Author : Maman Teddy Category : Romance
zuciya Sooraj ya sauƙe haɗe da cewa "Next week zanje USA zan taho dasu"
Kai Mas'oud ya jinjina cike da gamsuwa sannan yace.
"Amma baka karɓi ribanka na wannan month ɗin bafa"
Shiru yayi baice komai ba, aƙalla yaɗauki kusan 4 minute bai tankawa Mas'oud ba, ganin haka yasa Mas'oud yin murmushi kawai ya cigaba da shan tea ɗinsa.
Ganin bazai iya shan tea din bane yasanya shi miƙewa tsaye, yana ƙoƙarin barin wajen Mas'oud yace.
"Inason muyi magana dakai"
Komawa yayi ya zauna tare da ɗaukan wayarsa ya soma latsawa "Inaji!" yace ataƙaice.
"Aure nakeso nayi" Mas'oud yafaɗi haka yana wata ƴar dariya.
Ajiye wayan Sooraj yayi tare da dawo da duk wani attention ɗinsa ga Mas'oud.
"Aure kuma?" ya tambaya da ɗan mamaki.
"Eh Aure mana, gaskia Raj na gaji, shekaru 29 fa ba wasa ba, ko so kake na zauna sha'awa ta kasheni bansamu na kawar da ita ba?" Mas'oud yafaɗi haka yana mai kafe Sooraj din da idanu.
Sunkuyar da kai ƙasa Sooraj yayi tare da cije laɓɓansa, wani irin abu mai ƙuna yaji acikin ƙirjinsa, ahankali ya ɗago kansa ya kalli Mas'oud ɗin cikin wata irin murya kamar mai koyon magana yace. "Sha'awa!"
"Eh sha'awa, banason na faɗa halaka Raj, amma seriously ina da buƙatar mace akusa dani, ina da buƙatar zama cikakken mutum nima, inaga kawai zan tura su Baba gidansu Aisha, su tambayomin izinin aurenta, inaga hakan shine mafita, amma kai maikagani?" Mas'oud ya tambayi Sooraj.
Wani murmushi Sooraj yayi, wanda shi kaɗai yasan menene meaning ɗin murmushin nasa, leɓensa na ƙasa ya sake ɗan ciza, tare da fesar da iska ta bakinsa.
"Allah Ya sanya Alkhairi!" yafaɗa ataƙaice.
"Ameen" Mas'oud ya amsa yana maison karantar yanayin da Sooraj ɗin ke ciki, sai dai kuma sam ya kasa gano wani irin yanayi Sooraj ɗin ke ciki, saboda Sooraj murɗaɗɗen mutum ne, zai maka wahala gane gabansa da bayansa.
"Abba ya faɗamin yanda kukayi dashi, ina fata dai zakayi abun da ya keso?" Mas'oud ya tambayi Sooraj.
Miƙewa Sooraj yayi daga kan dinning ɗin, tare da ɗaukar wayarsa ya bar wajen. Da kallo Mas'oud ya bisa har ya shige ɗakinsa, kai kawai Mas'oud ya girgiza, sannan yadawo cikin falon ya zauna.
Yana shiga cikin ɗakinsa ya rufo ƙofar gam, jingina bayanshi yayi da jikin ƙofar tare da lumshe idanunshi, wani iri ya keji acikin jikinsa, baijin ayau zai iya ɓoye rauninsa. "Inama da ace zai iyayin kuka, inama da ace akwai wani wanda zaiyi sharing ɗin damuwarsa dashi, inama da ace zaiji abun da Mas'oud ya keji." Abun da yake faɗa acikin ransa kenan. Hanu yasa ya dafe saitin ƙirjinsa da keyi masa zafi. Aƙalla ya ɗau kusan sama da mintuna 10 tsaye ahaka, da ƙyar ya iya jan ƙafafunsa ya zauna akan gado, har yanzu idanunsa a rufe suke, jin kansa yake nayi masa ciwo, kwanciya yayi akan gadon tare da buɗe idanunsa, numfashi yake fitarwa a hankali.... Saida yaji yaɗan dawo normal sannan yatashi ya fita falo, can ya samu Mas'oud, sake ɗan tattaunawa sukayi kafun daga bisani suka bar gidan baki ɗaya.
Gumi ne keta fitowa daga jikinta, zaune take agefen gado ta takure jikinta waje ɗaya, wani irin ciwo mararta da cikinta keyi mata, sake matse ƙafafunta tayi, laɓɓanta kuwa sai rawa suke kamar wata wacce take jin sanyi, ahankali sautin kukanta ke tashi acikin ɗakin, jin mararta take kamar zata ɓalle ga zazzaɓi mai zafin gaske da ya rufeta. Jin bazata iya daure ciwon ita kaɗai bane, yasa ta tashi a daddafe ta nufi falo. Tana kaiwa tsakiyan falon ta faɗi a wajen tare da sakin wani ƙara, ciwonne ya ta so mata gadan gadan, kwanciya tayi aƙasa tanata mutsu mutsu da ƙafafunta yayinda ciwon ke ci gaba da nuƙurƙusanta. Kuka take sosai hatta numfashinta saida ya soma seizing.
Dawowarsu kenan daga Sheraton hotel inda sukaje suka gudanar da wani business ɗinsu, atare suka shigo cikin falon. Akuma daidai lokacinne kukanta ya dira acikin kunnuwansu, a ɗan razane Mas'oud ya kalli Sooraj, shima kallonsa yayi amma sai ya share ya ƙarasa cikin falon, idanunsa yaɗan waro ganin yanda take yashe aƙasa gaba ɗaya ta fita acikin hayyacinta, ɗan kwalin dake kanta ya zame gefe yayinda gashin kanta ya watse akan carpet ɗin dake malale a tsakiyar falon, yanayin yanda yaga takeyi shine abun daya ɗan tsoratashi, domin kuwa ta shiɗe sosai da alama ma bata cikin hayyacinta, amatuƙar tsorace Mas'oud ke kallon Yarinyar yana kuma kallon Sooraj, koda wasa bai taɓa tunanin Sooraj yana tare da yarinyar ba, a iya tunaninsa Sooraj yajima da sallamanta ta kama gabanta, wani irin bahagon tunani ne ya ɗarsu acikin ran Mas'oud, bakinsa cike suke da tarin tambayoyi amma dole ya adana tambayoyinsa.
Ƙarasawa inda take yayi haɗe da ɗan durƙusawa hanunsa yakai yaɗan bugi fuskanta "Ke!" ya faɗa yana mai sake ɗan tattaɓa fuskarta.
Wani irin nishi tayi take kuma gaba ɗaya jikinta ya sake komai nata ya daina motsi. Ya ɗan razana kaɗan da al'amarin nata, ɗaukarta yayi caɗak ajikinsa ya nufi ƙofar fita daga falon. Tsananin mamaki shiya hana Mas'oud rufa musu baya, tsayawa yayi ya kasayin komai kamar wani statue, ganin tsayuwar baza ta kai mishi ba, yasanya shima ya rufa musu baya, lokacin da ya fita waje har Sooraj ya sanyata acikin mota yana ƙoƙarin shiga gidan driver, da sauri Mas'oud yaje ya shiga motar ɓangaren mai zaman banza. Gudu sosai Sooraj keyi akan titi mintuna kaɗan suka isa asibiti, likitoti ne suka karɓeta sukayi ciki da ita.
Zama yayi akan wata kujera tare da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa. Agefen Sooraj Mas'oud shima ya zauna, shiru yayi ko wanne daga cikinsu da irin nazarin da yakeyi acikin ransa, tambayoyi ne cike azuciyar Mas'oud, shi kuwa Sooraj ya marasa wani tunani zaiyi, abubuwa sunyi masa yawa, ahankali idanunsa suka kaɗa sukayi jajur dasu, tananne kawai zaka iya fahimtar tarin damuwan da yake ciki. Wani likita ne ya fito daga cikin ɗakin da aka kwantar da Ziyada, ce wa yayi su Sooraj ɗin su sameshi a office ɗinsa, babu musu suka tashi suka rufa masa baya.
Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe abayyane tare dayin ƙasa da kansa.
Mas'oud ne yayi ƙarfin halin cewa "Yanzu likita wani hali take ciki?"
Gyara zama Likitan yayi tare da cewa.
"Kamar yanda na faɗa muku a farko, ba wani babban matsala bane, yawancin mata sukan samun irin wannan matsalolin idan zasu fara period, to itama tana ɗaya daga cikin irin waƴannan matan, amma babu wani damuwa zata warke insha Allah, Yanzu haka ta samu bacci, da ta farka kuma zamu baku Sallama, ga wannan saiku sayo shine magungunan da za tana sha" likitan ya faɗi haka yana me miƙowa Mas'oud wata ƴar farar takarda da yayi rubutu ajiki, amsa Mas'oud yayi tare da ɗan satan kallon Sooraj wanda har yanzu kansa ke ƙasa bai ɗago ba. Hanu dukansu suka miƙawa likitan suka sakeyin musabaha daga haka suka fice daga cikin office ɗin, direct wajen da ake biyan kuɗi Sooraj ya nufa, kuɗin gadon da aka kwantar da ita ya biya, sannan suka nufi pharmacy. Bayan sun karɓi maganin Sooraj ya sake biyan kuɗi, direct motarsa ya nufa, ganin haka yasa Mas'oud ya bi bayansa. Ƙoƙarin buɗe murfin motar yake, muryar Mas'oud ta dakatar dashi. ɗan tsayawa da abun da yakeyi yayi tare da juyowa ya fuskanci Mas'oud ɗin.
Shima Mas'oud fuskantar Sooraj ɗin yayi haɗeme da cewa.. "Wacece ita awajenka? Sannan mai yasa ka ajiyeta agidanka? Me wannan rayuwar da kukeyi take nufi SOORAJ ?" Mas'oud yayi masa duka waƴannan tambayoyin alokaci ɗaya.
(Sorry🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 17*
Buɗe murfin motar yayi ya shiga, batare da yace wa Mas'oud dake tsaye ƙala ba, zai rufe murfin motar ne, Mas'oud yayi saurin riƙe murfin ransa aɗan ɓace yace.
"Wai hakan da ka keyi me yake nufi ne Sooraj? me kake tunani idan su Abba sukaji abun da ka aikata? menene amfanin hakan!!"
Wani iska ya fesar daga bakinsa, tare da jingina bayanshi da jikin kujeran motar.
"Mai kakeson ji daga gareni Mas'oud?" yafaɗi haka cikin wata murya mai sanyi.
A ƙufule Mas'oud yace.
"Bansani ba" Juyawa Mas'oud yayi afusace yabar wajen, da ƙafansa ya nufi hanyar fita daga cikin asibitin, Sooraj na kallonsa ya tari taxi ya shiga, yana ganin tashin taxi ɗin ya jawo murfin motarsa ya rufe, kifa kansa yayi akan steering motar, tare da sauƙe wata ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, ya ɗauki kusan mintuna 6 ahaka, kafun daga bisani ya ta da motarsa ya fice daga cikin asibitin. Direct wani super market ya nufa, zama yayi akan wata kujera, tare da umartan wata ma aikaciyar wajen da ta haɗa masa duk wani abu da tasan mace na da buƙata, kama daga kan suturun sawa da dai sauransu, take ita kuwa tashiga aikinta, kaya masu kyau ta jidar masa hadda su pants, kasancewar tasan duk wata mace indai ta girma to tana da buƙatarsu, bai da mu da yawan kuɗin kayan ba haka ya cire ya biya, yaran dake aiki a wajen su suka kwashe kayan suka kai mishi cikin mota.
Kafun ya koma asibitin saida ya biya ta wani hotel yayi take away, sannan ya ɗauki hanyar komawa asibitin. Yana shiga asibitin direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.
Tana kwance tana baccinta cikin kwanciyar hankali.
Zama yayi akan wata kujera dake gefen gadon tare da lumshe idanunsa. Kamar jiran zuwansa take ahankali ta ɗan soma motsawa, jin motsinta da yanda numfashinta ke fita ne, ya san yashi buɗe idanunsa, haɗe da maida kallonshi gareta.
Ahankali ta soma ɗan ware manyan idanunta harta buɗesu tarwai, saidai kuma kallo ɗaya zakayi mata kasan taji jiki, domin kuwa hatta ƙwayan idanunta saida suka sauya kala, sunyi wani fari fat dasu.
Tashi tayi ta zauna tana mai ɗan cije laɓɓanta, sam batasan da cewa yana cikin ɗakin ba. "Aushhh" taɗan saki wani ƙara, saka makon murɗawan da taji maranta yayi, ɗan yarfe hannuwanta ta somayi, tare da soma yunƙurin sauƙa daga kan gadon, Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna, ji tayi gabanta ya wani irin faɗuwa, da sauri tayi ƙasa da kanta, tare da haɗiyan wani yawu dake maƙale a maƙoshinta.
Aƙalla yaɗauki kusan 50 second yana kallonta, abun da bai taɓa yi ba kenan, ahankali ya janye idanunsa daga kanta tare da kawar da kanshi gefe.
Shiru ne ya shiga tsakaninsu na kusan mintuna 2, jin wani abu me ɗumi tayi ya fito daga jikinta, hakan yasa ta ƙosa ta je banɗaki ta duba ko menene, ganin zaman bazai kaita ba yasa ta sauƙa daga kan gadon, banɗaki'n dake cikin ɗakin ta shiga tare da rufo ƙofar, tashi shima yayi ya fita daga cikin ɗakin.
Bugun zuciyarta ne ya tsananta, duk da kasancewar tasan abun da ta gani ajikinta mai yake nufi, amma sai da ta ɗan tsorita.
"Yanzu yazatayi kenan? wa zata faɗawa ya taimaketa?" Tambayar da tayiwa kanta kenan. Ji tayi ana knocking ƙofar banɗakin, ai saura ƙiris ta zame awajen da take tsaye saboda tsoro, atunaninta Sooraj ne ke buga ƙofar, ƙafafunta ne suka soma rawa. "Taya zata fara faɗa masa matsalanta?" still ta kuma sake tambayar kanta, jin anata buga ƙofar ba a tsaya ba, ya sa ta taho cikin sanɗa ta buɗe ƙofar, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, sakamakon ganin wata likita mace da tayi tsaye abakin ƙofar, ashe ma ita ke buga ƙofar ba Mai taimako ba, saɓanin tunaninta.
"Sannu ya jikinnaki?" nurse ɗin ta tambayeta.
"Da sauƙi" Ziyada ta bata amsa tana ɗan ƙaƙalo murmushin dole.
"Masha Allah haka ake so ae, ga wannan saiki kimtsa kanki ko" nurse ɗin ta faɗi haka tana me miƙo mata wata baƙar leda dake hanunta.
Karɓan ledan tayi tare da komawa cikin ban ɗakin, tana buɗe ledan taga pad's da kuma pant's ne aciki, wani ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe, gefe guda kuwa tsananin mamaki haɗi da kunya ne ke ɗawainiya da ita, da farko dai mamakin yanda akayi nurse ɗin tasan halin da take ciki take, na biyu kuma tsantsar kunyar nurse ɗin ne ya kamata, wani pant ta ɗauko wanda anriga da an maƙala pad ɗin ajikinsa, kallon yanda aka maƙala pad ɗin tayi da kyau, sai da ta ciro wani pant ɗin ta gwada maƙalawa taga yayi sannan ta sauƙe ajiyar zuciya, kasancewar dama bata san ya ake amfani dashi ba. Aɗaɗare ta fito daga banɗakin sai dai rashin ganin kowa da tayi acikin ɗakin hakan sosai yayi mata daɗi. Tana zama akan gado, akaturo ƙofar ɗakin, wannan nurse ɗin ce dai ta kuma dawowa, bayani tayi mata sosai akan yanda zata kula da kanta, da kuma yanda za tana tsabtace jikinta, sannan tace mata taje yayanta na jiranta a mota. Ɗaukan ledan da nurse ɗin ta bata tayi, sannan suka fito atare da nurse ɗin, har bakin motar Sooraj nurse ɗin ta rakota sannan sukayi sallama.
Tana shiga cikin motar ko gama gyara zamanta batayi ba ya yiwa motar key. Saida suka hau titi sannan ta ɗan saci kallonsa ta gefen idanunta, maganane abakinta, amma yanda fuskarsa take babu alaman wargi, yasa taja bakinta tayi gum, ita ayanda ta fuskanta ma shine, shi ko da yaushe ahaka fuskarsa take.
Basu yi wani tafiya sosai ba, ta ga ya gangara gefen titi tare da tsaida motar cak, juyawa yayi ya ɗauko wata leda dake aje a sit ɗin baya, miƙo mata ledan yayi tare da cewa.
"Kici yanzu yanzun nan sai kisha magani"
Baijirayi mai zata ceba ya buɗe murfin motar ya fita, tana kallonsa ya shige cikin wani waje mai kama da kamfani, wanda yake gaba kaɗan da inda ya aje motar tasa, ledan ta buɗe ta ciro take away ɗin, rubber spoon ɗin dake jikin take away ɗin, ta zare haɗe da sanyawa acikin abincin. ahankali take tsakalan abincin, gaba ɗaya bata wani jin daɗin bakinta, duk da cewa tana jin yunwa amma batajin abinci zai wani samu shiga cikinta sosai, bata wani ci abincin sosai ba, ta rufe take away ɗin tare da maidashi cikin ledan, goran ruwan da tagani a inda ya tashi tasanya hanu ta ɗauka, buɗewa tayi tare da kai bakin goran bakinta, lumshe idanunta tayi, tare da sauƙe wani irin ajiyar zuciya, tayi imani duk wani abu da zai fito daga gareshi to ƙamshi yake, hatta goran ƙamshinsa take, tana son wannan ƙamshin nashi har acikin ranta, bama ita kaɗai ba ta tabbatar duk wanda yaji ƙamshin nashi dole zai so sa. Bata fargaba sai kawai jin motsinsa tayi a gefenta, da sauri ta kalleshi don sam batasan da zuwanshi ba, buɗe wani waje mai kama da ɗan ƙaramin drawer dake cikin motar yayi, magungunanta ya ciro, da kansa ya ɓare magungunan ya miƙa mata, aƙoƙarinsa na ya zuba mata magungunan acikin hanunta ne hannayensu suka haɗe waje guda, da sauri ya zuba mata magungunan acikin tafin hanunta, tare da zare nashi hanun, ba don taso ba haka tasha magungunan kasancewar suna da ɗan ɗaci, tana sha ta jingina bayanta ajikin kujera tare da lumshe idanunta. Tuƙi yake amma gaba ɗaya hankalinshi na ga wayarsa yana duba wani saƙo da aka turo masa, ahaka har suka isa gida.
Yana danna horn mai gadi ya wangale masa gate ya tura hancin motar ciki.
Jin sun tsaya ne yasa ta buɗe idanunta ahankali, ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar ne, yasa itama ta buɗe murfin motar ta fita. Sawa yayi Kamalu driver ya shigar masa da kayan da ya sayo ciki.
Yana shiga cikin ɗakinsa ya kwanta flat akan gado tare da lumshe idanunsa, kamar an tsikareshi haka ya buɗe idanunsa da sauri, bakomai yasa hakan ba face, ganin oily eyes ɗinta da ya keyi suna yi masa yawo acikin nasa idanun, hakan kuwa na sawa yaji wani iri ajikinsa.
Ban ɗaki ya wuce ya haɗawa kansa ruwan wanka..
Itama tana shiga cikin ɗakinta, gado ta hau ta kwanta, tare da cusa kanta acikin pillow, abu kamar wasa sai ga wani sabon bacci ya sake ɗaukanta...
*** Tsakanin jiya da yau Alhamdulillah ciwon ya ɗanyi mata sauƙi, kwana biyunnan jinta take atakure, zuwa yanzu ta saba da makaranta, shiyasa takejin zaman gidan gaba ɗaya bayayi mata daɗi, gashi shima Ogan gidan ba ganinshi take ba, ita kaɗai take rayuwarta, jakar makaramtarta ta ɗauko ta shiga haɗa littatafanta, tana gamawa ta jawo ledan abincin da aka kawo mata ta soma ci, bata wani ci mai yawa ba ta ture abincin gefe, jin gidan ya ɗauki shiru babu alaman motsin kowa acikinsa ne yasa ta fita zuwa falo, kusan kullum TV plasma'n dake cikin falon a kashe yake, amma yau ga mamakinta akunne ta sa meshi, zama tayi akan sofa tare da maida hankalinta ga TV'n, tana nan zaune acikin falon har aka ƙira sallan Isha sai alokacin ta tashi ta koma ɗaki, tana shiga tayi kwanciyarta, kasancewar ba sallah takeyi ba.
1:30 na dare, ƙaran taɓa gate ɗin gidan da ake, shine yayi sanadiyar tashinta daga bacci, ahankali ta sauƙo daga kan gadon, bakin window ta nufa don ganin wake taɓa gate ɗin, duk da babu wadataccen haske aharabar gidan, amma inuwarsa kaɗai yasanya tagane wanene, domin akaf gidan babu wani mai irin yanayin jikinsa shi kaɗai ne, tana ganinsa da kansa ya buɗe gate ɗin gidan, sannan ya koma ya shigo da motarsa ciki, tana ganin ya mai da gate ɗin ya rufe ta ɗan saki wata ajiyar zuciya, mamaki da wani kokonto ne suka ɗarsu acikin zuciyarta, don son sake tabbatarwa da kanta cewa shiɗinne ko ba shi bane, yasa ta ɗan buɗe ƙofarta ahankali fitowa tayi ta tsaya abakin ƙofar, dai dai lokacin shi kuma ya buɗe