Sooraj Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   24 / 48

69K to 72K   out of 142.5K words

kawai, alaman ta gamsu.   Oummu na fita daga ɗakin. Zieyaderh ta fashe da kuka, sosai tayi kewar babanta, ko awani hali yake ciki Allah masani?  duk da cewa bai nuna mata ƙauna ba, amma ita har gobe, akwai ƙaunarsa acikin jininta, saboda koba komai Uba Uba ne koda baikasance na gari ba.

MONDAY

Cikin yanayi naɗan sauri sauri yake tafiya, don 8 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa garin Lagos.  Sanye yake da black and white suit wanda suka matuƙar yi masa kyau, black cover shoe ne ƙiran kamfanin Gucci sanye aƙafansa me tsadan gaske. ƙamshi kawai yaketa zubawa, yayinda gashin kansa keta shinning na mayukan da aka shafa masa,  yau kam masha Allah Yayi kyau har ya gaji da haɗuwa. 

Manta biology text book  ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna,  wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake  hannunsa.  Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking,      kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube,  da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya.    Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin.  Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace "Auchhhh!!"  dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne  yasake kamata, baki na rawa tace "Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!"

Baikulata ba haka yasanya hannu ya shiga tattara papers ɗinsa da suka watse.  ganin haka yasa itama tashiga tayasa tattarewa,  gaba ɗaya ƙamshinsa ya jefata acikin wani irin yanayi, jin kanta take cikin wani  baƙon yanayi, har wani iska ne ke shiga jikinta.   Idanunta ne yakai kan wani papers da iska ke shirin kaɗasa wani wajen, da sauri takai hannunta zata kamo paper'n,  shima hannunsa yakai batare

da yayi zato ba yaji hannunsa ya sauƙa akan nata, atare sukaji wani shock da sauri yajanye hannunsa daga kan nata tare da ɗaukan paper'n ya miƙe tsaye, baijira komai ba ya nufi wajen motarsa wanda tuni dama driver na jiransa, yana shiga gidan baya driver yayiwa motar key suka fice daga cikin gidan.   Saida taji alamun fitansu sannan ta iya miƙewa tsaye daga tsugunnen da take,  batare da ta saniba wani murmushi ya bayyana akan fuskarta take kuma saiga hawaye sun ziraro daga cikin idanunta, Wallahi ko za akasheta bazata iya fassara abun da takeji dangane dashi ba, tausayi ne? rauni ne? Ita duk takasa ganewa, tasan koma menene tabbas abun da takeji akanshi na musammanne,  idanunsa kaɗai da ta kalla ya sanya taji wani iri ajikinta, tabbas da zata samu mai bata amsar abun da takeji dangane dashi da taso hakan fiye da komai, watarana idan tagansa sai taji kamar tasanya masa kuka, watarana kuwa jitake kamar taje da gudu ta shige jikinsa tayi kuka sosai, wataƙila hakan zai ɗan sama mata salaman abun dake ranta.    Sam tama manta da cewa text book zata ɗauko sai kawai ta koma tashiga mota.
Luf tayi ajikin kujeran motar,  ƙamshinsa da har yanzu takejinsa acikin hancinta shiyayi fatali da duk wata nutsuwarta, sam tarasa me yasa takejin ƙamshin nasa har yanzu duk da cewa baya tare da ita,  hannunta takai tashafi fuskarta, sai alokacin ta gano daga inda ƙamshin ke fitowa, sake kai hannunta kan hancinta tayi tare da shunshunawa, tabbas hannunta da ya taɓa ne ke ƙamshin, wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, ɗaura hannun tayi akan fuskarta tare da lumshe idanu, ahaka har suka iso cikin school ɗin.  Yau kam tayi late duk da cewa bahaka tasoba, don sunada biology, kuma shine first period, bakuma taso tayi missing lecture ɗin biology ko kaɗan,     ai kuwa tana zuwa bakin class ta iske malami aciki, da ƙyar ya barta tashiga cikin ajin, tana zama akan chair ta sauƙe ajiyar zuciya, hannu Nasmah tasanya ta ƙasa ta muntsineta akan cinyarta,   ƙasa ƙasa tayi dariya tare da rumtse ido alaman taji zafin muntsinin, hakan da tayi kuma sai ya tuna mata da MR.HELPER ɗinta, yanayin yanda ya rumtse idanunsa da kuma yanda yace "Auchhh!!" Baƙaramin kyau yanayin yayi masa ba, musamman yanda pink lips ɗinsa suka motsa abun saiya ɗauki hankalinta, sai ayanzu moment ɗin kedawowa cikin brain ɗinta da kyau, wani murmushi tasake tare da lumshe idanunta.
"Kenan shima yanajin zafi idan abu yasameshi?" A zuciyarta ta tambayi kanta, wani murmushin ta sakeyi alokacin da ta tuna da kyawun idanunsa, a iya tsawon rayuwarta itakam bataga irinsa ba, bata kuma tunanin zata taɓa ganin wani irinsa.    Ataƙaice dai  har biology teacher'n yafita, bata tsinci komai daga cikin darasin daya koyar ba,  gaba ɗaya hankali da tunaninta yau akan Mr.Helper yake. 
Su Shukra da kansu yau sun fuskanci cewa tana cikin farinciki, don koda aka fita break zagewa tayi tayita zuba musu surutu. 

7:59 AM

Gyara zama yayi tare da ɗaura sit belt ajikinsa, bayansa ya jingina ajikin luntsumemiyar kujeran dake cikin jirgin, 8:00 daidai jirginnasu ya ɗaga zuwa sararin samaniya,  tafin hannunsa yakai ya rufe fuskarsa, ko hakan zaisa yaɗan rage stress ɗin dayake ciki, ahankali yaji wani baƙon ƙamshi na ratsa cikin hancinsa yana me cakuɗa da numfashinsa, mamakine yakamasa don sam baisan daga ina ƙamshin ke fitowa ba, ɗan waigawa bayansa yayi,  dayake  ɓangaren business class ne kowa sha'aninsa kawai yake, babu kowa kuma akusa dashi dasai yace na kusa dashine ke ƙamshin.  Sake shunshuna hannunsa yayi, sai alokacin ya tabbatar da cewa tabbas hannunsa ne ke ƙamshin, bawani turarene me ƙarfi ba, irin dai turaren nanne da idan mutum yasa saima ka matso kusa dashi kafun kajiyo ƙamshin.   "Itace!" yafaɗa in a silent voice ɗinsa, sake kai hannun kan hancinsa yayi tare da ɗan taɓe lips ɗinsa.   Azuciyarsa yace.
"Su ƙamshi manya"   Jarida ya ɗauka yashiga karantawa tare da watsar da duk wani tunani dake ransa.

Hadari ne sosai ya haɗu agarin kasancewar anacikin yanayi na damuna,  3:30 pm, fitowarsu sallan La'asar kenan.
Tana idar da sallan ta fito daga cikin masallacin, sosai take matuƙar son yanayi irin wan

nan,  ahankali sanyin iska ke busa ko ina, hijab ɗinta iska keneman yayewa, da sauri tasanya hannuwanta ta kameshi ƙam ajikinta.  Yanayin na fusgarta hakan yasa kai tsaye ta nufi wajen da garden ɗin makarantar yake.
Ƴan tsirarun ɗalibai ne awajen, kowa harkan gabansa kawai yake. Gefe da garden ɗin wasu kujeru ne masu kyaun gaske da aka tanada don zama,  tana zama aka soma yayyafi hakan yasa tatashi da sauri don komawa cikin makaranta.    Idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsaye yake ya sanya duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, idanunsa ƙyam akanta fuskarsa ɗauke da beautiful smile,   cike da mamakin ganinsa tasaki murmushi tare da sanya hannu ta kare kanta, kasancewar zuwa lokacin ruwa ya fara sauƙa kaɗan kaɗan.   ganin haka yasanyashi takowa yazo gab da ita, cikin sexy voice ɗinsa yace.
"Kina tsoron ruwa ne?"
Murmushi tayi wanda har saida ya bayyana white teeth ɗinta, kanta ta kaɗa masa alamar "Eh" ruwane ya ɓarke me ƙarfin gaske hakan yasa lokaci guda ta ruɗe, shikansa ƙarfin ruwan yabasa mamaki, hannunta ya kama zuwa wani ɗan rumfa dake wajen, duk da shigarsu rumfar iya kawunansu kawai ruwan zai tare amma banda gangar jikinsu.   Cikin yanayi na tsoro ta naɗe hannayenta akan ƙirjinta,  kallonsa tayi da fuskarta dake jiƙe da ruwa.  Murmushi yayi mata tare da ɗage mata giransa ɗaya, itama murmushin tayi masa tare da sake takure kanta waje ɗaya, don bawai sun tsirane daga ruwanba,  har yanzu yana dukan jikinsu, tuni uniform ɗinta yajiƙe sunbi jikinta sun lafe, shikansa Pharouk gaba ɗaya ya jiƙe duk da cewa akwai denim Jacket ajikinsa hakan bai hanashi jiƙewa ba.   bakinta har rawa yake saboda sanyi. 
"Zieyaderh!" yaƙira sunanta akasalance.

Ɗago fuskarta tayi ta kalleshi,  idanunsa ya sauƙe akan beautyful lips ɗinta wanda suka jiƙe suke kuma ɗigar da ruwa,  wani irin tashi yaji tsikar jikinsa yayi, take lissafin kansa suka shiga kuncewa, wani irin saliva dake maƙale a maƙoshinsa ya haɗiya, sam bata ɗauke idanunta akansa ba, yanayin sanyin da take ji yasanyata lumshe idanunta tare da ɗan buɗewa alokaci guda, hakan da tayi baƙaramin kyau yaƙarawa face ɗinta ba, take yaji wani irin different feelings na sauƙa ajikinsa, ji yake kamar yajawota jikinsa ya bata professional kissing, amma mene sunansa idan yayi hakan?  jingina bayansa yayi da jikin bango tare da lumshe idanunsa, bugun zuciyarsa ƙaruwa take, wani irin maganaɗisun sha'awarta ne ke fusgarsa,  lokaci guda mood ɗinsa ya sauya.  Cikin zaƙuwa da tsayuwan Zieyaderh ta juyo ta kalleshi acikin yanayinta na shagwaɓa tace "Am tired!!"  Ahankali ya buɗe idanunsa wanda sukai ja ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon kallon cikin idanunsa da tayi,  batasan irin wannan yanayin ba hakan yasa ahankali tace  "Are you okay?"

Akasalance yayi murmushin daya bayyana dimples ɗinsa.
"Yes am okay!" yafaɗa yana me ƙare mata kallo,  murmushi tayi masa sannan ta juya tacigaba da kallon ruwa sam ta manta bata maida hannuwanta ƙirjinta ta kare baiyanar dasukayi ba, don saboda yanayin sanyin da ake ciki yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa, hakan yasa nipples ɗinta ma suka miƙe tsaye, har idan kayi  mata kallon tsab zaka iya ganinsu.   Sauƙan idanunsa akan ƙirjinta baƙaramin gigita masa tunani yayi ba, take yaji tunaninsa ya tsaya cak, da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da sanya baki ya cije laɓɓansa. (Nasan team RAJ, zasuce inama da ita da Sooraj ne😝)    Wani irin tsawa da aka buga ne ya matuƙar firgitata har batasan sanda ta dawo baya da sauri ba, sambata kula ba ta faɗa jikinsa, ƙamƙame jikinta tayi ƙaƙam tare da rumtse idanunta.   "Innalillahi" kawai take ambata acikin zuciyarta don ta tsorata,  ashe ba ita kaɗaice ke ambatan hakan ba harda Pharouk don alokacin da bayanta ya mannu da ƙirjinsa baƙaramin ruɗewa yayi ba, har numfashinsa saida yashiga seizing na ƴan wasu minutes.    Hanneyansa dake rawa yaɗaura akan shoulder ɗinta, hakanne ya bata damar dawowa cikin hankalinta, da sauri ta matsa gefe, cikin wani irin kunya ta jawo hijab ɗinta ta rufe fuskarta.  "Me na aikata haka?" ta tambayi kanta cike da nadama.

Matsowa yayi gab da ita tare da sanya hannu ya ɗ

ago haɓanta, hijabin ya ja baya fuskarta ya bayya, da sauri ta kulle idanunta don batajin zata iya haɗa idanu dashi. 
Murmushi yayi mata ahankali ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta,  kiss yayi mata a forehead ɗinta,  tare da kai bakinsa daidai saitin kunneta ahankali yace  "Ki kulamin da kanki!"  Yana gama faɗan haka ya juya acikin ruwan  ya tafi, yayi hakane saboda matuƙar ya ƙara some minutes awajen, zai iya hugging ɗinta.  (Chab lallai Pharouk yau zakasha zagi awajen ƴan team ɗin SOORAJ)

Buɗe idanunta tayi ahankali cike da fargaba da kuma tsoron abun daya mata, babu wani namiji daya taɓa yi mata kiss saishi, mekenan hakan yake nufi? ta tambayi kanta cike da mamaki,  kallon bayansa tayi don zuwa yanzu yayi mata nisa, tafiya yake kamar baidamu da ruwan dake dukansa ba.    

*SOORAJ*
Tsaye yake acikin wata baranda, dagashi sai wani white crazy jeans dake sanye ajikinsa, bashida ko riga sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana,  glass cup ne ahannunsa wanda ke ɗauke da ruwan inibi,   ruwa da iska ake sosai, amma ko kaɗan baijin wannan sanyin ajikinshi.  Hakanan yakejin kansa cikin wani bad mood, baikuma san dalilin hakan ba, tunanin dake maƙale azuciyarsa ayanzu yafi komai damunsa, meyasa yake ganinta acikin idanunsa? meyasa yakeji tamkar anrubuta wani abu daya shafeta acikin zuciyarsa?  yana da buƙatar sanin meyakeji, da kuma dalilin dayasa yakejin hakan acikin rai da zuciyarsa. 

Ahankali ƙarfin ruwan ke tsagaitawa, ganin haka yasa cikin sauri ta nufi farfajiyan makarantar, harda ɗan sassarfa take haɗawa wajen shigewa cikin ajinsu,  Nasmah da Shukra dake tsaye bakin window sukayo wajenta da sauri cikin damuwa suka haɗa baki wajen tambayanta ina taje "Garden" ta basu amsa ataƙaice.   Sunyi mamakin hakan amma sai kawai suka share suka cigaba da hiransu.

Ruwan na tsagaitawa aka tashesu ko 5 ma batayi ba, saboda sosai garin ya ɗau sanyi.     Atare suka fito ita dasu Nasmah,     daidai lokacin wata baƙar Car ƙiran Jeep ta kunno kai cikin makarantar,   tsayawa sukayi a compound ɗin makarantar Zieyaderh na ta baza idanu ko zata hango Kamalu driver.    Ƙasa yayi da glass ɗin motar tare da kafeta da idanunsa, ahankali ya danna horn, hakanne ya ɗauki hankalin ɗalibai da yawa har kowa yajuyo yana kallonsa, idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsananin mamakine ya kamata, tabbas tasan ita yazo ɗauka, to ina Kamalu driver? ya ma akayi yasan antashesu?  Duk bata dame amsa mata waƴannan tambayoyin, hakan yasa tayiwa su Nasmah sallama tanufi inda yake.   Tana buɗe murfin motar wani sassanyan ƙamshin turare ya daki hancinta, saidai wannan turaren sam ba irin wanda yake gigita tunaninta bane.   Ɗan satan kallonsa tayi tare da cewa "Ina wuni"

Bai amsa mata ba sai dai murmushi da ya bayyana akan fuskarsa.    Har suka soma tafiya babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu, saidai kuma yana yawan satan kallonta lokaci zuwa lokaci, aranta mamakin yanda halinsu ya kusan zuwa ɗaya take.   "Kenan su duka familyn su haka suke?" ta tambayi kanta azuci.  "Uhmmm gwara wannan ma ae yana murmushi amma wancan Mr.Helper ɗin kam, ko murmushinsa bantaɓa gani ba" Ita kaɗai take magana da zuciyarta  har suka iso gaban wani tafkeken mall.

(Najidaɗin addu'o'in ku agareni, nagode Allah yabar ƙauna💜
then Gaskia kunbani dariya😅 wae don nace nan gaba abun dazai faru acikin book ɗin bazai muku daɗi ba shine duk kuka ruɗe haka, hahhhhh ku kwantar da hankalinku wasa nake muku😝)

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 36*

Agaban ƙaton mall ɗin yayi parking motar tare da dubanta, murmushi ɗauke akan fuskarsa yace  "Muje ki rakani sayayya"

Mamakine ya bayyana akan fuskarta, amma  sai ta share bata nuna ba, buɗe murfin motar tayi tare da fitowa waje.  Yana gaba tana biye dashi abaya,  haka suka nufi cikin ƙaton mall ɗin.   Direct ɓangaren kayayyakin  mata suka nufa,   ita dai binsa kawai take, aranta  tana me mamakin ganin sun shigo wajen sayayyar mata,   ɗan juyowa yayi ya kalleta,  matsawa gefe yayi tare da yi mata nuni akan ta shige gaba. Kallonsa tayi alaman me hakan ke nufi.    "Muje mana ko bazaki tayani zaɓa bane, matata zan sayawa kuma agemate ɗinki ce, shiyasa nafiso ki zaɓa mata masu kyau!"  Ya faɗi maganar yana me jujjuya wata brown ɗin abaya dake hannunsa.  Murmushine ya bayyana akan  fuskarta.
"Kenan dama yana da mata?" tayiwa kanta tambayar cike da ɗan mamaki.   Jin cewar matarsa zai sayawa, yasanya duk wani abu da tagani idan ya mata kyau saita ɗauka, dogin riguna kala uku ta zaɓa masa masu kyaun gaske, wanda suke asalin ƴan dubai new designer.    Da ace tasan kuɗinsu da bata ɗauka ba, don kowanne kuɗinsa yakai 35k, kaya masu kyau ta zaɓa masa, duk wanda ta ɗauka sai yayi murmushi yace yayi, daga ɓangaren kayayyaki ɓangaren chocolates and sweets suka nufa,  wannan kam shida kansa ya ɗauka, sai ya duba wanda baida zaƙi sosai sannan yake sanyawa acikin basket ɗin dake hannunsa. 
Koda suka kammala, cewa yayi tajirasa awajen da ake biyan kuɗi, komawa cikin mall ɗin yayi ya shiga dube duben ƴan abun da yake da buƙata.

Yana dawowa ya biya kuɗin, wani daga cikin yaran dake aiki awajenne ya kai musu kayan mota. 

 Ahankali yake murza steering motar, yana me gutsuran diary milk chocolate ɗin dake hannunsa, kallonta yayi tare da ɗan sakin murmushi  "Hummm" yafaɗa yana me miƙo mata chocolate ɗin alaman ta amsa.  Murmushi itama tayi masa tare da  kaɗa kanta alamar "A'a"

"Bafa kyauta bane, gutsura zakiyi ki bani!" ya faɗi haka yana me mayar da chocolate ɗin bakinsa.

Idanunta ta waro cike da mamaki, sai kuma abun yabata dariya wanda har hakan yasa ta dara,  kallonta yayi tare da cewa "Kina mamaki ne? bazan iya baki duka bane shiyasa!"   Yayi maganan murmushi ɗauke akan fuskarsa.

"Nagode ma"  Tafaɗa tana me gimtse dariyan dake bakinta, gaba ɗaya yasata nishaɗi don yanayin yanda yayi abun sai yazama tamkar wani small babyyy. 
Daga haka babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu har suka iso gida.    ƙoƙarin buɗe murfin motar take  muryarsa ya dakatar da ita, inda yake cewa tashiga da kayan da suka sayo ciki,   gidan baya inda aka sanya kayan ta buɗe tare da ciro ledodin ta wuce cikin gidan da su.  Bata samu kowa afalon ba hakan yasa kai tsaye ta wuce  sama,  tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin Oummu tare dayin  knocking.     "Yes,Come in!" Oummu dake ciki ta bada amsa ataƙaice.  Tura ƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama.  "Oummu naganinta ta saki murmushi tare da cewa.
"Ƴan makaranta andawo kenan?"

Murmushi itama tayi cike da girmamawa tace "Eh nadawo, Oummu sannu da gida!"

"Waƴannan ledodinfa na menene?" Oummu ta tambaya fuska ɗauke da mamaki.

"Ummmm dama Ya Almustapha ne yace nashigo dashi ciki!" tafaɗa cikin sanyin murya tana me aje ledodin.

Murmushi kawai Oummu tayi tare da cewa  "Aini nace yaje ya ɗaukoki, kasancewar naga anyi ruwa garin duk yaɗau ki sanyi, gashi Kamalu ma bayanan, ki cire uniform ɗin sai kici abinci ko!"

Kai ta kaɗa alamar "To" sannan ta juya ta fice daga cikin ɗakin.

Tana shiga ɗaki ta soma cire uniform ɗin, gaba ɗaya wani irin sanyi takeji, ruwan daya daketa baƙaramin shiga jikinta sanyinsa yayi ba, gashi harwani ciwo ciwo takejin kanta nayi.  Da ruwan ɗumi tayi wanka kana ta sanya wata doguwar riga me kauri, rigan irin jallabiyannan ne na mata, amma tana da kauri sosai, sannan kuma

24 / 48