Author : Maman Teddy Category : Romance
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 44*
Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata matuƙar nauyi ta sauƙesu akan Aunty Muhibbat. Cikin tsananin kulawa Aunty Muhibbat tace "Sannu Zieyaderh tashi kisa kaya sai muje asibiti ko, naji jikin naki yayi zafi sosai!"
Oummu ce tashigo cikin ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa, ƙarasowa gaban gadon da Zieyaderh'n ke kwance tayi cike da tausayin Zieyaderh'n tasanya hannunta ta taɓa wuyanta, jin zafi zau ajikinta, yasanya Oummu cikin damuwa sosai tace "Muhibbat sanya mata kaya naƙira Dr.Bashir yana hanya!"
"To" kawai Aunty Muhibbat tace tare da ɗauko wani lallausan arebian gown wanda aka tsara ado me ɗaukar hankali ajikinsa, miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa ta sanya, cikin ɗan kuzarin daya rage mata tasanya rigan wanda yabi gaba ɗaya surar jikinta ya lafe, komawa tayi ta kwanta tana me maida numfashi ahankali, jin kanta take kamar zai rabe biyu.
Blanket Aunty Muhibbat ta rufa mata, inda tabi bayan Oummu suka fice daga cikin ɗakin.
Wani irin shock ne yaji ya kama gaba ɗaya illahirin jikinsa, take yaji komai ya tsaya masa cak, yayinda maganan maroƙin ke ƙara yawo acikin kunnuwansa yana me hautsina ƙwaƙwalwa da tunaninsa, dummmm haka yaji acikin kunnuwansa yayinda yaji tamkar an buga masa guduma atsakar kansa, tunani gami da nutsuwarsa ne suka ɗauke gaba ɗaya, haka yazama tamkar wani statue, cikin tsananin farinciki da jin daɗi Mas'oud ya dafa kafaɗunsa tare da cewa.
"Ina matuƙar tayaka murna da farincikin samun Zieyaderh amatsayin mata, Allah ya tayaka riƙo!" Mas'oud ya faɗi maganar yana me ɗan bubbuga kafaɗan SOORAJ wanda har yanzu ya kasa ƙyafta koda idanunsa ne, fuska ɗauke da tsananin farinciki Almustapha ya ƙaraso inda Sooraj din ke zaune, hug ya basa tare da cewa.
"Happy Married life my brother, am very happy to day!"
Sai alokacin Sooraj ya motsa idanunsa inda yakeyiwa Almustapha wani irin kallo me ɗauke da tarin tambayoyi haɗi da ma'anoni daban daban.
Ƴan tsirarun abokansa da suka samu daman halartar ɗaurin auren ne suka ƙaraso inda yake, kowanne daga cikinsu bakinsa ɗauke da fatan alkhairi, shidai SOORAJ tamkar wani gunki haka yake binsu da idanu, wani irin gumi ne ke tsatstsafowa ta goshinsa, lokaci guda jikinsa ya soma karkarwa tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi, lura da hakanne yasanya Mas'oud kamo hannunsa suka fice daga cikin taron jama'an dake wajen, kai tsaye mota Mas'oud ya nufa dashi inda ya buɗe gidan baya ya tura Sooraj ɗin aciki kana yamaida murfin ya rufe.
Da ƙarfi ya rumtse idanunsa yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjinshi, wani irin sarawa kansa keyi, yayinda numfashinsa ke seizing yana me ƙoƙarin ɗaukewa, hannunsa yakai kan ƙirjinsa dake masa wani irin ƙuna, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur, da ƙyar ya iya haɗiye wani yawu me ɗaci wanda ya tsaya amaƙoshinsa, jiyake kamar ana watsa masa ruwan zafi akan fatarsa, yanajin kamar yata kurma ihu ko zai samu nutsuwa da salama acikin zuciyarsa, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar tare da cije laɓɓansa, idanunsa da suka kaɗa sukai ja kamar garwashin wuta ya lumshe tare da sanya hannuwansa duka biyu ya toshe kunnuwansa dake ta faman amsa masa amo.
Cikin mintunan da basu wuce 20 ba Dr.Basheer yasamu daman ƙarasowa cikin gidan, kai tsaye Aunty Muhibbat ce tayi masa jagora zuwa ɗakin Zieyaderh, saboda Oummu na fama da jama'arta.
Akan bedsite Dr.Bashir ya zauna tare da ciro kayan aikinsa ya soma kwada yanayin jikinnata, yana kammalawa ya haɗa wasu allurai guda biyu wanda zaiyi mata, drip ya shiga ƙoƙarin ɗaura mata don ya lura sosai take buƙatan ruwa, ganin manyan alluran dayake ƙoƙarin yi mata ne yasanya ta rumtse idanunta, cikin fitar hayyaci tare da sambatu irin na zafin zazzaɓi daya sauƙar mata lokaci guda tace. "Banason Allura, wayyo Yaya kazo kafaɗa masa banason allura, banason komai kai kawai nakeso!"
Baki buɗe Aunty Muhibbat ta kalli Dr.Bashir,
murmushi Dr.Bashir yayi mata tare da girgiza kansa cikin nutsuwa yace. "Karki damu zafin zazzaɓi ne yasanyata haka amma nanda 1 hour insha Allah zata ji sauƙi!"
Kuka Zieyaderh keyi sosai haka Dr.Bashir yayi mata allura, har ya gama yi mata alluran kuwa bata daina kuka ba, tun baigama haɗa kayan aikinsa ba wani irin fitinannen bacci ya soma fusgar ta, kasancewar manyan allurai yayi mata masu ƙarfi hakan yasa dole zasu sata bacci, lumshe idanunta wanda sukayi luhu luhu tayi, gaba ɗaya yanayin idanunnata sun sauya, yayinda suka koma kamar na wata wacce ke cikin tsananin maye.
Wata farar takarda Dr.Bashir yabawa Aunty Muhibbat inda yace anemamata magungunan idan tatashi sai abata tasha insha Allah Zata warke, godiya Aunty Muhibbat tayi masa inda daganan yayi musu sallama ya tafi, mintuna 5 kacal da tafiyan Dr.Bashir nannauyan bacci ya ɗauki Zieyaderh, ganin haka yasa Aunty Muhibbat gyara mata kwanciya tare da rufa mata blanket, rage mata gusun a.c tayi kana ta jawo mata ƙofar ɗakin ta fice, koda ta gayawa Oummu yanda sukayi da Dr.Bashir ƙiran Almustapha Oummu tayi tabashi takardan tare da gaya masa halin da Zieyaderh'n ke ciki.
Idanu Almustapha ya zaro waje cikin damuwa yace "Badai aurenta da SOORAJ ne matsalan ba?"
Kai Oummu ta girgiza masa tare da cewa "Bashi bane, don har yanzun bata sani ba, tunjiya dai take fama da zazzaɓin"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Allah ya bata lafiya"
Da "Ameen" su duka suka amsa kana ya fice don siyawa Zieyaderh magani.
Acan waje kuwa sannu ahankali jama'a keta watsewa inda kowa ke kama gabansa, Alhaji Mansur ne ya dubi Malam Garba wanda yazo ɗaurin auren dashi da ƴan tsirarun abokansa, cikin kulawa yayi musu iso zuwa cikin katafaren falonsa, shidai Malam Garba gaba ɗaya jinsa yake wani iri, burinsa shine yayi ido huɗu da angon ƴartasa don ya damƙa masa amanarta, saidai kuma yawan jama'an dake wajen yasanya sam baiga angon ba yadaiji wasu nacewa angon yanacikin mota amma dai bai ganshi ba.
Mas'oud ne ya buɗe murfin motar ya shigo, saidai ba inda Sooraj ke zaune yashiga ba ɓangaren driver ya shiga tare da yiwa motar key, tunda ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ɗagoba harkawo yanzu da suka kawo cikin katafaren gidannasa. Mas'oud na gama daidaita parking motar ya juyo da kallonsa ga Sooraj baikai ga cewa Komai ba, Sooraj ya buɗe murfin motar ya fita, sam bayako iya ganin gabansa da kyau hakan yasa yake ta gauraya hanya tamkar wanda ke cikin maye, kamar kububuwa haka ya wuce zuwa ɗakinsa dake sama, yana shiga yasoma kiciniyar cire babban rigan dake jikinsa, ƙarasawa gaban tangamemen glass mirror ɗin dake cikin ɗakin yayi, duban kansa da yayi acikin mirror ɗinne yasanyashi jin wani irin ɗaci amaƙoshinsa, cikin wani irin zafin nama haɗi da ƙunci, damuwa, da takaici yasanya hannunsa ya daki mirror'n, take mirror'n ya tarwatse, yayinda hannunsa kuwa yashiga zub da jini, cikin wani irin tururin ɓacin rai dake damunsa yasanya hannunsa gaba ɗaya yayi watsi da gaba ɗaya kayan shafan dake jere reras agaban mirror'n, wani irin ƙara yasanya tare da soma buga kansa ajikin bango, daidai lokacin Mas'oud ya ƙaraso cikin ɗakin, ganin abun da Sooraj ɗin ke aikatawa, sannan ga kuma hannunsa dake zubar da jini, yasanya Mas'oud ƙarasowa cikin ɗakin da sauri, cikin tsananin tashin hankali yace.
"Sooraj ka......"
"Shut up Mas'oud!!!" Sooraj yafaɗa atsawace wanda har saida Mas'oud yaɗan tsorata, cikin tsananin ɓacin ran dake cinsa azuciya yace.
"Mekuka aikata kenan Mas'oud? Nace me kuka aikata!!" Kunsan abun da kukayi kuwa?"
Azafafe ya shaƙe wuyan rigar Mas'oud cikin wata irin murya me amo, wanda tunda Mas'oud ɗin yake baisan cewa Sooraj na da'ita ba yace.
"Why do you do this to me? mehakan da kukayi yake nufi? You already know my problem Mas'oud! you know dat i am not a complete man, meyasa kuka zaɓi cutar da ita? bazan zauna da ita ba Mas'oud! bazan Zauna da ita ba!!"
Gaba ɗaya cikin ficewar hayyaci SOORAJ ke faɗan maganganun.
Tsananin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mas'oud cikin son kwantarwa da Sooraj hankali yace.
"Kadawo cikin hankalinka Sooraj, kai musulmi ne kasan ƙaddara kuma tana iya sauyawa ako da yaushe, sannan kyakkyawa takan iya zama mummuna, mummuna kuma takan iya zama kyakkyawa, dan Allah Sooraj kada ka aikata abun da zuciyarka ke shirya maka, nasan matsalanka Sooraj nasani amma nasan bazaka taɓa tabbata ahaka ba, nayarda dacewa wannan auren rufin asirine agareka dan Allah RAJ ka tausashi zuciyarka, kadawo cikin nutsuwarka!"
Mas'oud ya faɗi haka idanunsa cike tab da ƙwalla, tabbas ya hango tsananin damuwa da tashin hankali akan fuskar SOORAJ, amma basu da wani zaɓi, tunda Allah ya riga da yayi nasa.
Iska SOORAj ya fesar ta bakinsa tare da rumtse jajayen idanunsa, wani irin azababben ciwon kai yakeji, yayinda yakejin gaba ɗaya duniyar na juya masa, ahankali ya taka tare da ƙarasawa gaban bedsite ɗinsa, cikin zaƙuwa ya buɗe drawer'n bedsite ɗin, wata kwalba ya ciro wanda cikinta ke ɗauke da magani, cikin rufewar ido ya ɓalle murfin kwalban tare da kafa bakin kwalban acikin nasa bakin, arazane Mas'oud yayo kansa daniyar hanasa shan maganin, amma kafun yaƙaraso tuni Sooraj ya shanye maganin tas, cikin zafin nama Mas'oud ya ƙwace kwalban maganin daga hannun Sooraj cikin nuna damuwa yace.
"Please calm down RAJ, dan Allah ka nutsu kada kayiwa kanka illa!"
Kan gado ya faɗa tare da rumtse idanunsa, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe, wasu baƙin abubuwane ke ziyartan tunaninsa, akusa dashi Mas'oud ya zauna tare da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa, sosai damuwar abokinnasa ke damunsa, musamman yau da yaga gaba ɗaya RAJ ɗin ya fita a hayyacinsa, sai yakeji inama da ba'a haɗa baki dashi wajen ɓoyewa SOORAJ auren ba.
Tarin da Sooraj ɗin keyine yasanya Mas'oud juyowa ya kallesa, wani irin guda gudan jini dayaga yana fita abakin Sooraj ɗinne yasanyashi zaro idanunsa cikin tsananin kaɗuwa yace.
"RAJ dan Allah kada kayiwa kanka illa!"
Wani farin handkerchief yasanya ya goge jinin dake fita abakin sa, cikin ƙarfin hali ya sauƙo daga kan gadon, toilet ya nufa yana shiga ya wanke bakinsa tare da watsawa fuskarsa ruwa, wani irin dishi dishi yake gani yayinda jiri ke neman kadashi, adaddafe yafito daga toilet ɗin, zuwa lokacin baya ko iya ganin gabansa, hayyacinsa ne ke neman barin jikinsa, kan gadonsa ya faɗa, lokaci guda idanunsa suka rufe ruf..
Ganin haka yasanya Mas'oud lulluɓa masa blanket, wayarsa ya ciro ya dannawa Dr.Waleey likitan Sooraj ɗin ƙira, bayanin komai yayi masa, nan Dr.Waleey yace gashinan zuwa, mintuna kaɗan saiga Dr.Waleey yaƙaraso gidan, duƙufa yayi sosai akan Sooraj ɗin wajen gano matsalarsa, ganin cewa maganin da Sooraj ɗin yasha yana da illa sosai ne yasanyashi yi masa wata allura wanda zata sauƙaƙawa jikinsa wajen gusar da duk wata wahala,
kallon Mas'oud Dr.Waleey yayi cikin kulawa yace.
" Wani abu ya ɓata masa rai ne?"
Ajiyar zuciya Mas'oud yayi tare da jinjina kansa alamar.
"Eh"
Cikin tausayawa Dr.Waleey yace.
"Ciwonsa yayi worse yakamata kuna kiyaye ɓacin rai ko wani abu da zai na taɓa zuciyarsa, sannan yana da buƙatar kulawa ta musamman"
ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da cigaba da cewa.
"Ina tsananin tausayin Sooraj Mas'oud, saboda Allah ya haɗasa da ƙaddarori masu girma, saidai ina masa fatan samun sauƙi akoda yaushe"
Wasu magunguna ya ciro daga cikin jakarsa kana ya miƙawa Mas'oud, cikin kulawa yace. "Idan yatashi katabbatar yasha waƴannan magungunan zasu taimaka sosai!"
Kai Mas'oud ya jinjina tare da yiwa Dr.Waleey godiya daga haka sukayi sallama, zama Mas'oud yayi akan wata lallausan kujera dake cikin ɗakin tare da kai dubansa ga Sooraj wanda ke kwance kamar gawa, wani irin hawayene suka cika idanun Mas'oud har suka samu daman gangarowa, bayansa ya jingina da jikin kujera tare da lumshe idanunsa.
Ahankali idanunta ke buɗewa harta gama waresu tas, tashi zaune tayi tare da kai dubanta ga cannula'n dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, bayanta ta jingina da jikin gadon da take kwance, ahankali hayaniyan jama'an da suka cika gidan ke ratsawa cikin kunnuwanta, sake lumshe idanunta tayi yayinda wasu siraran hawaye suka samu daman gangarowa daga cikin idanunta, hannunta takai ta dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi, daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin nata, da sauri tasanya bayan hannunta ta share hawayen nata,
Oummu da Aunty Laylerh ne suka shigo cikin ɗakin, ganinta azaune yasanya murmushi bayyana akan fuskarsu,
cike da kulawa Oummu tace "Sannu Zieyaderh kintashi ya jikin?"
Cikin sassanyar muryarta wacce ke ɗauke da zallan damuwa tace "Da sauƙi!"
Aunty Laylerh ne ta zauna akan gadon tare da ɗan taɓa jikin Zieyaderh'n cikin kulawa tace "Masha Allah zafin jikin ya sauƙa, yanzu me kikeji ajikin naki?"
Ita kanta bazata iya tantance me takejiba saboda ciwon ba ajikinta yake ba azuciyarta yake, rashin sanin abun da zatace yasanya kawai ta nuna kanta, cikin kulawa Aunty Laylerh tace "Sannu ko"
Duban Oummu tayi tare da cewa, takawowa Zieyaderh'n tea me kauri da abinci idan taci sai tasha magani, hakan kuwa akayi Oummu da kanta ta haɗa mata tea da kuma pepper chicken, Aunty Laylerh da kanta tasanya Zieyaderh agaba akan cewa lalle dole sai tasha tea din, duk da cewa batajin daɗin bakinta haka dole ta daure taɗansha tea ɗin kaɗan, koda ta nuna ta ƙoshi Aunty Laylerh da kanta tashiga bata naman abaki, da ƙyar ta iya cin kaɗan ta kauda kanta gefe alaman ta ƙoshi,
shigowar Aunty Muhibbat cikin ɗakinne yasanya Aunty Laylerh cewa takai Zieyaderh'n tasakeyin wanka daganan sai a shiryata tunda dai sunga jikinnata daɗan sauƙi, wani irin ingantaccen ruwa wanda yaji haɗaɗɗen turaren wanka Aunty Muhibbat ta haɗa mata, ahankali take takawa saboda gaba ɗaya jikinta ba ƙarfi, toilet ɗin ta shiga tare da zare rigar jikinta, dayake ruwan nada ɗan ɗumi hakan yasa ta kwanta lif acikinsa, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tana mejin wani sabon yanayi nashiga jikinta, cikin rashin kuzari haɗi da kasala tayi wankan inda gaba ɗaya jikinta yasake gaurayewa da daddaɗan ƙamshi, alwalan sallan Azahar tayi kana fito daga cikin toilet ɗin, cikin ɗan kuzarin daya rage mata yayi sallah inda Oummu ta taturo Bilkh don ta gyarata. Kasancewar bata wani jin daɗi yasanya Bilkh yi mata light meckup, hakan kuwa baƙaramin fito da kyawunta yayi ba, wani haɗaɗɗen lace wanda yaji ɗinkin doguwar riga fitted gown tasanya, sosai leshin ya amshi jikinta kasancewar lace ɗin nada kalan ja, hakan yasa Bilkh ta naɗa mata ƙaton white vail ajikinta mai adon jan duwatsu, sosai tayi kyau, saidai ƴar rama kaɗan data bayyana ajikinta, yanayin yanda bilkh ta naɗa mata mayafinne yasanya yaɗan rufe rabin fuskarta kaɗan, Aunty Muhibbat ce tariƙota suka fice daga cikin ɗakin, kaitsaye ɗakin Oummu suka nufa, Oummu ce ita kaɗai zaune akan gado, akusa da ƙafan Oummu Aunty Muhibbat ta ajiyeta kana ta juya ta fice daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa Oummu ta ɗago Zieyaderh kana ta kawota kusa da ita, cikin tsananin kulawa tace.
"Cikar mutumcin ko wacce ƴa mace shine aure, haka kuma duk wata ƴa mace tana sanin ƙima da darajar kanta ne aduk lokacin da tayi aure, kamar yanda kika sani yau anɗaura miki aure saboda haka kin tashi daga sunan budurwa kin zama matar aure" ɗan numfasawa Oummu tayi tare da kamo hannuwan Zieyaderh cike da tausayawa tace
"Kigafarceni Zieyaderh, haƙiƙa ban aikata haka daniyar son zuciya ba, nayi hakane saboda inganta rayuwarku ku duka biyun, nakumayi hakanne amatsayina na uwa mai son cigaban ƴaƴanta, bansan yazakiji ba amma yazama dole na faɗa miki" sake hannun Zieyaderh'n tayi tare da sanya hannu ta ɗan ɗage mayafin dake kan Zieyaderh'n, hakan yasanya Zieyaderh taɗan ɗago ta kalleta, cikin kulawa Oummu tace.
"Anɗaura aurenki yau saidai kuma bada Almustapha aka ɗaura ba, kamar yanda kike tunani, nasan zakiji abun wani iri amma ƙaddara ta riga fata!"
Ɗago idanunta dake cike da mamaki tayi ta kalli Oummu, hannunta Oummu tasake kamawa cikin son kwantar mata da hankali tace
"Ƙwarai bada Almustapha aka ɗaura miki aure ba, dan Allah Zieyaderh kiyi haƙuri ki karɓi wannan ƙaddaran!"
Kan Zieyaderh ne ya ɗaure sosai don sam takasa fahimtan inda kalaman Oummu suka dosa, cikin sarƙewar murya tace "Oummu Nayarda da ƙaddara me kyau da kuma akasinta"
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da dafa shoulder ɗinta, cikin rauni tace
"Yana da buƙatarki acikin rayuwarsa, haƙiƙa nasan SOORAJ yana da damuwa yana kuma da buƙatar mai magance masa wannan damuwan, kiyi haƙuri ki karɓeshi amatsayin mijinki!"
Azabure Zieyaderh ta matsa baya tare da zaro idanunta cikin wani irin kaɗuwa ta soma jijjiga kanta yayinda gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa, jin sauƙan kalaman Oummun tayi tamkar sauƙan aradu acikin kunnuwanta, ganin yanda ta firgice yasanya Oummu kamo hannuwanta cikin sanyin murya tace "Nasan zakiji ba daɗi, sannan nasan bamu kyauta miki ba amma ya zamuyi ki ɗauka wannan tsarin Allah ne bana muba, dan Allah Zieyaderh ki riƙi aurennan amatsayin ƙaddaranki"
tuni idanun Oummu sun cicciko da ƙwalla. Rungume Oummu Zieyaderh tayi tare da sakin wani irin fitinannen kuka, kuka sosai takeyi yayinda gaba ɗaya jikinta ke karkarawa, jin Oummun takeyi kamar uwa mahaifiya agareta, cikin kuka tace "Kidaina roƙona Oummu ke uwace agareni kodawa kika haɗani bazan gujeba, bazan bijiremiki ba Oummu bazan taɓa gujewa hukuncinki agareni ba!!"
ta faɗi maganar tana me sakin sheshheƙan kuka, wasu irin hawayene suka sauƙo daga cikin idanun Oummu tabbas saiyanzu taƙara tabbatar da cewa batayiwa ɗan nata zaɓen tumun dare ba, wani irin ƙwarin guiwa da farincikin samun Zieyaderh amatsayi suruka da tayi tasanya hannunta akan bayan Zieyaderh dake kuka ahankali take shafa mata bayannata tare da cewa. "Nagode sosai Zieyaderh Allah yayi miki albarka!"
Zaunar da Zieyaderh'n tayi akan gadonta tare da soma ƙoƙarin share mata hawayen dake gudana akan fuskarta, cikin so da ƙaunarta tace "Ya isa haka kwanta ki huta kada ciwon kai ya kama ki!" a irin halin da take ciki batajin zata iyayiwa Oummu musu,luf ta kwanta akan gadon Oummu'n tare da cusa kanta acikin pillow, Oummu ce tafita aɗakin don amsa ƙiran wayan da akeyi mata, tanajin ficewar Oummu aɗakin tasaki wani sabon kuka mai tsuma zuciya kuka takeyi sosai wanda har saida numfashinta yasoma ƙoƙarin ɗaukewa, gaba ɗaya tunani da nutsuwa sun gudu daga gareta, jin motsin kamar za a bude ƙofar ɗakin ne yasanyata haɗiye kukanta tare da rufe idanunta, yanayin yanda zuciyarta ke bugawa yasanya ta sake cusa kanta acikin pillow'n, ajiyar zuciya da