Author : Maman Teddy Category : Romance
yatambayesa cike da tsananin mamaki, saboda duk wani maihankali dole ya tsoraci lamarin SOORAJ.
Kallon Mas'oud ɗin SOORAJ yayi da jajayen idanunsa, araunane yace "Inada hankali Mas'oud kamar yanda kaima kake dashi, abu ɗaya kawai nasani shine wannan itace ƘADDARATA!" yana kaiwa ƙarshen zancennasa ya miƙe tsaye tare da soma tattara kayan training ɗinsa, Mas'oud na kallonsa ya tattara komai nasa yafice daga cikin ɗakin training ɗin. Mas'oud kam kasa tashi yayi yazauna daɓas, sosai al'ajabi da kuma mamakin abokinnasa RAJ ke ƙara kamasa, shikam yanzu yayarda cewa aljana ce tashafi Abokinnasa.
SOORAJ kuwa yana fita daga wajen training ɗin direct motarsa yanufa, yana shiga yayi mata key tare da cillata kan titi..
Yana komawa gidansa yayi wanka, dakansa yashiga cikin makeken kitchine ɗinsa, wanda yazuba masa kayan amfani, babu abun da babu na amfani acikin kitchine ɗin. Ruwan tea yadafa kana ya juye a flask, kan dinning area yadawo yazauna tare da haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda ɗayan hanunsa ke riƙe da wayarsa yana latsawa. Safiya rana dare SOORAJ bayida wani abinci sama da ruwan tea, arana sai yasha tea sama da sau uku, abune mawuyaci yazauna yaci abinci kamar yanda kowa yakeci. Yana shanye tea ɗin ya miƙe tsaye, mug ɗin da ya haɗa tea ɗin aciki ya ɗauka ya wuce kitchine, wankewa yayi yamaida shi mazauninsa.
Falo yadawo yazauna akan ɗaya daga cikin lallausan kujerun falon, remote ɗin receiver yaɗauka, ya sanja tasha. Knocking ƙofar falon akasomayi, cikin gajiyawa yace "Yes come in"
Piter ne yashigo hanunsa riƙe da wasu zabga zabgan tsintsiyaye dakuma moper, ɗurƙusawa yayi cike da ladabi yace "Good Morning Sir"
"Morning" kawai yace tare da tashi yatattare wayoyinsa ya nufi bedroom, don bawa piter daman yin aikinsa da kyau.
Yana shiga ɗaki yafaɗa saman gado haɗe da jawo pillow yaɗaura kansa akai. Shiru yayi yana mai lumshe idanunsa, tun ɗazu kalaman Abbansa ketayi masa yawo acikin kunnuwansa, tabbas yasan dolene iyayensa suyi fushi dashi, amma shima bayin kansa bane, ƘADDARA ce baikuma isa kauce mata ba, amma yanda iyayen nasa suka ɗauki zafi sosai shine abun dayasanya yaji gaba ɗaƴa duniyar tayi masa ɗumi, shi kaɗai yasan kansa, shikaɗai yasan wanene shi, shine wanda yasan matsalarsa, taya ayanda yake zai iya zama da mace? sai yaushene iyayensa zasu fahimci matsalarsa? sama da shekaru 7 kenan yana fama da matsala guda ɗaya, shiɗin namijine, baida wani wanda zaije yafaɗawa damuwarsa, dole shine zai nemi maganin matsalarsa, haryau kuma akan neman maganin matsalannasa yake amma baidace ba, shikansa bazai iya fitowa fili yafaɗi abun dake damunsa ba, yabarwa kansa cewa matsalansa itace sirrinsa, zama da mace kamar mafarin tonuwar asirin sa ne, yajima yana tunanin cewa shi ba'ayisa don yazauna kuma yasan wata ƴa mace ba, amma dazaran yafara wannan tunanin yake saurin furta astagfirullah domin yasan saɓone yakeyi, to amma yazaiyi shima bayida zaɓi ne, akullum akuma koda yaushe da Allah kawai ya dogara....
*** Tana zaune aɗaki tayi jigum abubuwane suka haɗe mata, aƴan kwanakinnan sosai take mamakin sauyan da Inna Ma'u tayi, tarage sata yawan aikace aikace, sannan kuma koda aikanta ne yanzu andainayi bakamar daba da kullum ƙafarta na waje tana yawon zuwa aika, yanzuma tana zaune ne aɗakinta tana sauraran hayaniyar ƙawayen Inna Ma'u dake tashi a tsakar gidan, itadai batasan meke gudana acikin gidannasu ba amma tabbas tasan cewa akwai wani abu da za'ayi acikin gidan. Zulai ƙawar Inna Ma'u ce ta yaye yagalgalellen labulen dake ƙofar ɗakin nata. Ayatsine ta watsowa Ziyada dake zaune harara, "Uwar munafurci saiki fito ae" cewar Zulai, tana gama faɗan haka kuwa tasake labulen tayi tafiyarta.
Jiki asaɓule Ziyada tafito daga cikin ɗakin nata, Gani tayi su Inna Ma'u sun baje akan tabarma yayinda suka kwaɓa lalle awani babban fanteka.
"Zo maza ki zauna" ɗaya daga cikin ƙawayen Inna Ma'u tace da Ziyada.
Cikin sanyin daya zame mata sabo taƙaraso ta durƙusa agabansu, ƙirjinta sai bugawa da sauri yake saboda tsabar tsoronsu da take.
Zaunar da ita sukayi agabansu, yayinda suka sanya ta kwaye musu cinyoyinta, da ƙarfin gaske suka shiga durza mata ƙwaɓeɓɓen lallen ajikinta, hatta fuskarta saida suka mulke mata shi da lalle, itadai ganin abun take awani baƙon yanayi, saboda tasan agarin nasu idan za'awa mace aurene kawai ake yi mata haka, suna gama shafa mata lallen sukace taje ta wanke, wani irin daɗine yaziyarci zuciyarta, domin albarkacin wannan lallen da suka shafa mata yasa zatayi wanka, bata mantawa rabonta da wanka yau sati guda kenan, dokace mai zaman kanta Inna Ma'u takafa mata akan cewa duk randa tayi wanka, bazata sake yi ba sai bayan wani satin, ruwa takandama abaho tayi bayinsu, alokacin da tacire kayanta tasoma watsawa jikinta ruwa, saida ta sauƙe wasu lafiyayyun ajiyar zuciya harsau uku, saboda wani irin sanyin daɗi daya ratsata, dama ita tuncan haka nan Allah yayita, tanada tsananin sonyin wanka, amma kuma bata samu tanayi saboda uƙubar Inna Ma'u.
Inna Ma'u kuwa masifa ta rufe ƙawayennata dashi wai akan mai zasu kwaɓa lalle su shafawa Ziyada. Zulai ce tagyara zama haɗe da turo ɗaurin ɗankwalinta gaba. "Wallahi yanzu na tabbatar baki da wayo Ma'u, kinga wannan lallen damuka shafa mata, shizai sanya jikinta yaƙara kyau, hasken fatarta yasake fitowa, kinsan yarinyar shegiya ɗanbanzan kyaune da ita, to kinga yanzu zata ƙara kyau akan nada, idan Tsoho Ɗan Dashe kuwa yaganta, saiya ƙara susucewa akanta, kinga ke kuwa kinsamu hanyar da zaki amshe masa ƴan kuɗaɗe kice kuɗin gyaran jiki, ai abirni haka akeyi kinsan nifa nayi zaman birni"
Shewa Inna Ma'u tasanya haɗe da bawa Zulai hanu suka tafa, cike dajin daɗi tace "Wallahi shiyasa nake mugun sonki Zulai, kinsan kan duniya, aikuwa ayau yau saina karɓi wani abu daga wajensa" sake tafawa Inna Ma'u da Zulai sukayi daidai lokacin Ziyada tafito daga wanka, zanine ɗaure aƙirjinta kanta gaba ɗaya yajiƙe yake da ruwa, tana shigewa ɗakinta, Zulai tadawo da kallonta ga Inna Ma'u cike da mamaki tace "Wai Ma'u dama haka wannan yarinyar keda diri da kyau? nikuwa anya basu haɗa iri da larabawa ba?"
Taɓe baki Inna Ma'u tayi, domin ita aduniyarta babu abun datafi tsana kamar taji anyabi Ziyada, "To wama yasanine tsinannu, ai tunda nasamu nagama da uwarta itama yarinyar bawuya zata bani ba, wannan shegen idanun nasu masu kama dana aljanu yana ɗaya daga cikin abun dayasa na mugun tsanarsu, gashi komai na halittar uwarta ta kwashe!" Inna Ma'u tafaɗi haka cike da baƙin ciki.
"Aikuwa Ma'u kinyi farar dabara da kika haɗa auren ta da Ɗan Dashe, kinga zata ƙare rayuwarta cikin ƙasƙanci, kinsansa baya riƙe aure, duk da yagama tsofewa, amma baijirayi kansa ba, dakin tsaya kuwa kina nan zakiga wani sarki ko senata sunzo neman aurenta" cewar wata daga cikin ƙawayen Inna Ma'un, wato Lantana.
"Cab iye bakinki Lantana, ina darai kam ƙaryane wani mai arziki ya raɓi Ziyada, sam hakan bamai yiwuwa bane, koda kuwa zanyi yawone tsirara na gwammace nayi, dana bar jinin Maryama ta auri wani mai kuɗi, nama kashe maciji bansare kansaba kenan" Faɗar Inna Ma'u. Dariya suka sanya sudukansu, yayinda ƙawayennata sukacigaba da fonfata....
Ziyada kuwa tsabar taji daɗin jikinta da tayi wanka tana kwanciya kawai sai bacci ɓarawo ya saceta...
Washe Gari.
*** Tun tashinta yau takejin faɗuwar gaba, babban abun daya ɗaure kanta shine, ƴan uwan mahaifinta da tagani sun cika gidan, da'alama dai kamar biki za'ayi agidannasu bata kuma san bikin waye za'ayi ba. Tazo wucewa zata shiga banɗaki wata ƴar addar babanta ke cewa "Amarya Amarya bakya laifi Amarya agidan Tsohon najadu"
Jitayi gabanta yafaɗi cike da mamaki tajuyo tana kallon Hajara wacce tafaɗi maganar, bakinta na rawa tace. "Yaya Hajara wacece amaryan?"
Harara Hajara ta watsa mata domin dama tun can su bawani sonta suke ba. "Wace amarya kuwa inbanda ke, ko baki da labarin cewa gobe za'a ɗaura miki aure da tsohon najadu?" Dariya Hajara tasanya haɗe dacigaba dacewa "Abun yayifa yarinya ta auri wanda yagirmi ubanta" sai takuma sake bushewa da dariya.
Jikin Ziyada ne yasoma rawa, lokaci guda taji cikinta yayi wani irin murɗawa atsorace ta ƙaraso gaban Hajara tazube aƙasa, murya na rawa tace "Dan Allah Adda Hajara kifaɗamin gaskiya, auren waye za'ayi?"
Kallon kinma rainamin wayo Hajara tashiga yiwa Ziyada ahasale tace.. "Bansaniba munafuka, waye baisan cewa kema son auren kikeba? dama ai kowa yasancewa ke tsohuwar hanuce, wayasanima koshima Tsohon najadun ya ɗana"
Kuka Ziyada ta fashe dashi da gudu ta tashi tanufi ɗakin Inna Ma'u, tana shiga ta zube agaban Inna Ma'u dake tsaye, cikin kuka tace.
"Dan Allah Inna Ma'u kimin rai, kifaɗamin cewa maganar da Adda Hajara kefaɗi bagaskiya bane, wai dagaske aurena za'ayi, kuma ɗan dashe zan aura?"
Wata uwar tsuka Inna Ma'u taja haɗe da ɗauko ashar ta bankawa Ziyada cike da takaici tace
"To idan bakiyi aure ba kwaɗaki zamuyi mucinye? inbanda ƙaddarama me Ɗan Dashe zaiyi dake, shima dai dayake tsohon maye ne shiyasa, amma bacin haka banga maiyagani awannan busheshshen jikinnaki ba, da Allah nitashi kibani waje, kuma aurenki da ɗan dashe babu fashi, gobe iwar haka kinzama matarsa"
Kuka Ziyada tashiga rerawa hadda majina tana roƙon Inna Ma'u, amma Ina Inna Ma'u haka ta murje idanunta.
Komawa cikin ɗakinta tayi hankalinta amatuƙar tashe, zama tayi daɓas aƙasa haɗe da ɗauko wani mayafin mamanta ta rungumeshi ƙam acikin ƙirjinta, kuka take tamkar zararriya...
"Wayyo Mamana kinga rashinki abundaya jawomin, Ya Allah kataimakeni kakawomin ɗauki!" Ziyada tafaɗi haka cikin matsanancin kuka. Tsabar kukan da Ziyada tayi harsaida muryarta ta dashe. Tana zaune aɗaki taji muryan Babanta, a tsakar gidan nasu, da sauri ta ɗaga labulen ɗakin tana leƙensa, sosai takejin tsananin tausayin mahaifinnata, duk da cewa tana da ƙananun shekaru amma hakan baisa takasa fahimtan cewa wasu abubuwan dayake aikatawa ba acikin hayyacinsa yakeyinsu ba, ganin yafice daga cikin gidanne, yasa tafaki idon mutane tarufa masa baya, zaune ta iskeshi akan ɗan dakalin dake ƙofar gidannasu. Tsugunnawa tayi agabansa Cikin da shashshiyar muryarta da ta ƙoshi da kuka tace
"Baba!"
ɗagowa yayi ya kalleta, batare da ya amsa mata ba.
"Dan Allah Baba kataimakeni, wallahi banason ɗan dashe!" tafaɗi haka hawaye suna mai kwaranya daga cikin idanunta.
Shiru Malam Garba yayi cike da tausayin ƴartasa, lokaci guda kuwa ya zabura kamar anjona masa shocking.
"Uban maikikeyi anan?" yatambayeta atsawace.
Jikintane yasoma rawa, yayinda kuka yasakecin ƙarfinta, cikin kukan tace. "Dan Allah Baba kaceci rayuwata, katunafa ni amana ce Allah yabaka, dan Allah Karka bari acutar da rayuwata!!"
Wata uwar tsawa yakuma doka mata, haɗe da rufe idanunsa yakorata gida.
Haka takoma gida tana kuka maicin rai, lallai tasake tabbatarwa da kanta cewa ita cikakkiyar marar gata ce, zama tayi akan tabarmarta haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, lokaci guda taji zuciyarta tayi wani irin bushewa, yayinda wani tunani yaɗarsu acikin ranta...
(Menene ra'ayinku akan auren ZIYADA da Tsoho Ɗan Dashe? Bazan cigaba ba harsai naga ruwan comment da vote ɗinku, dama nace yawan comment yawan typing.)
*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*CHAPTER 5*
Wanene SOORAJ?
Alhaji Mansur Mai Nasara shi ne yakasance uba ga SOORAJ, Alhaji Mansur Mai Nasara wani hamshaƙin mai arziki ne dake zaune acikin garin Kaduna, Alhaji Mansur tsohon commissioner'n Ilimi ne dake zaune a cikin garin Kaduna, cikakken ɗan boko ne shi, wanda yatara dukiya, sannan mutum ne dayake jure gwagwar mayar rayuwa, wannan yasa mutane suka masa laƙabi da suna MAI NASARA, saboda duk wani abu daya sanya agaba saiyayi nasara akai. Hajiya Sulaimiya itace matarsa kuma mahaifiya ga SOORAJ, Hajiya Sulaimiya dai irin wayayyun matan nan ne, don asalinta yar ƙasar Sudan
ce, tana da kyau sosai, tsananin kyawunta yana ɗaya daga cikin abun daya sanya Alhaji Mansur, narka maƙudan kuɗaɗe wajen ganin ya aurota, zama sukeyi cike da so da kuma ƙaunar juna, koda yaushe cikin farinciki suke, shekaransu uku da aure Allah ya azurtasu da samun ƙaruwan yaro namiji, tun daga randa aka haifi SOORAJ Alhaji Mansur yaƙara ganin buɗi acikin arzikinsa, soyayyar duniya suka ɗauka suka ɗaura ta akan yaron nasu, komai Na SOORAJ irin na Mahaifiyarsa ne domin kyawunta ya ɗauko. sosai SOORAJ ke zuba tashen kyau da burgewa tun yana ƙarami, saidai yataso da wani irin hali, miskiline na ƙarshe, sannan sam baida yawan magana, komai nasa atsare yakeyinsa, tun yanada shekara 12 mahaifinsa ya turasa England acan yayi gaba ɗaya karatunsa, tundaga kan secondary school har zuwa Masters ɗinsa, P.H.D ɗinsa ne kawai yayi aƙasar America. Sosai SOORAJ yake da ƙwazo akan dukkan komai, babu ruwansa da kowa, rayuwarsa kawai yake, bashida wani aboki aduniya sama da Mas'oud, sosai abotarsu tayi ƙarfi da Mas'oud, kasancewar sun fara abotanne tun suna ƙanana, gaba ɗaya sirrin Mas'oud SOORAJ yasani, haka shima Mas'oud ɗin yasan wasu sirrukan SOORAJ, saidai akwai wani sirri da SOORAJ ɗin yaɓoyewa kowa, shikaɗai yasan matsalarsa. Tun daga kan SOORAJ Alhaji Mansur baisake haihuwa ba, amma hakan baisa sun tashi hankalinsu ba, kasancewarsu wayayyun ƴan boko, dama ba wani son tara ƴaƴa suke ba, ayanzu dai SOORAJ yana da shekara 30 aduniya, cikekken matashine mai tsananin ji da kansa, rayuwarsa yakeyi maicike da burgewa baruwansa da kowa, abune mawuyaci kaga dariyansa, duk yanda Ƴan Mata keson samun daman kai kansu garesa, hakan baya yiwuwa, domin SOORAJ wani irin mutum ne, da akomai nasa baya sanya mata aciki, duk wata mu'amalarsa baya sanya mace aciki, mace duk kyau da haɗuwarta sam bata gabansa, batama burgesa, duk wani irin karairaya da mace mai lafiya zata zo tayi agabansa bazata taɓa burgesaba, duk tsananin kyawun mace, SOORAJ bata burgesa, shi yariga daya sanya aransa cewa mace bata cikin tsarinsa. Ayanzu yana akine a babban bankin Nigeria dake cikin garin Abuja wato Central Bank Of Nigeria (CBN) yanzuma hutu ya ɗauka shiyasa ya zo Kaduna wajen iyaye da danginsa. A rayuwarsa yana tsananin son iyayensa, sai gashi kuma daga zuwansa sun laƙaba masa auren dole. Wannan shine taƙaitaccen tarihin SOORAJ MAI NASARA.
Kamar koda yaushe idan yana acikin damuwa yakan fita yazaga gari, wani lokaci har ƙauyukan dake kusa dasu yake zuwa, sosai yakejin daɗi idan yaziyarci ƙauyuka musamman irin ƙauyukan da fulani ke rayuwa acikinsu, yauma hakance takasance dashi, hakanan yaji yanason fita daga cikin gari, bayaso yakoma Abuja baije yaɗan zaga gari ba...
Tsab yashirya kansa cikin long pencil jeans black colour,and Black t-shirt, agaban t-shirt ɗinnasa anrubuta ( THE MAN) da farin fenti. white denim jacket fara irinta maza yaɗaura akan rigar dake jikinsa, sosai kayan suka amshi jikinsa kasancewarsa mai farin fata, wasu fararen takalma combat wanda aƙalla kuɗinsu zasu haura sama da 30k yasanya aƙafarsa, hmmm SOORAJ yanason gayu sosai, hakan yasa koda yaushe cikin ɗaukar hankali yake. Da turarukansa masu tsada ya feshe jikinsa, take ko ina naɗakinnasa ya gauraye da ƙamshi. Wayoyinsa haɗe da key ɗin Range Rover ɗinsa ya ɗauka, kana yafice daga cikin ɗakin.
Yanashiga cikin motarsa ya kunnata, maigadi ne ya wangale masa gate, yana cilla motar tasa kan titi yasoma murza steering motar ahankali cike da salo..
*ZIYADA*
Gaba ɗaya ko ina acikin garin yaɗauki shiru, babu wani abu dake kai kawo, kowa yana gida akillace, adai dai irin wannan lokacin mafi yawancin mutane suna kwance ne aɗaki suna bacci, duhun dare ne sosai, babu wani abu dake motsi, sai ɗan abun da baza'a rasa ba, kamar yanda ko ina yaɗauki shiru haka gidannasu ma yake shiru, babu motsin kowa, gaba ɗaya jama'ar gidan suna bacci, amma banda ita, idanunta sun ƙeƙashe sun bushe, babu wani alamun bacci acikinsu, tun tana kuka da iyaka ƙarfinta, harta koma sauƙe ajiyar zuciya akai akai, babu wani abu dake ɗaga mata hankali, kamar idan tatuna cewa gobe za'a ɗaura mata aure da Tsoho Ɗan Dashe, tsohon dakowa yasan cewa ba mutumin kirki bane, shiru tayi tana mai sake nazartan abun da zuciyarta ke raya ma ta. Tabbas awani ɓangaren tunanin dake kwance cikin zuciyarta awajenta shine daidai, amma kuma tawani wajen tanaga kamar hakan ba daidai bane, duk duniya bata da kowa sai mahaifinta da kuma danginsa da suka ɗauki karan tsana suka ɗaura mata. Tana zaune awajen taji ansoma ƙiraye ƙirayen sallan asuba, jitayi gabanta ya tsananta bugawa, lokaci ɗaya taji zuciyarta na ingizata, ɗan dangwalin kayanta taɗauka, haɗe da yaye labulen ɗakinnata tasako kanta kaɗan tana leƙa tsakar gidannasu, ganin bakowa yasa tafito saɗaf saɗaf ta nufi hanyar fita daga gidan, saida takai bakin ƙofa kafun ta tsaya tare da juyowa tana mai kallon ƙofar ɗakin Babanta, wata irin karyewa zuciyarta tayi, take sai ga hawaye nasauƙa akan kumatunta, sosai takeson Babanta, tasan duk wani abu dayakeyi mata balaifinsa bane, amma bata da yanda zatayi, dole ko duniya ne ma tashiga, dole tanesanta kanta ga faɗawa halakar auren tsoho ɗan dashe. Juyawa tayi aɗari tabar cikin gidannasu, gudu takeyi sosai harta yi nisa da gidajen dake cikin ƙauyen tasoma shiga jejin dazai sadata da bakin hanya, komai tanayinshine acikin ƙarfin hali, amma har aƙasan zuciyarta tsorone shimfuɗe..
Bai kwana acikin garin Kaduna ba, kasancewar dare yayi masa, sam shi ba mutum bane mai son tafiyar dare, hakan yasa ya gangara gefen hanya, anan ya kwana cikin motarsa. Asuban fari yakamo hanyar dawowa cikin gari, saboda yau ɗin yakeso ya koma Abuja. Gudu sosai yaketa shararawa akan titi kasancewar babu wasu yalwan motoci dake tafiya akan titin.
Ba ƙaramin tafiya bane daga cikin ƙauyen nasu zuwa bakin titi saboda haka sosai tagalabaita, ganin takusa kawo bakin titi ne yasa ta rage sauri tasoma tafiya ahankali, dama ƙarfinta yasoma ƙarewa. Jitayi kamar anabin bayanta, da sauri tawaiwaya aikuwa wasu maza tagani su biyu abayanta, waro manya manyan idanunta tayi cike da tsoro tana kallonsu, dariya suka bushe dashi, ɗayanne ya sanya harshe yalashi laɓɓansa, cikin yanayi irin na ƴan iska yace. "Baaba yau fa munyi babban samuwa, ɗanyen kaya ce"
Dariya wanda aka ƙira da suna Baaba yayi, ya karkace tsayuwarsa tare da kai hanunsa kan belt ɗin wandonsa. "Ay gaye yau zamu more" yafaɗi haka yana me zare belt ɗin wandonsa.
Ganin haka yasa Ziyada shiga cikin wani irin matsanancin firgici, aruɗe tasoma ja baya, da ƙarfin gaske ɗayan ya fusgota, ihu tashiga