Author : Maman Teddy Category : Romance
haɗe take da hula, hulan ta sanya ta rufe kanta. Saida tayi sallan Magriba sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito don samawa cikinta abinci. Ahankali take sauƙowa daga kan matattakalan falon, tunkafun ta gama sauƙowa, ƙamshin turaren daya zame mata abunso ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi tare da waresu alokaci guda, mamakine yakamata na rashin ganinsa afalon, don tasan tabbas indai taji ƙamshinsa to yana wajenne. Harta gama sauƙowa daga kan steps ɗin bata iske kowa acikin falon ba, kai tsaye kitchine ta wuce, kasancewar yau ba a haɗa abinci akan dinning ba. Fried cous cous and egg sauce aka dafa, kaɗan ta ɗiba don bata wani cika cin abinci da yawa ba, buɗe ɗayan food flask ɗin tayi, nan taga pepper soup ne na chicken's aciki, rufewa tayi don wannan ɗinma kaɗai ya isheta. fridge ta bude ta ɗauko ruwa, daidai lokacin Oummu tashigo cikin kitchine ɗin, ganin Zieyaderh a kitchine ɗin yasanya ta cewa.
"Yauwa Zieyaderh zoki kaiwa Sooraj coffee yana ɗakinsa"
Wani irin ƙululuuuuu haka ƴaƴan cikinta suka hautsina, ambatonsa ba ƙaramin faɗar mata da gaba yake yi ba, batasan mene dalili ba koda zancensa ake sai taji gabanta ya faɗi, ko kuma taji zuciyarta ta tsinke, ganinsa kuwa baƙaramin je fata acikin wani irin Yanayi yake ba. Bata gama idar da tunanin nata ba, Oummu ta miƙo mata wani tray me ɗan faɗi, wanda samansa ke ɗauke da kayan haɗin coffee da kuma ɗan madaidaicin cup me kyaun gaske, sai kuma small flask. "Idan kinje ki haɗa masa, ai dai kinga yanda na haɗa masa ranan ko?" Oummu ta tambaya tana me miƙa mata tray ɗin. Kamar wadda aka zarewa laka ajiki haka ta amshi tray ɗin tare da cewa "Eh nagani" Ficewa tayi daga cikin kitchine ɗin, yayinda zuciya da ƙirjinta keta bada wani irin sauti.
Dawowarsa daga Lagos kenan, dama baije don ya kwana ba, socks ɗin dake ƙafansa ya cire sannan ya zare suit ɗin dake jikinsa, maɓallan long sleve ɗinsa yashiga cirewa, yana kammalawa ya cire rigar tare da zare white singlet ɗin dake jikinsa, belt ɗin wandon shi ya zare yana me ƙoƙarin zame wandon ƙasa yaji ana knocking ƙofarsa, bai kula ba ya cigaba da cire kayansa, jin still ana knocking ɗinne yasanya shi ɗaukan wani 3 guater jeans ya sanya, ko gama zuge zip ɗin wandon baiyi ba, ya nufi wajen ƙofar ransa aɓace, ko damuwa da yanda saman maranshi ta bayyana baiyi ba. Itakuwa Zieyaderh dake tsaye gaba ɗaya atsorace take, harta gama yanke shawaran cewa zata koma kawai tace da Oummu ƙofar a kulle take. Da wani irin fushi ya buɗe ƙofar, idanunsu suka faɗa cikin na juna, kallonta yayi from head to toe sai kawai yasaki wata tsuka me sauti tare da komawa cikin ɗakin, ganin haka yasa jikinta ya shiga ƙyarma ba shiri ta bi bayansa, hannunta har rawa yake wajen aje tray ɗin, ƙoƙarin haɗa masa coffee ɗin take ya juyo tare da soma tahowa inda take, cak ta tsaya daga haɗa coffee ɗin da take, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tabbas kunnuwanta sautin takunsa suke jiye mata, wanda ke ɗauke da alaman cewa gareta yake zuwa, hakan yasa wani uban tsoro ya lalluɓeta, wanda har ya kaita ga kasa ɗaga kai ta kalleshi. Taku biyu kacal ya rage atsakaninsu yace. "Ke!!"
Da sauri ta ɗago kanta aɗan daburce tace "Umm!" sake matsowa kusa da ita yayi wanda hakan yasa gaba ɗaya takusa ficewa hayyacinta, gab da ita yazo har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sosai ta ruɗe sakamakon ganinsa agabanta, baƙaramin cika mata idanu yayi ba, gaba ɗaya ba ta iya ganin komai don yacika mata gaba da faffaɗan chest ɗinshi, haka ta zama wata ƴar cukula agabansa, gaba ɗaya jikinta ɓari yake.. Cikin wani irin husky voice ɗinsa yace. "Ke baki da hankali ko? Haka aka koyar dake bugun ƙofa?"
Yanzu kam ba iya gangar jikinta bane ke rawa, harma da laɓɓan bakinta, cikin daburcewa tayi ƙasa da idanunta don bazata iya kallonsa ba, idanunta ne suka sauƙa akan waist ɗinshi wanda har saman mararsa ta bayyana, kasancewar har yanzu bai ƙarasa jan zip ɗin wandon nasa ba, wasu jijiyoyine kwance akan maran nasa wanda suka mimmiƙe, ga wani irin murɗewa da cikinsa yayi, da sauri ta rumtse idanunta, tana me ƙara ƙanƙame jikinta. "Badake nake magana ba!!" Yafaɗa atsawace. Baƙaramin tsorata ta wannan tsawan yayi ba, har batasan lokacin da ta ƙanƙame jikinta sosai ba, bakinta na rawa tace "Dan Allah kayi haƙuri, Allah Bazan sake ba!"
Kallon fuskarta yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa, hannayensa ɗaure akan waist ɗinsa yace. "Buɗe idanunki!"
Kasa buɗe idanunnata tayi saima rawan jiki data ƙara, tare da kullesu ƙam.
"I say open your eyes!!!" Yafaɗa murya akausashe. Tun kafun ya gama idar da zancen, ta buɗe idanunta tare da sauƙesu akansa. Sarƙewar idanunsu waje guda yasanya idanunta sukayi wani irin juyawa, take suka wani irin lumshewa luuuuu kamar zata sume. Cikin tsawa yace "Wallahi idan kika sumemin saina wanka miki mari stupid girl!!" ae kuwa tamkar wanda ya watsawa ruwan sanyi saigata ta tsaya cak akan ƙafafunta, tare da sake maida idanunta ta rufe, saidai ya kasheta amma tabbas bazata iya kallon cikin ƙwayan idanunsa ba, musamman ma ayau, idan kuwa tace zata sake kallonsa to tabbas sumewa zatayi koda kuwa kasheta zaiyi bayan ta farfaɗo.
Tsaki yayi tare da nuna mata hanyar ƙofa murya akausashe yace. "Out!"
Ae kamar jira take haka ta tattari ƙasan riganta aguje ta fice, baki ya buɗe yana mamakin yanda tasa gudu kamar wacce aka turowa dodo. "Wannan yarinyar anya tana da lafiya kuwa?" Tambayar daya yiwa kansa kenan cike da mamaki, ƙofarsa ya rufe tare da murza mata key, bathroom ya shige tare da sakarwa kansa shower.
Aguje ta haura steps ɗin dake cikin falon, tana kaiwa ɗakinta ta shige tare da rufo ƙafar, kan gado ta faɗa tare da lumshe idanunta, har yanzu jikinta baiwani gama daina ɓari ba, saida ta ɗauki kusan 8 minute tana maida numfashi, kafun tasamu daman dawowa cikin nutsuwarta. Shiru tayi tare da cusa kanta acikin pillow, yau kam gaba ɗaya brain ɗinta ta cushe, yayinda tunaninta kuwa gaba ɗaya ya gudu.
Ruwan shower ne ke dukan lafiyayyar fatan jikinsa, yayinda hannunsa ɗaya ke dafe da bango, akasalance ya buɗe idanunsa, kasancewar yajima tsaye ruwa na dukansa, hakan yasa idanunnasa suka ɗanyi ja. So yake ya goge wannan tunanin daga cikin ransa, so yake wannan idanun su fice daga cikin nasa idanun, so yake duk wani abu dake cikin zuciyarsa ya goge, baishirya ɗaukan wannan ƙalubalen ba, bakuma yajin zai shirya har abada, hannu yasa ahankali ya kashe shower'n, tare da ɗaukan wani nead towel ya ɗaura akan waist ɗinshi. Haka ya fito daga cikin bathroom ɗin jikinsa na ɗigan ruwa, wani ɗan ƙaramin towel ya ɗauka ya shiga goge jikinsa, sama sama ya shafa mai ajikinsa, sannan ya sanya long jeans, shida kansa ya haɗa coffee ɗin yasha, jin ana ƙiraye ƙirayen sallan Isha ne yasanyashi miƙewa, wata farar rigar Dolce and Gabbana mai kamar na sanyi ya sanya, kasancewar ana yanayin sanyi hakan yasa ya jawo hulan dake jikin rigan ya rufe kansa dashi. Yana fitowa ya haɗu da Almustapha shima masallacin zaije saboda haka atare suka wuce.
Washegari.
Tun seven yagama shiryawa, wayarsa ya ɗauka tare da turawa shugaban makarantar text message, ko 4 minute ba ayiba saiga ƙiran shugaban makarantar ya shigo wayansa. Fuska yaɗan taɓe sannan ya ɗaga wayar, bayan sun gaisa ne, Principal ɗin yace.
"Naga saƙonka amma banƙi ta taka ba, saidai bakowa muke bawa irin wannan uniform ɗin daka buƙata ba, mukan bawa ire irenta ne yara da sukayi aure basu kammala school ɗinba, to idan zasu ci gaba da zuwa shine muke basu, amma tunda haka ka keso babu damuwa"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa "Nagode, sannan kuma karka manta idan ansamu wani problem ka ƙirani, kamar yanda kaƙirani a wancan time ɗin da aka kaita hospital, so ba matsala always zaka iya nemana!"
"Okay dont mention" Principal din ya faɗa tare da aje wayan.
Shima wayartasa ya aje tare da ɗaukan cover disigner shoe ɗinsa ya shiga sanyawa, iya kyau kam yayi sa, saidai kuma amma fuskar nan ahaɗe take babu alamar fari'a akanta.
Zaune suke su duka uku akan dinning ɗin, sanye take da kayan uniform ɗinta na riga da wando, ahakali take tsakalan chips ɗin dake gabanta, gaba ɗaya batajin daɗin zama acikinsu don haryau ganinta take amatsayinta na bare. Gaba ɗayansu ƙamshin turarensa ne ya cika hancinsu. Cikin ƙasaitarsa yake tahowa hannunsa ɗauke da wata ƴar briefcase me kyau, kujera yaja ya zauna cikin ƙasan maƙoshi yace "Barka da safiya Oummu" murmushi tayi masa tare da cewa "Barka, hope kunyi waya da commisioner?"
Kansa ya kaɗa mata alamar "Eh"
Mood ɗinta ne yaɗan sauya tare da cigaba da cewa "Ya faɗa maka cewa yarannan da suka harbeka sun faɗi wanda ya turosu ko? gaskiya nikam nashiga fargaba da tsoro, indai har akan aikinka za a iya turowa akasheka, me kenan kake tunanin zai faru anan gaba? zasu iyayin komai!" ta ƙare maganar fuskarta cike da damuwa.
Kafun Yayi magana Almustapha yace "Nima nayi mamaki ƙwarai da akace wai MR.J.J ne yaturo ayimaka hakan, wani irin tsananin gabane ke tsakaninka dashi ne wae? Meyake nema dakai ne, tunfa sanda aka baka BM yakejin haushinka, gaskia yanzu kam baikamata mubarshi ba!" ya ƙare maganar cikin yanayi naɗan ɓacin rae.
Aje mug ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa "Its Okay, anyi arresting ɗinshi jiya" yana gama faɗan haka ya miƙe tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa, briefcase ɗinsa ya ɗauka ya fice, duka suka bishi da kallo, hakanan yake shi koda yaushe baiso ayi magana me tsawo dashi, sai kace marar gaskiya.
Ture plate ɗin abincin dake gabanta tayi tare da ɗaukan school bag ɗinta dake gefe ta rataya.
Zieyaderh Oummu taƙira sunanta, "Na'am" ta amsa asanyaye. "karki manta inkin dawo ki sameni aɗakina kinsan gobene tafiyarmu" "To" kawai tace sannan ta juya tafice daga cikin falon, tana fitowa compound ɗin gidan shikuma motarsa na fita daga cikin gidan, mota tashiga ranta duk ba daɗi.
Ko amakaranta yau bata wani sake ba, bayan sundawo break ne aka turo wae principal na ƙiranta, saida gabanta yafaɗi amma haka ta daure taje, wata leda ya bata wanda ke ɗauke da wasu sabbin uniform har kala uku yace mata daga yau su zatana sanyawa. Sosai tayi mamaki amma sai bata nunaba ta amsa kawai ta fice, koda taje aji suka duba kayan, sket ne irin high waist ɗinnan wanda ƙasansa yake da faɗi, sai kuma wata ƴar rigar makaranta fitted da hijab ɗinta wanda idan tasa zai ɗan sauƙo mata kaɗan. Mamakine ya kashesu su dukansu. Shukra ce tace "Wannan fa kayan bakowa kesawa a school ɗinnan ba, kodai kinzama house wife ne bamusani ba?" hararanta Zieyaderh tayi tare da turo baki gaba cikin takaici tace "Ni bawata house wife ɗin dana zama!" dariya suka sanya su dukansu, daga haka sukaci gaba da hiransu, kaɗan kaɗan take sa musu baki. Har aka tashi sukuku haka takejin kanta, koda ta koma gida ko falo bata sauƙo ba, haka ta ƙare kwanciyarta aɗaki... Washegari Saturday. Ƙarfe 8 daidai ta kammala shiryawa cikin kayan da Oummu ta bata tace tasanya, riga da sket ne na tsadaddiyar atamfar Vlisco, wacce taji ɗinki, sket ɗin irin pieces ɗinnan ne yayinda rigan takasance fitted, sosai kayan suka amshi jikinta, kasancewar atamfar kalan Maroon gareta hakan yasanya ta sanya maroon hijab ajikinta, sosai tayi kyau duk da cewa batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, flat shoe ɗinta ta sanya tare da kallon kanta amadubi, ita kanta tasan tayiwa kanta kyau. Saida suka biya ta wani super market Oummu tayi sayayya sannan suka ɗauki hanyar zuwa KD inda acan ƙauyen su Zieyaderh yake. Ƙarfe 1 na rana daidai suka iso cikin ƙauyen nasu na Saminaka, tun daga lokacin ƙirjin Zieyaderh ke dukan uku uku, da ƙyar take iyayiwa Kamalu driver kwatance har suka iso ƙofar wahalallen gidansu, tun shigowarsu ƙauyen yara kebinsu yayinda manya kuwa ke bin haɗaɗɗiyar motarsu da kallo. Shawo kwanan Malam Garba kenan hannunsa ɗauke da wani buhu, turus haka yaja ya tsaya yana me bin motar daya gani fake aƙofar gidansa da kallo. Da sauri ya ƙarasa daidai lokacin kuma su dukansu suka fito daga cikin motar, koda zata shekara ɗari ne batanan bazai taɓa kasa gane jininsa ba, bakinsa abuɗe fuska ɗauke ɗa mamaki yake kallon Zieyaderh, itama kallonsa take lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ji take kamar taje ta rungume Baban nata, amma kuma tanajin tsoro. "Ziyada!" yaƙira sunanta muryarsa na rawa. Kasa amsa masa tayi sai kawai ta fashe da kuka. Shima hawayene kwance acikin idanunsa. Kamar wadda aka wurgo daga sama haka Inna Ma'u tafito daga cikin gidanta, don tuni labari yakai mata cewa wata haɗaɗɗiyar mota fa faka aƙofar gidanta. Bakinta awangale taƙarasa gaban yarinyar da take kallonta kamar Zieyaderh, hannu tasa taɗan taɓa fuskar yarinyar dake kuka, "Laaaaa ha'ila wallahi itace, shegiyar gari kin gama gararanbanki kindawo ko?" Inna Ma'u tafaɗa tana me ƙarewa Zieyaderh kallo, mamaki kuwa aranta kamar zai kasheta. Ƙasa Zieyaderh tayi da kanta, Malam Garba shine wanda ya kama hannunta tare da duban Oummu dake tsaye yace.
"Hajiya kushigo daga ciki!" Babu musu Oummu ta bi bayansa yayinda yake riƙe da hannun Zieyaderh, aikuwa Inna Ma'u ma rufa musu baya tayi bayan ta tsaya ta gama ƙarewa motar da sukazo da ita kallo, harwani yawu ta haɗiya natsananin kwaɗayi dason abun duniya, musamman ma da ta hango ɗan ragowan lemun fanta dake gaban motar.
Gudu gudu sauri sauri haka taje ta ɗauko tabarma ta shumfuɗawa Oummu baki har kunne tace "Hajiyan Birni zauna mana!" Murmushi Oummu tayi tana me kallonta sannan ta zauna aranta tace "Kamar bayanzu tagama zagi ba" Malam Garba da kansa ya kawo musu ruwa, ita dai Zieyaderh laɓewa tayi abayan Oummu, don har cikin ranta tana jin tsoron abun dazai biyo baya.
Gyara zama Oummu tayi tare da ɗagawa baban Zieyaderh gaisuwa, amutumce ya amsa, kafun tasake wata magana Inna Ma'u tayi saurin cewa. "Mutanen Binni Sannu marabanki da zuwa Hajiya!" Still murmushi Oummu tayi tare da jinjina kanta alaman yauwa. Batare da ta bari kowa acikinsu yace wani abuba tace "Lallaima Zieyaderh wato dakika gudu kaina kikeso na aurawa tsoho ɗan dashen? ko kuwa kina tsammanin nida ubanki muna da kuɗin da zamu biyasa abun daya kashe ne, wallahi mudai kin cucemu akan guduwarki saida duk wani ɗan abun dana mallaka ya ƙare saboda ɗan dashe cewa yayi sai mun biyasa kudin daya kashe, kin cuceni kin cuci mahaifinki wallahi!!" Imma Ma'u tafaɗi haka tana me matse wasu munafukan hawayen ƙarya data ƙaƙalosu da ƙyar. Sake cewa tayi "Amma Allah ne zai mana sakayya, koda yake ma ai yanzu nasan kintara kuɗi sosai ko bakomai zan fanshe asarata" tana murmushi ta ƙare maganar. Oummu kam mamaki al'ajabi haɗi da tsoro al'amarin matar ya bata, wato dai ita ko agaban wayene bazata iya ɓoye maitanta ba. Cikin sauri taɓuɗi baki zata sake cewa wani Abu, da sauri Malam Garba yace "Ya isa haka Ma'u, dafari ya kamatane mufara sanin ina taje bawai irin waƴannan kalaman yakamata ayi mata ba" afusace Inna Ma'u tajuya zata faɗa masa baƙar magana sai kuma tatuna da wani abu tafasa. Saita fara yaƙen ƙarya tana me ƙarewa komai dake jikin Zieyaderh kallo.
Murmushin takaici Oummu tayi tare da kai dubanta ga Baban Zieyaderh, sannu ahankali tayi masa bayani akan cewa ɗantane ya tsinci Zieyaderh bawai yawon iskanci ta tafi ba. Ajiyar zuciya me ƙarfi Malam Garba ya sauƙe tare dayiwa Allah godiya daya sanya ƴarsa ta faɗa hannu na gari. Itakuwa Inna Ma'u afakaice take hararan Oummu aranta kuwa cewa tayi "Kuji ƙaryan banza, yo koma gaskiya ne wayasan abunda sukeyi dashi ɗannaki, kai banma yarda ba yanda yarinyarnan tayi ɓul ɓul da ita akwai abun da take aikatawa wata ƙilama cikine da ita" tana gama ƙimtsa zancen zucinta tayiwa Zieyaderh ƙuri, ba inda take kallo kamar cikinta, wai adole saita gano ko cikine da ita, burinta bai wuce taga tumbinnata yaɗan taso ba ta tabbatar da zarginta.
Godiya sosai Malam Garba ya shiga yiwa Oummu na irin riƙon amanar da tayiwa ƴarsa, don har acikin ransa yana me nadamar irin rashin kulawan daya nuna mata abaya, sannan kuma yana ƙaunar ƴarsa sosai, dan itace kaɗai jininsa aduniya, amma yazaiyi da sharri da kuma tsoron Inna Ma'u da yake, duk itace ummul aba'isin faruwar komai. Miƙewa yayi yace zaije ya samo musu fura. Aikuwa yana fita Inna Ma'u tace "Hajiyan birni ince dai ɗannaki daya tsinceta gidanki ya kawota ba gidansa ba?"
Mamakine ya kama Oummu cike da mamakin tambayar tace "Mekike nufi?" da sauri Inna Ma'u ta washe baki tare da cewa "A'a babu abun danake nufi kawai dai tambaya ne, ke Zieyaderh cire lufayan mana kisha iska" Tafaɗa cike da zaƙuwan son ganin yanda cikar halittan Zieyaderh'n ya koma, tayi rantsuwa matuƙar taga cikin Ziryaderh yaɗan tasa to wallahi saita cucesu maƙudan kuɗaɗe. (Chaii guys Inna Ma'u fa ta tsananta😆)
Kallon Oummu Zieyaderh tayi, idanu Oummu ta mata alaman karta cire mayafinta, aikuwa saita yi burus da maganan Inna Ma'u. Wani irin malolon baƙin cikine ya cika zuciyar Inna Ma'u, don sarai ta ga lokacin da Oummu tayiwa Zieyaderh'n idanu. Aranta tace "Wallahi ko zaku mutune saina laƙaba muku wani sharrin dasai kunbani kuɗi ƴan iska"
Babu jimawa Malam Garba ya dawo hannunsa ɗauke da ƙwaryan nono, babu wani ƙyama haka Oummu ta zage tasha nonon daganan tace da Malam Garba idan ba damuwa tanaso tayi magana dashi. "Magana kuma dashi kaɗai?" Inna Ma'u ta tambaya tana zare ido. Babu wanda ya kulata saima iso da Malam Garba yayiwa Oummu zuwa soro tayanda babu wanda zaiji abun da suka tattauna, cike da fahimtan juna Oummu tayi masa bayanin duk wani abu dake tafe da ita, har acikin ransa yayarda da matar da kuma kamalanta saboda haka atake ya amincewa buƙatarta baƙaramin daɗi