Author : Maman Teddy Category : Romance
tace. "Naƙoshi."
Aje cup ɗin yayi tare da sanya hannayensa ya kama waist ɗinta, cikin kulawa ya matso da fuskarsa daf da nata, forehead ɗinsa ya ɗaura akan nata, har takai ga hancinsu na gogan na juna, idanunsa ya lumshe ahankali yake fitar da wani irin numfashi, itama lumshe idanun nata tayi tare da sakar masa jikinta gaba ɗaya, sosai yanda numfashinsu ke cakuɗa dana juna yasanyashi jin wani irin kasala na sauƙar masa, ɗan matsar da fuskarsa gefe yayi, ahankali yake ɗan goga mata lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa agefen nata fuskar, lumshe idanunta tayi tare da sakin wata irin ajiyar zuciya, sosai hakan da yakeyi mata, ke yi mata daɗi, musamman yanda lallausan gashinnasa ke gogan fresh skin ɗinta, hannunta ta ɗaura akan shoulder ɗinsa, yayinda shikuma ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta, slowly haka yake yawo da harshensa acikin kunnenta, kasa jurewa tayi har saida ta ƙara shigewa cikin jikinsa, bakomai ke zautar da itaba kamar yanda harshensa ke yawo acikin kunnenta, gefe guda kuwa ga daddaɗan ƙamshinsa dake zautar da ita, ahankali ya kwantar da kansa akan wuyanta, numfashi yake fitarwa ahankali bakinsa ke motsawa da alama wani abu yake son faɗa, tabbas yana so ya furta mata saidai yanajin zuciyarsa nayi masa nauyi, yanajin kamar bayanzu yakamata ace ya faɗa mata ba, sake lumshe idanunsa yayi haɗe da matseta acikin jikinsa, sosai ƙamshin dake fita ajikinta keyi masa daɗi, mintuna sama da goma suka shafe ahaka batare dakowannensu ya ƙara ƙwaƙƙwaran motsi ba, tuni Zieyaderh kuwa wani irin bacci ya fara fusgarta, don aduk sanda tajita cikin jikinsa wani daɗi takeji na musamman, sannan tana samun wata irin gamsuwa, ahankali yaɗan janye jikinsa daga nata, duban fuskarta yayi, itama dubansa tayi da idanunta wanda suka fara ɗan lumshewa, ɗaukanta yayi caɗak inda ya ƙarasa da ita zuwa kan gado, kwantar da ita yayi akan gadon tare da jawo blanket ya rufe mata rabin jikinta, sunkuyowa daidai fuskarta yayi lumshe idanunsa yayi ahankali ya ɗaura laɓɓansa akan nata, slowly yaɗanyi sucking lips ɗinta, hannunsa yasanya yashafi gashin kanta, ɗagowa yayi tare da kashe mata gaba ɗaya hasken ɗakin, hannayensa ya tura cikin aljihun wandonsa kai tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Tanajin ficewarsa ta lumshe idanunta, sannu ahankali tarin ƙaunarsa ke ƙara ratsa cikin jiki yana huda jijiya da ɓargonta.
Daga ɓangaren nasu kai tsaye babban compound ɗin gidan ya nufa, direct wajen da cars ɗinsa ke ajiye yanufa, wata ɓaƙar mercedes benz ya shiga, koda maigadi ya wangale masa makeken gate ɗin, ahankali ya cilla motar tasa kan titin dake shimfuɗe direct tundaga ƙofar gidannasu har zuwa ƙarshen hanyar da zata fitar dakai a unguwar tasu ta Maitama.
Sannu ahankali yake murza steering motar, zuciyarsa ɗauke take da tunaninta mai tarin yawa, sosai yakejin wani abu na musamman agame da ita na game gaba ɗaya jikinsa, da tunani kala kala acikin ransa yaƙaraso haraban babban asibitin.
Cikin nutsuwa yake tafiya yayinda ya nufi hanyar da zata sadashi da office ɗin Dr.Waleey.
Amna sakateriar Dr.Waleey na ganinsa ta miƙe da sauri cikin mayen sonsa da tajima tanayi taɗan ƙaraso da sauri, cikin ƙasa da murya tace.
"Ranka ya daɗe barka da zuwa."
Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya ce da ita komai ba, ganin fuskarsa atsuke kamar koda yaushe yasanya ta juya da sauri ta nufi office ɗin na Dr.Waleey, bawani jimawa tafito inda tanuna masa ƙofan office ɗin alaman ya shiga, baiko kalli inda take ba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki.
Dr.Waleey naganinsa ya saki murmushi tare da tasowa ya bawa SOORAJ ɗin hannu suka gaisa, kujera ya nunawa Sooraj ɗin, bayan Sooraj ya zauna ne yajawo kujeran dake facing na Sooraj din shima ya zauna.
Cikin rashin sabo da yawan magana Sooraj yaɗan ɓata fuska, cike da aji yasanarwa Dr.Waleey irin zazzafan zazzaɓin dake damun jikinsa, sannan yaƙara da sanar masa yanda kansa ke masa bala'in ciwo kamar zai rabe gida biyu.
Murmushin tsananin jin daɗi Dr.Waleey yayi don aɗan bayanin da Sooraj ɗin yayi masa tuni yagano abun dake damunsa, cikin jin daɗi da kuma son kwantar masa da hankali Dr. Waleey yayi ajiyar zuciya, tare da gyara zama, kana yace.
"Ƙwarai naji daɗin wannan labarin SOORAJ, tabbas alamomin zazzaɓi da ciwon kannan da kakeji alamane dake nuna cewa kaima yanzu kazama cikakken Namiji mai lafiya, dama cutarka ba da ita aka haifeka ba, sannan kuma ba sihiri ko shafar aljanu bane, cuta ce da Allah Kan iya sawa kowani bawa, Allah Shi ya ɗaura ma kuma gashi ayanzu shi ya yayema, tabbas wannan yana daga cikin ƘADDARANKA dama ita Jarabawa takanzowa bawa ta inda baizata ba, sannan idan tayi tsanani Allah yakan sauƙaƙata, kada kayi mamakin samun lafiyarka SOORAJ saboda cuta da kuma sauƙi duk na Allah Ne, Allah Ne kaɗai kan iya bayar da lafiya ga bawa aduk lokacin dayaso."
Ɗan numfasawa Dr.Waleey yayi tare da ɗaukan wata farar takarda yaɗanyi rubutu kaɗan akai, miƙawa Sooraj paper ɗin yayi cikin kulawa yace.
"Ga wannan idan kafita sai kasaya a babban pharmacy, magungunane da zasu sauƙaƙa wajen hana zafin zazzaɓin yin ƙarfi, bare har yakai ga ya dameka, kuma sannan zazzaɓin ya shigeka ne saboda yanayin yanda ka sarrafa jikinka batare daka saba ba, Insha Allah Nanda wani lokaci komai zai dawo normal, sannan ayanzu zakanajin wani irin feeling na tasomaka sosai, kada kace zaka jure abunda kakeji, ka ƙoƙarta yin sex akai akai zai taimaka ƙwarai wajen dawo maka da cikakkiyar lafiyarka."
Amsan papern Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye, jin surutan da Dr.Waleey'n keyi, har yasanya kansa ya fara yi masa ciwo, hannu ya bawa Dr.Waleey inda sukayi musabaha daga nan yayi masa sallama, koda ya fito daga cikin office ɗin na Dr.Waleey haka Amna tabisa da wani irin mayataccen kallo harya ɓacewa ganinta, sosai yake tsananin burgeta, kama daga yanda yake dressing da kuma yanda yake aiwatar da komansa cikin nutsuwa, haka kuma sosai MISKILANCI nsa ke burgeta, duk da cewa miskilancinnasa ya zarce misali amma ahaka take kwaɗayin rayuwa dashi, saidai kuma tasan kamar yanda wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, haka shima yayi nesa da ita, don yazama kamar wutsiyar raƙumi itakuwa tazama tamkar ƙasa, dama ance hanyar jirgi daban hakama na mota daban.
Yana isa compound ɗin asibitin direct inda motarsa take ya nufa, yana shiga yabata wuta.
Gudu sosai yake shararawa akan babban titin dazai sadashi da unguwar ta Maitama, sanye yake da baƙaƙen kaya ajikinsa yayinda yasanya wata baƙar mask ya rufe gaba ɗaya fuskarsa, idanunsa kawai zaka iya hangowa, ayanda yakejin zucia da ransa na tafasa yanajin komai ma zai iya aikatawa, ayau bayajin zai iya haƙuri yashanye ɓacin ran da SOORAJ ke ɗura masa, SOORAJ ya ƙwace masa komai, a sanadin sa yarasa abubuwa da dama, asanadin SOORAJ yarasa babban matsayin dayake kai, sanadin SOORAJ company'nsa wanda yake matuƙar ji dashi ya durƙushe, akodayaushe sunan companyn ƙera abayas na SOORAJ dake Dubai ne ke yawo ƙasashe ƙasashe ba nasa ba kamar yanda yakeso, SOORAJ yasashi ya rasa abubuwa da yawa, ciki kuwa harda yarinyar dayake fatan kashe ƙishin ruwansa akanta, saboda haka baya tunanin zai iya barin SOORAJ ya rayu cikin duniya.
SOORAJ kuwa ganin ya kusa shigowa cikin unguwar tasu ta maitama ne yasanyashi ɗan ƙara gudun motar, daidai zaisha wata kwana batare da ya kula ba wata mota tayiyo kansa da gudun gaske, shima batare daya taka birkin motar tasa ba yayi kan motar, wani irin karo da sukayine yasanya gaba ɗaya motocin nasu tashi sama, alokaci guda kuma suka faɗo ƙasa, cikin ƴan mintuna ƙalilan gaba ɗaya motocin suka fara fitar da hayaƙi.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*Wattpad*
@fatymasardauna
#romance.
*(Gabaki ɗayan wannan fejin sadaukarwa ne agareka HAMEED, ina maka fatan farinciki me ɗorewa a iya ka tsawon rayuwarka.!❣️)*
*Chapter 53*
Sosae duka motoci biyun ke fitar da hayaƙi, kasancewar ba kaɗan ba motocin sukayi mummunan buguwa, hayaƙi ne ke cigaba da fita sosai ajikin motar kowannensu, cikin matsanancin sauri, haɗi da gaggawa, ƴan sandan dake gadin area'n, suka taho domin bawa waƴanda ke cikin motar taimakon gaggawa, domin kuwa nanda wasu lokuta idan wani bai taimaka ba, lallai gaba ɗaya motocin zasu iya kamawa da wuta, cikin sauri da dabara haka ƴan sandan nan suka shiga ƙoƙarin fito da kowannensu daga cikin motar, gaba ɗayansu babu wani wanda yake da alaman numfashi ajikinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata fuskokinsu, har takai ga baka iya tantance kamanninsu, Ambulance ƴan sandan suka ƙira take cikin ƴan mintuna ƙalilan aka zo aka kwashesu dukansu, Kaitsaye babban privet hospital ɗin dake cikin garin Abuja wato Nizamiyye Hospital aka nufa dasu.
Direct Emergency aka wuce dasu, lokaci ɗaya aka soma basu taimakon gaggawa.
Zaune take akan stool ɗin dake aje gaban dressing mirror, sanye take da towel ajikinta, yayinda jikinta ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alamu fitowarta daga wanka kenan, ahankali take murza sassanyan body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi ajikinta, harwani ɗan lumshe idanu takeyi, saboda sosai ƙamshin body lotion ɗin keyi mata daɗi, har takai tanajin batason daina goga maiɗin ajikinta, koda ta kammala sama sama ta shafa powder akan kyakkyawar fuskarta, wani ɗan light pink lipstick ta goga akan ƴan madaidaitan laɓɓanta, black eye pencil ta ɗan goga acikin idanunta, mascara tasanya taɗan taje eyelashes ɗinta, take suka ƙara mimmiƙewa sukayi zara zara dasu.
Kallon kanta tayi amadubi naɗan wasu sakanni kana ta lumshe idanunta, moment ɗinsu na ɗazu ne kawai ke yawo acikin brain ɗinta, sosai takejin daɗin kasancewa dashi, domin aduk sanda take tare dashi takanji wani abu na musamman na yawo cikin jikinta.
Ahankali ta tashi daga kan stool ɗin inda ta nufi gaban babban drawer ɗinsu, ɓangaren kayanta ta buɗe inda ta zuba musu ido, tunanin wanda zata saka take, nan dai ta zaro wata doguwar rigar atamfan ABC, wanda take da kalan blue wato shuɗi, sosai zanin keda kyau, yayinda aka shumfuɗa mata wata haɗaɗɗiyar straight gown me kyaun gaske, rigar irin doguwar nance, sosai kuma aka fitar da shape ɗin ta, yayinda gefe da gefen rigar dama da hagu suka kasance atsage, tun daga ƙasa har gefe da gefen cikinta abuɗe suke, wani dogon pencil crazy jeans ta sanya, tare da ɗaura tsagaggen doguwar rigan akai, sosai tayi kyau, musamman yanda haɗaɗɗen shape ɗinta ya bayyana ta cikin tsagun rigar, dayake jeans ɗin yakama jikinta sosai, parking dogon gashin kanta tayi yayinda ta naɗeshi a tsakiyar kanta, wani ɗan madaidaicin blue vail ta yafa akanta, wanda ya kawo har kan cikinta, sosai tayi kyau cikin shigarta ta, ƙarasawa gaban mirror tayi tare da ɗaukan body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wanda akullum ƙamshinsa ke ƙara zautar da ita ta fesa ajikinta, wani flat shoe tasanya aƙafanta, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta fice, kaitsaye ɗakin da zai sadata da babban falon na Oummu ta nufa, taku biyu ya rage mata taƙarasa zuwa cikin falon taɗan tsaya, daidaita nutsuwa haɗi da tafiyarta tayi, sannan ahankali tatura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Zaune ta samu Oummu acikin katafaren falon nata, fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata sallaman da takeyi, cikin ladabi haɗi da biyayya ta ƙaraso har gaban Oummu, durƙusawa tayi tare da gaisheta, cikin sakin fuska Oummu ta amsa mata, tare da tambayanta ya take, cikin yanayi naɗanjin kunya Zieyaderh tayi ƙasa da kanta, haka Oummu ke ta janta da hira, itakuwa har cikin ranta kunyan Oummu takeji musamman idan ta tuna abun daya faru daren jia atsakaninta da Mr.Helper. Wayar Oummu dake aje bisa kan dinning table ne tasoma ruri alaman shigowar ƙira, Da sauri Zieyaderh ta tashi don ɗauko mata wayan, sam tamanta cewa agaban Oummu take hakan yasa take taka ƙafarta ahankali, duk dama bawani zafi takeji sosai acikin jikinnata ba.
Da kallo mai ɗauke da tsantsar nazari Oummu ta bita, wani tunani dayazo cikin ran Oummu ne yasanyata sakin murmushi mai ɗauke da tsananin jin daɗi, daidai lokacin Zieyaderh ta dawo hannunta ɗauke da wayar Oummu'n, cikin ladabi ta miƙawa Oummu wayar tare da dawowa ta zauna, da sallama Oummu ta amsa wayar, saidai jin abun da ake faɗa mata acikin wayar yasanya ta miƙewa tsaye, cikin tsananin fargaba haɗi da tsoro tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!." Wayar dake saƙale akan kunnen nata ne ya sulale ya faɗi ƙasa, take idanunta suka cika tab da ƙwalla, cikin fargaba Ziryaderh ta kalli Oummu'n, ji tayi gabanta ya faɗi take wani irin tsoro ya shiga jikinta, hakanan tunaninsa ya faɗo mata arai, jikinta na rawa taƙaraso kusa da Oummu'n, kallonta Oummu tayi take kuma saitaji wasu irin hawaye mssu ɗumi sun gangaro daga cikin idanunta, wani irin matsanancin tausayin kansune ya kamata, ganin hawaye na fita daga cikin idanun Oummu yasanya taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta.
Hannu Oummu takai ta dafa kafaɗan Zieyaderh wacce itama idanunta sun cicciko da hawaye, duk da kasancewar ma batasan menene ke faruwa ba, daidai lokacin akaturo ƙofar falon aka shigo, Mas'oud ne ya shigo shima fuskarsa ɗauke da tsananin damuwa haɗi da tashin hankali, Oummu naganinsa taƙaraso garesa cikin sauri da ruɗewa takamo hannunsa, murya ɗauke da rauni tace.
"Mas'oud, SOORAJ!."
Idanu Mas'oud ya lumshe cike da tausayinsu, cikin son kwantar wa da Oummun hankali yasanya hannunsa ya share hawayenta,murya ƙasa ƙasa yace.
"Muje mu dubasa Oummu."
Da sauri Oummu tajuya ta haura sama don ɗauko mayafinta.
Zieyaderh kuwa gaba ɗaya kanta ya kulle, jin an ambaci sunan SOORAJ,yasanya jikinta ya ɗauki rawa, sosai wani irin tsoro ya shigeta, bata fatan jin cewa wani mummunan abune ya sameshi, bazata iya jurewa ba, sam bazata iya jure abun da zai cutar mata dashi ba.
Oummu ce ta sauƙo daga kan mattakalan cikin sauri, ƙoƙarin yafa ƙaton mayafinta tayi, cikin kulawa ta dubi Zieyaderh dake zaune idanunta cike da ƙwalla, hannayen Zieyaderh'n ta kamo, duka suka ɗunguma sukayi waje, cikin motar Mas'oud suka shiga, dawani irin speed Mas'oud yaja motar, kai tsaye Nizamiyye hospital suka nufa.
Sosai likitoci suka duƙufa akansu wajen basu agaji da taimakon gaggawa, sama da awa ɗaya likitotin nan suka share akansu suna ƙoƙarin ceto rayuwarsu, saidai kuma sunyi iyayinsu, amma abun naneman fin ƙarfinsu, duk da cewa Sooraj baiwani ji ciwo sosai ba, saidai buguwa daya samu ahanannu da kuma ƙafansa kawai, amma kuma yayi suman da har yanzu bai dawo cikin sense ɗinsa ba, shikuwa Pharouk sosai yasamu buguwa akansa, hannunsa da ƙafansa gaba ɗaya sun karye, gashi jikinsa gaba ɗaya ya kukkuje, sannan shi ne wanda yafara farfaɗowa kafun RAJ saidai kuma sam baya iya zuƙan numfashi da kansa, dole yasanya aka wuce dashi ICU domin ciwon nasa yayi tsanani, shikuwa Sooraj sun bashi duk wata taimako da zasu iya, daganan aka wuce dashi wani ɗakin hutu bayan sunyi masa wata allura mai ƙarfin gaske, wanda aƙalla zaiyi bacci na 5 hours kafun ya farka, suna kuma sa ran idan yafarka zai tashi lafiya ƙalau insha Allah.
Idanunta ne suka sake cika da hawaye ganin sun tsaya abakin ƙofar shiga asibitin, nanfa gabanta yafara dukan uku uku, take wani irin rauni ya cika zuciyarta.
Haka suka nufi cikin asibitin kowa da abun da yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.
Kaitsaye Mas'oud wajen wani babban likita me suna Dr.Anas wanda awajensa case din su Sooraj ɗin yake ya nufa, nan Dr.Anas ya ɗanyi musu ƙarin bayani tare da kwantar musu da hankali, sosai zuciyar Oummu dana Mas'oud suka ɗan samu salama jin cewar jikin Sooraj ɗin da sauƙi, har ma zai iya farfaɗowa zuwa anjima, ita kuwa Zieyaderh tuni zuciyarta tanarke da tsananin tausayin mijinta, take taji ba abun da take burin gani daji kamar sa.
Dr.Anas dakansa yayi musu jagora har zuwa ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance, Dr.Anas ne ya dubesu tare da cewa idan suka shiga kar su cika surutu saboda zai iya affecting ɗinsa.
Haka suka shiga cikin ɗakin kowanne zuciyarsa ɗauke da fargaba, kwance suka iskesa flat fuskarsa na kallon sama, dagashi sai dogon wandon jeans a jikinsa, hannunsa na dama ɗaure yake da bandage haka ma ƙafarsa ɗaya itama an nannaɗeta da bandage, sannu ahankali ruwan da aka ɗaura masa ke ɗiga ajikinsa.
Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar shigowar, lumshe idanunta tayi take saiga hawaye sun kwaranyo bisa kan ƙuncinta, hannunta tasanya ta dafe daidai saitin zuciarta da keyi mata zafi, ahankali su Oummu suka ƙarasa jikin gadon, hannu Oummu tasanya ta shafi lallausan sumar kansa, take kuma saiga hawaye zun kwaranyo daga cikin idanunta, Mas'oud ma ƙarasowa yayi yaɗan shafa kan SOORAJ ɗin, Dr.Anas ne yayi musu alama akan subiyosa zuwa waje, babu musu dukansu suka bi bayansa, aɗan wani corridor ya tsaya dubansu yayi da kyau tare da cewa cikinsu su bar mutum ɗaya wanda zai kula da Sooraj ɗin, Oummu ne ta dubi Zieyaderh, cikin sanyin murya tace.
"Zieyaderh kibi Mas'oud ku koma gida ni zan zauna dashi kafun ya farka."
Da sauri Zieyaderh ta girgiza kanta so take tacewa Oummu A'a amma kuma bata da bakin musa mata, Dr.Anas ne ya dubi Oummu tare da cewa.
"Bashida mata ne?."
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe, kana tace "Yana dashi."
Jinjina kai dr Anas yayi tare da yiwa Zieyaderh dake hawaye duban tsab, take jikinsa ya basa cewa itace matar Sooraj ɗin, duban Oummu ya kumayi cikin ɗan sakin fuska yace.
"Inaga kubar wannan sarauniyar hawayen ta zauna idan yaso sai ku ku koma, zaki iya kulawa dashi ae ko sarauniyar hawaye?." yaƙare maganan yana ɗan Murmushi.
Duk da yanayin da suke ciki saida Oummu da Mas'oud suka ɗan murmusa, maganar Dr.anas kuwa suka bi, inda Mas'oud ya maida Oummu gida don zataje tayi musu girki, nan akabar Zieyaderh.
Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga, cikin nutsuwa take takowa har zuwa inda