Author : Maman Teddy Category : Romance
numfashi take ta sauƙewa ahankali, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci ɓarawo yayi gaba da ita.
Tunda ya kwanta bai tashiba sai ƙarfe 4, da wani irin zazzafan zazzaɓi ya buɗe idanunsa yayinda yakejin gaba ɗaya komai na duniya bayayi masa daɗi, lumshe rinannun jajayen idanunsa yayi tare da ɗan yunƙurawa, cikin ɗan kuzarin daya rage masa ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, koda ya miƙe tsaye wani luuuu haka yaji tamkar wanda zai faɗi, adaddafe ya nufi bathroom ɗinsa. Shower ya kunna tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya dafe bango, lumshe idanunsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya, sauƙan ruwan shower ɗin akansa ba ƙaramin nutsuwa ya samar masa ba, sake gyara tsayuwarsa yayi still hannayensa dafe da bango ya lumshe kwawawan idanunsa, sannu ahankali komai ke dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, sai yanzu yakejin nutsuwar yin tunani, wani irin saliva me ɗaci ya haɗiya amaƙoshinsa, tabbas ƘADDARA tayi masa sauyi irin wanda bai zata ba, kusan minti 20 ya ɗauka agaban shower'n ruwa na dukan pure skin ɗinsa, jikinsa ya janye kana ya kashe shower'n, gaban sink ya ƙarasa tare da ɗauro alwala.
Cikin wani tsadadden getzner blue colour ya shirya kansa, wanda yaji ɗinkin half jumper, sosai kayan sukayiwa jikinsa kyau, sallaya ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan La'asar, wanda baisamu daman yiba sakamakon bacci da yake. Wayoyinsa ya tura acikin aljihun wandonsa, ɗan jim yayi tare da jingina bayansa da jikin bango, wani irin sarawa kansa keyi masa yayinda zazzaɓi ke ƙara cin ƙarfin jikinsa, idanunsa da ako yaushe suke farare ƙal sai gashi yau gaba ɗaya sun sauya kala sun koma launin ja, key ɗin motarsa ya ɗauka inda ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fice, mercedes ɗinsa ya buɗe ya shiga, kansa ya kifa ajikin steering motar tare da fesar da wani irin numfashi, wayarsa ce takawo haske alaman shigowar saƙo, ganin sunan Oummu yasanyashi shiga cikin saƙon. _"Kozo cikin gaggawa inason ganinka!"_ shine abun da aka rubuta acikin saƙon,
Murza key ɗin motar yayi tare dayin reverse, maigadi ne ya wangale masa gate ya tura hancin motar tasa waje.
Gudu sosai yakeyi akan titin wanda shikansa baisan dacewa gudu yakeyi ba domin gaba ɗaya nutsuwarsa bata jikinsa, gawani irin ciwon kai dake addabarsa kamar kansa zai rabe gida biyu haka yakeji.
Tashinta kenan daga baccin da tayi, wani sabon zazzaɓine yasake rufeta saidai na yanzu baikai na ɗazu ba, hakan kuma yana da nasaba da kukan da tasha ta ƙoshi, Aunty Muhibbat ce ta tursasata akan cewa taje bathroom ɗin Oummu tayi wanka tazo ashiryata don anjima da dare za'a damƙata ga Mijinta, badon tasoma haka Aunty Muhibbat tasata agaba harcikin toilet suka shiga ta haɗa mata ruwan wanka, cikin rashin kuzari tayi wanka yayinda ta ɗaura wani farin towel ajikinta, kwata kwata iya cinyarta towel ɗin ya tsaya, hannunta tasa ta dafe kanta sakamakon tunowa da cewa tabar kayanta akan gadon Oummu, sannan kunya bazai barta tafita da wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ba.
Daga waje yayi parking motarsa inda yashiga cikin gidannasu da ƙafafunsa dayake magriba ta kawo kai sannan gaba ɗaya mutanen da suka zo bikin suna ɗayan ɓangaren dake cikin gidannasu hakan yasa kai tsaye ya wuce ɓangaren Oummu ganin bai ganta afalo bane yasanyashi haurawa sama kaitsaye.
Ahankali taɗan buɗe ƙofar ban ɗakin ta leƙo kanta, ganin babu kowa acikin ɗakinne yasanyata fitowa cikin sauri batare da ta tsaya goge ƙafanta dake ɗigan ruwa ba,
yana zuwa ya ɗaura hannunsa akan handle ɗin ƙofar tare da turata ciki, daidai lokacin ita kuma ta kawo tsakiyan ɗakin jin motsin taɓa ƙofa yasanya ta juyo arazane bisa tsautsayi ruwan dake ƙafanta ya gogi tiles take tsantsin tiles ɗin ya ɗebeta wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin dake jikinta ya zame yayi ƙasa.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 45*
Wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin jikinta ya zame ya faɗi ƙasa, cikin tsautsayi ƙafanta ya bugi jikin gado, suuuuu haka tatafi zata faɗi, cikin abun da baiwuce 1 second ba ya ƙaraso cikin ɗakin, da sauri yaƙarasa tare da sanya duka hannayensa biyu ya tarota, inda ya zube ƙasa kan guiwowinsa, cikin tsananin tsautsayin dake jansa ya sauƙe idanunsa akan naked pure white breast ɗinta, da sauri ya rumtse idanunsa yayinda lokaci guda yaji tamkar andoka masa guduma atsakiyar kansa, gaba ɗaya jikinsa ne ya soma ɓari,
Ita kuwa Zieyaderh tamkar wata matacciya haka gaba ɗaya jikinta ya sandare, yayinda ta kulle idanunta ƙaƙam, cikin tsananin tsoron dake ɗawainiya da zuciyarta haɗi da fusgewar numfashi ta ɗan buɗe idanunta kaɗan, wani irin ƙara tasake sakamakon ganin fuskarsa da tayi, cikin tsananin ruɗewa haɗi da zabura ta tashi daga jikinsa,
aruɗe ta soma ƙoƙarin neman towel ɗinta daya faɗi, don suturce jikinta, irin yanayin ruɗewan da tayi yasanya takasa ganin towel ɗin, wanda kuma yashe yake agabanta, cikin hanzari ta jawo blanket ɗin dake kan gadon na Oummu ta rufe gaba ɗaya jikinta dashi, zamewa ƙasa tayi tare da sakin wani irin marayan kuka wanda ke ɗauke da tsananin takaici da kuma haushin kanta, wata fitinanniyar kunyace gaba ɗaya ta rufeta.
Jin diran sautin kukanta da yayi acikin kunnuwansa, yasanyashi miƙewa daga durƙuson dayayi, cikin dauriya dason kawar da zazzafan ciwon kan daya kawo maza cafka lokaci guda, ya juya tare da nufan hanyar barin ɗakin.
Kasancewar har yanzu idanunsa arufe suke, hakan yasanya sam baikula da Oummu da kuma Aunty Muhibbat dake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin ba,
jin cewa yayi karo da mutum ne yasanyashi saurin buɗe idanunsa, nan ya sauƙe su akan fuskar Oummu dake tsaye tana kallonsa, kansa ya sunkuyar ƙasa tare da raɓawa ta gefenta zai wuce, cike da mamakin yanda idanunsa sukai jajur Oummu tace.
"Kajirani a falon ƙasa".
Kansa kawai ya jinjina mata alaman. "To"
Ahankali yashiga taka matattakalan da zai sadasa da falon ƙasan.
Oummu kuwa dubanta takai ga Aunty Muhibbat, gane abun da Oummun ke nufi yasanya Aunty Muhibbat murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta shiga da sauri, don ta duba Zieyaderh wacce sautin kukanta ke ratsa kunnuwansu.
Oummu kuwa juyawa tayi tare da fasa shiga ɗakin, kaitsaye tanufi matattakala don sauƙa ƙasa.
Da auri Aunty Muhibbat ta ƙaraso inda Zieyaderh'n ke zaune, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya acikin blanket tana kuka.
Kallon towel ɗin dake ƙasa Aunty Muhibbat tayi tare da sakin murmushi, cikin kulawa ta zauna akan gado tare da sanya hannu ta dafa kafaɗa Zieyaderh.
"Jikinne har yanzu?" ta tambaya tana me ƙoƙarin jawota ta zaunar da ita akan gadon Oummu.
Jin muryar Aunty Muhibbat acikin kunnuwanta, yasanyata sake ɓoye kanta acikin blanket, tare da ƙara sautin kukanta.
Still murmushi Aunty Muhibbat tayi cikin rarrashi tace.
"Kukan ya isa haka, ko so kike kanki yayi miki ciwo? maza tashi ki sa kayanki kinji, ko SOORAJ yayi miki wani abune?" Aunty Muhibbat ta tambaya.
Cikin sheshsheƙan kuka tagirgiza kanta alaman.
"A'a"
Murmushi Aunty Muhibbat tayi tare da cewa.
"To tashi kisa kayanki, ko so kike kowa yazo yana ganinki ba kaya?"
Cikin nutsuwa Oummu ta kai dubanta garesa, murya asanyaye ta ƙira sunanshi.
Amsa mata kawai yayi batare daya ɗago kansa ya dubeta ba.
Cikin kulawa ta gyara zamanta tare da cewa.
"Duk da wannan bashine karo na farko da muka fara yi maka aure ba, amma inaso kasancewa wannan auren daban yake da sauran, bandamu ba koda zakaji cewa hakan da mukayi rashin kyautawa ne agareka, saidai inason kasan cewa ban taɓajin ina yimaka sha'awar rayuwar aure da wata mace ba kamar Zieyaderh,
kamar yanda kaine ka kawota kakuma riƙeta tunkan musan da ita, ayanzuma haka nakeso kacigaba da riƙeta, kai ba ƙaramin yaro bane Sooraj, kamar yanda na gargaɗeka abaya akan sakin aure, to awannan karon ma zan gargaɗeka, Wallahi! Wallahi!! Sooraj idan har ka saki yarinyar nan Zieyaderh kamar yanda kake sakin sauran matan da muke aura ma to tabbas saina tsinemaka!!"
Amatuƙar razane Sooraj yaɗago kansa da idanunsa wanda sukayi jajur ya kalli mahaifiyar tasa, gani yayi sam babu alamar wasa akan fuskarta, sake gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
"Kada kaɗauki maganata amazaunin wasa, idan kuma kace bahaka ba lallai zan shayar dakai ruwan mamaki"
Miƙewa tsaye tayi tare da ɗan soma tattakawa har takai bakin steps taɗan tsaya tare da juyowa, dubansa tayi kana tace.
"Bazan baka ƴar mutane katafi da ita gidanka ba, dole anan zaku zauna, saboda haka anjima za'a kai maka amaryarka, cikin part ɗinka dake gidannan, sannan kuma Wallahi idan ka cutar da ita ban yafe maka ba!" Tana gama faɗin haka ta juya tare da soma haura steps ɗin.
Ahankali Sooraj yaɗago idanunsa wanda suka zama tamkar garwashin wuta yabi bayan mahaifiyar tasa da kallo, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da lumshe kyawawan idanunsa, jiki asaluɓe haka ya tashi ya bar cikin falon.
Wani irin haɗaɗɗen lace purpule colour mai taushi wanda yaji ɗinkin riga da sket ta sanya, sosai kayan ya zauna ɗas ajikinta, inda farar fatarta ta sake bayyana acikin purpule colour lace ɗin, tsayawa ajikin madubi tayi tare da duban kanta, wani irin kunyane ya kamata sakamakon ganin yanda gaba ɗaya rabin ƙirjinta ya bayyana ta saman wuyar rigar, rumtse idanunta tayi ayayinda taji tsikar jikinta na tashi, sakamakon tunowa da yanda hannayensa suka sauƙa akan naked skin ɗinta da tayi, da sauri ta sanya hannu ta rufe fuskarta, wani irin haushi da kunyan kanta takeji, turo ƙofar ɗakin da akayine ya sanyata shiga cikin nutsuwarta.
Aunty Muhibbat da Bilkh ne suka shigo, ganin yanda tsadadden leshin ya zauna ajikin Zieyaderh yayi mata kyau, yasanya Aunty Muhibbat sakin murmushi tare da cewa.
"Masha Allah!"
Zama tayi akan stull ɗin mirror yayinda Bilkh tashiga aikin tsantsara mata kwalliya akan kyakkyawan fuskarta, duk da cewa bawani uban kwalliya sosai akayi mata ba, amma sosai
tayi kyau, ɗauri mai kyau Bilkh tayi mata tare da yafa mata wani babban mayafi ajikinta wanda yake purpule colour marar nauyi, sosai Zieyaderh tayi kyau irin mai ɗaukar hankalin nan, yayinda oil lipstick ɗin da aka shafa mata akan lips ɗinta keta shinning.
Sooraj kuwa yana fita daga cikin falon na Oummu kai tsaye gaba ɗaya gidan ya bari inda ya wuce night club, can yaje suka haɗe da Mas'oud.
Ƙarfe 8 daidai Aunty Muhibbat ta kamo hannun Zieyaderh inda ta ƙarasa da ita har gaban Oummu da ke zaune akan kujera.
Hannun Zieyaderh Oummu ta kamo cike da ƙaunar biyayya irin na yarinyar tace.
"Haƙiƙa kamar ƴata dana haifa ta cikina haka nakejinki Zieyaderh, saboda haka zanyi miki duk wani abu irin wanda uwa mahaifiya keyiwa ƴarta".
Ɗan numfasawa Oummu tayi haɗe da cigaba da cewa.
"Idan akace miki zaman aure ba'ana nufin zaman wasa bane, zaman aure bayana nufin zamane da zaki zauna kiyi abun da kikeso ko kuma kiyi duk abun da kikaga dama ba, aduk sanda mace tayi aure to tana zaune ne aƙarƙashin mijinta akuma ƙasan ikonsa, haƙiƙa aure wani babban sinadarin rufin asirine ga kowacce ƴa mace, aure yana ƙarawa mace ƙima da daraja sosai, sannan kuma idan kikaji ance miki zaman aure bawai yana nufin kullum zaman daɗi akeyi ba, kamar yanda harshe da haƙori suke saɓawa awasu lokutan haka ma mata da miji ke saɓawa, wani lokaci harma fiye da haka, saboda haka dole saikinyi haƙuri kin kuma jure daɗi da rashinsa kafun zaman aurenki yayi kyau, sannanne kuma zakici riba, Mijinki tamkar Uba yake agareki saboda haka koda wasa karkiyi ƙoƙarin taka maganarsa, idan yace kiyi koda bakyaso kiyi matuƙar bai saɓawa addini ba, kada ki taɓa tunanin ɗaga muryarki sama akan ta mijinki, sannan kada kitaɓa sanya masa baki idan yana magana, mace tagari mai nutsuwa,hankali, da kuma ilimi bata taɓa ɗaga muryarta sama akan muryar mijinta, sannan kuma bata taɓa tanka masa idan yana magana harsai ya gama, sannan macen da tasan kanta itace macen da ako yaushe take tausasa zuciyar mijinta, idan yana fushi ta rarrashesa, idan tayi masa laifi ta basa haƙuri, haka kuma koda shine yayi mata laifi amma idanunsa suka rufe yake ganin kamar laifinta ne takan kwantar da kanta ƙasa ta bashi haƙuri, zanji daɗi matuƙa idan kika zamo mace tagari acikin gidan aurenki"
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da dafa kafaɗan Zieyaderh wacce ke aikin zubar da hawaye, cikin kulawa ta sake cewa.
"Nasan babu soyayya atsakaninki da Sooraj amma har acikin raina ina fata da kwaɗayin ganin ɗorewar zamanku, kada kice don bakyasonshi zaki ƙuntata masa, haka kuma kada kice don baya sonki zaki ƙuntata masa, kada kice don bakwason juna komai ya umarceki da yi bazakiyi ba, kisani dun wani abu dazakiyi masa wanda yakasance ba daidai ba to Allah Bazai barki ba saiya kamaki da laifi, sannan mala'iku zasu rubutamiki zunubi akan duk abun da kika aikata masa wanda yake ba daidai ba, kiyi haƙuri kizauna dashi da daɗi ko babu, sannan kiriƙe muku sirrinku koda wasa kada kitaɓa barin wani yaji sirrinku, kizama mai haƙuri akullum akuma koda yaushe insha Allah Allah Zai zama gatanki ako ina!"
Kuka me ƙarfine ya ƙwacewa Zieyaderh hakan yasa ta kifa kanta ajikin Oummu tashiga rera kukanta, itama Oummu hawayene suka cika idanunta amma saita shanye tare da sakin murmushi, hannu tasanya ta ɗago Zieyaderh tare da share mata hawaye, cikin son ƙarfafa mata guiwa tace.
"Allah yamiki Albarka kema yabaki ƴaƴa masu biyayya!"
Aunty Muhibbat ce tazo ta kama Zieyaderh inda kai tsaye suka wuce ɓangaren SOORAJ wanda aka sake ƙawatasa aka kuma zuba masa sababbin kayan funitures masu kyau da burgewa komai dake cikin falon kalan pitch and milk colour ne, sosai falon yayi kyau, daga gefe guda kuwa one bedroom ne kaɗai acikin falon wanda shima aka ƙawata cikinsa da furnitures light pink da fari, sosai komai yayi kyau, akan haɗaɗɗen gadon dayaji lallausan katifa Aunty Muhibbat ta zaunar da ita, inda ta sanya mayafi ta rufe mata gaɓa ɗaya jikinta, nan itama tayi mata ɗan taƙaitaccen nasiha, cikin dabara tace mata zataje ta ɗauko wayarta tana zuwa, kai kawai Zieyaderh ta iya jinjina mata alaman to.
Aunty Muhibbat na fita daga cikin ɗakin ta saki murmushi, don wayo kawai tayiwa Zieyaderh babu wani wayarta da zata je ɗaukowa, tafaɗi hakane kawai don tabarta tatafi cikin salama.
9:00 pm
Tun tana jiran dawowan Aunty Muhibbat harta gaji, sannu ahankali takejin wani irin bacci na fusgarta, yayinda agefe guda kuwa takejin wani amai da tashin zuciya na taso mata, wani irin luuuuu haka takejin kanta kamar wanda jiri ke shirin kaiwa ƙasa, lumshe idanunta tayi tama mejin wani abu me ɗumi daya fito ajikinta, da sauri ta yaye mayafinta tare da saƙƙowa daga kan gadon, banɗaki ta nufa, inda tana shiga ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya don babu makawa tasan cewa period ɗinta ne yazo, mamakine ya cikata ganin cewa wannan karon mara da cikinta basuyi mata ciwo kamar yanda suka saba yi mata aduk lokacin zuwan period ɗinta ba, tsabtace jikinta tayi tafito zuciyarta ɗauke da fargaba, don sam batasan yanda za'ayi ta samu pad ta sanya ajikinta ba, tana fitowa daga cikin toilet ɗin ta jingina bayanta da jikin bango, idanunta ne ya sauƙa akan ƙatuwar trolly ɗinta, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙarasawa gaban trolly ɗin, tana zuge zip ɗin jakan tazaro pad ɗinta tare da komawa cikin bathroom ɗin da sauri, tsabtace jikinta tayi tare da dawowa ta zauna aɗan bakin gadon, takure jikinta waje ɗaya tayi tare da lumshe idanunta, cikin ƴan mintunan da basu wuce 15 ba bacci ɓarawo ya ɗauketa..
11:00 pm.
Dai dai motarsa tashigo cikin harabar gidan, yana gama daidaita parking ɗin motar a parking lot, ya buɗe murfin motar ya fito tare da sawa motar tasa key, ahankali yake tafiya har ya shigo cikin babban falon gidan, duhune gaba ɗaya ya mamaye falon yayinda ko ina ya ɗauki shiru, kaitsaye ƙofar da zata sadashi da ɓangarensa ya buɗe ya shiga, direct bedroom ya nufa, ahankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, yana shiga ya maida kofan ya rufe tare da murza mata key, yana juyowa idanunsa suka sauƙa akanta, kwance take tana bacci abaki bakin gado yayinda ta duƙunƙune jikinta waje ɗaya, dagani kai kasan bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, wani irin duka ƙirjinsa yayi ahankali ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa da jikin ƙofar ɗakin, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ware idanunsa ahankali ya kuma sauƙesu akanta, sam yama manta da batun kawota ɗakinsa da Oummu tayi masa ɗazun, sama da minti goma ya ɗauka yana kallon yanda ta nannaɗe jikinta waje ɗaya, sake lumshe idanunsa wanda sukai ja yayi tare da ɗan cizon laɓɓansa, sam baiso ace ƙaddaransa ta shafeta ba, sai yanzu yafahimci dalilin dayasa wasu lokuta takan tsaya masa azuciyarsa, saiyanzu kuma yagane cewa zanen ƙaddaranta ne shumfuɗe azuciyarsa, maganganun da Oummu tayi masa ɗazunne suka shiga dawowa cikin kunnensa filla filla, ahankali ya raba bayansa da jikin ƙofan tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kayan jikinsa ya soma ragewa yayinda ya cire rigar dake jikinsa, bathroom ya wuce inda ya sakarwa kansa shower, yajima atsaye ruwa na dukan jikinsa, ahankali wata irin nutsuwa ke sauƙar masa, yana gama wankan yayi alwala kana ya fito daga cikin toilet ɗin, kaitsaye gaban ƙaton sif ɗin kayansa ya nufa, wani dogon wandon jeans ya sanya, tare da barin murɗaɗɗiyar surar jikinsa awaje batare daya sanya riga ba, wani farin towel ya ɗauka yashiga goge kansa dake jiƙe da ruwa, yana kammalawa ya feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa, kashe gaba ɗaya makunnan wutan ɗakin yayi, kan wata doguwar kujera dake cikin ɗakin ya nufa, kwanciya irinta ruf da ciki yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, gajiyayyun idanunsa ya lumshe yana me fitar da numfashi ahankali, kasancewar amatuƙar gajiye yake hakan