tsoro nakeji Oummu"
Shaye da mamaki Oummu tace "tsoron me?"
Ƙasa yayi da murya tare da cewa "Tsoron abun da muka shirya, nayi wani tunani, yakamata mugayawa RAJ gaskiya Oummu kinsan zuciyarsa, kar azo ayi abunnan kuma yace bayaso, sannan karkuma bayan anyi yazo yace zaiga laifina"
Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Karka damu Almustapha, naɓoye hakanne bawai don wani abuba saidon inason wannan auren yafi waƴancan auren nasa ƙarko, jikina yajima da bani cewa awannan karon SOORAJ bazai saki matar da zan aura masa ba, kayi haƙuri Almustapha mucigaba da gudanar da shirinmu ayanda muka tsara!"
Murmushi Almustapha yayi tare da ɗaukan yankakken apple yakai bakinsa cikin yanayi na jin daɗi yace "Amma gaskiya Oummu kada asa lokacin bikinnan da yawa, don kinsan bazan iya jurewa ba watarana kada nayi abun dazai sanyashi gane plan ɗinmu!"
"Karka damu banajin bikinnan zai wuce 3 weeks saboda nima akwai abun danake hangowa, saidai kuma ita yarinyar ce bansan yazataji ba idan taji haƙiƙanin wanda ta aura."
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 39*
Amatuƙar gajiye ta dawo daga makaranta, gaba ɗaya ƙafafunta ciwo suke, kasancewar yau ɗin kusan awa guda suka ɗauka tsaye acikin Lab, tana shiga cikin ɗaki tasoma rage kayan jikinta, wani white towel ta ɗaura aƙirjinta wanda ya kawo har kan santala santalan cinyoyinta, bathroom ta wuce kai tsaye, wanka tayi tare da ɗauro alwala. Wata pencil tightly skin gown tasanya wanda bayanta taƙasa yake aɗan tsage, sosai rigan tabi haɗaɗɗiyar surar jikinta ta lafe, wani ɗan madaidaicin hijab ta sanya ajikinta, kai tsaye tanufi ɗakin Oummu, tana knocking door ɗin, Oummu ta bata izinin shigowa, Zaune tasameta akan wata luntsumemiyar kujera dake cikin ɗakin, gabanta wasu takardune yayinda hannunta ke ɗauke da pen. Da murmushi akan fuskarta ta amsawa Zieyaderh gaisuwan da tayi mata, tare da ɗan zare farin glass ɗin dake sanye a idonta tana me cewa "Ya school ɗin?" "Alhamdulillah!" Zieyaderh ta amsa aɗan sanyaye, ƙatuwar leda wanda ke ɗauke da tambarin sunan wani super market Oummu ta miƙo mata tare da cewa. "Ungo amshi Kayan da kuka saya da Almustapha ne, ashe wai ke ya sayawa sai kimasa godiya"
Asanyaye takarɓi ledan dake shaƙe da kaya, cikin sanyin daya sake zama sabo agareta tace "Oummu kitayani godiya, nagode sosai!"
Murmushi Oummu tayi irin tasu ta manya tare da cewa "Ae kinfi kusa dashi ayanzu zai kyautu kiyi masa godiyan da kanki!"
Murmushi kawai tayi cike da kunya ta sadda kanta ƙasa tare da miƙewa tsaye, da ƙyar ta iya jan ledan don tana da nauyi, haka tafita daga cikin ɗakin tanajin wani iri acikin zuciyarta. Tana shiga ɗakinta ta Zazzage ledan akan gado, tabbas sayayyan da sukayi ita dashi ne, sam bata wani ji farinciki ba, juyawa tayi ta fice aɗakin don samawa kanta abun da zata ci, batajin cin wani abu hakan yasa ta tsiyayo fresh milk me sanyi, kanta aƙasa take haura step ɗin da zai sadata da samannasu, sam bata kula da cewa shima yana zuwa ba, haɗuwarsu waje ɗaya ne yasanya gaba ɗaya fresh milk ɗin ya zube masa ajiki, cikin tsautsayi cup ɗin ya faɗi ya tarwatse a wajen. Aɗan razane ta ɗago kanta ta kalleshi, daidai lokacin shima ya ɗago kyawawan idanunsa, idanunsune suka sauƙa acikin na juna, da sauri tayi baya kasancewar sunyi matuƙar kusa da juna, bisa tsautsayi ta aje ƙafanta akan fasassun glass, wani irin ƙara ta sake tare da rumtse idanunta ƙam, beautyful eyes ɗinsa yaɗan zaro waje tare da kallon ƙasa inda ƙafanta tuni har ya soma fidda jini. Ƙaran da tayi shiya janyo hankalin Oummu, da sauri ta fito tare da ƙarasowa inda suke, cikin yanayi na damuwa tace
"Subahanallahi me ya faru?" cikin tsananin zafin dake ratsa har ƙwaƙwalwarta, ta buɗe idanunta da suka tara ruwan hawaye kana sukai ja, yunƙurin ɗaga ƙafanta ta somayi, amma zafin da takeji ya hanata, hakan yasa ta saki wani ɗan siririn ƙaran wahala, small pink lips ɗinsa ya ɗan ciza tare da raɓawa ta gefenta zai wuce. "SOORAJ me kayi mata ne?" cewar Oummu tana me ƙoƙarin kama ƙafan Zieyaderh don ta duba, fuska ɗauke da ɗan mamaki yasake ɗan waro Idanunsa alaman ni kuma mezan mata, kana ya taɓe lips ɗinsa.
"Subahanallah tayaya haka ta faru? Glass fa ta taka" Oummu tafaɗa tana me riƙe da ƙafan Zieyaderh, wanda har yanzu yake fidda jini, ƙarasowan Almustapha cikin falon kenan ya taraddasu atsaitsaye, da sauri ya ƙaraso garesu yana me cewa "Lafiya kuwa Oummu me ya faru?"
"Fasashshen glass ta taka, please zoka riƙemin ita naɗauko first aid box sai kayi mata treatment!" Oummu ta faɗa cike da tausayin halin da Zieyaderh ke ciki.
Babu musu Almustapha ya haura kan step ɗin tare da sanya hannayensa duka biyu ya kama kafaɗun Zieyaderh, wanda hakan yasa harta ɗan kwanto cikin jikinsa. Sauƙe hannayensa akan kafaɗunta, yayi daidai da bugawar zuciyarsa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dunƙule hannuwansa, lokaci ɗaya yaji wani irin jiri na neman kadashi, aɗan hanzarce ya juya cikin azama yabar falon.
Da taimakon Almustapha ta iya ɗingisawa zuwa kan kujera, sosai takejin zafi domin kuwa glasses ɗin sun ɗan caketa sosai, Oummu ne ta dawo hannunta ɗauke da first aid box, zama Almustapha yayi akan sofa tare da ɗaukan ƙafannata ya ɗaura akan wani ɗan madaidaicin stull, da cotton yayi using wajen goge mata jinin da ya ɓata ƙafannta, hannunsa yasa ya kama ƙafan, cike da kulawa ya shiga dubawa ko akwai wata ɓoyayyar kwalba dake a
cikin ƙafar, ganin babu yasanyashi ɗaukan hydrogen ya haɗa da auduga ahankali yake ɗan goga mata akan ciwon, kuka tasanya me sauti tare da rumtse idanunta, sosai takejin zafin hydrogen ɗin, murmushi Almustapha yayi ganin yanda take kuka tana me cije baki, cike da salon tsokana yace.
"Haba Bae da zafi ne?"
Tsaida kukannata tayi tare da buɗe jajayen idanunta, samun kanta tayi da murguɗa masa baki tare da yunƙurin zame ƙafarta daga hannunsa, murmushin daya bayyana white teeth ɗinsa yayi tare da cewa "Am sorry ai nama gama!" Kallon Oummu tayi tare da ɗan marairaice fuska, Murmushi Oummu dake tsaye tana kallonsu tun ɗazu tayi, aranta kuwa cewa tayi "Anya abun danayi kyautawa ne?" "Idan baizama kyautawa ba to tabbas za a ƙirasa da son kai!" Wata zuciyarta ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Allah shine shaidana nayi hakane don samun nutsuwa da salama azuciyar su dukan biyun, idan hakan bai yiwu ba kuwa to tabbas ko mai ya faru NI CE SANADI, sannan hakan zai zama kamar rashin adalci ne ga rayuwar ZIEYADERH!" maganan da Almustapha ke matane ya sanyata dawowa daga tunanin da take, inda yake cewa
"Yakamata taje ta huta, daga nan zuwa da safe karta taka ƙafan muga idan babu wani matsala shikenan, idan kuma mukaga ƙafar ta kumbura sai muje hospital!" Ya ƙare maganar yana me ƙoƙarin rufe first aid box ɗin dake gabansa.
Da taimakon Oummu Zieyaderh ta iya ɗingisawa zuwa ɗaki, adaddafe ta iya yin alwalan sallan magriba saboda zafi da ƙafan ke mata, haka ta samu tayi sallah nanma saida dabara don dazaran ta shumfuɗe tafin ƙafanta aƙasa tofa zafi zai ratsa gangar jikinta.
Yana barin falon haka yaji zuciyarsa nayi masa wani iri, yanajin yanayinsa duk ba daɗi, peter dake ta zaman jiransa tun ɗazu a waje yana ganinsa yataso da hanzari tare da buɗe masa murfin motar, shiga cikin motar yayi ransa duk ajagule, kallon agogonsa yayi yaga 5:50 am. Tsuka yaja tare da lumshe idanunsa da suka ɗan nuna alamun ɓacin rai acikinsu, 6 daidai jirginsu zai tashi amma gashi har yananeman yin late akan wannan stupid girl ɗin, wani siririn tsuka yaja akaro na biyu, shikam ya lura kamar yanda take mashiririciya haka komanta ma yake, yayi imani haukane kaɗai yake wanzar da irin tsoron da yake ganinta aciki da zaran ta ganshi. Hakanan yakejinsa cikin ƙuncin rai, suna isowa airport ya buɗe murfin motar agurguje, da sauri peter ya miƙo masa wata ƴar black trolly wanda abubuwan amfaninsa ne ke ɗauke aciki. Amsa yayi kana yashiga can cikin airport ɗin, saida ya kammala komai kafun yataho agurguje ya shiga cikin jirgi don 5 minute kacal ya rage flight ɗin ya tashi. Yana zama akan kujera ya sauƙe wani irin ajiyar zuciya tare da jingina bayansa da jikin kujeran, sit belt ya ɗaura kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, kamar yanda jirginsu ya tashi zuwa sararin samaniya haka arai da zuciyarsa yake fatan ace damuwarsa tayi ƙaura daga gareshi, awannan tafiyan yanason samawa zuciyarsa nutsuwa sosai, musamman akan sabon cutar da ta ɗauko mai wanda yakasa sanin gabansa balle bayansa.
Kwance take luf akan gado yayinda ta baza gaba ɗaya gashin kanta akan pillow, duk da cewa anɗau wasu mintuna dajin ciwon nata amma har yanzu tanajin zafi, wannan zafin da takeji ajikinta shine zafin daya tafi har zuwa cikin zuciyarta, ko wani bugu ɗaya na zuciyarta yakan zo matane da wani sabon sauyin yanayi, akowanni daƙiƙa ji take soyayyarsa na hauhawa acikin zuciyarta, sake gyara kwanciyarta tayi tare da lumshe idanunta.
SINGAPORE
Adaidai wannan lokacin shima ya gyara kwanciyarsa tare da lumshe kyawawan idanunsa, ako wani bugun zuciyarsa ɗaya yana tafiyane da sauye sauyen tunani da yake samu daga ƙwaƙwalwarsa, hannunsa ya ɗaura adaidai saman mararsa tare da ware idanunsa, sauƙesu yayi akan haɗaɗɗen adon zanen dake kewaye saman ɗakin, daga gefe guda kuwa ƙoyayen wutane keta aikinsu wajen bada kaloli masu ma'ana da ɗaukar hankali, domin duk bayan ko wani second kowanne daga cikinsu yake fidda wani irin diffrent colour na haske me kyau, daddaɗan sanyin garin da kuma iskan da ake shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na sau ba adadi, burinsa bai wuce bacci ya ɗaukesa ba, don zuwa yanzu zuciarsa takai ƙololuwa wajen matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani, bayan haka kuma gashi akwai gajiya sosai atattare dashi, sauda dama yakan zurfafa tunaninsa akan rashin lafiyansa, saidai kuma yasan komai na Allah Ne sai idan yasone zai baka lafiya, saɓanin haka kuwa kowani irin magani zakasha kodako yana maganin cutar taka sai kaga baiyi maka komai ba, yana matuƙar buƙatar lafiyarsa ayanzu saboda yanaji ajikinsa cewa nan gaba kaɗan zai cire rai da rayuwa, da kuma samun ingantaccen farinciki, tabbas ƙaddaransa babbace amma zaici gaba da ɗaukanta ahaka har izuwa lokacin mutuwarsa.
Bayan tayi sallan asuba bacci tayi sosai hakan yasa ba itace ta farka ba sai after 8. aɗan zabure tatashi daga kwancen da take tare da sanya hannu ta murza idanunta, ganin hasken rana ya bayyana raɗau ta window'n ɗakinne yasanyata zuro ƙafafunta ƙasa da sauri, agurguje tayi wanka tare dayin brush, koda ta fito sama sama tashafa body lotion ɗinta, sauri sauri tasanya kayan uniform don tasan zuwa yanzu tayi latti sosai, zama tayi akan bed tare da jawo cover shoe ɗinta wanda yake na makaranta, ƙoƙarin sanyawa ta somayi, ciwon dake cikin tafin ƙafanta ne yasoma yi mata ɗan zafi sakamakon safa data sanya, shikuma ciwon baison zafi, ɗan rumtse idanunta tayi tare da soma ƙoƙarin tura kafanta cikin takalmin. Turo ƙofar ɗakin Oummu tayi bakinta ɗauke da sallama, ganin Oummu yasanyata sakin murmushi tare dayin ƙasa da kanta cikin girmamawa tace da Oummu
"Ina kwana!"
"Lafiya lau, kinsamu tashi kenan yanzu shigowana na biyu kenan, ya ƙafan naki?" Oummu ta tambaya cike da kulawa.
"Da sauƙi Oummu, saidai yana ɗanmin zafi amma basosai ba"
Kallonta Oummu tayi tare da cewa
"Yanaganki cikin uniform? halan dai baki san ƙarfe nawa bane yanzun ko, kuma ma ai bazaki iya jigilan zuwa school da wannan ciwon aƙafanki ba!" Oummu tafaɗa cike da kulawa
Cikin yanayi naɗan sanyi ta gyaɗa kanta, don bata da abun cewa.
Murmushi Oummu tayi tare da dafata cike da kulawa tace "To kizauna yau ba zuwa school don mahaifiyar Almustapha da kuma wasu daga cikin ƴan uwana sun taso musamman don zuwa ganin amaryarsu!" Oummu taƙare maganar tana murmushin jin daɗi.
Faɗuwar gaba da tsinkewar zuciyane suka ziyarceta alokaci guda, amma saita ɗan daure ɗago kanta tayi ta kalli Oummu, murmushi Oummu ta mata cike da son ƙarfafa mata guiwa tace "Karki damu kanki akan komai Zieyaderh, ninan matsayin uwa nake awajenki idan kina da abun da kikeso ko abun da bakyaso duk ki sanar dani nikuma Insha Allah Zan sha re hawayenki, nasan ƴan uwana dukansu masu fahimta ne, so bakida wata matsala dasu nakuma san insha Allah Zaki samu ƙauna ta musamman daga garesu, karki damu kinji!" Oummu taƙare maganar cike da lallashi.
Kai Zieyaderh ta kaɗa mata alaman "To"
Cike da jin daɗi Oummu tace "Yauwa ki saki jikinki, ki cire uniform ɗin zan turo akawomiki abinci, sannan kizauna cikin shiri don anjima zan turo meyin kwalliya tazo ta gyaramin ke"
Kasa cewa komai tayi har Oummu tafice daga cikin ɗakin, ɗan guntun murmushin dake kan fuskarta ne ya koma, take kuma saiga hawaye suna gangarowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hannu ta share cike da tausayin kanta, haƙiƙa tasan duk wannan abubuwan suna faruwa ne kawai saboda tarasa abu ɗaya aduniyarta wannan abun kuwa bakomai bane face UWA MAHAIFIYA haƙiƙa duk wata Uwa haskece ga rayuwar ƴarta mace matuƙar itaɗin takasance UWA ta gari, UWA itace ginshiƙi sannan kuma farinciki arayuwar ƳAƳANTA, hannu takuma kaiwa ta share hawayenta, sakamakon knocking door ɗinta da taji anayi, tana buɗewa tayi kiciɓus da Nabila hannunta ɗauke da tray ɗin abinci, Nabila ɗaya daga cikin tarin ƴan aikin gidanne amma ita tana ɓangaren kitchine ne, itace me share sharen kitchine da goge duk wani inda aka ɓata, fuskarta ɗauke da ɗan murmushi ta amshi tray ɗin, yayinda Nabila ta juya ta koma, aje tray ɗin abincin tayi tare da soma bubbuɗe plates ɗin dake saman tray ɗin, plate ɗin farko soyayyan