Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   30 / 48

87K to 90K   out of 142.5K words

sanar dashi cewa acikin satin zasu kammala haɗa kayan lefensu  zakuma su kawo har ƙauyen Saminaka, sanin halin Inna Ma'u yasan ya Malam Garba cewa idan sunma haɗa lefen su barshi a wajensu idan yaso duk randa aka kai yarinya ɗakinta sai abata. Sosai su Oummu sukayi na'am da hakan don Oummu itama ganauce akan hali irin na Inna ma'u.
***  Sosai su Oummu suka ta da maganan bikin gadan gadan Inda Oummu ta bawa Aunty Muhibbat milions ɗin kuɗi wanda za a haɗo lefe dashi, musamman Aunty Muhibbat ta hau jirgi zuwa Dubai don acanne take da tabbacin samun ingantattun kaya masu kyau da nagarta, jin wannan auren suke tamkar shine aure na farko da  za'a farayi acikin family ɗinsu,  Zieyaderh kuwa aƴan kwanakinnan sosai tashiga busy kasancewar sun fara test ɗin first time, kuma yanzune karatunnasu yake zafi sosai, hakan yasa gaba ɗaya hankalinta naga karatun ta, awannan karon so take tazo first class acikin ajinsu, inda suka sanya gasa su Ukun ko wacce burinta shine tazo first class,  yauma agajiye ta dawo daga makarantar inda tun shigowarta taga haraban gidan cike da motoci,  gyara zaman school bag ɗin dake rataye a kafaɗanta tayi kana ta tura ƙofar falon tashiga bakinta ɗauke da sallama.  Oummu da Aunty Muhibbat ta iske acikin falon sai kuma waƴansu mata guda biyu, gaba ɗaya tsakiyan falon cike yake da wasu akwatuna masu tsananin kyaun gaske,  akwatuna ne har guda 24 inda kowani set shida yake ɗauke da nasa kalan, cike da girmamawa Zieyaderh ta rusuna tagaida Aunty Muhibbat, fuska ɗauke da murmushi Aunty Muhibbat ta amsa mata tare da tambayanta ya makaranta,
da "Alhamdulillah!" ta amsa mata, harta kusa haura step ɗin dazai sadata da ɗakinta muryar Oummu ya tsaida ta inda take cewa tashirya sannan ta zuba kayanta a akwati tazo zasu wuce gidan Hajiya Arabi da Aunty Muhibbat, Hajiya Arabi wata matace wacce ta matuƙar iya gyara mace daga ciki har waje, ta iya gyaran amarya sosai hakan yasa duk wani wanda yakeji da kuɗi idan yatashi gyara ita yake nema, gyaranta yana da matuƙar tsada amma kuma yana da kyau sosai, hakan yasa Oummu ta narkamata  maƙudan  kuɗaɗe don ta gyara mata Zieyaderh.

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

               *WATTPAD*
         @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 42*

Tana shiga cikin ɗakin tasoma rage kayan dake jikinta, wani mini pink towel ta ɗaura  kana ta wuce bathroom, cikin nutsuwa tayi wanka  tare da ɗauro alwala.   Kasancewar yanayin na yau ana ɗan zafi yasanya komai bata shafa ba ta zura wata  jallabiya irin ta mata wacce take da adon duwatsu haɗi da zanen beuty's followers agabanta, sosai rigan ta amshi jikinta kasancewar rigan nada kalan ja hakan yasa taƙara bayyana hasken fatarta, ɗan ƙaramin trolly ɗinta tajawo, sif ɗin kayanta ta buɗe ahankali tashiga  ɗiban kayan tana zubawa acikin trolly ɗin,  wani irin tunanine ke yawo aƙasan zuciyarta, hakanan taji batason barin gidan, duk da kasancewar acikin ƴan kwanin bata ko ganinsa bare jin labarinsa, wani irin kewane ke cinta azuciya,  tanaso taji wannan daddaɗan ƙamshin nasa mai ratsa zuciya, tanaso taga koda gilmawansa ne,  da tunani iri iri acikin ranta haka ta kammala haɗa ƴan kayanta wanda tasan zata buƙata,  gyalen jallabiyan ta yafa akai zuwa jikinta kasancewar yana da ɗan girma, ahankali take sauƙowa daga kan step hannunta riƙe da trolly da kuma school bag ɗinta dake rataye akan kafaɗunta.

Oummu naganinta tace.
"Yauwa kin kimtsa ko, kici abinci sai ku wuce"  da  "To" kawai ta amsa kana ta aje jakakkunan nata ta nufi dinning area, ɗaya daga cikin kujerun wajen taja ta zauna tare da ɗaukan plate tayi serving kanta,  ahankali take tsakuran abincin tana kaiwa bakinta, sam batajin test akan harshenta,  sama sama take jiyo hiran Oummu da Aunty Muhibbat inda duk maganan tasu akan auren nata ne sukeyi,  itakam har yanzu ganin abubuwa take kamar al'amara, don bata taɓa ganin aure irinnata ba, sam ta rasa awani matsaya take, don ita kanta takasa gane kanta,  ahankali take ɗiban abinci acikin spoon tana kaiwa bakinta,  wani irin baƙon ƙamshin turaren daya shigo hancinta ne yasanyata ɗago kanta takalli cikin falon, idanunta ne suka sauƙa akan sa wanda shigowarsa cikin falon kenan shiɗinma kuma kallonta yakeyi, tarine ya sarƙeta yayinda abincin da takeci ya shaƙe maƙoshinta,  da sauri ya ƙaraso kan dinning ɗin tare da ɗaukan bottle water, ɓalle murfin yayi kana ya miƙo mata, da sauri ta amsa takai bakinta, saida tasha har kusan rabin goran sannan ta ajiye tare da sunkuyar da kanta ƙasa ahankali take maida numfashi don har idanunta saida suka sauya kala sukayi ja.
"Are you okay?" Almustapha wanda yasha ado cikin jan shadda ya tambayeta.
Kanta ta kaɗa masa alaman "Eh"
Murmushi yayi tare da ɗan ranƙwafowa gaf da ita cikin yin ƙasa da murya yace "Ehem ƴan mata kin ruɗe ne saboda kinga nayi miki kyau ko?"
Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi fuskarta ɗauke da mamakin jin maganarsa. Idanunsa ɗaya ya kashe mata tare da zura hannayensa cikin aljihun  wandonsa,  haɗa idanu da suka sakeyi yasanya ta murguɗa masa baki,  murmushine ya suɓuce masa tare da ɗan zaro idanunsa,  ƙasa ƙasa yace "Ni kika murguɗawa baki ko, watarana zaki murguɗawa wanda zai cire bakin gaba ɗaya"  yafaɗi haka yana me ƙoƙarin  komawa cikin falon, bayansa tabi da kallo harya ƙarasa kusa da Oummu ya zauna, miƙewa tayi itama tare da    ƙarasowa cikin falon,  dubanta Oummu tayi cikin kulawa tace "Harkin kammala?"  murmushi tayi tare da ɗaga kanta alaman "Eh" 
Miƙewa Aunty Muhibbat tayi tare da ɗaukan mayafinta cikin kulawa ta dubi Almustapha tare da cewa "Muje ka sauƙe mu ko!"  
Trolly ɗinta ta ɗauka tare da kallon Oummu, itama Oummun kallonta takeyi murmushi tayi mata tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki nima gobe zanzo insha Allah!"
asanyaye ta gyaɗa kanta alaman to.
Almustapha ne ya fara yin gaba, sai Aunty Muhibbat yayinda tarufa musu baya,  har jikin motar Almustapha Oummu ta rakosu, inda Aunty Muhibbat tabuɗe gidan baya ta shiga, hakan yasa dole ta shiga gaba badon taso ba.  Koda suka ɗauki hanya Almustapha da Aunty Muhibbat ne keta hiransu, ita kuwa shiru tayi tana kallon hanya. 

Asokoro  shine unguwar da Hajiya Arabi take, agaban wani tamfatsetsen gate Almustapha ya tsaida motar, nan Aunty Muhibbat tasoma ƙoƙarin buɗe murfin motar, jakanta  ta ɗauka tare da kai dubanta ga Zieyaderh "Muje ko" tafaɗa tana me ƙoƙarin fita daga cikin motan.
buɗe murfin motar tayi itama tare da ɗaukan trolly bag ɗinta, atare suka shiga cikin gidan ita da Aunty Muhibbat, tundaga compound ɗin gidan sukejin tashin ƙamshi kamar wani wanda sukazo kamfanin turare,  ƴan tsirarun ƴan mata ne ke zazzaune awata runfa dake compound ɗin.  kowacce harkan gabanta takeyi,  aunty muhibbat nagaba  tana biye da ita abaya haka suka shiga cikin wani haɗaɗɗen falo,  wata farar mata tamkar balarabiya akyau suka iske zaune acikin falon tana ganinsu ta saki murmushi tare dayi musu barka da zuwa.
ƙarasowa cikin falon sukayi Inda Aunty Muhibbat ta zauna akusa da matar itakuwa Zieyaderh akan sofa ta zauna tare da gaishe da Hajiya Arabi wacce ta kafeta da idanu. Fuska ɗauke da murmushi Hajiya Arabi ta amsa mata tare da duban Aunty Muhibbata tace "Tun ɗazu ae nake zuba idanun ganinku"
Murmushi Aunty Muhibbat tayi tare da cewa.
"Taje school ne yanzu dawowanta, dan Allah Arabi ki gyara mana ita da kyau kinsan amaryace irin tagaban goshinnan"
Dariya Hajiya Arabi tayi tare da cewa "Kada ki damu Muhibbat ina da tabbacin har tukuici saikun bani!"
Dariya Aunty Muhibbat tayi tare da miƙewa tsaye, zaman jakan dake rataye akan kafaɗanta ta gyara tare da cewa.
"Ni zan wuce sai munyi waya" duban Zieyaderh tayi tare da cewa  "Ki kwantar da hankalinki nanma kamar gida yake, ki nutsu kuma amiki gyaran da kyau, idan kinje makaranta banda yawan yawo ki nutsu awaje ɗaya."  kai Zieyaderh ta jinjina mata alaman to.
Ƙwala ƙiran wata mata Hajiya Arabi tayi nan wata ƴar dattijuwar mata taƙaraso cikin falon, nuna mata Zieyaderh Hajiya Arabi tayi tare da cewa ta kaita masauƙi na musamman domin tun yau da dare zasu fara aikinsu.   "To" Matar tace tare da duban Zieyaderh tace "Muje ko" babu musu ta ɗauki trolly ɗinta tabi bayan matar yayinda Aunty Muhibbat kuwa suka fice daga falon ita da Hajiya Arabi. 
Matarnan nagaba Zieyaderh na binta abaya haka suka nufi wani ɗaki,   koda suka shiga cikin ɗakin ɗakine mai girma wanda ke ɗauke da ƴan madaidaitan gado har guda uku masu kyau, sai kuma sif ɗin ajiye kaya da kuma dressing mirror, ƙasan ɗakin amalale yake da wani red carpet me kyau, idanunta ne ya sauƙa akan wasu kyawawan ƴan mata guda biyu wanda ko wacce ke zaune akan gadonta, wayoyinsu ne ahannunsu da alama chatting sukeyi.
Gadon dayake shine na ƙarshe Matarnan ta nunawa Zieyaderh tare da nuna mata inda zata ajiye akwatinta,  saida matar me suna Mama Ladi  ta gwada mata komai sannan tabar cikin ɗakin, haɗa idanu Zieyaderh tayi da ɗaya daga cikin ƴan matan, murmushi tayi mata tare da cewa "Sannu" itama Zieyaderh'n murmushi tayi tare da ɗaga mata kai alaman yauwa.
Trolly ɗinta ta ajiye tare da warware mayafin dake jikinta, kasancewar lokacin sallan magriba ya gabato anata ƙiraye ƙirayen sallah hakan yasanya ta shiga bathroom tare da ɗauro alwala. tana fitowa ta buɗe trolly ɗinta tare da zaro hijab ta sanya,  ɗaya daga cikin ƴan matan da ta samu acikin ɗakin me suna Humaira ne ta miƙo mata sallaya, godiya tayi kana ta shimfuɗa ta gabatar da salla, ba ita tatashi akan sallayan ba sai da ta gabatar da sallan Isha, tana ninke sallayan, Mama Ladi tashigo cikin ɗakin hannunta ɗauke da basket wanda cikinsa ke ɗauke da food flask, da kuma plates guda uku,   dubanta takai ga Zieyaderh inda tace "Idan kinci abinci Hajiya tace ki sameta a falo"  "To" kawai tace tare da cire hijab ɗin dake jikinta. Humaira ce ta jawo basket ɗin gabanta tare da ɗaukan plates ɗin tashiga zuba haɗaɗɗiyar coconut rice dake ɗaya daga cikin food flask ɗin da aka kawo, dubanta takai ga ƴar uwarta mai suna Nina cikin kulawa tace "Hajiyar chatting zakici abinci ne?"
Hankalin Nina nakan waya batare da ta ɗago ba tace
"Aa sai zuwa anjima"
Baki Humaira ta taɓe tare da zuba abincin acikin plates biyu  kana ta ɗaura musu pepper chicken akan coconut rice ɗin, miƙowa Zieyaderh plate ɗaya tayi tare da cewa "Sister ga abinci kici,  sunana Humaira waccar kuma cousin ɗina ce sunanta Nina, ke kuma fa ya sunanki?"
Murmushi Zieyaderh tayi aranta tace "Nasmah two" afili kuwa cewa tayi "Zieyaderh"
"Nice name!" Humaira tafaɗa tana me komawa kan bed ɗinta ta zauna, Zieyaderh kuwa kasancewar ba wani yunwa takeji sosai ba hakan yasa bata wani ci abincin da yawa ba, mayafinta ta ɗauka ta fice don amsa ƙiran Hajiya Arabi, a falo tasamu Hajiya Arabi, wani yellow'n towel Hajiya Arabi ta bata tace tacire kayanta, wani ɗan ɗaki ta shiga ta cire kayan nata tare da ɗaura towel ɗin, kasancewar towel ɗin nada girma hakan yasa ya sauƙo har zuwa kan guiwanta, wani irin kunya takeji amma babu yanda zatayi dole haka ta fita, wani ɗaki suka shiga me girma wanda keta ƙamshin kayansu humra da dai sauran kayan gyaran jiki, kujera Hajiya Arabi ta nuna mata zama tayi akai tare da miƙe ƙafafunta, wani kwalba me ɗauke da wani irin farin ruwa Hajiya Arabi ta ɗauko daga cikin wani glass, ƙarasowa gaban Zieyaderh tayi tare da buɗe kwalban ruwan cikin kwalban wanda ke da masifaffen ƙamshi ta shiga shafawa Zieyaderh agaba ɗaya jikinta har zuwa kan cinyoyinta, bayan ta gama ne tace da Zieyaderh tashafa akan ƙirjinta da kuma cikinta, hakan kuwa akayi ganin idanun Hajiya Arabi ba akanta yake ba yasanya ta zame towel ɗin tashafa akan ƙirjinta har zuwa kan lafaffen cikinta, tana gamawa Hajiya Arabi takuma shafa mata wani ruwa saidai shi kalansa yellow ne saɓanin wancan dayake white, shima balaifi yana da ƙamshi sosai,  bayan tagama shafa mata yellow'n ruwan ta ɗauko wani abu dake cikin wani ɗan bowl kaman kwaɓaɓɓen dulka tashiga shafa mata saidai wannan karon harda fuskanta aka shafa,    wani cup dake cike da wani irin abu kamar zuma Hajiya Arabi ta miƙowa Zieyaderh tare da cewa tatashi tsaye tashanye, cikin ɗari ɗari Zieyaderh takai  cup ɗin bakinta,  amaimakon taji ɗaci saitaji abun nada ɗan zaƙi hakan yasa ta rufe idanunta ta shanyesa tas, tana aje kofin Hajiya Arabi ta ƙara miƙo mata wani shima nasa kalan da ban saidai kuma shi yana da bauri bakamar wancan ba, shima rufe idanunta tayi ta shanye,  still tana ajiye kofin Hajiya Arabi ta miƙo mata wani ɗan kwalba wanda cikinsa ke ɗauke da wani abu kamar zuma saidai shi danƙonsa yazarje na zuma, haka Hajiya Arabi ta dinga ɗura mata abubuwa wani yayi mata dadi wani kuwa akasin haka, saida wannan kwaɓaɓɓen dulkan yayi 1 hour ajikinta sannan Hajiya Arabi ta haɗa mata wani ruwan wanka wanda aka cika turaren wanka acikinsa,  koda tayi wanka wani irin tashin ƙamshi jikinta keyi, bacci takeji sosai hakan yasa agajiye ta nufi ɗakin  su, Nina nanan tana ta aikin chat, yayinda Humaira kuwa ke waya,  wata riga marar nauyi tasanya tare da kwanciya luf akan gado, idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, ahankali kalaman soyayyan da Humaira ke faɗawa wanda take waya dashi ke shiga kunnenta, wani irin abune taji ya daki zuciyarta take heart ɗinta yasoma beating da sauri, sake lumshe idanunta tayi kana ta cusa kanta cikin pillow da haka bacci ya ɗauketa.
Washe gari tun 7 tagama shiryawa, tun kafun tasanya komai acikinta Hajiya Arabi ta bata tatacciyar madaran shanu wanda babu ko ɗigon mix acikinta, kamar yanda ta faɗa mata tace kada tasha azaune, atsaye tashanye gaba ɗaya madaran sannan taɗanci soyayyen dankalin da aka kawo musu amatsayin break fast, bakwai da rabi daidai Kamalu driver yazo don kaita makaranta.  Gaba ɗaya yau bata je ko ina ba koda suka fita break basuje ko ina ba acikin aji sukayi ciye ciyensu, su Nasmah sai tsokananta suke wai tafara ƙamshin amarci.  Koda aka tashesu Kamalu driver ne yazo ya maidata gidan Hajiya Arabi,  tana cire uniform tayi wanka ko abinci bata ciba Hajiya Arabi ta miƙo mata wani tsumi, saida tasha wasu haɗin magunguna kusan kala uku sannan taci abinci, kasancewar agajiye take hakan yasa ta kwanta tare da ɗaukan littafin Agric Science ɗinta tana karantawa kasancewar gobe zasuyi test,    Nina ce tashigo cikin ɗakin gaba ɗaya jikinta sanye da dulka, kallon Zieyaderh tayi tare da cewa "Hajiya tace kije kina da baƙuwa"
"To" kawai tace kana ta sauƙo daga kan gadon, sosai taji daɗi ganin Oummu da tayi, da sauri ta ƙarasa tare da rusunawa agaban Oummu'n cikin girmamawa tace "Oummu barka da zuwa"
Murmushi Oummu tayi tare da cewa "Yauwa Zieyaderh ya kwanan baƙunta?"
"Alhamdulillah ta amsa tana murmushi.
Daidai lokacin Hajiya Arabi ta fito daga cikin ɗakin ta, nan tazauna suka ɗan taɓa hira da Oummu, koda Oummu tazo tafiya har bakin mota Zieyaderh ta rakata, nan Oummu ta buɗe jakarta tafito da kwalin waya ƙirar iphone 9 plus, miƙawa Zieyaderh tayi tare da cewa "Kiriƙe wannan akwai sim card aciki kuma nayi miki setting komai, zanna ƙiranki muna gaisawa, idan kina da buƙatar wani abuma ki sanar dani"
Amsan wayar tayi tare da yiwa Oummu godiya, nan Oummu ta ɗora da cewa "Naƙira shugaban makarantarku munyi magana, kasancewar lokacin da zaku fara exam zai kama lokacin biki, saboda haka nasanar masa komai yakumace ba matsala za'asa wata ɗaliba tayi miki, ki kwantar da hankalinki, idan kina da damuwa ki sanar dani kinji!" Oummu taƙare maganar cike da lallashi.
Murmushi Zieyaderh tayi tare da cewa "Nagode sosai Oummu"

Saida taga tafiyansu Oummu'n sannan takoma cikin gida, zama tayi akan gadonta tare da buɗe kwalin wayar,  dalleliyar iphone 9 plus grey colour ne ta bayyana acikin kwalin,  yayinda aƙasan kwalin aka shumfuɗe fararen ƴan dubu dubu wanda aƙalla zasu kai 8k, murmushi kawai tayi tare da ciro wayan kana ta maida kwalin ta rufe tasan Oummu tayi hakane saboda tasan idan ta bata kuɗin bazata amsa ba. Kasancewar komai arubuce yake kuma yanzu kanta awaye yake hakan yasa ta kunna wayar tare dayin downloading games ɗin da zasu ɗebe mata kewa. Koda tayi sallan Isha wajen Hajiya Arabi ta nufa, yau kam gyaran da akayi mata har ya zarce najiya, sai kusan wajen 10 sannan tayi bacci.

Wasa wasa yau kwananta 4 agidan Hajiya Arabi wani irin gyaran jiki ake mata na mussaman, acikin ƴan kwanakin huɗun jikinta ya soma sauyawa fatarta taƙarayin smooth yayinda face ɗinta ke shining, acikin  kwanki huɗunan  kullum da safe tatacciyar madaran shanun take fara sha kafun tayi break fast, wasu irin haɗaɗɗun magungana Hajiya Arabi ke bata, wanda har ƙarfinsu ya soma taɓa ta, don ayanzu takan yawan jin kanta acikin wani irin yanayi,, ɓangaren su Oummu kuwa shirye shiryen biki suke sosai hidima suka shiryawa bikin ba ɗan kaɗan ba.

*Singapore*

Kwance yake akan tangamemen gadonsa yayinda gaba ɗaya jikinsa ke lulluɓe da blanket, ahankali ya buɗe kyawawan idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja, hannunsa yasanya ya dafe kansa dake masa masifar ciwo,  yau kwanansa uku kenan yana fama da wani irin zazzafan zazzaɓi, da zaran yayi tari kuwa saidai yaga jini ta bakinsa na fita,   wani irin ciwo yakeji sosai ajikinsa,  yau kwanansa uku banda ruwa baisa komai acikinsa ba, ahankali yaɗan tashi tare da jingina bayansa da saman gadon, rumtse idanunsa yayi tare sanya hannunsa ya riƙe saitin heart ɗinsa dake beating da sauri,  Numfashi  me ɗumi ya fesar, sai kuma ga tari ya biyo baya farin handkerchief yasanya yashiga goge jinin dake fita daga bakinsa, tsabar zafin zazzaɓin dake jikinsa har karkarwa laɓɓan bakinsa keyi, cikin dakiya ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, ahankali ya sauƙo daga kan gadon, sanye yake da long jeans black colour, kasancewar baisanya riga ba hakan yasa murɗaɗɗun muscles and 6 packs ɗinsa suka bayyana, cikin dauriya tare da aro jarumta ya nufi toilet, agaban sink ya tsaya tare da kunna fanfo ya wanke

30 / 48