Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   28 / 48

81K to 84K   out of 142.5K words

doya ne da egg sauce  agefe,  plate na biyu kuwa pepper soup ne na kayan ciki, ɗayan plate ɗin kuwa shawarma ne me zafi har turiri take,  duk acikin abu ukun babu cimarta, hakan yasa da ƙyar ma ta iya cin doyan, sannan ta haɗa da tea, kaɗan taci abincin ta ture gefe, bathroom tashiga ta wanke hannunta, tray ɗin ta ɗauka da niyan sauƙa ƙasa, aikuwa  3 steps kawai ta kawo sukayi kiciɓus da Oummu tare da wata ƴar budurwa dake bayanta, wacce aƙalla bazata haura 27 years ba,   murmushi Oummu tayi tare da duban budurwar  cikin sakin fuska tace
"To Bilkh gama ƴar tawa please kiyi mata irin wanda kika jima bakiyi ba!"
Murmushi wacce aka ƙira da sunan Bilkh tayi cikin hausarta me bada wani irin sauti tace "Bakomai Hajiya Insha Allah zaki yaba da wannan aikin sosai!"

Murmushi Oummu takumayi tare da ƙwaɗawa  Nabila ƙira, dama dayake tana kusa hakan yasa tataho da sauri, tray ɗin dake hannun Zieyaderh Oummu ta amsa tare da miƙawa Nabila tace takai kitchine, duban Zieyaderh tayi cike da kulawa tace "Zieyaderh wannan itace Bilkh shahararriyar me kwalliya ce,  please ki bata haɗin kai, maza ki mata jagora zuwa ɗakin ki"

Murmushi Zieyaderh tayi tare da cewa "To" itadai har yanzu kanta akulle yake don batasan menene za a mata ba.   Suna shiga cikin ɗakin Bilkh ta baje ƙaton ƙaton akwatin meckup ɗinta wanda tazo da shi.  Kallon Zieyaderh tayi tare da ce mata taje tayi wanka, musu banata bane hakan yasa ta wuce toilet, wanka tasakeyi kana ta ɗauro babban towel ajikinta wanda bazai bayyana tsiraicinta ba, tana fitowa Bilkh ta zaunar da ita tare da fiddo da wani tsadadden mai daga cikin akwatin meckup ɗinta ta shiga shafa mata, ita Zieyaderh abunma mamaki ya bata don bataga amfanin shafa mata mai ba bayan itama tanada nata hannun, tana kammala shafa mata mai ɗinne ta zaro wata galleliyar atamfa wacce taji ɗinkin fitted gown me kyau, wanda yana daga cikin kayan da Oummu ta miƙo mata lokacin da Zieyaderh ke wanka,  miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa tasanya,  amsa tayi tare da komawa bayan drawer ta laɓe anan tasanya rigan gudun kada Bilkh taga tsiraicinta, ita kuwa Bilkh abubuwan da zata buƙata taketa haɗawa,  sosai rigan ya zauna ɗas ajikin Zieyaderh baƙaramin kyau kuwa tayi ba, akan wata kujera Bilkh ta zaunar da ita, saida tayi mata duk wani abu daya kamata kafun cikin nutsuwa ta shiga tsantsarawa Zieyaderh meckup akan beauty and innocent face ɗinta.    Bawani lokaci sosai suka ɓata ba kasancewar ba wani meckup aka mata akan fuskar nata sosai ba, simple ne amma yayi kyau sosoi,  take tsananin kyawun Zieyaderh ya sake bayyana,  tsantsara mata ɗaurin ɗankwali Bilkh tayi bayan ta nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyan kanta,  wani haɗaɗɗen sari me kyau da tsada kalan ja Bilkh ta ɗauka,  miƙar da Zieyaderh tsaye tayi tare da soma nannaɗa mata sarin ajikinta, kasancewar atamfar dake jikinta baƙine me ratsin ja, hakan yasa baƙaramin matching yayi da material sarri ɗin ba.
"Wow!" Bilkh ta faɗa bayan ta gama nannaɗawa Zieyaderh sarri ɗin, ita kanta sosai kyawun Zieyaderh ya ɗauki hankalinta, haƙiƙa ita kanta tasan ta iya kwalliya wanda zai gyara mace ya me da mummuna kyakkyawa, amma awannan karon tana da tabbacin cewa ba kwalliyarce tayiwa Zieyaderh  kyau ba, ita Zieyaderh'n ce tayiwa kwalliyan kyau. Turaruka masu ƙamshi da tsada ta fesawa Zieyaderh wacce tazama so silent.  Shigowar Oummu cikin ɗakinne yasa duk suka kalleta. Fuska faɗaɗe da murmushi tace  "Masha Allah, lallai Bilkh aikinki yayi kyau!"

Murmushi Bilkh tayi tare da cewa
"Hajiya ita yarinyar takice me kyau!"
Murmushi me sauti Oummu tayi sannan taja hannun Zieyaderh suka fice daga cikin ɗakin, yayinda Bilkh kuma ta ɗauki wayarta ta soma latsawa.  Tun shigowansu cikin katafaren falon Oummun dayake na musamman gaba ɗaya waƴanda suke cikin falon suka maida kallonsu gareta, matane su Uku zaune acikin falon kowacce idan ka ganta kamar ka latsa jini yafito tsabar fari da jin daɗi, kallo ɗaya zaka musu kafuskanci cewa manyan masu akwai ne.  Cike da fari'a ɗaya daga cikin matan wanda itace bata da yawan shekaru kamar na su Oummu ta tarbo su, hannun Zieyaderh wacce kanta ke ƙasa ta riƙe tana me cewa  "Masha Allah!" agaban sauran matan ta zaunar da Zieyaderh kan wani lallausan carpet. 

Atare duka matan suka haɗa baki wajen cewa "Masha Allah!" don kowaccensu ta yaba da kyau da kuma ƙuruciyar Zieyaderh,  duk da bata ɗago kanta sun kalleta da kyau ba amma kunyanta kaɗai ya isa gamsar dasu. Cike da ladabi Zieyaderh ta gaidasu, dukansu suka amsa fuska asake cike dajin daɗi.  Oummu ce tace taje ta kawo musu drinks da kayan fruits, aikuwa babu musu Zieyaderh ta miƙe, cikin mintuna kaɗan ta cika musu gaba da kayan fruits da drinks wanda duk tanayin aikinne cikin nutsuwarta, ba laifi sukam sun gamsu da yanayin tarbiyan yarinyar sosai, fatansu ɗaya shine Allah yasa tazamo itace matar zama agareshi.  Koda ta kammala gabatar musu da komai ɗakinta ta koma tare da ƙarasawa gaban madubin ɗakin ta shiga duba irin kyawun da tayi, don zuwa lokacin Bilkh tama jima da tafiya. Wani irin murmushi me sanyi tayi tare da sanya hannu ta shafi fuskarta daketa fidda ƙyallin kyau hancinta kuwa sai shinning yake. 

Gyara zama Hajiya Sauba tayi tare da duban ƴar uwarta cike da jin daɗi tace "Gaskiya Sulaimiyya na yaba da hankalin wannan yarinyar sosai Allah yabasu zaman lafiya!"

Da Ameen Oummu ta amsa tana murmushi.

"Nima kuwa na yaba ƙwarai Allah yasanya alkhairi, amma fa wani hanzari ba gudu ba Sulaimiyya  yakamata ace anyi bikinnan acikin watannan, saboda banga amfanin jinkirtawa ba" Cewar Aunty Laylerh.

"Wannan tunanin shine araina Aunty Laylerh, kuma Insha Allah zamusa auren nan bada jimawa ba, domin kuwa daren jiya maganan auren mukayi da Abbansa yakuma ce zasuje shida abokinsa har can garin su yarinyar!"

Murmushin jin daɗi su duka sukayi tare dayin addu'an Allah yatabbatar da alkhairi acikin auren.

(Chaiii wani gurmin sai  ranan da RAJ ɗinku yayi aure zai angwance😝  am so sorry jia banyi update ba naɗan shiga busy ne🙏🏻)

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                *WATTPAD*
         @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 40*

Hira Oummu da ƴan uwanta sukayi sosai inda suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance.  Aunty Muhibbat wanda takasance itace ƙaramar cikinsu ta kalli Oummu tare da cewa "Ni aganina idan babu damuwa, zamanta ya dawo wajena saboda kinga ina tare da shuwa arab saboda haka ba ƙaramin gyara zata samu ba"   murmushi Oummu tayi tare da cewa "Hakane amma aikinsan tana zuwa makaranta, duk da ma dai muntsara kan cewar awannan year din zata zana waec nd neco ɗinta" 

Cike da jin daɗi Aunty Muhibbat tace "To Allah yasa ayi komai dai a sa'a" da "Ameen" suka amsa su dukansu, basu wani jima sosai ba suka kama hanyar tafiya bayan sun jibgewa Oummu tsarabobi masu yawa da suka kawowa surukarsu Zieyaderh.

Ɓangaren Zieyaderh kuwa jin kamar ta takura yasanya cikin nutsuwa ta shiga warware sari ɗin dake jikinta tare da aje sa gefe.  Ajiyar zuciya ta sauƙe akaro na barkatai, tare da ɗan jingina kanta da saman gadon da take zaune akai, tunanine cike fal  azuciyarta, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasanyata ɗago kanta ta kalli bakin ƙofan, Nabila ce tashigo cikin ɗakin cikin ɗan rusunawa tace "Hajiya tace ayi mata ƙiranki"
Murmushi Zieyaderh ta ɗanyi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye "Ganinan zuwa" tafaɗa tana me zura bedroom slippers aƙafanta.  Kai tsaye ɗakin Oummu'n ta nufa, ɗan tsayawa tayi ajikin ƙofan tare dayin knocking.  Sanin cewa itace yasa Oummu dake zaune akan gado ta bada izinin shigowa, da sallama ɗauke abakinta ta shigo tare da neman waje taɗan rusuna daga gefe.

Oummu da yawancin lokuta fuskarta baya rabo da murmushi yanzun ma murmushine ɗauke akan fuskarta, miƙowa Zieyaderh wata haɗaɗɗiyar ƴar jaka me kyau tayi,  amsan jakan Zieyaderh tayi tana me kallon Oummu cike dason ƙarin bayani, "Kyautane daga surakanki, inafata zakiyi murna zakuma ki yaba da kyautar!" Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin manna farin glass akan idanunta.

Jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi sunkuyar dakanta ƙasa tayi asanyaye tace "Nagode sosai Oummu amma sai nake ga kamar kyautan sunyi yawa, duk dama banga menene aciki ba!"

Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Bana tunanin kyautar tayi yawa kedai ki amsa kawai, gaba kuma idan kunsake haɗuwa sai ki musu godiya"

Cike da jin nauyin Oummu'n tasake yi mata godiya sannan tatashi ta wuce ɗakinta. Koda taje zama tayi akan gado tare da buɗe jakar, wani ɗan box me kyau da burgewa taciro daga cikin jakan, tare da buɗewa, wani danƙareren agogon hannu na gwal ne ya bayyana acikin kyakkyawan box ɗin. agogone na mata me matuƙar ɗaukar hankali, kyawawan duwatsunsa sai ɗauke ido suke, sake fito da wani box ɗin tayi wanda har yamafi wancan ɗin girma,  shi kuwa wani irin danƙareren sarƙa da ɗankunnen gwal ne acikinsa  me kyaun gaske, sosai design ɗin sarƙan ya mata kyau,   har batasan sanda ta saki lallausan murmushi akan fuskarta ba, ganin kyaututtukan nada yawane yasanyata zazzage jakan gaba ɗaya akan gado,  nan tayi arba da wasu arebian gown masu kyaun gaske, tare da wasu kwalaben humra masu ƙamshi irin masu kama jiki ɗinnan, cike da jin daɗi ta tattara kayan ta maida cikin jaka, sosai kayan suka mata kyau saidai kuma tasan matsayinta baikai nanba, bai kamata ace amatsayinta na ƴar wanda ba kowa ba ayi mata irin wannan hidiman,   shigowar Nabila cikin ɗakinne yasanya ta tsaida duk wani abu da take tana kallonta.

"Hajiya tace ashaida miki kina da baƙo awaje"

Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi yayinda taji gabanta ya ɗan faɗi cikin yanayi naɗan mamaki tace "Baƙo?"
Kai kawai Nabila ta iya kaɗa mata alamar "Eh"  kasa cewa komae tayi har Nabila ta juya ta fice daga cikin ɗakin,  Vail ɗinta me kyau da walwali ta sanya tarufe jikinta,  cikin fargaban sanin ko waye haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita, bata samu kowa afalon ba hakan yasa kaitsaye tanufi ƙofar da zai sadata da compound ɗin gidan.

Tsaye yake ajikin motarsa ƙirar jeep yasha kyau cikin shigarsa ta half jumper White and blue colour, yayinda ya kafa hular Zanna bukar mai adon blue akansa, haɗaɗɗen sajen dake kwance akan fuskarsa ne ya kwanta luf akan ƙuncinsa, yana ganinta yasaki murmushinsa mai kyau wanda har saida gefe da gefen kumatunsa suka loɓa, ganinsa baƙaramin faɗar mata da gaba yayi ba,take mood ɗinta ya sauya daga ƙwarin guiwa zuwa raunin zuciya, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kasa ƙarasowa inda yake, murmushi yayi ganin ta tsaya batare da ta ƙaraso garesa ba, ahankali yashiga takawa har zuwa inda take, daddaɗan ƙamshin turarensa ne yasanar mata da zuwansa, ahankali ta ɗan lumshe idanunta tare da buɗesu, kanta taɗan ɗago ta kallesa, idanunsune suka sarƙe acikin na juna kasancewar shiɗinma kallonta yake,  kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saima wani irin marairaicewa da idanun nata suka yi, shiɗinma kallonta yakeyi da sexy eyes ɗinsa wanda suke wani irin lumshewa kaɗan kaɗan,   cikin wata irin murya me sanyi yace "Anan zaki barni bazaki bani wajen zama ba?"

Kanta ta sunkuwar ƙasa tare da ɗanyin murmushi,  kallonta tamayar ga wajen ɗan shaƙatawan dake cikin gidan wanda aka ƙawatashi da wasu kujeru guda huɗu masu kyau gaba ɗaya flowers sun zagaye wajen yayinda sukayiwa rumfar dake wajen ƙawanya, kallonsa tayi sannan tanufi wajen shima ya rufa mata baya. Akan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna yayinda shima ya zauna akan kujeran dake facing nata. Ƙasa tayi da kanta tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta murya asanyaye tace. "Ina wuni!"  murmushin daya bayyana dimples dinsa yayi batare daya amsa taba sai idanu daya zuba mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, don kokaɗan meckup ɗin dake kan beauty face ɗinta bai goge ba,   jin shiru bai amsata bane yasanyata turo bakinta gaba aɗan shagwaɓe tace "To ba gaisheka nake ba kuma kaƙi amsawa!"  Murmushi yayi harsai da haƙwaransa suka bayyana. "To ae banji bane, please kiɗan ƙara ɗaya sainaji!" Yafaɗa cikin salon kwaikwayon maganarta.     Idanunta ta ɗago kana taɗan watsa masa hararan wasa tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta dayasha baby pink colour lipstick, lumshe idanunsa yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran, wani irin shauƙi ne ke shigansa, sosai yanda tayi da bakinta yayi masa kyau,  cikin wani irin yanayi yace. "Kullum ƙara kyau kike, idan kina fushi kyau kike ƙarawa, idan kina murmushi kyau kike ƙarawa, haka ma idan kina gabana kyau kike ƙarawa,  inajin kamar sonki acikin jinina yake Zieyaderh, ko sau ɗaya ne please ki amsa min cewa kina sona!" yaƙare maganar yana me kafeta da mayun idanunsa wanda suka ɗan sauya kala,  gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da ɗan ciza laɓɓanta, ƙirjinta ne yake bugu da sauri, maganan aurenta da Almustapha ne yazo yayi tsaye aranta, tabbas tanajin wani abu na daban dangane da Pharouk, to amma bata da tabbacin cewa wannan abun soyayyace, koda ma acd sonsa take mecece amfanin soyayyar? yanzu burinta shine ta koyawa zuciyarta soyayyar Almustspha, dan sai da soyayya ne kaɗai zata iya kyautata masa azaman aurensu.  Ɗago idanunta da sukayi raurau da hawaye tayi daniyar yiwa Pharouk magana, saidai tuni maganan nata ta maƙale sakamakon Ido biyu da sukayi da Almustapha dake tunkaro inda suke,  ganin ta tsaida idanunta abayansa yasanyashi ɗan waigawa don ganin abunda take kallo, idanunsa ne suka sauƙa akan kyakkyawan saurayin dake zuwa garesu, kwata kwata bai wuce saura taku shida ya ƙaraso inda suke ba, tashi tsaye yayi yana me fuskantar saurayin, daidai lokacin Almustapha ya ƙaraso, dayake shi jan ajin nasa baya hanasa fari'a, hakan yasa bawani ɓata lokaci ya miƙawa Pharouk hannu don su gaisa,  ganin haka yasa Pharouk ma bashi hannu suka gaisa, cike da kulawa Almustapha ya kalli Zieyaderh wanda kanta ke ƙasa, hakanan gabanta keta faɗuwa, cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa yace "Inason aron baƙon naki naɗan wasu mintuna, inafatan bazan takuraki ba?"

Wani iri taji yayinda wani irin nauyi da kunyarsa suka lulluɓeta alokaci guda, jikinta asanyaye ta miƙe tsaye tare da kaɗa kanta alaman "Babu komai"  cikin nutsuwa haka tajuya tanufi cikin gida, ita kanta bazata iya tantance awani hali take ciki ba awannan lokacin. Kamar wanda ƙwai ya fashewa haka ta haura sama ko lura da Oummu dake tsaye a bakin kitchine batayi ba, Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da duban hanyar da Zieyaderh'n tabi, wani irin fargabane taji ya kamata, sai yanzu takejin tsoron haɗin da tayi, musamman ma da taga yanayin da Zieyaderh'n tashiga ayanzu, shiru tayi tare da faɗawa wani sabon duniyar tunani.
Ita kuwa Zieyaderh tana  shiga ɗaki ta rufo ƙofarta, samun kanta tayi da sulalewa ta zauna daɓas aƙasa, batare da ta ankara ba taji wasu hawaye masu ɗumi suna sauƙa akan ƙuncinta, tabbas wannan sabuwar ƙaddaran da ta tsinci kanta aciki tayi mata girma, ƘADDARA tana neman haɗa aurenta da Almustapha, sannan kuma agefe guda ga Pharouk da yake neman ta amsa masa soyayyarsa, ƘADDARA mafi girma awajenta kuwa itace soyayyar Mr.Helper, hannayenta tasanya ta share hawayenta,  wata zuciya ce me bata ƙwarin guiwa akan ta yarda da duk wata ƙaddara da tazo mata me kyau ko akasin haka, samun kanta tayi da kwanciya luf akan gado, mintuna ƙalilan bacci ɓarawo ya saceta.

Pharouk. Gudu sosai yake sharawa akan babban titin gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya jikinsa, maganganun da Almustapha ya faɗa masa suketa yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, da ƙarfi ya daki steering motar ransa amatuƙar ɓace yace
"Bazan taɓa zama looser akaro na biyu ba SOORAJ, awannan karon tabbas bazan bari kasake nasara akaina kamar lokutan baya ba,  bazan taɓa bari ka auri Zieyaderh ba SOORAJ!!"  wani irin murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, ahankali yashiga rage gudun da yakeyi tare da ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa tahanyar aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa.
***
Oummu ce ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin wanda yake mallakin Mijinta ne, Abba dake tsaye yana sanya garen kayansa ya ɗan juyo tare da kallonta murmushi yayi mata tare da cewa "Saboda kawai ɗanki zaiyi aure shiyasa kika kasa zaune kika kasa tsaye ko Sulaimiyya!" yaƙare maganar cikin yanayi na ɗan tsokana.

Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarta tare da cewa "Yanzuma ai nashigo ne nasanar dakai abokan tafiyanka sun iso"

Murmushi ya kumayi tare da cewa "Bake kaɗai kikejin farinciki aranki ba Sulaimiyya nima inaji, saidai kuma ata wani ɓangare na zuciyata ina ɗauke da fargaban abun da zaije ya zo"

"Insha Allah Alhajina babu wani abu da zaizo sai alkhairin Allah!" Tafaɗa cikin son ƙarfafa masa guiwa.
Yaji daɗin maganan nata sosai hakan yasa yayi murmushi, har wajen motarsa Oummu ta rakasa inda ya haɗu da manyan aminansa su Uku suka kama hanyar airport, kai tsaye suka wuce Kaduna, daga nan kuma zasu shige cikin motocinsu su wuce ƙauyen saminaka.

Itakuwa Zieyaderh gaba ɗaya wunin yau batajin daɗin jikinta, hakanan takejin kanta cikin ƙunci, wani irin kewa me taɓa zuciya takeji yana ratsa duk ilahirin jikinta, gaba ɗaya su Shukra sun lura da rashin walwalan da takeyi kwana biyu, yanzuma zaune suke su duka ukun akan wani ɗan dakali suna me shan iskan dake kaɗawa asararin samaniya.  Cikin yanayi naɗan zolaya  Nasmah tace "Amarya badai wai cin amarcin aka fara tun yanzu ba? naga gaba ɗaya duk kin rame, sometimes kuma kina cikin damuwa"
Hararanta Zieyaderh tayi tare daɗan murguɗa mata baki cikin yanayin ɓata fuska tace
"Ni ba amarya bace"
Dariya Nasma da Shukra suka sanya, wanda hakan yaƙara ƙular da ita. "Uhumm kigama zille zillenki yarinya wallahi sai mun fidda ankon bikin ki ehe, sannan kuma sai mun sha rawa koya kikace Besty" Shukra tafaɗa tana kallon Nasmah. "Ƙwarai kuwa" Nasmah tafaɗa tana me gimtse dariyanta. Cikin turo baki gaba Zieyaderh ta miƙe daga zaunen da take tare da nufar hanyar da zai sadata da class ɗinsu.  Kallo su Nasmah suka bita dashi harta ɓacewa ganinsu, sannan

28 / 48