Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   9 / 47

24K to 27K   out of 140.6K words

ne.

Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana.   Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan,  sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba, "To kenan ya akayi ta koma kan gado?" tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta.   Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi.  Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar. Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi.    "Ya jikinna ka dai?" Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba.

Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaɗo ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta.

"Da sauƙi!" Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin.

"Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?" Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa.

"Babu" ya bashi amsa ataƙaice.

"Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!"

Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo.

Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya" 

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta.   Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa,  kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa,  tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban,  tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake.

Muryarta na rawa tace "YAH...YAH!!"   ita kanta batasan ya akayi ta ƙirasa da wannan sunan ba.

Cak ya tsaya daga murza hanunnasa da ya keyi haɗe da buɗe idanunsa da suka zama jajur dasu,  ɗago da kansa yayi ya kalleta.

Sai da taji gabanta ya faɗi alokacin da  idanunsa suka sauƙa acikin nata idanun,  bakomai ya tsorata ta ba kamar yanda taga idanunsa sun rikiɗe daga farare zuwa jajaye.

Ko second biyu bai ɗauka ya na kallonta ba ya sauƙe idanunsa ƙasa.

Ƙwalla ne suka cika idanunta, murya araunane tace "Dama.... dama.. Bansani ba ne ko kanajin yunwa"  tafaɗi haka tana mai murza ƴan yatsun hanunta.

"Miƙomin rigana"  yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ko ya tanka mata maganan da takeyi ba, babu musu ta ɗauko rigan nasa tazo ta miƙa masa, tashi tsaye yayi daga kan gadon haɗe da sanya rigarsa,  Kallon ƙafansa ƴayi yaga ko takalmi baida shi.  Hanu yasa ya dafe goshinsa.

  "Ina wayata?"
yayi mata tambayar yana mai tsareta da idanunsa.

"Wayanka?" tafaɗa tana mai rarraba idanunta.

Yanayin yanda tayi maganar ne yasashi ƙanƙance idanunsa haɗe da ware su alokaci guda.

   "Wa ya kowani nan?" ya tambayeta yana mai ƙoƙarin maƙala aninayen dake gaban rigarsa.

"Ni da Kamalu driver ne" tabashi amsa tana mai wasa da ƴan yatsun hanunta.

Ɗauke kansa kawai yayi daga kallonta, dai dai lokacin Dr.Haisam yashigo cikin ɗakin.

Sooraj na ganinsa yace "Ko zan iya samun aron waya?"

Murmushi Dr.Haisam yayi haɗe da cewa "Eh" ciro wayarsa yayi ya miƙawa Sooraj ɗin.

Number'n Khalid yasanya acikin wayan Dr.Haisam haɗe dayin dialing. Ringing biyu Khalid yaɗauki ƙiran,    "Ina Mahfuz Specialist Hospital, kazo kayi dropping ɗina a gida"   Baijira mai Khalid ɗin zaice ba ya kashe wayan, miƙawa Dr.Haisam wayar yayi.  Takardan sallamansa Dr.Haisam ya miƙa masa.

Mintuna kaɗan Khalid ya iso cikin asibitin.   Yana shigowa ɗakin, cikin tashin hankali ya kalli Sooraj cike da kulawa yace "Raj maiyasa meka haka, harda zuwa asibiti?"

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa " stress ne kawai, muje ko"  yaƙare maganar cikin yanayi na ƙosawa.

Motar Khalid suka shiga, suna zaune agaba ita kuma tana zaune agidan baya,     Khalid ne ke ta tambayar Sooraj jikin nasa cike da kulawa, amma kuma shi Sooraj ɗin cikin halin ƙosawa yake mayar masa da amsa.

Suna isowa gida Khaleed yayi musu sallama ya koma, dama aiki yabari a office ɗinsa ya zo.

Wanka yayi haɗe dayin brush sai alokacin yaji wani ɗan iskan yunwa na ƙwaƙulan cikinsa,   dogon wando yasanya da wata riga marar nauyi, kana ya zura slippers ɗinsa ya fita zuwa falo.

Direct kitchine ya wuce, ruwan zafi ya tafasa haɗe da juyewa acikin flask.  Cup ya ɗauka ya haɗa tea, hannayensa ya sanya akan waist ɗinsa, yana ƙarewa kitchine ɗin kallo.   itace ta faɗo masa arai, yasan gaba ɗaya zaman yunwa tayi acikin a asibitin.

Ruwan zafi ya ɗaura akan gas, mintuna ƙalilan ruwan ya tafasa  indomie ya jefa acikin ruwan haɗe da sanya spiece.  yana tsaye acikin kitchine ɗin, har Indomie ɗin ya nuna, acikin wani plate na tangaran mai kyau ya juye indomie'n.  hanunsa riƙe da plate da kuma cup ɗin tea ɗin ya fita zuwa falo.

Zaune  take akan gado, tayi jigum fitowanta daga wanka kenan, ta sanya wani riga da sket ƴan kanti.  Zuwa yanzu idanunta har sun soma rufewa sbd yunwa, gaba ɗaya ƙarfin jikinta ya gudu, duk da zama da yunwa ba sabon abu bane a wajenta..
Wani irin murɗawa taji cikinta nayi.   Hanu yasa ajikin ƙofar ya ƙwanƙwasa, batare daya jira anbuɗe ƙofar ba ya juya ya koma cikin falon. Zama yayi akan kujera haɗe da ɗaukan cup ɗin tea ɗinsa ya soma sipping da kaɗan kaɗan.

Cikin rashin ƙarfi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, ganinsa zaune a falon yasa ta nufo cikin falon.

Durƙusawa tayi agabansa, kafun tace wani abu, ya turo mata plate ɗin imdomie ɗin gabanta.

Ɗago da kanta tayi ta kallesa, gani tayi kwata kwata idanunsa ba'akanta suke ba.  Ɗaukan plate ɗin tayi ta ɗaura akan cinyarta, loman farko da tayi ta lumshe idanunta, wanda suke cike da gajiya da kuma bacci,  sosai takecin indomie'n harta manta ma da cewa agabansa take.
Duk abun da takeyi yana lure da ita, duk wani motsin da tayi yana kallonta ta gefen idanunsa.    Bata gama cin indomie'n ba har ya kammala shan tea ɗinsa yatashi yabar wajen, tana kammala cin indomie ɗin taji wata nutsuwa ta sauƙar mata, ɗaki ta koma tana kwanciya bacci yaɗauketa.

*** *** ***

Tun tashinta yau ta riga da ta gyara ɗakin da take kwana tsab, hakanan taji sha'awar shiga kitchine ɗin gidan, gani take kamar wahala take bashi don kullum saiya saya mata abun da zata ci, duk da cewa baya wuni agidan amma yana turowa ana kawo mata. Yanzu rabonma da ta sanya shi acikin idanunta kusan kwana biyu kenan.

Tsayawa tayi a kitchine ɗin tana ƙarewa ko ina da ina kallo, ita sam bata wani iya girkin zamani ba, shinƙafa kawai ta iya dafawa,   wata drawer dake cikin kitchine  ɗin ta buɗe, kayan abinci ta gani shaƙe acikin drawer'n,   ruwa ta ɗaura akan gas, wanda da ƙyar ta iya kunnasa, saura ma kaɗan wuta ya kama hanunta.   neman inda zata samu kayan miya tashiga yi, saidai neman duniya tayi bataga wani abu mai kama da kayan miya a kitchine ɗin ba, dolenta haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kitchine ɗin.

Fitowarta yayi daidai da shigowarsa cikin falon. Sanye yake da suit coffee colour, ya yinda ƴar cikin rigan ta kasance milk colour, Sosai yayi kyau. Har batasan sanda tasake baki tana kallonsa ba.

Kallonta yayi tare da kawar da kansa gefe.  "Ɗauko mayafinki" yace da ita ataƙaice.

Babu musu ta koma ɗaki ta ɗauko mayafinta.

Tafiya suke kowannensu da abun dayake saƙawa acikin zuciyarsa.  Gaban wani tangamemen gate taga sun tsaya yayinda yasoma danna horn ɗin motar. Wangale musu gate ɗin akayi ya tura hancin motar ciki. adai dai wani ƙaton parking space ya yi parking motar. "Muje" yafaɗa yana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar, yana gaba tana biye dashi abaya, gaba ɗaya hankalinta naga tsirarun mutanen da tagani suna shawagi a tafkeken farfajiyan wajen, daga mata har mazan dake wajen sanye suke da uniform maroon and milk colour. Direct office ɗin Mr. Isyaka Nuhu suka nufa, har cikin office ɗin akayi musu iso. Cike da mutuntawa Sooraj yabawa Mr. Isyaka Nuhu hanu suka gaisa. Fuska cike da fari'a Mr.Isyaka Nuhu ya dubi Ziyada haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj. "Wannan itace yarinyar?" Ya tambaya.

"Eh" Sooraj yabasa amsa.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da danna ƙiran wata number, yanajin an ɗaga ƙiran yace "Kasameni a office ɗina" yana aje wayar bawani jimawa saiga wani mutumi yashigo cikin office ɗin.

Kallonsa Mr.Isyaka Nuhu yayi haɗe da cewa.

"Kuje da yarinyarnan kayi mata interview"

"Okay Sir!" mutumin daya shigo ya faɗi haka haɗe da kallon Ziyada yace "Muje ko"

Kallon Sooraj tayi saidai kuma taga sam idanunsa ba akanta yake ba, wayarsace ma ahanunsa yana dannawa..


(manage)


*Vote me on Wattpad*
@fatymasardauna
[4/7, 8:40 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

    *Written by*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

#romance

         *Chapter 14*

Basu wani jima ba suka fito daga ɗakin da akeyiwa duk wani ɗalibi da yakasance sabon zuwa interview.  Direct office ɗin principal ɗin suka koma zuciyar Ziyada cike take da farinciki da kuma jin daɗi, addu'anta ɗaya Allah yasa hasashen da takeyi yazamanto gaskia.

"Har kun gama interview ɗin?" Mr. Isyaka Nuhu ya tambayi Sir. Yusuf wanda shine ke yiwa duk wani sabon ɗalibi dazai shigo makarantar interview.

"A'a Sir ai ma bata taɓa zuwa makaranta ba, inaga kawai sai dai afarayi mata lesson"
Sir.Yusuf yafaɗi haka cikin siga irinta bada shawara.

Jinjina kai Mr. Isyaka Nuhu yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj wanda har yanzu wayarsace riƙe ahanunsa yana latsawa. 

"To kaji abun da yace, ya kagani ko za'a fara yi mata lesson ɗin, idan ta ɗan soma iya wasu abubuwan sai abata ko s.s.one ne"

Sai alokacin ya ɗago kansa, wannan murmushin nasa da baya wuce kan laɓɓansa yayi haɗe da cewa. 
"Bakomai hakan yayi, yaushe za'a fara lesson ɗin?"

"Ai tunda kusan munkammala komai ko yau ma idan kun shirya sai afara yi mata" Inji cewar Mr. Isyaka Nubu (Principal).

"Okay ba damuwa, ni zan wuce"  Sooraj yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, hanu yabawa Principal ɗin sukayi musabaha, kana yabawa Sir. Yusuf ma suka gaisa,  ko kallon gefen da take baiyiba ya fice daga cikin office ɗin.

Principal ne yace da Sir.Yusuf  suje ya samo mata malamin lesson su fara tun yau, hakan kuwa akayi,   Wani Teacher Abdallah Sir.Yusuf ya samo mata, wanda shine zaina koyar da ita lesson everyday, hatta ranan saturday da sunday zai na zuwa koya mata gida, domin biyanshi za'ana yi.

abubuwa masu sauƙi Teacher Abdallah yafara koya mata, sam babu wani abu da ta fahimta tana dai jinsane kawai, duk kuwa yanda taso ta fahimci abubuwan sam ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka.
***
Zaune yake atamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan parking shirt dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin, turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba, yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take jin son sa acikin ranta, komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa, uwa uba kuma kyau da kwarjininsa dake tafiya da imanin duk wata mace da zatayi tozali dashi,  cikin takunta nason ɗaukar hankalinsa tasoma takowa zuwa cikin office ɗin.   Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi wacce ta shigo cikin office ɗin nasa,  jiyayi wani abu ya toshe masa maƙoshi,  sam yatsani ganinta ko kaɗan bayaso tana raɓarsa, baisan ita wace irin mace bace wacce bata da zuciya ko kaɗan.    Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba,  cikin muryar shagwaɓa tace. 

  "Barka da hutawa ranka ya daɗe"

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita,  bakinta da yaji pink lips stick taturo gaba. "Maiyasa kakemin hakane wai Raj? at least dai ko kallona yakamata ace kayi wajenka fa nazo" taƙare maganar tana ɗan bubbuga ƙafafunta, alaman shagwaɓa.

Sai alokacin Sooraj ya ya ɗago kansa, saidai bai kalli inda take ba.    "Kina da buƙatar wani abu ne?" yatambayeta ata ƙaice.

"Kainake da buƙata Raj, wallahi kainake da buƙata, kafi kowa sanin yanda na damu dakai, maiyasa kake min haka ne? kadubeni Raj nacika mace irin wanda take girgiza zuciyoyin maza amma maiyasa bazaka dubeni ba? na amince ma kayi duk wani abun da kakeso dani amma maiyasa bazaka amince min ba!" taƙare maganar kamar zatayi kuka.

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da tashi ya ƙarasa gaban fridge, buɗewa yayi ya ɗauko ruwa mai sanyi, saida yasha sosai kafun ya sauƙe goran ƙasa,  inda suit ɗinsa ke aje ya nufa, ɗaukan suit ɗin yayi ya saƙala ahanunsa,  touch watch ɗin dake hanunsa ya duba,  gani yayi akwai sauran time sosai kafun lokacin tashinsa ya cika, amma a yanda  Aneesa tashigo masa office baya jin zai ƙara mintuna biyu acikin office ɗin.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da rufe laptop ɗinsa,   juyawa yayi ya nufi ƙofar fita yana mai karkaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa.

Da sauri Aneesa tasha gabansa, idanunta cike da ƙwalla tace "Please Raj ka tsaya atare dani, kasani kaine burina da kuma fatana, maiyasa kakemin haka ne?"   hawayene suka gangaro daga cikin idanunta.

Sai alokacin Sooraj ya ɗaura idanunsa akanta, kallonta yayi tun daga samanta har zuwa ƙasa. sannan yasaki wani killer smile.

  "Bani hanya na wuce"  ya faɗa mata haka cikin halin ko inkula.

"Bazan baka hanya ba Raj, harsai kamin abinda nakeso, please Raj kasani akullum da buƙatarka nake kwana, please kabani dama ko sau ɗaya ne." 

Ƙanƙance idanunsa yayi haɗe da tamke fuskarsa alokaci guda, cikin takaici yasanya hanunsa ya turata gefe, harsai da kanta ya bugu da bango, ƙofar office ɗin ya buɗe ya fice abunsa.

Kuka Aneesa tasanya mai ɗauke da tsananin ɓakin ciki da takaici,  takardun dake kan table ɗin office ɗin ta soma watsarwa a ƙasa tana kuka, ta tsani wannan banzan halin na Sooraj,  a kullum baida wani buri da ya wuce ya wulaƙantata, mai tarasa wanda har zai tsaneta haka? alƙawari tayiwa kanta matuƙar ta rasa Sooraj to kowacce mace aduniya ma tarasashi domin bazata taɓa ɓari ya auri wata mace ba idan ba ita ba.

Yana fita ya wuce wajen da yayi parking motarsa, sama sama yake amsa gaisuwar  ma'aikatan dake gaidasa.  Yana shiga cikin motar yayi mata key haɗe da ficewa daga cikin bank ɗin, direct wani hotel ya nufa......

Sosai Teacher Abdallah ya dage ya zuba mata lesson,  lokacin da aka kaɗa ƙararrawan tashi ga duka ƴan makarantan dai dai lokacin shima ya dakata daga koyar da ita english lesson ɗin da ya keyi.    Tana fitowa ƙofar ajin taga cincirondon ɗalibai maza da mata kowa na ƙoƙarin kama gabansa, ko ta ina acikin makarantar ɗalibaine, yayinda parking space ɗin makarantar kuwa ke cike da tarin motoci, har waje motoci ne a fake, duk wani ɗan makarantan dazaka kalla, kallo ɗaya zakayi masa ka hango alamun zaman naira ajikinsa, domin daga mata har mazan gaba ɗayansu ƴan gayu ne, da alama kuma kowa yanaji da kansa.

Kamalu driver ta hango ya nufo inda take, wata ajiyar zuciya ta sauƙe, domin kuwa da har tafara tunanin yanda za ayi ta koma gida ita kaɗai.

Gaba ɗaya yau tsananin farincikinta ya kasa ɓoyuwa, jinta take cikin farinciki. Haka ta koma gida zuciarta cike da jin daɗi. Wunin ranan gaba ɗaya haka tayishi cikin jin daɗi, duk yanda taso ganinsa tayi masa godiya abun yaci tura, domin kuwa ko motsinsa bata jiba

*** *** ***

Kullum sai Ziyada taje Lesson Kamalu driver ne ke kaita shine kuma ke dawo da ita, sosai ta kejin daɗin lesson ɗin nata, yanayin yanda ta dage tasanya son karatun acikin ranta shi ya ƙara sanya teacher Abdallah dagewa wajen ganin ya koyar da ita yanda zata fahimta,  zuwa yanzu dai tana ɗan fahimtan abubuwa da kaɗan kaɗan, musamman ma wajen karatun Hausa da kuma rubuta shi,  ta ɗan ƙware ta wajen wannan fanni, har ma idan taga abu zata iya karantashi, English ɗinne dai sai a hankali. 

Tun ɗazu aka tashe su saidai ga mamakinta yau Kamalu driver baizo ɗaukanta ba, gashi ɗaliban da suka rage acikin makarantar basu wuce ƴan tsiraru ba sam basu da wani yawa.   Kalle kalle take tayi ko zata hango Kamalu driver amma babu shi babu alamarsa.  Tsaye take a harabar makarantar, sanye take da doguwar riga da kuma Hijab, hannayenta nannaɗe suke akan ƙirjinta. 

Tun daga nesa yayi parking ɗin motar, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, ahankali ya ware idanunsa haɗe da sauƙesu akanta,   hakanan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akanta, kusan 2 minute ya ɗauka yana kallonta, mai da idanunsa yayi ya rufe,  wani irin gajiya haɗe da kasala ne yaji sun sauƙar masa alokaci guda.  Buɗe murfin motar yayi haɗe da zuro ƙafafunsa waje.  Tun fitowarsa daga cikin motar idanun ɗaliban da ke wajen ya dawo kansa.  Yanayin yanda yake taku cike da nutsuwa shine abun daya burgeta, har batasan sanda ta saki wani murmushi ba.  Yana ƙarasowa inda take yace.

"Kijirani a mota" baijirayi mai zata ce ba, yayi gaba abunsa, tana kallonsa ya shige cikin office ɗin principal.  Juyawa ita tayi ta nufi inda ya aje motar tasa, jingina tayi da jikin motar tana jiran zuwansa. Baiwani jima ba ya dawo hanunsa riƙe da wata leda.

Tunda suka ɗauki hanya babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu kowa da irin tunanin da yake saƙawa acikin zuciyarsa,  yarda da abun da zuciarta ke gaya mata da tayi yasanya ta gyara zama cikin wata murya mai sanyi tace. "Nagode

9 / 47