Sooraj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Adventure

Chapter   19 / 47

54K to 57K   out of 140.6K words

baƙaramin kyau yaga yayiwa kansa ba, musamman yanda kwarjininsa yasake bayyana afili, sosai ya fito a cikakken Namiji wanda ya amsa sunansa,  turarukansa ya ɗauka ya feshe jikinsa da su take ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa,    wayarsa yaɗauka yasanya acikin aljihunsa tare da ɗaukan key ɗin Black Range rover car ɗinsa,   cikin takunsa me ɗauke hankali yake tafiya Iya kyau yayishi har ya gaji   (Team RajZiyada please kuyi imagine  yanda Sooraj ɗinku ya haɗe.lol)

Ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin dake cikin falon, Plate ɗin da taci abincine riƙe ahanunta tafito daniyar zata kaisa kitchine,   ƙamshin dayake kashe mata jiki yake kuma sanyata acikin wani irin yanayi shine yafara dukan hancinta lokaci guda ya gauraya da numfashinta, saboda tsabar daɗin ƙamshin batasan sanda ta lumshe kyawawan idanunta ba, tana buɗesu kuwa idanunta suka sauƙa akan zallan kyawu da kwarjinin dake dosowa cikin falon, wani irin dokawa taji ƙirjinta yayi, take jikinta yasoma karkarwa kamar maijin sanyi batare data kulaba tayi missing step ɗaya take tatafi zata faɗi da sauri tariƙe ƙarfen dake gefen matattakalan plate ɗin hanunta kuwa faɗuwa yayi dayake plate ɗin  irin na cikin gift set ɗinnan ne tassss haka ƙaran fashewarsa ya cika falon,  jin ƙaran fashewan abu abayansa yasanya shi juyowa, ido huɗu sukayi shida ida,  kallon yanda plate ɗin ya tarwatse awajen yayi, baiko sake kallon gefen da take ba yasakai yafice daga cikin falon yana gyara zaman agogonshi, ita kuwa Ziyada tamkar wacce aka dasa haka ta kasa motsa koda ɗan yatsan ƙafanta ne,  wani irin ƙarya idanunta ke mata don har yanzu gani take tamkar yana wajen.

"Zieyadah!"

Ƙiran sunanta da Ummu tayi shiyayi sanadiyar sauƙar da idanunta ƙasa murya asanyaye tace "Na'am"

Kallon plate ɗin daya tarwatse aƙasa Ummu tayi cikin ɗan mamaki tace.
"Ya akayi haka ta faru?"  

"Umm dama bankula bane shine yafaɗi!" Ziyada tafaɗa tana me ƙoƙarin maida ƙwallan dake cikin idanunta.

"Inadai baijimiki ciwo ba?" Ummu ta tambayeta cike da kulawa. 

"Eh!" tasake faɗa murya araunane.  

"Shikenan to kidai kula kada yamiki illa, ni zan fita bazan jimaba zan dawo ki kula sosai" Ummu tafaɗa tana me gyara zaman gyalen dake jikinta.

"Adawo lafiya" cewar Ziyadah tana me ɗan satan kallon Ummu wacce tasha ado da gwala gwalai masu tsadan gaske, itakam da badon ɗan zaman da tayi acikinsu ba to tabbas da zatace ba Ummu bace ta haifi Sooraj domin sam jikin Ummu bainuna hakan ba zallan kudi da jindaɗi haɗi da wayewa kawai jikin Ummu ya nuna.  

Haka Zieyada ta gyara wajen amma gaba ɗaya tunaninta yana wani waje daban, daga wani ɓangare na zuciyarta kuwa daɗi takeji ranan monday zasu koma makaranta.

Sooraj kuwa yana fita haɗaɗɗiyar car ɗinsa ya shiga tare da bata wuta,   kai tsaye Central Mosque ya nufa domin samun sallan jumma'a, koda aka idar da sallan daga masallacin direct JABI LAKE yanufa don sunyi da Mas'oud zasu haɗu acan.

Vote
   &
Comment

1/june/2020

          fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ !!!*

    *Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

            *Wattpad*
    @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 28*

Inda yake zaune wani secret wajene me kyau da burgewa, wajen tamkar garden haka yake domin anƙawatasa da korayen furanni masu sanyin ƙamshi.
Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar chair wanda aka ƙawata tsakiyanta da wani haɗaɗɗen table me kyau, drinks ne kala kala ke jere asaman table ɗin,  gefe dashi Mas'oud ne ke sipping coconut juice,  yayinda Sooraj ke aikin latsa wayarsa, azahirin gaskia idan kaga yanda  gaba ɗaya attention dinsa  ke kan  wayan zakayi tunanin wani abu me amfani yake aiwatarwa, saɓanin haka kuwa kwata kwata  hankalinsa ba ga wayar yake ba, idanunsa ne kawai ke kan wayan amma gaba ɗaya tunaninsa yayi nisa izuwa wani ɓangare na daban,  duk abun dayake Mas'oud na kula dashi, ɗan aje cup ɗin coconut juice ɗin yayi tare da duban Sooraj...

"Bazaka taɓa daina sakanka adamuwa ba matuƙar bazaka fito ka faɗa mana damuwarka ba, haka kuma bazaka warke daga ciwon dake damun zuciyarka ba matuƙar ba zaka amayar da abun dake cikinta ba, har yaushene zakana ɓoye matsalanka RAJ? taya kake tunanin zaka samu sassauci da kuma nutsuwar zuciya bayan bakanemi hakan ba? shin ni bankai na zama abokin da zaisan matsalarka bane RAJ? tun muna ƙanana muke abota me yasa har yanzu bankai jigon dayakai sanin sirrinka ba?"  Duka waƴannan tambayoyin Mas'oud yayiwa Sooraj alokaci ɗaya fuskarsa ɗauke da damuwa.

Ɗan numfasawa Sooraj yayi tare da ɗago kansa,  ɗan kallon Mas'oud yayi sannan ya kau da kansa gefe,  lips ɗinsa ya ciza tare dayin wani shu'umin murmushi, wanda shikaɗai yasan ma'anarsa, cikin husky voice dinsa yace.   "Babu wani wanda zai fahimci matsalata Mas'oud, idan nafaɗa maka matsalata ba lallai ka yarda ba,  idan nace maka bansan waneneni ba nasan bazaka taɓa yarda ba, wannan dalilin shiasa banason nayi sharing damuwata da kowa, saboda damuwata damuwata ce ni kaɗai!" cikin wani irin yanayi ya ƙare maganar tare da haɗiyan wani saliva me ɗaci da ya tsaya a maƙoshinsa.

Cike da mamaki haɗi da rashin fahimta Mas'oud yace "Banfahimci inda kalamanka suka dosa ba Sooraj, me hakan yake nufi?"

"Aure ne banaso Mas'oud, sam banason zama da kowace mace, nafison nayi rayuwata ahaka" ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da kallon kansa, daɗan ƙarfi ya cije laɓɓan bakinsa kana yaci gaba da cewa "Bazan taɓayiwa wata mace amfani amatsayin namiji ba, niba kamarka bane bakuma kamar sauran maza bane, inada rauni Mas'oud inada rauni wanda yake barazanar durƙushewar rayuwata, ita ƙaddara tana iya zuwa wa bawa aduk yanda baizata ba, ta ɓangarena haka tawa ƙaddaran take, amma banajin akwai wata wacce zata rayu dani ahaka, banajin zanyi wani farinciki.... "  Kasa ƙarasa maganan yayi sakamakon wani irin nauyi dayaji ƙirjinsa yayi,  bada kowani lokaci yacika yin magana me tsawoba, hakan yasa yanzu yakejin kansa tamkar zai faɗo ƙasa, yayinda yakejin tamkar ana hura masa wuta acikin ƙirjinsa.  Bottle water Mas'oud ya miƙo masa, babu musu ya amsa bai aje bottle water'n ba har saida ya tabbatar da babu wani sauran ruwa acikin goran, wani irin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe,  ɗago idanunsa da suka soma rikiɗewa daga farare zuwa jajaye yayi ya kalli Mas'oud daya kafesa da idanu,    wani ɗan murmushi yayi tare da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan fuskarsa.

''Zan tafi, kada ka manta ranan monday muna da meeting" yanakaiwa nan azancensa ya miƙe tsaye kota bakin Mas'oud bai tsaya jiba yayi gaba, binsa  Mas'oud yayi da kallo har ya ɓacewa ganinsa, wani irin iska me zafi Mas'oud ya fesar tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa,  sai ayanzu brain ɗinsa ke ƙoƙarin harhaɗo masa matsalolin Sooraj, batun yauba ya kamata ace yagano menene matsalan, tunanine barkatai suka shigo cikin brain ɗinsa, wasu abubuwa daya tuno da kuma maganganun da sooraj yafaɗa masa yanzu sune suka taimaka wajen kawo masa haske daga duhun daya shiga, wani irin faɗuwa yaji gabansa yayi yayinda bugun numfashinsa ya soma fita da sauri sauri,  abayyane ya furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!"  kansa ya kifa ajikin table ɗin, take yaji ruwan hawaye naƙoƙarin cika idanunsa, da sauri ya yi ƙoƙarin maidasu, car key dinsa ya ɗauka, haka ya bar wajen jiki babu ƙwari.

Sooraj kuwa tafiya kaɗan yayi ya gangara gefen titi tare da yin parking din motar,  kansa yakifa akan steering motar tamkar me bacci, aƙalla yaɗauki sama da 30 minute awajen har saida yajisa ya fara zama normal sannan yasake ta da motar ya cillata kan titi.
***
Monday.

Kamar yanda duk wani ma'aikaci da student's  sukasani Monday ranace me mahimmanci agaresu, sannan kuma ranace da ko wani ɗalibi yakewa kansa shirin makaranta na musamman kasancewar ansha hutu harna tsawon kwana biu.

Ɓangaren Ziyada ma hakance takasance domin kuwa yau zasu koma makaranta inda zasu tafi S.S.2

Tun ƙarfe 5 da ta tashi tayi sallan asuba bata yarda takoma bacci ba,  ƙarfe shida da rabi daidai ta shiga toilet donyin wanka.

Wanka da brush tayi sannan ta fito ɗaure da towel ajikinta, zama tayi agaban mirror tare da ɗaukan body lotion  ɗinta ta shiga shafawa ajikinta,  normal green tea powder ta shafa akan fuskarta tare da goga wani man leɓe me kalan pitch,  eye black pencil taɗauka tagoga acikin idanunta, take idanunnata suka ƙara bayyana kyawu da girmansu,  tashi tayi daga gaban mirror'n tare da buɗe drawer tazaro gogaggun uniform ɗinta,  tsab tashirya kanta cikin riga da wando na uniform ɗinnata wanda yake matuƙar amsar jikinta, zama tayi akan bed tare da ɗaukan white socks ɗinta  ta zura a ƙafafunta, dogon gashin kanta ta kanannade tare da kamasa da ribbom, ɗan madaidaicin hijab ɗinta ta sanya,  ƙarasawa gaban mirror tayi tare da duban kyakkyawar fuskarta, ita kanta tasan tayi mugun sauyawa wani irin haske tare da kyau ne suke sake bayyana atattare da ita akullum kwanan duniya, sau da dama idan ta dubi kanta amadubi takan ga kamar ba itace Ziyadan ƙauye ba, kamar sauyata akayi, musamman ma yanzu da hips ɗinta suka ƙara cikowa shape ɗinsu yazama abun ɗaukar hankali, shiyasa bata taɓa yarda ta zauna haka batare data rufe jikinta ba, ita kanta yanzu tasan cewa cikar ƴan matancinta da bai bayyana ba ada, shine yake  bayyana yanzu, domin kuwa ayanzu babu wani abu daya rage na ƴanmatanci ajikinta da baifito ba, saidai kuma ita kaɗaice tasan haka kasancewar bata yarda kayan da take sawa su nuna hakan.

Tana kammala kimtsa kanta tajawo ƙatuwar school bag ɗinta ta aza akafaɗanta, har wani sanyi takeji aranta yau zataje taga ƙawayenta Nasmah da Shukrah sosai take kewarsu.

7:15 am  Ahankali take sauƙowa daga kan step ɗin yayinda ta kanannaɗe hannayenta acikin hijabinta. 

Ummu ce zaune acikin katafaren falon, laptop na companyn apple ne aje agabanta da alama wani aiki takeyi, kasancewar har da wani ɗan madaidaicin farin glass dake sanye a idanunta. 

Karasowa cikin falon Ziyada tayi cike da ladabi tarusuna tare da cewa.  "Barka da da safiya Ummu Ina kwana!"

Juyowa Ummu tayi fuskarta ɗauke da murmushi da "Lafiya" ta amsa mata sannan taƙara da cewa
"Har kinshirya da wuri haka?"

Murmushi tayi tare da ɗan kaɗa kanta alamar "Eh"  

Agogo Ummu takalla taga babu wani sauran time hakan yasa tace da Ziyada ta ɗauki food flask ta sanya abinci aciki tatafi dashi,  hakan kuwa Ziyada tayi, koda tazo fita daga cikin falon tsaida ita Ummu tayi ta bata 500 tace tasaya chocolate,   cike da jin nauyi Ziyada ta girgiza kanta alamar bazata amsa ba.
Murmushi Ummu tayi ta tura mata kuɗin acikin jakanta sannan tahaura sama.   Fitowa tayi daga cikin falon tana ƙara gyara zaman school bag ɗinta wanda yake rataye kan kafaɗanta.    Kamalu driver ta tarar tsaye ajikin mota yana jiranta,  tafiya ta cigaba dayi tana me gyara igiyan jakar makarantarta.   Kansa tsaye yake tafiya yana me ƙoƙarin maida wayarsa daya amsa ƙira yanzu cikin aljihun wandonsa, babu wanda yakula da wani acikinsu, sam bata ankaraba saiji tayi ta buge mutum, kafun ta gama daidaita nutsuwarta ma tuni fitinannen ƙamshinsa ya gauraya da numfashinta, aɗan daburce taja baya,  chest ɗinsa daidai saitin inda kanta ya buga ya ɗan riƙe,   bakinta na rawa tace "Dan Allah kayi haƙuri bansan kana zuwa bane!" 

Kallonta yayi daga ƙasanta har sama, yana kawowa  daidai  fuskarta yatarar da ƙwalla sun cika idanunta, ƙiris suke jira su gangaro.   Wani irin haushi da takaicinta ne suka cikasa, cikin wata murya me ɗauke da amo yace  "Are you insane?"   

Ƙasa tayi da kanta aikuwa saiga hawaye kam sun ziraro kan kuncinta.    Wani baƙincikintane yasake kamasa, hannunsa yakai ya kamo haɓanta tare da ɗago fuskarta,  manya manyan idanunta ta zaro waje tana kallonsa,  bazato ba tsammani ya hankaɗata gefe yayi shigewarsa abunsa,  ƙiris yarage tafaɗi, wani irin wawan ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ɗaukar school bag ɗinta data faɗi ƙasa ta nufi wajen Kamalu driver.

Tunda suka ɗauki hanyar makarantar take tunani, akan fuskarta kuwa hawayene caɓa caɓa, wasu na koran wasu.

"Me turetan da yayi yake nufi? wulaƙanci kenan kome?" abun da take ta tambayar kanta kenan.  Wata zuciyarta ce tace da ita "Baki da hankali Ziyada, dama irin waƴannan mutanen idan ba alfarma ba mene zai haɗaki dasu? sam baki da daraja da kimar da zaki raɓesu"  Hannu takai kan fuskarta ta share hawayenta,  aranta taƙudiri aniyar zatayi karatu sosai itama ta zama wata, daganan saita fita daga cikin rayuwarsu baki ɗaya.  Da wannan tunanin azuciyarta har Kamalu driver ya ajiyeta acikin makarantar, tun bata gama fitowa daga cikin motar ba Nasmah ta taho da sauri ta rungumeta, wani irin daɗi Ziyada taji tuni ta manta da wata damuwa itama ta rungume Nasmah...

"I miss u so much my ƙawa!" Nasmah tafaɗa cike dajin daɗin ganin Ziyada. 

"Miss you too!!" Ziyada itama tafaɗa tana murmushi, ƙarasowar Shukra yasa Ziyada sakin Nasma, ta rungume Shukra dukansu dariya suka sanya cike dajin daɗin ganin juna, suna maƙale da juna haka suka nufi wajen taron assembly, koda aka kammala assembly'n  direct sabon ajinsu suka nufa S.S 2A.   Kamar yanda suke a wancan ajin hakama suke a wannan ajin sit ɗinsu ɗaya, Ziyada ce ke tsakiya sai Nasma da Shukra dake gefenta. 

Ƙarfe 10 am daidai  aka fito dasu break,   kai tsaye wajen da aka tanada na musamman doncin abincin ɗalibai suka nufa, soyayyen doya da chicken sauce din da Ziyada ta zo dashi shi suka fara ci kafun daga bisani suka ɗaura da snacks. 

11:00 am

Mota ƙirar Jeeb ce baƙa tayi parking awajen da ake faka motoci dake cikin school ɗin,    Farouk wani irin ajiyar zuciya me sanyi ya sauƙe tare da lumshe sexy eyes ɗinsa, sai yanzu yaji sanyi acikin ransa da ya gansa acikin  makarantar,  zare key ɗin motar yayi tare da buɗe murfin motar ya fito, sanye yake da jumper na  shadda sky blue wanda taji aiki me kyau,  sanye yake da tsadaddiyar hulan zanna akansa wanda ta ƙarawa fuskarsa kyau, sosai yayi kyau sai fidda ƙamshi yake,  bayi da tantama akan inda zai sameta saboda haka direct office ɗin principal yanufa, koda yaje permission ya nema akan yanason ganin wata ɗaliba mesuna Ziyada Mansoor Mainasara, domin da wannan sunan akayi mata register. Da yake  principal ɗin ya sanshi, babu ɓata lokaci ya tura S.S 2A don aƙirata kasancewar a time ɗin sungama break  harsun koma class.

Ba ƙaramin faɗuwa gaban ziyada yayiba jin wai ana ƙiranta daga office ɗin principal,  gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, a iya saninta bata da wani wanda zaizo nemanta, haka ta nufi office ɗin principal ɗin zuciyarta cike da fargaba,  a corridor ɗin dazai sadata da office ɗin idanunta sukayi mata tozali dashi, wani irin duka taji ƙirjinta yayi sai kawai ta tsaya cak tare da sunkuyar da kanta ƙasa, murmushin daya bayyana cute dimples ɗinsa yayi tare da takowa zuwa gareta, wani irin kallo yakeyi mata, komai nata ya sauya tasakeyin kyau sannan taƙara girma duk dacewa ba jiki tayi ba amma tabbas kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa ta ƙara girma.   Gaf da ita ya matso har yazama baifi saura taku ɗaya tsakaninsu ba.  "I miss you!!" yafaɗa cikin wata irin murya yana me kallon small lips ɗinta.

Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta, ahankali taɗago da fuskarta idanunsune suka faɗa cikin na juna ƙasa tayi dakanta tana mai wasa da yatsun hanunta, sam bataji wani abuba da takalli cikin idanunsa, saɓanin Oga Sooraj da idan takalli cikin beauty eyes ɗinsa take rasa nutsuwarta.   

Kallon yanda take lallanƙwasa yatsun hanunta yayi, yaɗan saki murmushi, jiyake kamar yajawo ta jikinsa ya bata tight hug, komai nata na musammanne babu abun dake burgesa atattare da ita kamar sanyinta.

"Muje mu zauna ko!" yafaɗa yana meyi mata nuni da wata bishiya wacce ƙasanta ke ɗauke da wani bench wanda akayi da cement.  Bata iya musa masa ba  saidai har yanzu kanta aƙasa yake,  zama tayi akan bench ɗin tare da jawo hijab ɗinta ta ɗan rufe gefen fuskarta,  shima akan bench ɗin ya  zauna   har ƙamshinsu na iya gauraya waje guda.     "Nayi kewarki da yawa, bazan sake bari kiyimin nisa har haka ba,  bansan da yaushene kika kama zuciata ba, please My cute babyy na ki juyo na kalli fuskarki!" yaƙare maganar cikin sanyin murya.

Har acikin ranta taji kalamannasa saidai tanaji kamar sunyi mata nauyi.  Hannayenta tasanya taɗanja hijab ɗinta baya, tare da ɗago kanta ta kalleshi, shi ɗinma kallonta yake, murmushi ya sakarmata tare da ɗanyin ƙasa ƙasa da idanunsa, wani iri taji ajikinta hakan yasa itama taɗanyi masa murmushi.  Cikin muryar shagwaɓa tace "Shine kaɗauko ni daga aji bayan kasan karatu zamuyi ko!"

"am sorry babyyyna inason ganinki sosai shiyasa."

Murmushi tayi tare daɗan satan kallonsa,  Idanunsa ɗaya ya kashe mata hakan yasa ta cusa kanta acikin cinyoyinta tana sakin wani smile,   agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa ya duba, time ɗin dazai koma office yakusa hakan yasa shi kamo hanunta, da sauri taɗago kanta ta dubeshi murmushi yayi mata tare da sake matsowa daf da ita, cikin wata irin murya me sanyi yace.    "I love you!!!" 

(((   "Fatymasardauna kina mana rowan Sooraj"    "Teemah sardauna bakya kyauta mana gaskiya bakya mana update da wuri"      "Please me yasa yau bakiyi Sooraj ba?"     "Haba teemah don Allah kina mana update akan lokaci"  "Gaskiya typing ɗin da kike mana yana kaɗan please ki ƙara mana yawan page"   Irin waƴannan ƙorafe ƙorafen kullum nake samu daga wajen wasunku, am really sorry  bani da wani buri daya wuce nafaranta muku amma kuma lokaci yanamin jinkirin hakan,  idan ta sonane kullum na baku update na Sooraj amma kuma hakan baya yiwuwa, please kunamin uzuri nima ba ason raina hakan ke faruwa ba,  idan nace zanna muku typing kullum to kaina zaiyita min ciwo ne nasan kuma bazakuso hakan ba don Allah kuɗau uzurina, nasan kuna sona kuma kuna ƙaunar novels ɗina, nima kuma inasonku sosae sosae 💞)))

        *Vote*
*and comment 😉*

             fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ !!!*

     *Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My life (Sardauna)*

               *Wattpad*
        @fatymasardauna

#romance

            *Chapter 29*

"I love you!!!"  ya faɗa slowly yana me murza

19 / 47