Author : Maman Teddy Category : Romance
sosai take kewarsu.
7:15 am Ahankali take sauƙowa daga kan step ɗin yayinda ta kanannaɗe hannayenta acikin hijabinta.
Ummu ce zaune acikin katafaren falon, laptop na companyn apple ne aje agabanta da alama wani aiki takeyi, kasancewar har da wani ɗan madaidaicin farin glass dake sanye a idanunta.
Karasowa cikin falon Ziyada tayi cike da ladabi tarusuna tare da cewa. "Barka da da safiya Ummu Ina kwana!"
Juyowa Ummu tayi fuskarta ɗauke da murmushi da "Lafiya" ta amsa mata sannan taƙara da cewa
"Har kinshirya da wuri haka?"
Murmushi tayi tare da ɗan kaɗa kanta alamar "Eh"
Agogo Ummu takalla taga babu wani sauran time hakan yasa tace da Ziyada ta ɗauki food flask ta sanya abinci aciki tatafi dashi, hakan kuwa Ziyada tayi, koda tazo fita daga cikin falon tsaida ita Ummu tayi ta bata 500 tace tasaya chocolate, cike da jin nauyi Ziyada ta girgiza kanta alamar bazata amsa ba.
Murmushi Ummu tayi ta tura mata kuɗin acikin jakanta sannan tahaura sama. Fitowa tayi daga cikin falon tana ƙara gyara zaman school bag ɗinta wanda yake rataye kan kafaɗanta. Kamalu driver ta tarar tsaye ajikin mota yana jiranta, tafiya ta cigaba dayi tana me gyara igiyan jakar makarantarta. Kansa tsaye yake tafiya yana me ƙoƙarin maida wayarsa daya amsa ƙira yanzu cikin aljihun wandonsa, babu wanda yakula da wani acikinsu, sam bata ankaraba saiji tayi ta buge mutum, kafun ta gama daidaita nutsuwarta ma tuni fitinannen ƙamshinsa ya gauraya da numfashinta, aɗan daburce taja baya, chest ɗinsa daidai saitin inda kanta ya buga ya ɗan riƙe, bakinta na rawa tace "Dan Allah kayi haƙuri bansan kana zuwa bane!"
Kallonta yayi daga ƙasanta har sama, yana kawowa daidai fuskarta yatarar da ƙwalla sun cika idanunta, ƙiris suke jira su gangaro. Wani irin haushi da takaicinta ne suka cikasa, cikin wata murya me ɗauke da amo yace "Are you insane?"
Ƙasa tayi da kanta aikuwa saiga hawaye kam sun ziraro kan kuncinta. Wani baƙincikintane yasake kamasa, hannunsa yakai ya kamo haɓanta tare da ɗago fuskarta, manya manyan idanunta ta zaro waje tana kallonsa, bazato ba tsammani ya hankaɗata gefe yayi shigewarsa abunsa, ƙiris yarage tafaɗi, wani irin wawan ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ɗaukar school bag ɗinta data faɗi ƙasa ta nufi wajen Kamalu driver.
Tunda suka ɗauki hanyar makarantar take tunani, akan fuskarta kuwa hawayene caɓa caɓa, wasu na koran wasu.
"Me turetan da yayi yake nufi? wulaƙanci kenan kome?" abun da take ta tambayar kanta kenan. Wata zuciyarta ce tace da ita "Baki da hankali Ziyada, dama irin waƴannan mutanen idan ba alfarma ba mene zai haɗaki dasu? sam baki da daraja da kimar da zaki raɓesu" Hannu takai kan fuskarta ta share hawayenta, aranta taƙudiri aniyar zatayi karatu sosai itama ta zama wata, daganan saita fita daga cikin rayuwarsu baki ɗaya. Da wannan tunanin azuciyarta har Kamalu driver ya ajiyeta acikin makarantar, tun bata gama fitowa daga cikin motar ba Nasmah ta taho da sauri ta rungumeta, wani irin daɗi Ziyada taji tuni ta manta da wata damuwa itama ta rungume Nasmah...
"I miss u so much my ƙawa!" Nasmah tafaɗa cike dajin daɗin ganin Ziyada.
"Miss you too!!" Ziyada itama tafaɗa tana murmushi, ƙarasowar Shukra yasa Ziyada sakin Nasma, ta rungume Shukra dukansu dariya suka sanya cike dajin daɗin ganin juna, suna maƙale da juna haka suka nufi wajen taron assembly, koda aka kammala assembly'n direct sabon ajinsu suka nufa S.S 2A. Kamar yanda suke a wancan ajin hakama suke a wannan ajin sit ɗinsu ɗaya, Ziyada ce ke tsakiya sai Nasma da Shukra dake gefenta.
Ƙarfe 10 am daidai aka fito dasu break, kai tsaye wajen da aka tanada na musamman doncin abincin ɗalibai suka nufa, soyayyen doya da chicken sauce din da Ziyada ta zo dashi shi suka fara ci kafun daga bisani suka ɗaura da snacks.
11:00 am
Mota ƙirar Jeeb ce baƙa tayi parking awajen da ake faka motoci dake cikin school ɗin, Farouk wani irin ajiyar zuciya me sanyi ya sauƙe tare da lumshe sexy eyes ɗinsa, sai yanzu yaji sanyi acikin ransa da ya gansa acikin makarantar, zare key ɗin motar yayi tare da buɗe murfin motar ya fito, sanye yake da jumper na shadda sky blue wanda taji aiki me kyau, sanye yake da tsadaddiyar hulan zanna akansa wanda ta ƙarawa fuskarsa kyau, sosai yayi kyau sai fidda ƙamshi yake, bayi da tantama akan inda zai sameta saboda haka direct office ɗin principal yanufa, koda yaje permission ya nema akan yanason ganin wata ɗaliba mesuna Ziyada Mansoor Mainasara, domin da wannan sunan akayi mata register. Da yake principal ɗin ya sanshi, babu ɓata lokaci ya tura S.S 2A don aƙirata kasancewar a time ɗin sungama break harsun koma class.
Ba ƙaramin faɗuwa gaban ziyada yayiba jin wai ana ƙiranta daga office ɗin principal, gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, a iya saninta bata da wani wanda zaizo nemanta, haka ta nufi office ɗin principal ɗin zuciyarta cike da fargaba, a corridor ɗin dazai sadata da office ɗin idanunta sukayi mata tozali dashi, wani irin duka taji ƙirjinta yayi sai kawai ta tsaya cak tare da sunkuyar da kanta ƙasa, murmushin daya bayyana cute dimples ɗinsa yayi tare da takowa zuwa gareta, wani irin kallo yakeyi mata, komai nata ya sauya tasakeyin kyau sannan taƙara girma duk dacewa ba jiki tayi ba amma tabbas kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa ta ƙara girma. Gaf da ita ya matso har yazama baifi saura taku ɗaya tsakaninsu ba. "I miss you!!" yafaɗa cikin wata irin murya yana me kallon small lips ɗinta.
Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta, ahankali taɗago da fuskarta idanunsune suka faɗa cikin na juna ƙasa tayi dakanta tana mai wasa da yatsun hanunta, sam bataji wani abuba da takalli cikin idanunsa, saɓanin Oga Sooraj da idan takalli cikin beauty eyes ɗinsa take rasa nutsuwarta.
Kallon yanda take lallanƙwasa yatsun hanunta yayi, yaɗan saki murmushi, jiyake kamar yajawo ta jikinsa ya bata tight hug, komai nata na musammanne babu abun dake burgesa atattare da ita kamar sanyinta.
"Muje mu zauna ko!" yafaɗa yana meyi mata nuni da wata bishiya wacce ƙasanta ke ɗauke da wani bench wanda akayi da cement. Bata iya musa masa ba saidai har yanzu kanta aƙasa yake, zama tayi akan bench ɗin tare da jawo hijab ɗinta ta ɗan rufe gefen fuskarta, shima akan bench ɗin ya zauna har ƙamshinsu na iya gauraya waje guda. "Nayi kewarki da yawa, bazan sake bari kiyimin nisa har haka ba, bansan da yaushene kika kama zuciata ba, please My cute babyy na ki juyo na kalli fuskarki!" yaƙare maganar cikin sanyin murya.
Har acikin ranta taji kalamannasa saidai tanaji kamar sunyi mata nauyi. Hannayenta tasanya taɗanja hijab ɗinta baya, tare da ɗago kanta ta kalleshi, shi ɗinma kallonta yake, murmushi ya sakarmata tare da ɗanyin ƙasa ƙasa da idanunsa, wani iri taji ajikinta hakan yasa itama taɗanyi masa murmushi. Cikin muryar shagwaɓa tace "Shine kaɗauko ni daga aji bayan kasan karatu zamuyi ko!"
"am sorry babyyyna inason ganinki sosai shiyasa."
Murmushi tayi tare daɗan satan kallonsa, Idanunsa ɗaya ya kashe mata hakan yasa ta cusa kanta acikin cinyoyinta tana sakin wani smile, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa ya duba, time ɗin dazai koma office yakusa hakan yasa shi kamo hanunta, da sauri taɗago kanta ta dubeshi murmushi yayi mata tare da sake matsowa daf da ita, cikin wata irin murya me sanyi yace. "I love you!!!"
((( "Fatymasardauna kina mana rowan Sooraj" "Teemah sardauna bakya kyauta mana gaskiya bakya mana update da wuri" "Please me yasa yau bakiyi Sooraj ba?" "Haba teemah don Allah kina mana update akan lokaci" "Gaskiya typing ɗin da kike mana yana kaɗan please ki ƙara mana yawan page" Irin waƴannan ƙorafe ƙorafen kullum nake samu daga wajen wasunku, am really sorry bani da wani buri daya wuce nafaranta muku amma kuma lokaci yanamin jinkirin hakan, idan ta sonane kullum na baku update na Sooraj amma kuma hakan baya yiwuwa, please kunamin uzuri nima ba ason raina hakan ke faruwa ba, idan nace zanna muku typing kullum to kaina zaiyita min ciwo ne nasan kuma bazakuso hakan ba don Allah kuɗau uzurina, nasan kuna sona kuma kuna ƙaunar novels ɗina, nima kuma inasonku sosae sosae 💞)))
*Vote*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
phatymasardauna
*Dedicated To My life (Sardauna)*
*Wattpad*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 29*
"I love you!!!" ya faɗa slowly yana me murza yatsun hanunta dake cikin nasa.
Da sauri ta ɗago golding eyes ɗinta ta kallesa, wani irin abune taji yana yawo acikin jikinta, sam batasan me yasa wani yanki na zuciyarta ke ƙoƙarin accepting ɗinshi ba, hannayenta dake cikin nashi ta soma ƙoƙarin zarewa, babu musu yasake hannun nata, sai dai kuma be janye mayun sexy eyes ɗinsa daga kanta ba. Murmushin daya bayyana kyawunta tayi tare da miƙewa tsaye, batare da ta kalleshi ba tace "Zan koma class"
Shima miƙewa tsaye yayi tare da ɗan sakin murmushin daya sanya dimples dinsa loɓawa, wani farin envelope yazaro daga cikin aljihunsa, wanda aka ƙawata bayan envelope ɗin da zanen flowers masu sheƙi, gwanin burgewa, miƙa mata envelope ɗin yayi, ɗago ɗara ɗaran idanunta tayi ta ɗan kalleshi, mumushi yayi mata kamar zai shige jikinta haka ya sake matsowa gaf da ita, yanayin idanunsa ne suka sauya, take taji wani sabon abu na sauƙa ajikinta. "Pleaseee!!" yaja maganan tare da ɗan ƙanƙantar da idanunsa. Adaburce tashiga kakkare jikinta, sam bata sabayin irin wannan kusancin da wani namiji ba, gaba ɗaya duk abun da Farouk keyi mata ganinsu take wasu daban, kowacce kalma da zata fito daga bakinsa jinta take tayi mata nauyi, takan rasa nutsuwarta idan taganshi akusa da ita sosai, domin wani irin faɗuwar gaba takeji, ganin irin mood ɗin data shiga yasanyashi sake kamo soft hand ɗinta, envelope ɗin ya ɗaura mata akan hanunta, tare da bin kyakkyawar fuskarta da ido, sam batasan da yaushene kuma ya akayi taganta tana tafiya ba, sauri tashiga yi burinta ɗaya taganta acikin class, gaba ɗaya ma ta manta da cewa basuyi sallama ba. Shikuwa Farouk wani killer smile ya sake bayan yaga shiganta cikin class, baisan me yasa ba hakanan yake losing control ɗinsa idan yana kusa da ita, ayanda ya fahimce ta yarinyace wacce take real innocent, batasan komai agame da soyayya ba, da wannan daman zaiyi amfani wajen koya mata sonsa, zai koya mata yanda zata sosa fiye da kowa, daga ƙarshe kuma zaiyi ƙoƙari wajen ganin ya sameta amatsayin Mallakinsa, sosai yake sonta, sosai yake kuma son kasancewa tare da ita. Da wannan tunanin ya ƙarasa wajen da yayi parking motarsa.
Kamar wacce aka jefo haka ta faɗo cikin class ɗin, ko izinin shiga ajin bata nema ba. da yake a bencin gaba suke kuma malamin dake cikin class ɗin, gaba ɗaya hankalinsa naga board yana rubutu, shiyasa bai kula da shigowanta ba harta zauna, kallonta Shukra da Nasmah sukayi, cikin ƙasa ƙasa da murya Nasma tace. "I hope ba wani abun kikayi ba, naga jikinki duk yayi weak"
Sai alokacin taɗan soma dawowa sense ɗinta, murmushi ta ƙaƙalo tare da girgiza kanta alaman babu komae. Nasmah bata sake cewa komai ba ta maida hankalinta ga karatun da ake musu.
Duk abunda Malamin Chemistry ɗin ya koya musu ta bayan kunnen Zieyaderh yabi ya wuce, sam ko kaɗan hankali da tunaninta ba akansa suke ba, tunaninta yayi nisa ne izuwa wani waje daban, Farouk shine wanda yayi tsaye aranta.
"I love you!!!"
kalmar daya furta mata shiketa dawowa cikin tunaninta, lumshe beauty eyes ɗinta tayi tare da sakin wani murmushi wanda batasan da bayyanarsa ba, hakanan taji wani sanyi aranta, sosai daɗin kalman ke ratsata, kulawa shine abun da ta rasa tun tana ƙarama, kalmar Soyayya kalmace da babu wani wanda ya taɓa furta mata shi, hakan yasa takejin ayanzu tamkar wani kyautan farinciki Farouk ya bata, duk da cewa kai tsaye bazata iya tantance me takeji agame dashi ba, amma tabbas zuciya koya take tanason me kyautata mata, tana a wannan tunaninne har malamin chemistry ɗin yafita batare da ta saniba, kasancewar period ɗinsa ya ƙare, dafa ta da Shukra tayi shi yayi sanadiyar ɓacewan tunanin da take.
"Lafiyanki ƙalau kuwa Zieyaderh?"
Shukra ta tambaya tana me ƙarewa fuskar Zieyaderh'n kallo.
Board ta kalla tare da ɗan waiwayawa bayanta, cikin mamaki tace.
"Wae ina chemistry teacher'n ya fita ne?"
"Da ke zai tsaya jira?" Shukra ta bata amsa tana me harhaɗa text books ɗin dake watse saman desk ɗinta.
Murmushi kawai Zieyaderh tayi tare da duban Nasmah, cikin sakewa tace.
"Gaskiya ban fahimci abun daya koyarba please Nasmah taimaka min"
Dukansu tsaida abunda sukeyi sukayi tare da kallonta.
"Bazaki taɓa fahimta ba ae tunda anzuba miki kalaman love acikin brain ɗinki" Shukra tafaɗa tana me guntse dariyar dake ranta.
Hararanta Zieyaderh tayi tare da cewa "Love kuma?"
Dariya Nasmah da Shukra sukayi tare da tafawa, kallonsu tayi kawai itama saitayi murmushi,
jujjuya envelope ɗin dake hanunta ta shiga yi.
"Lover gurl!" Shukra tafaɗa tana dariya.
Kallonta Zieyaderh tayi, cikin yanayi na shagwaɓa tace "Allah Shukra banaso fa" Dariya dukansu suka sanya, envelope din dake hanunta ta soma ƙoƙarin buɗewa, duk suka zuba mata ido.
Wani golding colour neck chain ne me kyau da tsadar gaske ne ya bayyana acikin envelope ɗin.
"Wow!!" Nasma da Shukra suka haɗa baki wajen faɗa, da sauri Nasma ta karɓi envelope ɗin ta ciro chain ɗin, saboda tsabar kyawun chain din har ɗauke musu ido yake.
Kallon Zieyaderh Nasmah tayi tare da cewa "Gaskiya guy ɗinnan ya haɗu, wannan chain ɗinfa na gold ne, zaikai 50k fa!"
"Wasa ma kike, zai iya kai 60k wannan neck chain din, gaskia guy ɗinnan ya iya bada gift" Shukra tafaɗa tana me jujjuya chain ɗin ahanunta.
Zaro idanu Zieyaderh tayi sakamakon jin kuɗin chain ɗin, cikin yanayi na tsoro tace.
"Zan maida masa gaskiya ni bazan karɓa ba"
Baki Nasma da Shukra suka sake suna kallonta, cikin nuna mata batasan me takeyi ba Shukra tace "Zaki mayar masa fa kikace?"
"Eh, bazan iya sawa ba gaskiya" Zieyaderh tafaɗi haka har acikin azuciyarta.
Dariya suka sanya su duka biyun, cikin dariya Nasmah tace
"Allah har yanzun baki waye ba babe, ae idan masoyinka ya maka kyauta baka maida masa."
Murmushi kawai Zieyaderh tayi kana ta kifa kanta akan desk, wani abune taji ya tsaya mata arai, har abada bazata taɓa manta matsayinta da kuma wacece itaba, sam bazata yaudari kanta ba, tanajin su Nasmah nata yaba neck chain ɗin tayi musu shiru,, Shigowan Islamic teacher yasanya su yin shiru, tare da bada hankalinsu gareshi. Gaba ɗaya wunin ranan Zieyaderh asukurkuce tayishi, abu biyune ke tsaye aranta, ƙarfe 5 pm daidai aka kaɗa musu ƙararrawan tashi. Amatuƙar gajiye takejin kanta, sama sama sukayi sallama dasu Nasmah, kana tanufi inda Kamalu driver ke tsaye yana jiranta, gidan baya ta buɗe ta shiga, duk da cewa tafi yawan zama agidan gaba, don bata damu da zaman gidan baya ba.
Tunda suka ɗauki hanya ta maida hankalinta kan titi, sanyin AC'n dake tashi acikin motar ne ya sanya tasomajin sanyi, hakan yasa ta duƙunƙune jikinta.
Saida sukazo gaban tamfatsetsen gate ɗin gidan Kamalu driver ya danna horn, take aka wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motar ciki.
Wata Black colour jeep ce tayi parking a gefen gidan, wanda tun barowarsu makaranta take biye dasu batare da sunsan da hakan ba. Murmushi Farouk yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, key ya sake yiwa motar tare dayin reverse, sai yanzu yakejin sanyi aransa, sam bada wasa yakeson Zieyaderh ba, so yake ya mallaketa, so yake ta soshi fiye da yanda zata so kowa, aransa ya gama yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, saboda haka da confidence ɗinsa ya juya yakoma inda ya fito.
Kamalu driver na gama daidaita parking, agajiye ta buɗe murfin motar ta fice, school bag na riƙe ahanunta ta nufi hanyar da zai sadata da babban falon gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin falon, babu kowa afalon sai TV plasma wanda yaketa aiki shi kaɗai, direct sama ta wuce, kamar zata wuce ɗakinta sai kuma ta ƙarasa gaban ɗakin Ummu tayi knocking, daga cikin ɗakin Ummu dake zaune tana karanta jarida tace "Yes come in"
Tura ƙofar ɗakin tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, ganinta yasa Ummu taɗanyi murmushi.
"Barka da gida Ummu" Zieyaderh tafaɗa cikin ƙasa da kai.
"Yauwa Zieyaderh kindawo ko, ya school ɗin?"
"Alhamdulillah!" Zieyaderh tafaɗa still aɗan kunyace, domin har acikin zuciyarta tanajin girman Ummu.
"Masha Allah, to je kicire uniform ɗin akwai abinci a dinning" Cike da kulawa Ummu tafaɗi haka.
Miƙewa Zieyaderh tayi tare da cewa "to"
Har ta fice daga cikin ɗakin Ummu bata daina kallonta ba, hakanan alkunyan Zieyaderh'n ke burgeta, sam baruwanta da rawan kai, komai nata acikin sanyi takeyinshi, tabbas zata sowa ɗanta Almustapha samun kyakkyawar yarinya kamar Zieyaderh, ta yanke hukunci aranta zata samu Mas'oud suyi magana, lallai tanason ganin iyayen Zieyaderh, don tanason nemawa ɗanta Almustapha auren Zieyaderh a wajensu, tasan Almustapha bazai taɓa ƙin zaɓinta ba, musamman ma idan yaga Zieyaderh tasan dole zai sota, dama kuma shi bai da wata matsala bakaman SOORAJ ba wanda komai nasa aƙa'idance yake.
Zieyaderh kuwa tana shiga cikin ɗaki ta soma rage kayan jikinta, towel ta ɗaura aƙirjinta tare da shigewa bathroom, da ruwa me ɗan ɗumi tayi wanka, take taji gajiyan dake nannaɗe a muscles ɗinta sun soma warwarewa, Ko body lotion bata shafa ajikinta ba ta zura wata slim net gown red colour ajikinta, wanda take da guntun hannu, sosai rigan tayi mata kyau, hasken fatanta yasake bayyana sosai, wani mayafi me shara shara ta ɗauka tayane kanta zuwa ƙirjinta dashi, ko bedroom slippers bata sanya ba haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice, wani irin yunwane ke ƙwaƙulan cikinta, kaitsaye dinning area ta nufa, food flask ne masu kyaun gaske jere a kan babban royal table ɗin, kulan farko data buɗe white rice ne aciki wanda yaji carrot da piece, ɗayan kulan kuwa chicken soup ne wanda za