Author : Maman Teddy Category : Romance
ƙofar falon ya shigo, key ya murza ajikin ƙofar sannan yabar key ɗin ajiki, Yana maiƙoƙarin cire rigar dake jikinsa ya ƙarasa gaban fridge. Buɗewa yayi ya ɗauko goran Fearless. Wuceta yayi tamkar baiganta ba, alhali kuma tunshigowarsa idanunsa suka gane masa ita, harya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar ɗakin nasa, sai kuma ya dakata batare da ya juyo ba yace.
"Me kikeyi anan?"
Ziyada dake ƙoƙarin komawa ɗaki, taji sauƙar muryartasa tamkar rugugi acikin kunnuwanta, da sauri ta juyo garesa saidai bata iya kallonsa ba, duk da cewa ya bata baya.
"Babu"
Tace murya asanyaye.
"Wani abu ya faru ne?" Yasake tambayarta still batare daya juyo ya kalleta ba.
"A'a" Ta bashi amsa muryarta naɗan rawa, hakanan idan yana gabanta sai taji wani irin tsoronsa ya kamata.
Murɗa ƙofarsa yayi ya shige ciki
tare da rufo ƙofar, tana tsaye taji ya murzawa ƙofar key ta ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da komawa nata ɗakin itama, da ƙyar ta samu bacci yasake ɗaukanta.
Shikuwa bai iya samu bacci ya ɗaukesa ba, har sai da yasha maganin da ke taimaka masa wajen sanyashi bacci, duk da haka dai baccin baiyishi cikin daɗin rai ba.
7:00
Daidai ta gama shiryawanta, tayi kyau acikin uniform ɗinta kamar kullum, tana kammala saka white socks ɗinta, tasoma jin ana knocking ƙofar falon, school bag ɗinta ta rataya bisa kafaɗanta sannan tafi ta zuwa falon, dama bata saba ganinshiba don haka batasa aranta zata ganshi ba. Tana buɗe ƙofar wanda ke kawo mata abinci kullum yaɗan yi mata murmushi, itama murmushin tayi masa tana ƙoƙarin gaidashi ne ya miƙo mata wata kula mai kyau wacce take da ɗan mariƙi a samanta.
"Madam ga saƙonki inji Oga" yace da ita.
Karɓa tayi, shikuma ya juya yayi tafiyarsa, komawa cikin falon tayi tare da buɗe kulan. Kulan irin mai hawa ukunnanne wato (3pieces) hawan farko da ta buɗe soyayyen dankali ne aciki wato chips da kuma ƙwai, sai hawa na biyun dake ɗauke da gasashshen nama mai albasa, hawan ƙarshe shine ke ɗauke da shinkafa fried rice wacce taji liver, ɗaukan kulan tayi ta riƙe ahanunta, tana fita waje ta samu Kamalu yana tsaye ajikin mota yana jiranta. Tunda suka ɗauki hanyar makarantar yau Kamalu keta mata zuba, ita dai ba gadon magana bace hakan yasa take amsa masa kaɗan kaɗan, shikuwa sai labarai yaketa bata, ganin yanda take amsa masa ne, yasa aranshi yace "Duk yanda akayi itaɗin jinsin Oga ce, da'alama duka zuri'arsu haka suke basason magana"
Yau kam Su Nasmah sun rigata zuwa, tana zama Nasmah ta ce "Ki koma kinyi late"
Dariya ta yi tare da ɗan satan kallon Shukrah, matsawa kusa da Nasmah tayi sosai cikin ƙasa da murya tace.
"Yau maiyasamu Shukrah na sake ganin fuskarta babu walwala?"
Baki Nasmah ta taɓe haɗe da cewa. "Hmm barta kawai kekam wahalane bai ishetaba, wai fa soyayya take kullum kuma sai sunyi faɗa da saurayin"
Idanu Ziyada taɗan zaro waje cike da mamaki tace. "Soyayya!"
"Eh Soyyayya" Nasmah ta faɗa tana ɗan kallonta.
Shiru Ziyada tayi tare da jin wani abu acikin ranta. "Kenan dama Soyayya gaskia ce?" tambayar da tayiwa kanta kenan sannan ta kuma sake tambayar kanta "Menene alamomin soyayya?"
"Yanaga kamar kina tunani" Cewar Nasmah da ta shiga mamakin yanayin da taga Ziyada ta shiga.
"Babu" Ziyada tafaɗi haka tana ɗan yin murmushi, Malamin English ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka bada gaba ɗaya hankalinsu gareshi.
Yau a wajen da aka tanadar musamman dan cin abincin ɗalibai sukaci abincinsu, ita dai Shukrah gaba ɗaya bata da wani walwala, Ziyada da Nasmah ne kawai suketa sha'aninsu. Shaƙuwar da ke tsakanin Ziyada da Nasmah shine ke ƙarawa Ziyada jin daɗin rayuwar makarantar. Yau ba atashesu ba har sai biyar da rabi kasancewar anshiga dasu meeting akan jarabawan da zasu fara next month. Agajiye ta dawo gida ga ciwon cikin dake sanɗanta, da ruwan zafi tayi wanka sannan ta kwanta.
11:00 ta farka daga ɗan baccin daya ɗauketa, wani irin ciwon da cikinta keyi mata shine abun daya ɗaga mata hankali, Kuka take hanunta dafe da saman mararta wanda takejinta kamar zata ɓalle.
Yana zaune akan gado yana danna laptop ɗinsa, ahankali ƙaran kukanta ya shiga kawowa kunnensa ziyara. Ɗauke hanunsa yayi daga kan laptop ɗin tare da yin shiru yana mai sauraran yanda kukan nata ke tashi. Kallon agogo yayi yaga ƙarfe 11:10 na dare, wata ƴar ƙaramar tsuka yaja tare da sanya hanu ya dafe goshinsa. "Me na ɗaukowa kaina ne?" tambayar da yayiwa kansa kenan.
Jin kukannata na daɗa ƙaruwa ne yasan yashi miƙewa, ƙofar ɗakin ya buɗe ya fita, tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin da take yana mai tunanin shiga cikin ɗakin. Jin taƙi daina kukan ne yasashi murɗa handle ɗin kofar ya shiga. Yashe ya ganta aƙasa tanata birgima gaba ɗaya gashinta ya watse akan tiles, kuka take irin na fitar hayyaci. Ƙarasawa yayi inda take yashe aƙasan tana ta mutsu mutsu, hannayensa yasanya ya kama kafaɗunta, jin sauƙar hanun mutum akan kafaɗunta yasanya ta kama hunun nasa ta damƙe da ƙarfi, da ɗayan hanunnasa da bata kama ba yayi amfani wajen ɗago haɓarta, gaba ɗaya fuskarta ta ɓaci da hawaye, zara zaran eye lashes ɗinta sun jiƙe da hawaye sun manne akan fatarta. Hanunsa dake cikin hanunta ta ƙara matsewa tare da sakin wani ƙara, ji take kamar taita buga kanta ajikin gini ko zata samu salama, ganin yanda take shiɗewa ne yasanya shi ɗagata caɗak ya nufi kan gado da ita, kwantar da ita yayi, tare da ɗauko magungunanta ya bata.
***
After 30 minute har yanzu gunjin kukanta ne ke tashi acikin ɗakin, sama da mintuna talatin kenan da bata magani amma har yanzu ciwon bai lafa ba, tun tanayin kukan da duka jarumtarta har takai tanayin kukan acikin yanayi na galabaita, hankalinsa ne yasoma tashi, wayarsa ya ɗauka ya ƙira Number'n Dr.Waleey, shaida masa abun dake faruwa Sooraj yayi, shiru yayi yana maijin amsar da Dr.Waleey ke bashi, cikin rashin ƙarfin guiwa ya aje wayartasa bayan sunyi sallama da Dr.Waleey'n, shiru yayi haɗe da zuba mata mayun idanunsa, sosai zuciyarshi ta karaya akanta, wani irin tausayinta yaji ya daki zuciyarsa, duk wanda yaganta acikin irin wannan halin sai ya tausaya mata, musamman yanda tayi buji buji da gashin kanta, ga numfashinta dake ƙoƙarin sarƙewa tsabar kukan da tayi, maganganun Dr.Waleey ne suke dawowa cikin kunnensa. Bayajin zai iya aikata abun da Dr.Waleey yace yayi, sannan kuma bayajin zai iya jure ganinta acikin halin wahala, baisan maiyasa yake jin son taimakonta ba tun farko, ayanzu yanaji inama da ace tun farko bai taimaketa ba, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi sakamakon yanda yaga takeyi, baida wani zaɓi wanda ya wuce ya taimaketa, tashi yayi ya nufi gadon, sautin bugawar zuciyarshi ne ya tsananta yayinda ƙirjinsa ke tsalle kamar zai faɗo ƙasa, da ƙarfi bugun zuciyarsa ke harbawa...
(Na yau dana gobe duka na haɗa muku😝 kuji daɗinku ku more, idan ku naga kamar naso kaina, sai ku karanta rabi yau gobe ku ƙarisa karanta rabi😂)
[12/April/2020]
*Vote Me On Wattpad*
@fatymasardauna kwana biu bana baku update da wuri🙏🏻 Fans ɗina na Facebook ina gaisuwa)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 18*
Ƙirjinsa ne ke ta dokawa kamar zai fito waje. Yana ƙarasawa gaban gadon yaja ya tsaya tare da kafeta da idanunsa, jin kukanta yake har acikin ransa, hannayen rigansa ya ɗan naɗe tare da nufar toilet ɗin ɗake cikin ɗakin, heater ya kunna ya tari ruwan zafi acikin wani ɗan madaidaicin bucket, towel ya ɗauko sannan ya fito daga cikin toilet ɗin. Ƙafansa ɗaya yasanya ya taka kan gadon, baisan tayaya kuma ta ina zai fara ba, hakan baikamacesa ba, sannan kuma sam hakan ba aikinsa bane, saidai kuma sosai yake tausayin halin da take ciki. Aƙalla yaɗau kusan mintuna 10 a haka ya kasa aikata komai, yayinda ita kuwa har yanzu take aikin kuka gaba ɗaya tasake fita hayyacinta, zama yayi akan gadon tare da sanya towel ɗin acikin ruwan zafi, hannayensa ne suka ɗauki rawa, ya kasa koda kai hanunsa jikinta, zuciyarsa bugawa take, hanunsa yakai kan wuyanta ya ɗan taɓa, ji yayi babu wani zazzaɓi sosai ajikinnata, rumtse idanunshi yayi tare da kai hanunsa kan lafeffen cikinta, tamkar wanda aka jonawa shocking haka hannayensa ke rawa, da ƙyar ya iya ɗan ɗage rigan dake jikinta yayi sama dashi, still hannayensa na rawa yasanya hanu ya ɗanyi ƙasa da sket ɗinta, towel ɗin yaciro daga cikin ruwan zafin tare da ɗan matsawa ya rage ruwan dake jiki, sake rumtse idanunshi yayi tare da ɗaura towel ɗin adai dai kan cikinta, wani ƙara tasanya tare da ɗan soma yunƙurin tashi zaune, baisan sanda yasanya ɗayan hanunsa ya maida ita ta kwanta ba, sai alokacin ya samu damar buɗe idanunshi ya sauƙesu akan fuskarta, hawaye ne kawai ke gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya ta galabaita. Sake danna towel ɗin yayi akan cikinta, gani yayi ta sake rumtse idanunta, ahankali yake ɗan matsa towel ɗin akan cikinta, ƙasa ya somayi da towel ɗin daidai kan mararta ya tsaya, Yanayin yanda yake matsa towel ɗin akan maranta ne, yasanya ta jin wani ɗumi na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, sake maida towel ɗin cikin ruwa yayi tare da ɗan matsewa, sake manna mata yayi akan maranta, haka yadinga yi mata har tsawon wasu lokuta, ahankali kukanta ya tsaya cak, wani irin ajiyar zuciya take sauƙewa akai akai, fitar numfashinta ne ya soma sanja sauti, ya zama na yana fita slowly, duk wannan abun da yake mata, bai bari idanunshi sun kaishi ga kallon jikinta ba. Cikin wani irin yanayi na wahala ta kamo hanunsa na hagu ta riƙe acikin nata hanun, ganin haka yasa ya aje towel ɗin agefe, ɗan ranƙwafowa yayi tare da kawo bakinshi dai dai saitin kunnenta, ahankali ya soma hura mata iskan dake bakinsa acikin kunnenta. Daddaɗan ƙamshin turarensa ne ke ziyartan hancinta, yayinda iskan bakinsa dake hura mata ya kasance garkuwa wajen samun nutsuwarta, ahankali taji wani irin salama na sauƙar mata, cikin wani irin yanayi hucin numfashinsu ke gauraya waje guda, jin yanda sautin numfashinta ya sauya ne, yasanyashi ɗan ɗago da kansa ya dube ta, gani yayi tana fitar da numfashi ahankali da alama bacci ne ya ɗauketa, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗago kansa daga ranƙwafon da yayi, hanunsa dake cikin nata ya kalla wanda ta damƙeshi gam. Ƙoƙarin cire hanunsa daga cikin nata yayi, amma yaji ta sake riƙe shi gam, cikin ɗan dabara ya samu ya zare hanunshi, hannayensa ya ɗaura akan kafaɗunta tare da gyara mata kwanciya, blanket ya rufa mata, sannan ya rage mata hasken ƙwan wutan dake cikin ɗakin, tashi yayi ya fita tare da jawo mata ƙofar. Ɗakinshi ya koma yayi kwanciyarsa, ya jima kafun bacci ɓarawo ya samu damar ɗaukarsa.
Tunda ta kwanta ba itace ta farka ba sai ƙarfe 8:00 daidai na safiya, ahankali take buɗe gajiyayyun idanunta da suka kumbura sukayi luhu luhu dasu, kasancewar daren jiya tasha kuka sosai, tashi tayi ta zauna akan gadon tare da sanya hanu ta shafi saman mararta, ko ɗigon ciwo bataji ajikinta saidai kasala kawai dake damunta, lumshe idanunta tayi tana mai ƙoƙarin son tunano abun da ya faru da'ita a daren jiya, ita dai bazata iya cewa ga abun daya wakana ba, amma tabbas tasan ta ganshi acikin idanunta, sannan kuma taji daddaɗan ƙamshinsa acikin hancinta, amma wata zuciyar ta na faɗa mata cewa ba shi bane. Zuro ƙafafunta ƙasa tayi daga kan gadon tare da tashi tsaye, banɗaki ta wuce ta haɗawa kanta ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sosai taji daɗin wankan da tayi domin ya ƙara taimakawa wajen warware mata gajiyan dake jikinta.
Cikin sauri sauri ta zura kayan uniform ɗinta, safa'nta ta sanya tare da ɗaukan school bag ɗinta, duk da batasan ƙarfe nawa bane yanzun, amma tabbas da dukkan alama yanda taga rana ta bayyana raɗau tasan tayi latti, fitowa falon tayi tana mai ƙoƙarin cusa wani littafi dake hanunta acikin jaka, sam bata lura dashi ba kasancewar bata kawo ma aranta cewa zata ganshi ba.
"Ina zakije?" muryarsa ya doki dodon kunnenta, cak ta tsaya daga tafiyar da takeyi, tare da dawo da kallonta zuwa inda taji sautin muryar ta fito.
Zaune yake akan dinning table yasha kyau cikin riga da wando na suit amma baisanya suit ɗin ba, sai dai tana aje agefensa, parking shirt ne ajikinsa Navy blue colour wanda ta ƙara masa kyau. Cup ɗin tea ne ahanunsa yana sha da kaɗan kaɗan.
Bazata iya jure kallonshi ba, saboda sosai yake mata kwarjini. "Dama zanje makaranta ne!" tabashi amsa cikin muryarta mai sanyi.
Shiru yayi kamar bazai amsa mata ba, sai kuma ya ɗago kansa yaɗan kalleta. "Zokici abinci!" yace da ita ataƙaice.
Duk da tasan cewa tayi latti, amma bazata taɓa iya faɗa masa hakan ba, batasan tayaya zata iya fara zama tare dashi ba, amma ya zatayi? Ƙarasawa gaban dinning ɗin tayi tare daɗan durƙusawa. "Ina kwana!" tace dashi cikin sassanyar murya.
Kansa kawai ya kaɗa mata batare da ya amsa ba, aɗaɗare ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake dinning table ɗin. Food flask da kuma plate ɗin dake gabanshi ya turo mata, kana ya cigaba dashan tea ɗinsa, wayarsa ya ɗauka yasoma latsawa. Buɗe food flask ɗin tayi ta ɗan ɗibi abincin kaɗan, gaba ɗaya ta kasa sakewa taci abincin, jin kanta take atakure, duk abun da takeyi yana lure da ida ta gefen idanunshi, miƙewa tsaye yayi tare da ɗaukan suit ɗinsa ya sanya.
Saida ya ɗanyi tafiya kaɗan sannan ya tsaya, batare da ya juyo ya kalleta ba yace.
"Yau bazakije school ba kizauna agida" Baijira abun da zata ce ba yayi gaba abunsa.
Bata ɗauke idanu akanshi ba har saida yafice daga cikin falon.
"Yau bazakije school ba ki zauna agida"
Tamaimaita abun daya faɗa cikin ɗan nazari, kenan yana nufin tazauna agida kada taje makaranta? Babu mai amsa mata, hakan yasa ta ci gaba da tsakalan abincin. Bata wani ci abincin sosaiba tatashi ta koma ɗaki, uniform ɗinta ta cire sannan ta dawo falo ta zauna, ƙurawa tv idanu tayi tana kallon yanda ake koyar da girki.
***
Shikuwa yana fita daga falon direct wajen lafiyayyar motarsa ƙirar Range Rover Blue colour ya nufa, yana shiga Kamalu driver yaja suka fice daga cikin gidan. Yau meeting suke dashi a Transcop hilton saboda haka direct can suka wuce. Tun ƙarfe 9 da suka shiga meeting ɗin basu suka fito ba sai 11 daganan yawuce office.
Ziyada kuwa dake zaune agaban tv, duk wani abu da ake koyarwa na girki taɗaukeshi tsab akanta, hatta abun da tagani jiya a kitchine wani mai kamar kofi,(Blender) yau taga yanda ake amfani dashi, ashe abun markaɗe ne ita bata sani ba, suna gama koyar da girkin, suka sako wani film shine abun daya ƙara ɗauke mata hankali. Ba itane ta tashi agaban tv'n ba harsai bayan sallan Azahar. Kitchine ta shiga cike da karambaninta yau taci alwashin sai tayi girki. Ruwa ta zuba atukunya cike da karambani ta kunna gas, duk abun da taga sunyi acikin tv'n ta riƙeshi yana kanta, ruwan na tafasa ta wanke shinkafa ta zuba, fridge ɗin dake cikin kitchine ɗin ta buɗe ta ɗibi kayan miya, saida ta wankesu sannan ta ɗauko irin abun da taga sunyi markaɗe aciki gaba ɗaya kayan miyan ta juye acikin blender tare da ɗaukanshi can ca ɗak takaishi gaban socket, kamar yanda taga sunyi haka itama tayi ta jona sa ajikin socket, ƙaran da taji yayi kaɗai saida ya kusa fasa mata ƙirji, don baka ɗan ba ta tsorata, can gefe ta koma tana ganin ya markaɗu ta siɗaɗo da ƙyar ta iya kashe socket ɗin, duba shinkafarta tayi taga ta nuna, haka ta sauƙe shinkafar batare da ta kashe gas ɗin ba, da sauri sauri ta juye markaɗen acikin wata tukunya sannan tasanya mangyaɗa akan markaɗen don ita agarinsu haka suke miyansu. Baƙaramin jimawa tayi ba kafun ta samu miyan ya soyu mata, hmmm nan akeyinta sam batasan me zata sanyawa miyan don kashe mata tsami ba, haka ta zuba kayan haɗi ta rufe miyar, mintuna kaɗan ta kashe gas ɗin lokacin miyar tayi, komawa ɗakinta tayi tayi wanka, wata doguwar riga blue colour ta sanya mai kyau, rigan irin arebian gown ɗinnan ce, sosai ta amshi jikinta, zuciyarta fara tas ta nufi kitchine ɗin, daɗi takeji yau zataci abincinta, bata taɓa mantawa awasu lokuta da dama a ƙauye idan tayi girki babanta yaci yakan yaba girkin sosai, sannan ita kanta Inna Ma'u idan tanacin girkin har santi take, hakanne ma yasa aka sallama mata gaba ɗaya girkin gidan. Food flask ta ɗauka ta juye shinkafan aciki, sannan ta ɗauki plate ta zuba nata, miyan ma juyeshi tayi acikin wata kula gaba ɗaya kulolin takaisu kan dinning table ta ajiye..
Akan sofa ta zauna tare da ɗan ƙwashe ƙafafunta, cikin ɗari ɗari takai loman farko na abincin bakinta, saboda atunaninta miyan tayi tsami sosai, sai dai kuma koda taci abincin, ga mamakinta sai taji miyar batayi wani tsami sosai ba, hasalima mutum zai iyaci hankalinsa kwance. Sosai taci abincin tana kammalawa ta je kitchine ta wanke plate ɗin. Dawowa falon tayi ta zauna, tana zama tajiyo ƙarar horn ɗin motarshi, tashi tayi da sauri ta tafi jikin window ta ɗan leƙashi, yatsun hanunta tashiga murzawa aranta tana cewa.
"Allah yasa ya yarda yaci abincinnata"
(😆Lallai Sooraj zaici daɗi shinkafa da miya available, please waye zaizo aci shinkafarnan dashi😝.... Then saiku sani gobe fa babu update. Seriously i'am tired editing kaɗai yana bani headache)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ