Author : Maman Teddy Category : Romance
kanshi ba screen ɗin wayarsa kawai yaketa shafawa, kamar wacce aka razana haka taɗauki fork tashiga tsakalan chips ɗin da ɗaya ɗaya tana kaiwa bakinta. Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana latsa phone dinsa kafun ya ɗago, bowl din fruit salad ɗinsa yajawo ahankali yasanya spoon aciki, 2 spoon kawai yayi ya sake mayar dakansa ga wayarsa, Ummu gaba ɗaya tana lura dashi, duk da tasan cewa bayida yawan cin abinci, amma yanda yanzun yaƙi maida hankali yasha fruid salad ɗin yasanya taji ba dadi acikin ranta, cike da kulawa ta ƙira sunanshi "SOORAJ!"
Ahankali yaɗago kanshi ya kalleta batare dayace wani abuba.
Ɗan ɓata fuska Ummu tayi tare da cewa. "Kasan dai me Dr. yace akanka ko? saboda haka yanzu lokacine da zakaci abinci sosai, rashin cin abincin shine zaisa kadingajin kanka kamar baka da lafiya"
Ɗan yamutsa fuska yayi tare da kaɗa mata kansa alamar "Yaji"
Kansa yamaida ga bowl ɗin ya ɗeɓo fruid salad ɗin yakai bakinsa. Abba daya kammala cin tuwonsa ya ɗago yana goge hanunsa da tissue. Sam babu wanda yayi zato saijin muryarsa sukayi yace.
"Sooraj Ina magananmu ta tsaya?"
Dummmm haka Sooraj yaji gabansa yafaɗi, har acikin ransa yama manta da maganan da sukayi da Abban.
Shirun da yayi yasa Abba ci gaba da cewa. "Ayanzune zan matsamaka fiye da da akan maganan aurenka Sooraj, kaduba kai bakajin kunya ne ace har yanzu mahaifiyarka itace zata nunamaka abun daya dace? kula dakai ayanzu ba haƙƙin mahaifiyarka bane, yakamata ne ace kana da mata domin kulawa da irin waƴannan abubuwan, saboda haka ina mai tabbatar maka da tunkan nama abun dazaisa kaji babu daɗi ka nemo mata kakawomin ko acikin satinnan ne ni zan aura maka ita!" Cikin maganganun Abba gaba ɗaya babu wasa, yana gama faɗan haka ya miƙe tsaye yabar wajen. Gaba ɗaya tunanin Raj ne ya tsaya cak, sam baiyi tunanin Abbansa zai sake tada wannan maganan ba, musamman ma da yanzu bawai wani lafiyane ya isheshi ba, inama da Abba yasani dabaiyi maganan nan ba, domin kuwa gaba ɗaya ya sukurkutamasa tunani, duk wani ɗan annushuwan dayake ciki ya kau.
"Ina fata dai kaji abun da mahaifinka ya faɗa ma? kasan shi kakumasan abun da zai iya aikatawa saboda haka tunkan yazaɓama da kanshi kai kazaɓarwa kanka, don na tabbata wannan karon bazai maka da sauƙi ba!" Ummu tafaɗi haka itama tana me miƙewa tsaye, bata wani tsayaba tabi bayan mijinta, akabarsu su biyu akan dinning table ɗin.
Hakanan Ziyada taji murfin ƙirjinta na ƙoƙarin faɗawa.
"Aure akeso yayi?" ta tambayi kanta, sam bata wani fahimci inda kalaman Iyayen Sooraj ɗin suka dosa ba, amma kuma da dukkan alama aure sukeso yayi, tsintar kanta tayi da kasa cigaba da tauna chips ɗin dake bakinta sai kawai ta haɗiyeshi.
Shikuwa Sooraj hannayensa yasanya ya rufe fuskarsa da tafukan hanunsa, wani numfashi me ɗumi ya fesar ta bakinsa, wani irin dokawa ƙirjinsa keyi, sam bayason yaji anyi masa maganan da zata alaƙantasa da mace, bayajin zaiyi aure a irin wannan lokacin, bayamajin akwai wata wacce zata soshi ayanda yake, koda ma wata ta soshi shibabu soyayya atsarinsa, baisan menene so ba, baitaɓayi ba baisan yazai fara ba.
Sam bazata iya jure zaman wajenba, don haka saɗaf saɗaf tamiƙe tsaye tare da juyawa zata bar wajen.
"Waye sa'anki dazakibar masa ragowan dattinki anan?"
Husky voice ɗinsa yadaki dodon kunnenta wanda ya tilasta mata tsayawa, jikinta naɗan rawan tsoronsa ta juyo, plate ɗin data ci abinci tasoma ɗaukewa sannan ta haɗa dana su Ummu ta nufi kitchine, har yanzu bai sauƙe hannuwansa daga kan fuskarsa ba amma kuma komai take yana kallonta. Baitashi akan dinning arean ba harsaida ta tsabtace wajen ta goge, duk abun da takeyi atsorace takeyinsa, fatanta ɗaya kar tayi kuskure yayi mata masifa, tana tsaka da goge kan haɗaɗɗen royal table ɗin yatashi cikin tafiyarsa ta isa yanufi ɗakinsa. Tana ganin shigewarsa ɗaki, ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tare da share hawayen dasuka silalo daga cikin idanunta.
28/May/2020
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
fatymasardauna
#romance
*Chapter 26*
Hanunta tasa da sauri ta goge hawayen daya sauƙo mata akan ƙuncinta, kitchine ta koma ta tare da cigaba da wanke wankenta......
RAJ
Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa. Maganganun Abba gaba ɗaya sun gama dagula masa lissafi, ko tantama bayayi koda sun nemo zaɓinsu sun aura masa awannan karonma bazai iya jure zama da mace ba, dole zai saketa, sannan kuma dole ne zasuyi fushi dashi, ayanzu kam baya tunanin zai sake yarda alaƙa ba masa nauyin wata ƴa mace akansa, koda sau ɗayane yanason iyayenshi su fahimcesa amma kuma hakan ya gagara, kashe shower'n yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa, baidamu da yanda jikinsa ke ɗigan ruwa ba ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje damuwowin dake ranshi to tabbas ƙwaƙwalwa da zuciyarsa bazasu iya ɗauka ba, kaya ya sanya ajikinsa tare da ɗaukan car key ɗinsa yafice daga cikin ɗakin, direct compound ɗin gidan ya nufa, wata baƙar 4matic ya buɗe yashiga tare dayi mata key, tun mai gadi baigama wangale gate ɗin da kyauba ya cilla hancin motarsa waje.
Tafiya yake amma gaba ɗaya hankali da tunaninsa suna wani waje daban, ababban ƙofar asibitin yayi parking, yau bakamar ko yaushe ba, don bai shigar da motar tasa ciki ba kamar yanda ya saba.
Direct office ɗin Dr.Yunus ya nufa, yana knocking aka bashi izinin shigowa, kujera yaja ya zauna tare da miƙawa Dr.Yunus hannu sukayi musabaha, cike da fari'a Dr.Yunus yace. "Yajikinnaka ina fata dai ankama waƴanda suka aikata laifin?"
"Dasauƙi!" Sooraj yafaɗa aɗan gajarce kasancewar bayason zancen yayi tsawo.
Murmushi Dr.Yunus yayi domin sarai yasan halin Sooraj sai mutum ya shekara yana masa magana baitanka ba.
Gyara zama Dr. Yunus ya sakeyi tare da cewa "Result ɗinka yana ajiye tun after 1 week" Wata ƴar drawer dake jikin table Dr.Yunus ya jawo tare da zaro wata farar envelope.
Miƙawa Sooraj yayi tare da cewa "Komai yananan daidai, nayi duk wani bincikena dazanyi Sooraj amma gaskia bangano wata sabuwar matsala ba, magungunan dana baka acan baya sune kawai zakana sha har abubuwa su daidaita!" Dr.Yunus yafaɗi haka cike dason kwantar da hankalin Sooraj.
Wani murmushin gefen baki wanda yafi kuka ciwo Sooraj yayi, shikaɗai yasan wani irin zafi zuciyarsa keyi masa awannan lokacin, karɓan takardan kawai yayi tare da sake bawa Dr. Yunus hanu sukayi musabaha, daganan yafice daga cikin office ɗin, wani irin kallon tausayi Dr.Yunus keyiwa Sooraj, sosai matsalan Sooraj ɗin ke ɗaure masa kai, iya binciken duniya sunyi shida abokan aikinsa amma sam su basu iya gano matsalan Sooraj ba, hasalima komai nasa lafiya lau yake bashi da wata tawaya a halittar jikinsa. .
Tunda yafito daga cikin office ɗin Dr.Yunus yake ganin duhu a idanuwansa, cikin cijewa ya ƙarasa wajen da motarsa take, yana shiga ya kifa kansa ajikin steering motar tare da fesar da wani breath me ɗumi, aƙalla yaɗauki kusan mintuna 9 ahaka batare dako motsi yayi ba, gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya cak.
Da ƙyar ya iya ɗago kansa, idanuwansa tamkar jan garwashin wuta haka suka koma, Envelope ɗin da Dr.Yunus ya basa ya buɗe, tare da zaro wata ƴar farar takarda dake ciki, ahankali ya warwareta tare da sauƙe idanunsa akan rubutun dake cikin takardan . Yana gama karanta abun dake cikinta ya duƙunƙuneta tare da rumtse idanunsa da ƙarfi. Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza tare da ɗauko wata lighter ya kunna, takardan yakawo jikin lighter'n take ta kama da wuta, sauƙe glass ɗin motar yayi ƙasa tare da cilla takardan waje, take takardan ta ƙone ƙurmus, key yayiwa motarshi tare da cillata kan titi yabar wajen....
Ziyada kuwa tana kammala wanke wankenta, ta shige ɗaki bata kuma sake fitowa ba, duk da cewa zaman ɗakin bawani daɗi yakeyi mata ba amma kasancewar bata da abunyi yasanya ta gwammacewa kanta zama waje ɗaya.
***
After 3 days.
Tunda Abba yayiwa Sooraj maganan aure sai ya zamana Sooraj baya zaman gida kwata kwata, idan yafita tun safe bazai dawoba sai after Sallan Isha, kafunnan Abba yajima da dawowa suna tare da Ummu, sam bayason Abba yasake ɗago masa da wannan maganan domin magana ta gaskiya aure agareshi bamaiyiwuwa bane.
Itakuwa Ziyada adaddafe haka take rayuwar cikin gidan duk dama Ummu na sake mata amma bawai wani sabawa sukayiba shiasa takejin kanta atakure, kallone kaɗai abun dake ɗebe mata kewa ayanzu, daga gefe guda kuwa tana lissafin hutunsu wanda yanzu saura musu 1 week sukoma makaranta, har Allah Allah take lokacin yazo, duk da batasan menene makomarta a wajensu ba, batasaniba ko zasu koreta ko zasu barta...
5:15 pm.
Kwance yake akan makeken bed ɗinsa wanda yaji bedsheet na alfarma, dagashi sai long pencil jeans yayinda earpiece ke saƙale a kunnuwansa, gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗinsa, Samsung Galaxy S20 ɗinsa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira. Saida wayar takusa katsewa sannan ya zare earpiece ɗin dake kunnensa, ganin sunan Abba nayawo akan screen ɗin wayar yasanyashi ɗaga wayar da gaggawa, yana kara wayar akan kunnensa. Abba dake tsaye cikin falonsa jin Sooraj ɗin ya ɗaga wayan yasanyashi cewa.
"Kazo kasameni yanzu afalona!" ƙit yakashe wayan batare dayaji me Sooraj ɗin zaice ba.
Ahankali Sooraj yasauƙe wayan daga kunnensa tare da sauƙe ajiyar zuciya, rufe laptop ɗin yayi tare da zuro ƙafafunsa ƙasa, wata bruberry button shirt fara ya ɗauka ya sanya ajikinsa, bedroom slippers yasanya aƙafansa kana yafice daga cikin ɗakin. Tun da ya doshi falon Abban yaji zuciyarsa na bugawa, sam baison sakejin wani abu dazai ɗaga hankalinsa.
Zaune yasamu Abba akan kujera yana duba jaridan daily trust dake riƙe ahanunsa, zama yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa. "Sannu da hutawa" yace da Abba cikin nutsuwa.
Gyara zama Abba yayi tare da aje jaridan dake hanunsa. Kallon Sooraj ɗin yayi sosai tare da ɗanyin gyaran murya. "Ina ka ajiye maganan da mukayi dakai? Shin kasamo wacce kakeso ɗin kokuwa?" Abba yatambaya babu alaman wasa akan fuskarsa.
Ɗan shiru Sooraj yayi tare da haɗiye wani yawu me ɗaci da lokaci guda ya tsaya masa amaƙoshi. "Kayi haƙuri Abba, amma Bansamuba!" yafaɗi haka cikin raunanniyar murya.
"Shikenan babu ma buƙatar kasamo da kanka, Na auramaka ƴaƴan abokaina basau ɗaya ba basau biyu ba kana sakosu babu wani babban dalili, to ayanzuma zan sake ɗaurama aure da ƴar abokina Alhaji Naseer, ina tabbatarmaka da cewa wannan shine naƙarshe, sannan kuma koda wasa idan ka sake kayi gigin sakinta wallahi! wallahi!! babuni babu kai, zan janye hanuna daga duk wani lamarinka, ai kai ba ƙaramin yaro bane kasan daidai kakumasan ba daidai ba, wannan umarni nake baka saika shirya inaso acikin satinnan kaje ka ganta, sannan kuma tana shekaran ƙarshe na kammala degree ɗinta, saboda haka da zaran tagama za a ɗaura muku aure, tashi kabani waje!!!" Abba yaƙare maganar murya akausashe.
Sooraj dake zaune wani irin jiri ne ke ɗibansa, tamkar sauƙan garwashi ajiki haka yaji sauƙan maganganun abba acikin kunnuwansa, take idanunsa suka sauya kala daga farare zuwa jajaye, wani irin ɗaci yakeji amaƙoshinsa, da ƙyar ya iya tashi yanufi hanyar fita daga falon, da kallo Abba yabisa har ya ɓacewa ganinsa, shikam har acikin ransa yasoma zargin ko aljana ce ta shafi Sooraj ko kuma asiri aka mishi, saidai koma menene shidai yana kan ra'ayinsa na dole Sooraj sai yayi aure, domin aganinsa idan da akwai mace akusa dashi to ko bakomai zata rage masa kaɗaici.
Sooraj kuwa koda yabar part ɗin Abba kai tsaye garden yanufa, wani irin ƙunci yakeji azuciyarsa, jiyake kamar yaita tsala ihu kozai samu relief, zama yayi akan wata beautiful chair tare da lumshe idanunsa, wani irin zafi zuciyarsa keyi masa ahankali yake ambaton sunan Allah acikin ransa lokaci guda yaɗanji zuciyarsa tayi sanyi, sake lafewa acikin kujeran yayi tare da maida idanunsa ya kulle tamkar wanda yake bacci.
Ziyada ce ta fito daga part ɗinsu, hanunta ɗauke yake da wani bowl me kyau, sanye take cikin riga da wando na Indian mai kama da pakistan, dayake kalan kayan blue ne shiyasa suka mata kyau sun karɓi white skin ɗinta sosai, ɗan kwalin kayan ta yafa daga kanta zuwa ƙirjinta. Kai tsaye take tafiya zuwa Inda Ummu tace taje ta ciro mata mango, zatayi mango juice. Tana jefa ƙafanta acikin garden ɗin wani Irin sassanyan ƙamshi yadaki hancinta, wani irin ni'ima ne ke tashi acikin garden ɗin, sanyine me daɗi yake ratsa ko ina najikinta, baki buɗe haka take kallon komai dake cikin garden ɗin sosai wajen ya ƙawatu, ƙamshin kayan itatuwane kawai ke tashi. Cikin nutsuwa take tsinkan jajayen mango ɗin. Ahankali ya ware idanunsa ya sauƙesu akanta, lumshe idanunsa yayi tare da sake buɗewa, duk da cewa bayanta kawai yake iya gani amma yanayin yanda take motsa jikinta yasanyashi kasa ɗauke idanunsa akanta, tana kammala tsinkan mango'n tajuya daniyan barin wajen, batare data kulaba tayi tuntuɓe da wani ɗan itace take bowl ɗin dake hanunta ya faɗi mangon ya watse. Bisa tsautsayi itama ta faɗi akan guiwowinta, rumtse idanunta tayi cike dajin zafi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da miƙewa tsaye bowl ɗin ta ɗauka tashiga bin Mangon da ya watse tana ɗauka da ɗaɗɗaya, tana maidawa cikin bowl, kanta aƙasa yake hakan yasa sam bata lura da akwai mutum awajen ba. Batare data luraba taji tataka wani abu tamkar ƙafan mutum, tana ɗagowa sukayi ido huɗu dashi, wani irin faɗuwa gabanta yayi take ƙirjinta yashiga dukan uku uku, ɗago idanunta dake ƙasa tayi take suka faɗa acikin nasa idanun, wani irin abu taji, wanda yataso tundaga ɗan yatsan ƙafarta har zuwa kanta da jijiyoyin jikinta. Pink lips ɗintane suka soma rawa da'alama magana takesonyi amma ya maƙale, ahankali yayi ƙasa da rikitattun idanunsa, sauƙesu yayi akan small lips ɗinta wanda suketa ɓari sukaɗai.
(Note editing🙏🏻kuyi haƙuri yau nashiga busy shiasa banyi muku update da wuri ba please kuyi manage!)
30/May/2020
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
(🌺I'm really proud of you my Wattpad fans, i felt happy with the way you are commenting and voting my work therefore I dedicate this page to you🌺)
*Chapter 27*
Kauda idanunsa gefe yayi tare da ɗauke duk wata annurin dake kan fuskarsa. Ziyada dake tsaye tsaye still akansa cikin wata sarƙaƙƙiyar murya tace.
"Kayi haƙuri....ban...kula bane!"
Bai juyo ya kalleta bama bare tasa ran zai tanka mata, saboda haka ta ɗanja da baya tare da nufar hanyar fita da ga garden ɗin, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi wasu ruwan hawayene suka cika idanunta, itakam batasan me yasa tazama wawiya har haka ba, sam batasan meyasa dazaran abu yashiga tsakaninta dashi take saurin kuka ba, da wannan tunanin ta isa ga babban ƙofan da zai sadata da falon Ummu, hannayenta tasanya ta share hawayen dake kan fuskarta, sannan ta buɗe ƙofar tashiga.
Shikuwa Sooraj tunda yakawar da kansa gefe baisake koda ƙwaƙƙwaran motsi ba, lumshe beautiful eyes ɗinsa yayi tare da maida kansa jikin kujeran, daddaɗan iskan dake hurawa acikin garden dinne ke ratsa ko ina na jikinsa, hakan yasa yaji zuciyarsa ta ƙarayin sanyi.
Zieyada kuwa atare da Ummu suka haɗa Mango juice, babban jug ɗin da mango juice ɗin ke ciki Ummu ta bata tace tasanya a fridge, koda tasanya mango juice ɗin acikin fridge kaitsaye ɗakinta ta wuce, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe manya manyan idanunta, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune, hannayenta tasanya duka biyu ta murza eyes ɗinta, wani irin ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin da ta fuskanci cewa gizo ne idanunta ke mata, bawai shiɗin bane, wani irin yaar taji ajikinta sakamakon tunowa da cikin kyawawan idanuwansa da tayi, tabbas idanunsa kaɗai sun isa rikita duk wata ƴa mace, matuƙar zata kallesu, wani irin sirrin kyau ne ke ƙunshe acikin idanunnasa, aduk randa tsautsayi yasanyata kallon cikin idanunsa ji take kamar zata suma, wasu abubuwane ke yawo ajikinta yayinda takejin kanta kamar wata wawiya, eye balls ɗinsa tamkar magnet ne acikin nata idanun dake matuƙar zautar da ita, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta wanda bata san ma tayi ba, sakamakon tunawa da kyakkyawar fuskarsa da tayi.
"Yana da kyau sosai!!"
Tafaɗa abayyane cikin wata irin murya me sanyi. "Ko abacci ma kyau yakeyi, shi komai nasa me kyau ne!!!" Tasake faɗa tana me murza ƴan yatsun hanunta, itakanta batasan maganganun da take faɗa suna fitowa fili ba, gaba ɗaya ashagalce take, fararen ƙafafunta ta zuro ƙasa tare da tashi tsaye, direct wajen window ta nufa, ɗan yaye labulen window'n tayi tare da soma bin ko ina dake cikin compound ɗin gidan da kallo, idanunta ta tsayar asetin ƙofar shiga garden ɗin, dai dai lokacin yafito daga cikin garden ɗin hanunsa riƙe da wani green apple, tafiya yake kansa tsaye yayinda skin ɗinsa keta walwali kallo ɗaya zaka masa kasan hutu da kudi sun zauna masa, tundaga wajen da take tana iya hango yanda tarin suman dake kansa ke sheƙi, gashi ya kwanta luf luf tamkar sajen dake kwance akan fuskarsa, bata taɓa ganin wani irinsa ba, shi na dabanne ko acikin maza, hannunta takai ta dafa glass din dake jikin window'n, fuskarsa kawai take kallo, akullum tana mamakin yanda yake rayuwarsa babu annuri akan fuskarsa, koda yaushe haka yake baka taɓa ganin dariyarsa, kafun kaji maganarsa ma wahala ne, shi komai nasa is difference, Maganan aurensa ne ya faɗo mata lokaci guda ta marerece fuska tare da ɗan taɓe soft lips ɗinta. "Wace zata aureshi?" tambayar da tayiwa