Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   37 / 48

108K to 111K   out of 142.5K words

lips ɗinta, yasanyata jin wani irin bacci na fusgarta,  ganin kamar tayi bacci yasanyashi soma ƙoƙarin zare bakinsa daga cikin nata, wani sabon kukan shagwaɓa ta saka masa, sam bayason kukanta hakan yasa yaƙara kamo harshenta yana sucking ahankali, lokaci k'ank'ani bacci ya ɗauketa,  hawayen da suka cika cikin idanunsa ne suka samu daman gangarowa, ahankali hawayennasa ke ɗiga bisa kan kyakkyawar fuskarta, sake hugging ɗinta yayi tight, wani irin tausayinta ne ke ɗawainiya da zuciyarsa,  bai taɓajin zafin ƙaddaransa sosai har haka ba, sai yanzu daya kasa bata abun da takeso daga gareshi, haƙiƙa baicancanci zama miji agareta ba, yana da rauni, wanda kuma raunin zai iya shafar rayuwarta, wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauƙe, daga gefe kuwa har yanzu jikinsa ɗauke yake da zazzafan zazzaɓi, yayinda yakejin wani irin abu ya riƙe masa waist ɗinsa, sosai yakejin azaba acikin jikinsa, saidai kuma duk da yanda yakejin wahala ajikinsa, baikai ya zuciyarsa dake barazanar tarwatsewa ba,  yanayin yanda numfashinta ke sauƙa akan wuyansa, shi ya sanyashi lumshe idanunsa, cikin wasu y'an mintuna ƙalilan bacci ya ɗaukesa, haka sukayi bacci lips ɗinsu haɗe dana juna,yayinda bugun zuciyarsu ke tafiya atare.

6:00 am.
Ahankali yaɗan ware idanunsa wanda suka ƙanƙance saboda bacci,   tarwal ya gama buɗe idanun nasa inda ya sauƙesu akan kyakkyawar fuskarta, sosai ya kura mata kyawawan idanunsa,  zara zaran eye lashes ɗinta wanda ke ɗauke da busassun hawaye ya kalla, kana yagangaro da kallonsa harzuwa kan ƴan ƙananan laɓɓanta, wanda cikin yanayi na bacci ta ɗan buɗesu batare da ta sani ba, hannunsa yakai kan kyakkyawar fuskarta inda ya haɗe mata laɓɓan nata waje guda, ahankali ya zare jikinsa daga cikin nata, ƙafafunsa ya zuro ƙasa kana ya miƙe tsaye daga kan gadon, kaitsaye bathroom ya wuce,  shower ya sakarwa kansa inda zuciyarsa ke cunkushe da tarin tunani kala kala,  aƙagauce yayi wanka tare da ɗauro alwala,  koda ya fito daga cikin toilet ɗin wata jallabia yasanya tare da shumfuɗa sallaya ya tada sallah,  koda ya idar da salla'n, sosai yayi addu'o'i kana yashafa, miƙewa yayi cikin nutsuwa ya ƙarasa gaban sif ɗin kayansa,   ɓangaren da suit's ɗinsa suke ya ɓuɗe, wata haɗaɗɗiyar black shinning suit ya ciro tare da wata white long sleeve, koda ya sanya kayan sosai sukayi masa kyau, yayinda suka fitar da cikakken kamanninsa na ma'aikacin  banki, sosai yayi kyau, inda yasanya wasu tsadaddun takalma toms aƙafafunsa,  cumb ya ɗauka inda yashiga gyara kyakkyawan sajen dake ƙarawa farar fatarsa kyau,   turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa, take ƙamshin nasa ya cika gaba ɗaya ɗakin,     wata ƴar madaidaiciyar briefcase ya riƙe ahannunsa, cikin takunsa mai ɗauke da nutsuwa, ya ƙarasa jikin ƙofar fita daga cikin ɗakin, har yakai hannunnsa kan handle ɗin ƙofar saikuma yaɗan tsaya, idan da ason zuciyarsa ne shine juyawa ya kalleta, saidai kuma yanajiyewa kansa abun dazai faru dashi nan gaba, bahaka yake ba sam, bakuma yaso ya zama haka, saboda ita arayuwarsa karo na farko daya zubda hawayensa, saboda ita kaɗai yafarajin tsanan kansa da rayuwa, saboda ita kaɗai ya bari akaron farko rauninsa ya bayyana, inda ya zubar da ƙwalla sanadin lalurarsa, sam bayason sakeyin wannan ganganci. Murɗa handle ɗin ƙofar yayi yafice,  cikin isa yake takunsa har ya kawo compound ɗin gidan, motarsa ƙiran range rover black colour ya shiga, maigadi ne ya wangale masa gate ɗin gidan, shi kuma ya tura hancin motartasa waje.

7:00 am.
Daidai alarm ɗin dake gefen gadon wanda batasan waya saitashi ba yasoma ƙara kamar zaicire kunnen mai sauraro, wannan ƙaran alarm ɗinne yasanyata buɗe idanunta,  ahankali taɗan buɗe idanun nata tare da yunƙurawa ta tashi zaune, kallonta takai ga window'n ɗakin, nan taga gari gaba ɗaya yayi haske, bayanta ta jingina da saman gadon, cikin gajiyawa da jin ƙaran alarm ɗin tasanya hannunta ta kashe,  dogon gashinta da yake a hautsine ta haɗa waje ɗaya, lumshe idanunta tayi, yayinda take shaƙan daddad'an ƙamshin da ɗakin ke fitarwa, lokaci guda moment ɗinsu na daren jiya yashiga dawowa cikin ƙwaƙwalwarta, wani irin mimmiƙewa tsikokin jikinta sukayi, yayinda takejin wani irin yaaarrr acikin jikinta,  kamar yanda bazata taɓa iya mantawa da kanta ba, haka tayi imani bazata taɓa iya mantawa da moment ɗinsu na daren jiya ba, sake lumshe idanunta tayi musamman tuno yanda yake tsotsan harshenta slowly da tayi,  wani irin ɗanɗano na musamman yawun bakinsa ke ɗauke dashi, laɓɓanta taɗan ciza ahankali don kuwa haryanzu tanajin marar nata nayi mata ciwo kaɗan kaɗan, cikin rashin kuzari ta sauƙo daga kan gadon, kayan jikinta ta cire,  inda ta ɗaura wani sky blue towel aƙirjinta, wanda ya tsaya zuwa kan santala santalan cinyoyinta farare ƙal ƙal, wanda ɗigon tabo ɗaya babu akan shinning skin ɗin nata mai tsananin taushin gaske.  Ruwa me ɗan ɗumi ta haɗawa kanta, inda dashi tayi wanka, bayan tayi wankanne ta ɗauro alwala, sam bataji daɗin makaran da tayi ba,  wata simple women gown ta zura ajikinta inda ta sanya hijab,  sallah tayi, tana idarwa taɗanyi azkar kana ta mik'e.
Wani irin fitinannen yunwa takeji na ƙwaƙulan cikinta, kasancewar rabonta da abinci tun jiya da yamma,  ɗaure dogon gashin kanta tayi batare da ta sanya ɗan kwaliba ta fita zuwa falo, ko ina ta kutsa kanta saitaji wannan fitinannen ƙamshin nasa na neman ruguza mata zuciya, ita tarasa wannan wani irin turarene wanda ajikinsa kawai takejin irin ƙamshin.
Kaitsaye kitchine ɗin dake cikin falon ta nufa,  duk da kasancewar tanajin yunwa, amma batajin cewa wani abu na abinci zaisamu mazauni acikin cikinta, tea ta haɗa kana ta dawo falo ta zauna, tanƙwashe ƙafafunta tayi yayinda ahankali take sipping tea ɗin, wayarta wanda tunjiya take aje kan table ɗin dake tsakiyar falon ne, takawo haske, lokaci guda kuma sassanyar muryan mawaƙinnan  Atif Aslam tasoma tashi acikin wayar alaman shigowar k'ira, ɗan yunƙurawa tayi ta ɗauki wayar.
"Shukra" Shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, cikin hanzari ta ɗaga ƙiran tare da karawa akan kunnenta,  kafun tace wani abu Shukra tayi saurin cewa.
"Amarya bakya laifi koda kuwa ace kin ciji ango!."

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba cikin yanayinta me ɗauke da sanyi tace.
"Bakida wani abun da zakicemin ae Shukra, yanzu ƙin zuwa da kukayi keda Nasmah kun kyauta kenan?."
Dariya Shukra tayi, cikin yanayi na tsokana tace.
"Rufa mana asiri mu mutu agida maza sukaimu ba mata ba, mu ƴan gidan zuwa, me zamuzo muyi miki keda kike ƙarɓan special lecture awajen Mr.Handsome ɗinki, mukan ae dai kuma saita waya!."

Tsuka Zieyaderh tayi cikin ƙosawa da tsokanan da Shukran keyi mata tace.
"Nifa banason iskanci Shukra, ƴar iska kawai."

Dariya sosai Shukra da Nasmah wacce kejin duk maganganun Zieyaderh'n suka sanya,  jin dariyar Nasmah yasanya Zieyaderh sake ɓata fuska, ahasale tace.

"Kun maidani mahaukaciya ko?."

Ɗan gumtse dariyannasu sukayi, cikin salon tsokana Nasmah tace.

"Sorry ƙawata, ya tsamin jiki,  nasan fushi kikeyi damu, am so sorry idan muka haɗe a school zamu taushi zuciyarki."
Shukra ne ta caɓe da cewa.
"Inafatan dai kina gwada masa irin wannan salon shagwaɓan naki, dannasan idan kina gwada masa ko aiki bazaina fita ba." 
Gyara zamanta tayi cikin zaƙuwa tace.
"Dan Allah ƙawata faɗamin aure da daɗi ko? hmmm nima Inatsananin son aure, gaskiya bazan iya jurewa ace harsai na ƙare secondary school ba, seriously na ƙosa nima nazama cikakkiyar mace."
Shukra tafaɗi maganan dayake har cikin zuciyarta hakane,  duk da kasancewar basu da wani shekaru masu yawa, amma tagamsu da cewa yin aure tun mace nada yarintarta yafi komai daɗi, sannan kuma maza da yawa sunfi sha'awar ƙananan yara kamarsu, badon komai ba saidan suna da daɗin zama, ita yarinya aduk yanda ka koyar da ita haka zaku tafi, bata da wani buri kaman ganinta tare da mijinta tana zuba masa shagwaɓa da sakalci, yayinda shikuma zaizama tamkar soko akanta, sam ita bazatayi wannan dogon karatun awaje kamar yanda wasu keyi batare da tayi aure ba, saboda yawanci hakan najawo matsala sosai ga rayuwar ƴa mace,  saboda awannan lokacin da kayi zurfi cikin karatu bakowane zaiji sha'awar aurenka ba, sannan kuma ba lallaine kasamu irin mijin da kake muradi ba.

Hararan wayan Zieyaderh tayi tamkar suna ganinta, cikin gajiya da tsokanar tasu tace.
"Allah yashiryaki Shukra,nikam yanzu kinfi ƙarfina."

Fari da ido Shukra tayi tare da cewa.
"Naƙirane dama na tuna miki cewa next week zamu koma school, so sauran bayanin sai mun haɗu a school, nasan zuwa yanzu kin ƙara fresh, hope baki manta islamic lecture'n da akayi ranan a school ba?."

Kunyane ya rufe Zieyaderh, cikin ƙosawa tace.
"Allah yashiryaki Shukra, bazaki taɓa sanjawa ba."

Dariya suka saka atare, inda sukayi sallama akan cewa sai sun haɗu a school din.

Awannan rana haka Zieyaderh taƙare zamanta agidan ita kaɗai.

Dare nayi tana idar da sallan isha kuwa bacci ya ɗauketa anan falo kan kujera,  yauma baidawo gidanba sai ƙarfe 9, ganinta kwance afalo yasanyashi wucewa ɗaki kai tsaye, wanka yayi inda yashirya kansa cikin ƙananun kaya marassa nauyi,  kwanciya yayi akan gado tare da jawo blanket ya rufe jikinsa,  da tunani kala kala acikin ransa, haka bacci ya ɗaukesa. 

Yauma kamar jiya tun 6:00 am yafice daga cikin gidan,   haka ya wuceta kwance afalo tanata sharar bacci, koda ta tashi taganta kwance afalon baƙaramin mamaki tayi ba, nan tatuna da cewa baccine ya ɗauketa jiyan batare data shiryawa hakan ba,  kaitsaye bedroom ta nufa, sannu ahankali take ƙarewa cikin ɗakin kallo, komai dake ciki nead, da dukkan alama dai babu wani wanda ya kwana acikinsa, cikin zuciyarta tace.
"Kenan baidawo ba? ko yayi tafiya ne?."
Sanin bata dame amsa mata tambayoyin nata, yasanya ta wuce toilet, wanka tayi, yauma dai ta makara hakan yasa ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallah.
****
Wasa wasa yau kwananta 6 bata sashi acikin idanunta ba,   kullum batajin motsinsa, batasanin fitansa ba kuma tasanin dawowarsa,   daga gefe guda kuwa wani irin masifaffen kewarsa ne ke ɗawainiya da zuciyarta, sosai takejin wani abu na daban akansa, sannan kuma aduk sanda ta tuna da moment ɗinsu na ranan, saitaji wani irin feeling ya taso mata, sosai take buƙatan hakan daga garesa, sau ɗaya tak yashayar da ita yawun bakinsa, amma gaba ɗaya hakan ya zautar da ita.

Zaune take jigum akan gado, wata sleeping gown ne ajikinta me kalan light pink, sosai rigan tayi mata ɗas ajiki, wani ɗan madaidaicin hijab ta ɗaura akan rigan,  baccine cike a idanunta, amma haka take ƙoƙarin shanyewa, kasancewar gobe ne zasu koma school hakan yasa tun da yamma tagama kimtsa duk wani abu da zata buƙata, tuni har gugan uniform ɗinta tayi, kasancewar tagaji da zaman gidan, yasanya har Allah Allah take gobe tayi.
Yau ta ƙuɗurta aranta cewa bazata taɓa yin bacci ba harsai ta ganshi, takuma sanardashi maganan komawarsu makaranta gobe,don sunyi waya da Oummu, inda Oummu dakanta tace tasanar da shiɗin cewa gobene komawarsu school, saboda yanzu dole saida izininsa za take zuwa school ɗin.

Sama da mintuna talatin taɗauka zaune akan gadon har bacci yaɗan ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.
10 pm daidai ya shigo cikin gidan,  yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa batare daya kula inda take ba,  towel ya ɗaura akan waist ɗinshi inda ya nufi bathroom, kwana biyunnan baƙaramin azabtuwa yakeyi ba, sosai yakejin zafi azuciyarsa, shikansa yanajin kamar yana hora zuciyarsa da horo mafi girma, baisan meyasa abun dayakeji ajikinsa ke ƙara yawaita kullum ba,  ƙaran ruwan dake tashi daga cikin toilet ɗinne yayi sanadiar buɗe idanunta,  Ajiyar zucia ta sauƙe, tare da ɗan langwaɓar da kanta gefe, fargaba ne aranta don batasan daya zata fuskancesa da maganan ba.

Baiwani jima cikin toilet ɗin ba, yafito, farar bathrube ne ajikinsa, gaba ɗaya kansa jiƙe yake da ruwa, kaitsaye gaban mirror yanufa, da wani ɗan ƙaramin towel ya goge jikakkiyar sumar kansa. yana gama tsane ruwan ya tako ahankali ya zauna abakin gadon, wani ɗan madaidaicin table yajawo gabansa, inda ya ɗaura laptop ɗinsa akai, cikin nutsuwa yashiga ajiye wasu bayanai cikin Email ɗinsa.

Ahankali taɗan sauƙo daga kan gadon, kanta aƙasa ta tako har zuwa inda yake, samun kanta tayi da durƙusawa agabansa tare dayin ƙasa da kanta, cikin rashin sanin madafa tasoma murza ƴan yatsun hannunta, bugun zuciyarsa data tsananta ne yasanyashi gane cewa tana kusa dashi, lumshe idanunsa yayi batare daya buɗe ba yace. "Menene?."
Kaman dama shitake jira, gyara zamanta tayi cikin nutsuwa haɗi da yarintar dake ɗawainiya da ita tace...
"Dama...umm dama gobe hutun mu na school zai ƙare, shine Oummu tace na gaya maka."

Shiru yayi tare da ɗan juyowa ya sauƙe shanyayyun idanunsa akanta, jin yayi shiru ne yasanyata ɗan cije laɓɓanta, ahankali ta ɗago fararen idanunta aniyarta shine taɗan saci kallonsa, karab idanun ta suka sauƙa cikin nasa idanun, ganin yanda idanunsu suka sarƙe cikin najuna ne, yasanyata ɗan lumshe idanunta, kana takuma buɗesu alokaci guda, cikin wani irin yanayin da ƙwayan idanunnasa suka shigar da ita taɗan kwaɓe fuska kamar wacce ke sonyin kuka, ahankali take motsa bakinta kamar wacce takeson faɗan wani abu, karo na farko kenan arayuwarsa dayaji don kansa yana sha'awan yin kissing ɗin bakinta, sannu ahankali yakejin gargasan jikinsa na buɗewa, lumshe idanunsa yayi don bazai iya jurewa abun dayakeji ba, can ƙasan maƙoshi yace.
"Naji kije ki kwanta."
Jin maganarsa yasanya taji zuciyarta tayi mata sanyi, ahankali tatashi ta koma kan gadon, nannaɗewa tayi acikin lallausan blanket ɗin dake ta tashin ƙamshinsa, cikin wani irin shauƙi ta cusa kanta acikin pillow, ahankali take sauƙe ajiyar zuciya akai akai, ta rantse aduniya itakam bataga wani kyakkyawa mai kyawawan idanu tamkarshi ba, shi komai nasa na musammanne, magana ma yanayinta ne kawai alokacin dayaga dama, zuciyarta cunkushe da tunaninsa haka tayi bacci.

Shikuwa SOORAJ duk yanda yaso cigaba da aikin nasa kasawa yayi, don wani irin baƙon al'amarine ke ziyartar gaba ɗaya gangar jikinsa, akasalance ya rufe laptop ɗin tare da miƙewa tsaye, ahankali ya karasa gaban sif d'in kayansa, wani 3 guater jeans ya sanya, yayinda Kai tsaye ya nufi kan doguwar kujeran dake cikin dakin, kwanciya yayi tare da lumshe idanunsa, kasancewar adan gajiye yake yasanya baiwani jimaba bacci b'arawo ya d'aukesa.

Duk sammakon tashi da ta buga, Saida ta samu yarigayeta tashi, don ko da ta tashi daga baccin tsaraban k'amshinsa kawai ya barmata, cikin tsanaki tayi wanka, tana idar da sallah ta dauki sassanyan body lotion dinta Mai dadin kamshi tashiga shafawa ajikinta, sama sama ta shafa powder, wani dan pink lipstick ta goga akan labbanta, kamar yanda take ko yaushe bata cika kwalliya ba, hakama yanzun batayi wani kwalliya ba, dogon sket high waist, and long sleeve ta sanya, Wanda sune suke mazaunin kayan uniform dinta, tubke dogon gashin kanta tayi inda ta zura Dan madaidaicin hijab din makarantar tata, Wanda tsayinsa ya kawo harkan cikinta, katuwar school bag dinta ta rataya bisa kafadanta, agurguje haka tafita daga cikin dakin don kuwa lokacin har bakwai da rabi tayi, kamar da can baya yau dinma Kamalu driver ne ya kaita makarantar, sosai sukayi murnan ganin juna ita dasu Shukra, ba ita tasamu daman karyawa ba, Saida suka fita break, sosai yau din taji dadin makarantar saboda koba komai ya kore mata kadaici.

5 daidai aka tashesu atare suka jero tare da su Shukra, tafe suke suna hira harsuka iso babban compound din makarantar, tuni driver'n Nasmah yazo daukarta saboda haka tayi musu sallama tatafi, tana tafiya kuwa saiga driver'n gidan su Shukra shima yazo daukarta, haka suka watse sukabar Zieyaderh ita kadai, agogon dake daure atsintsiyar hannunta takalla 5:16 pm, fuska tadan kwabe tana me sake ware idanunta wai ko zata hango Kamalu, sannu ahankali hadaddiyar motar da takawo Kai cikin makarantar ta karaso gareta, agefe da ita kad'an motar wacce tasha tintect ta faka, bude murfin motar yayi tare da zuro da k'afafunsa k'asa, sannu ahankali ya fito gaba dayansa daga cikin motar, Sanye yake da k'ananan Kaya, yayinda ya manna sun glass akan idanunsa, Sam Bata kalli gefen da yake ba, cigaba tayi da duddubawa ko zata hango Kamalu driver, amma abun mamaki ko irin motarsu Bata hango ba.

Wani irin bak'on k'amshin da yaziyarci hancinta shiya Sanya tadan waiga bayanta, donjin daga Ina k'amshin ke fitowa, sauke idanunsa akanta yayi daidai da bugawar zuciyarta, lokaci guda kirjinta yayi wani irin tsalle kamar zai fad'o, cikin tsananin mamakin ganinsa tadan zaro idanunta waje,
wani irin kawataccen murmushi yayi mata, cikin takunsa ya karaso gab da ita, tsakanin su bai wuce saura taku daya ba ya tsaya tare da lumshe munafukan idanunsa, sun glass din ya zare daga kan idanunsa, inda ya waresu tas akanta, wani irin kallo, Mai dauke da tsananin shauki ya bita dashi, cikin kwantar da murya yace.

"I missed you so much babe, ganinki ya fiye min komai ayanzu, I Love you so so much!" Pharouk Yakare maganan Yana me byyana zallan shaukin dake ransa afili, kanta ta sunkuyar kasa, samun kanta tayi da kasa ce masa komai, batare da zato ko tsammani ba taji ya kamo hannuwanta, arazane ta d'ago kanta ta dubeshi, kansa ya langwabar gefe cikin salo irin nasa yace.
"Bazan iya jure rashinki ba, duk da nasan cewa anyi Miki Dole wajen aura masa ke, Inasonki Zieyaderh, burina shine kasancewa dake, please Kar kice Zaki rabu Dani, karkice zaki k'i aminta Dani, Inasonki!."
yakare maganar Yana me kokarin murza Yan yatsun hannunta, gaba daya ta rude tana kokarin zare hannunta, Amma rikon da yayi mata bana wasa bane.
Daidai lokacin wata hadaddiyar mota Kiran 4matic takawo Kai cikin makarantar, gaba daya fiye da Rabin daliban makarantar kowa ya kama gabansa, Yan tsirarune kawai suka rage, irinsu Zieyaderh da ba'azo daukarsu da wurine ba.
Ahankali yayi parking motar inda dagowan da zaiyi idanunsa suka Masa mummunan gani, ganin daya sanya kirjinsa wani irin dokawa, ganin daya sanyashi Jin wani irin d'aci amak'oshinsa, ganin daya sanyashi jin wani irin jiri yayinda wani irin tari ya taso masa, har takai numfashinsa na kokarin carkewa.


(Bani da bakin da zan baku hakuri bisa jinkirin yi muku update dana samu, wallahi wani babban uzurine ya rikeni, ina fatan zakumin uzuri, insha Allah

37 / 48