Author : Maman Teddy Category : Romance
Oummu taji ba, nan suka tsaida magana cewar zata turo manya don atsaida magana, inda shikuma yace ko babu wasu manya ya yarda da ita ya bawa Ɗanta Almustapha Auren Ƴarsa Zieyaderh, duk lokacin da suka shirya kawai suzo ayi biki.
(uhhhh guys kushiryafa kuna da biki😝)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*This page is dedicated to you my dear @Zeety delight... heart you dear*
*Chapter 37*
Da tsananin farinciki ɗauke akan fuskar ko wannensu Oummu da Malam Garba suka shigo cikin gidan, Inna Ma'u na ganin hakan wani ƙaton baƙinciki ya ɗarsu azuciyarta, hakanan taji ajikinta cewa hanyar ƙaruwa suka tattauna, ae kuwa nan ta ƙudura aranta cewa Oummu na tafiya sai tayi maganin Malam Garba, yadae santa ae yakuma san wacece ita.
Kallon Zieyaderh Oummu tayi fuska ɗauke da murmushi tace "Inaga ya kamata ae ace mutafi tun yanzu, kada tafiyan dare ya kamamu"
Jin abun da Oummu tace yasanya ƙirjinta bugawa, ahankali ta ɗago idanunta tare da ɗan satan kallon mahaifinnata, cikin rashin sa'a tasamu shiɗinma kallonta yake, da sauri tayi ƙasa da kanta, murmushi yayi tare da cewa "Bakomai kuje Zieyaderh Allah Yakiyaye hanya ya tsare, nima inanan zuwa tunda yanzu nasamu adreshin inda kuke."
Wani irin sanyi ne Zieyaderh taji na ratsa zuciarta, sam batayi tunanin mahaifinta zai barta ta koma ba.
"Chab amma kuwa Garba kayi banzan hali, yanzun barinta zakayi ta koma, oh wato kaidai ba ka gaji da jin zagin da mutane ke mana agarinnan ba, karka manta fa duk akan ɓatanta sunanmu ya ɓaci, to babu inda zataje tananan tadawo kenan!" Inna Ma'u ta faɗa amasifance, don sam bata tsammaci haka ba.
"Haba Ma'u meyasa ne bazaki sanja ba, dan Allah Kibar yarinyarnan tayi tafiyarta, tafara karatu acan birni, tsayar mata da karatunta bashida wani amfani" Malam Garba yafaɗi haka cikin ɗan lallashi saboda yasan halin kayansa sarai ba mutumci.
Cike da kumfar baki Inna Ma'u tace "Dole kace haka mana saboda ƴar kace, ai dama ninasan banice na haifeta ba, kuma zaman birni kam wannan algungumar ƴar taka ta gama yinshi....." Bata gama rufe bakinta ba taji sauƙar wani abu me ɗan nauyi akan cinyarta, idanu ta zaro lokaci guda tare da haɗiye maganan dake bakinta, take yanayin fuskarta ya sauya daga ɓacin rai zuwa murmushi. "To Alhamdulillah, irin wanga farare bugun can babban birni, Hajiyan Birni Allah ya ƙara arziki!" Inna Ma'u tafaɗa bakinta har kunne, kuɗine masu yawa Oummu ta aje mata don rufe bakinta, ai kuwa lokaci guda sai ga bakinnata ya rufu . cike da nishaɗi tace.
"To yanzu sai yaushe zaku kuma dawowa?" yanayin yanda tayi maganan tana me ƙoƙarin cusa kuɗin cikin lalitantane yabasu daria amma sai suka gimtse, ɗauke da ɗan murmushi Oummu tace.
"Nan bada jimawa ba Insha Allah, Nangaba kaɗan kema nasan zaki kaimana ziyara!"
"Sosaima kuwa, kice ziyarori ma ba iyaka ziyara kaɗai ba, don fa basau ɗaya zanzo ba!!" Inna Ma'u tafaɗa cikin jin daɗi, dama ita abun duniya shine kanta.
Har wajen mota suka rakasu, bayan motar Oummu ta buɗe wanda ke shaƙe da kaya, Kamalu driver tasanya ya shiga ciro kayan yana kaiwa cikin gidansu Zieyaderh, kayan abincine kala kala da kuma wata leda dake ɗauke da kayan sawa, atamfofi da shadda irin na maza, godiya kam ba irin wanda baban Zieyaderh baiyi mata ba, duk da yanuna mata cewa kayan sunyi yawa, amma saitace masa ba komai, koda ta bashi kuɗi ƙin amsa yayi babu yanda batayi dashi ba amma haka yaƙi amsa, Inna Ma'u kuwa daɗine ya isheta, musamman ma ganin ana shigar da kayan abinci cikin gidanta. Haka su Zieyaderh suka baro cikin ƙauyen zuciarta cike da kewan babanta. Har bacci tayi a hanya kafun su iso, gaba ɗaya zaman mota ba daɗi ji take duk jikinta yayi mata wani iri.
Suna isa gida kowa ɗakinsa ya wuce, don gaba ɗayansu agajiye suke, da ruwan zafi tayi wanka kana tabi lafiyar gado.
Sunday.
Yawanci duk ranan weekend atare suke cin abinci akan dinning, tun 8 tatashi tayi wanka, riga da sket na 1million stones tasanya wanda suka amshi jikinta sosai, tayi kyau. Wani ɗan madaidaicin mayafi ta sanya ta rufe jikinta, a kitchine ta samu Oummu cike da ladabi ta gaida ta, fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata, yauma kamar koda yaushe itace ta shirya gaba ɗaya abincin akan dinning. Ƙamshin turaren Almustapha daya shiga hancinta shi yasanyata ɗago da kai ta ɗan kalleshi, ƙasa tayi da kanta tare da gaidashi, amsa mata yayi yana me jan kujera ya zauna, sosai yau ɗin tayi masa kyau acikin shigarta, duk da cewa bai taɓa ganin kwalliya akan fuskarta ba amma gaskiya tana da kyau sosai.
Oummu da Almustapha ne suke taɓa hira kaɗan kaɗan yayinda ita kuma take serving ɗinsu, tunaninsa ne kwance aƙasan zuciyartaz hakanan taji wani iri da bataga ya fito ba, tunaninta ne ya katse sakamakon wani daddaɗan sanyin da taji yana ratsa jikinta, gefe guda kuma ni'imtaccen ƙamshinsa dake zautar da'ita ne yashiga cakuɗa da numfashinta.
Sanye yake da blue crazy jeans and Blue t-shirt mai kyau da tsada ƙiran company'n D&G, sosai yayi kyau kwarjininsa yasake bayyana, yayinda gashin kansa kuwa sai shinning yake, kujera yaja ya zauna, dakansa yayi serving kansa, wajen haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda kansa ke ƙasa, yau babu waya ahannunsa amma duk da haka yi yake kamar hankalinsa baya garesu, gaba ɗaya wajen ya ɗauki shiru, kowa abincinsa yakeci yayinda akabar mutane biyu daga cikinsu da saƙar zancen zuci, gaba ɗaya hankalinta yana garesa, so take ta ɗago idanunta ta kallesa amma fargaba ya hanata.
Tissue Oummu ta ɗauka ta goge bakinta tare da dubansu su dukansu, cikin nutsuwa tace "Ina da buƙatar hankulanku agareni dukanku!" Almustapha ne ya fara aje cokalin dake hannunsa tare da duban Oummu, itama Zieyaderh ɗago kanta tayi ahankali tana me kallon Oummu'n, shikam ko motsawa baiyiba, kana bai kuma daina shan tea ɗinsa ba.
Gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
"Sooraj da Almustapha inaso nayi maganannan ne agabanku saboda ko ba komai kamar yayye kuke awajenta, sannan awajenta zataji maganar amatsayin sabuwace, saɓanin ku da kuka taɓa jinta" ɗan numfasawa tayi kana tace..
"Zieyaderh!"
Tun kafun ta kammala maganganun nata ƙirjin zieyaderh ke bugawa, asanyaye tace. "Na'am!"
Tashi Oummu tayi daga inda take zaune, tare da jawo wata kujera ta zauna gab da Zieyaderh'n, hannayen Zieyaderh Oummu ta kamo cike da son gamsar da ita tace.
"Haƙiƙa kowacce uwa tanaso ɗanta ko ƴarta su samu abokan zama na gari, burin kowacce uwa adunia shine ƴarta mace ta dace da mijin aure, haka ma kuma ɗanta namiji ya dace da macen aure, tamkar ƴa haka na ɗaukeki Zieyaderh, bazan taɓa son wani abu dazai cutar dake ba, bazan miki dole ba, saboda kema kina da ra'ayi kamar kowa, halayyanki da kuma irin nutsuwarki yasanya naji ina kwaɗayin da ki ƙara zama acikin zuri'ata, duk da cewa munatare dake ayanzu, amma anan gaba ba lallaine mukasance tare ba, dole watarana aure zai ɗaukeki ya nesantaki damu, bazanyi baƙinciki ba idan kika samu adalin miji daga wani waje na daban, amma zanfi so ace daga cikin zuri'ata kika samu wannan adalin mijin, ba daga wani waje daban ba, kamar yanda nace bazan miki dole ba, ba kuma umarni nake baki ba, saidai ganin ya cancanta yasanya ni yin tunanin haɗaki aure da ɗana Almustapha!"
Dummmmmm tamkar ankwaɗa mata katuwar guduma akan ƙirjinta haka taji, yayinda agefe guda kuwa taji sauƙan kalaman Oummu acikin kunnuwanta tamkar almara, wani irin abune taji ya sarƙemata maƙoshi, take tasoma tari har saida manya manyan idanunta suka rikiɗe daga farare zuwa jajaye, da sauri Oummu ta ɗauko ruwa ta bata, cikin ikon Allah tanasha tarin ya ɗan lafa, jingina bayanta tayi da jikin kujera tare dayin ƙasa da kanta, me Oummu ke faɗane? Kodai kunnuwanta ne basuji mata da kyau ba? Aure kuma da Almustapha? Waƴannan tambayoyin sune cike aranta, ganin komai take kamar ba da gaske ba. Dafa shoulder ɗinta Oummu tayi cike da kulawa tace "Karki taɓa cutar da kanki Zieyaderh, idan har kinaga hakan zai sa ki cutu to karki ɓoye ki sanardani, bazan taɓa miki dole ba, nayi hakanne kuma badon na cutar dake ba saidon ina kwaɗayin ganinki cikin zuri'ata, duk da nasan cewa banice na haifi Almustapha ba, amma inayi masa son da nake yiwa ɗana SOORAJ, kuma ina masa kwaɗayin zamowarki mata a garesa!!"
Hawayene suka cika idanun Zieyaderh, har takai ga sun soma sauƙa akan hannunta, wani irin bugawa zuciyarta keyi, ita kanta batasan awani irin hali take ciki ayanzun ba, gaba ɗaya kalaman Oummu sunzama tamkar wani sinadari na bayyanar da raunin zuciyarta.
Ganin hawaye na ɗiga daga idanun Zieyaderh yasa Oummu cewa.
"Ya isa daina kukan, idan kingama cin abincin kije ki kwanta, komai ya wuce nafahimci halin dakike ciki!" tana gama faɗan haka ta miƙe tare da soma ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Zieyaderh ta riƙo hannun Oummu, cak Oummu ta tsaya tare da juyowa, ɗago manya manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace.
"Kiyi haƙuri Oummu ba ina kukane saboda banason abunda kikazomin dashi ba, nayarda ke uwace agareni, saboda haka NA AMINCE!" taƙare maganar ƙirjinta na mata wani irin suka, yayinda gaba ɗaya gaɓɓan jikinta sukayi weak, so take tafashe da kuka me sauti, so take ta kalli koda ɓangaren da yake ne kozataji sanyi, so take yace wani abu, to amma metakeso yace ɗin, itama kanta batasani ba.
Cike da farinciki Oummu tashafa kanta cikin ƙaunar biyayya irin nata tace.
"Nagode sosai Zieyaderh nakuma ji daɗi da baki watsamin ƙasa a idona ba, haƙiƙa ke yarinyar kirkice, Insha Allahu Kuma zakiyi alfahari da wannan haɗin, kije ɗaki ki huta kinji!" Oummu ta ƙare maganar cike da lallashi. Babu musu kamar wacce ƙwai ya fashewa ajiki haka ta tashi daga zaunen da take, har yanzun bazata iya ɗaga idanunta ta kalli ko wanne daga cikinsu ba, cikin ƙwallan da suka sake cika idanunta ta haura sama daɗan sauri burinta taje tayi kuka kozataji sauƙi aranta.
Tunda suka fara maganar har kawo iyanzu bai koda ɗago kansa ya kallesu ba, sannan baidaina abun daya keyi ba, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin da tsabar zafi har tiriri yake, hayaƙin dake fita acikin kofin tea ɗin shine ya sanya gaba ɗaya fuskarsa ta ɗanyi zufa, sam baijin wannan zafin shayin akan harshensa hasalima tamkar wanda yakeshan ruwan randa haka yaji test ɗin shayin ya sauya a bakinsa.
Kallon Oummu dake tsaye tana murmushi Almustapha yayi jikinsa asanyaye yace
"Oummu kinaga kamar ba matsala kuwa?" Still murmushi Oummu tayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa tace.
"Babu wata matsala Almustapha ka kwantar da hankalinka, kaidai ka shirya bikinka yakusa zuwa Insha Allah" Tana gama faɗan haka ta wuce zuwa ɗakinta.
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannu ya dafa saitin zuciyarsa, har acikin ransa yaji wani irin farinciki, da sauri yatashi ya nufi ɗakinsa sam yama manta da Sooraj dake zaune agefensa.
Shikaɗai ya rage zaune akan dinning ɗin, ahankali ya aje cup ɗin dake hannunsa, tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa, miƙewa tsaye yayi kai tsaye ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, baijin zai samu relief idan ba shower ya sakarwa kansa ba, bathroom ya shiga tare da kunna shower, tsayawa yayi saitin shower ɗin ruwa na dukan kai da jikinsa, ahankali yake fidda wani numfashi me zafi.
Tana rufe ƙofar ɗakinnata da gudu ta faɗa kan gado, kanta ta cusa acikin pillow tare da sakin kuka me sauti. Sosai tayi kuka wanda ita kanta batasan na menene ba, batasan metakeji acikin zuciyarta ba, saidai tabbas tasan tanajin wani irin yanayi na babu daɗi, ya zatayi idan bata amincewa Oummu ba, ko ba komai su ɗin sunkasance mutane masu tsananin karamci agareta, idan har bata amince da maganan Oummu ba menene sunanta? BUTULU? tabbas Oummu tabata kulawa, sannan duk da batasan wacece itaba ta zauna da ita bata ƙyamaceta ba, shin saɓamata daidai ne? koma badon Oummu ba kodanshi ya cancanci tayiwa mahaifiyarsa biyayya, koba komai shiɗin wani ne na musamman awajenta, idan taƙi aminta da maganan mahaifiyarsa tabbas tasan bazaiji daɗi ba, amma kuma meyasa takejin wani abu dangane dashi? meyasa baice wani abuba alokacin? "Mekikeso yace?" wata zuciar ta tambayeta, shiru tayi da kukan da take tare da soma sauƙe ajiyan zucia akai akai.
Kusan 30 minutes ya ɗauka ruwa na dukan jikinsa, da ƙyar ya iya kashe shower'n tare da ficewa daga cikin bathroom ɗin, sauya shigarsa yayi zuwa wani white yard wanda yaji ɗinkin half jumper da wando, sosai kayan sukayi masa kyau, saidai rashin walwalan dake kan fuskarsa na yau ya zarce na kullum, ɗan makullin motarsa ya ɗauka tare da wayarsa kana yafice daga cikin ɗakin.
Tuƙa motar yake amma batare dayasan ina ya nufa ba, ganin ya soma gajiyawa ne yasanyashi gangarawa gefen titi yayi parking ɗin motar, ahankali ya kifa kansa akan steering motar, shikansa baisan mene dalilinsa na tsayuwa awajen ba, baisan dalilin daya sanya yakejin kansa acikin wani irin bad mood ba, mekenan? me hakan yake nufi? hakanan yaji kansa acikin damuwa, to amma abun tambayar shine damuwar tasa na menene? shikansa baisan akan mene yake damuwan ba, dalilinsa na sanya kansa cikin damuwa yayi ƙaranci, tabbas yanaji ajikinsa cewa idan har ya bari tunanin dake ƙwaƙwalwarsa yasamu mafaka acikin ƙirjinsa to tabbas zuciyarsa zata buga.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 38*
Ɗago kansa yayi daga jikin steering motar tare da sakin wani murmushi mai ɗauke da tarin ma'anoni, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba, ƙarfe 11 dae dae, ɗan ƙaramin tsuka yayi tare da tada motar ya cillata kan titi.
Zieyaderh kuwa tana gama koke kokenta baccine ɓarawo ya saceta wanda sai yanzun ta tashi, ji tayi yanayinta ya sauya tamkar wata marar lafiya, bathroom tashiga tayo wanka, tare da dawowa ta zauna akan gado, tv ta ƙurawa ido amma azahirin gaskiya hankali da tunaninta ba ga tv'n yake ba, tunaninsa ya matsanta mata, lallai tana da buƙatar me fayayyace mata halin da take ciki, Shukra, itace wacce ta fara faɗo mata arai, tabbas tasan idan tasamu Shukra to zata fayyace mata komai, to amma idan Shukra ta bata amsar da zai hautsuna tunaninta fa? ajiyar zuciya ta sauke tare da soma ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta, sam yau haka taji zaman gidan ya isheta, komai jinsa take ba daɗi.
Wuse zone 4
SOORAJ, zaune yake akan wata kujera dake kusa da haɗaɗɗen dinning table ɗin dake cikin falon, cup ɗin coffee ne agefensa yayinda yake signing ɗin wasu papers dake gabansa, Mas'oud ne ke zaune akan kujeran dake facing nasa, wayar dake hannunsa ya ajiye tare da kai dubansa ga Sooraj, cikin yanayi na ɗan damuwa yaƙira sunansa.
Batare daya tsaida aikin da yakeyi ba, batare kuma daya ɗago ba yace "Ummm"
Gyara zama Mas'oud yayi tare da cewa "Oummu tayimin magana akan auren Almustapha da Zieyaderh, sannan tace dani gobe Abba zaizo nakuma ce mata zan sameshi muyi magana, gaskiya RAJ nayanke shawaran zan sanar da Abba komai adangane da rashin lafiyanka!"
Aje pen ɗin hannunsa yayi tare da ɗago kansa ya dubi Mas'oud.
"Faɗa masa matsalata bashida wani amfani Mas'oud, kabari kawai badai aure suke so nayi ba, nashirya zanyi" Yafaɗi haka cikin halin ko inkula.
"Yin aurenka bashine mafita ba Sooraj samun lafiyanka shine abunso, ya zakayi da matar idan har baka samu lafiya ba?" Mas'oud ya tambaya cike da tsananin tausayinsa.
Murmushin gefen baki Sooraj yayi tare da ɗan cizan lips ɗinsa, adai dai wannan lokacin shikaɗai yasan me yakeji.
Ɗan numfasawa Mas'oud yayi tare da cewa "Amma RAJ auren Zieyaderh da Amustapha abun na damuna sosae!"
"Why?" Sooraj ya tambaya ataƙaice.
"Sooraj" Mas'oud yaƙira sunansa. Ɗago kai yayi ya kalli Mas'oud ɗin batare daya amsa ba, shima Mas'oud din kallonsa yake, tabbas shikam akwai abun daya jima yana hangowa acikin idanun SOORAJ, amma baitabbatar da abunba sai ayanzu, wani tarin tausayin Sooraj ɗinne yasake kamasa, haƙiƙa Sooraj baisan komaiba agame da so, shi mutum ne wanda yake rayuwarsa shi kaɗai, baya sharing damuwarsa da kowa, saboda haka ba lallai ya fuskanci cewa wani abu na damunshi ba, koda ma yafahimci hakan ba lallaine yasan menene abun ba. Kawar dakae gefe Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka tare da cewa "Nagama signing papers ɗinnan, ka kula sai munyi waya!"
Kasa ce dashi wani abu Mas'oud yayi harya fice, shikam Allah Yasani tausayin SOORAJ yake, tabbas yau ya hango damuwa me tarin yawa a cikin idanun SOORAJ.
Monday
Tun kafun 7 yau tagama shiryawanta, bata da wani buri wanda ya wuce taje ta sanar da Shukra damuwanta kozata ji sauƙi acikin zuciyarta, duk yanda Oummu taso ta tsaya tayi break ƙi tayi haka ta tafi makarantar da yunwa acikinta.
Shiru Shukra tayi tare da ɗan nazantar maganganun da suka fito daga bakin Zieyaderh.. "Bansan ya zanyi ba Shukra, bansan me yasa nakejin haka dangane dashi ba" Zieyaderh tafaɗa cikin yanayi na damuwa.
Murmushi Shukra tayi tare da dafa shoulder ɗinta, gyara zama tayi tare da cewa "Zaki iya yarda da cewa kin kamu da son sa?"
Idanu Zieyaderh ta zaro waje tare da dafe ƙirjinta dake bugawa, cikin yanayi na tsoro tace "SO fa kikace Shukra?"
"Eh SO, karki yarda ki ƙaryata zuciyarki akan alamomin so da take gwada miki, tabbas Son shi kike Zieyaderh, don so ne kaɗai ke kawo waƴannan alamomin, idan ba so ba, me zae sanya dan kinganshi gabanki yana faɗuwa? me zaisa tunaninsa ya samu mafaka azuciyarki ba dare ba rana? Idan baso ba me zai sanya tsananin tausayinsa wanzuwa acikin ranki? Wannan duk alamomin SO ne Zieyaderh, hmmm bana faɗa miki SO ya wuce duk wani tunaninki yana zuwa da alamomi masu yawa, haƙiƙa sonda kike masa irin sane wanda yake sanya ciwo azuciya, kiyarda kawai sonshi yana daga cikin ƘADDARA'nki!"
Shiru Zieyaderh tayi tare da rumtse idanunta, tabbas bazata